A Rubuce Take (K'addarata) page 53 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 53 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 53 Hausa Novel - Novels Elite

*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*

      (K'addarata)


Page 53         "Daga yau,duk sanda kike ke daya a  nan,ki kunna tv din falo,ki kamo saudi qur'an.....kinjini ko?" Ya furta yana kama kunnensa,saita gyada masa kai


"Good.....sannan,baki iya addu'a ba sanda mutum yaga abinda ya tsoratashi?" 


"Na iya" ta fada a sanyaye


"To daga yau ita zaki dinga ya,kada na sake ji ko ganin kina ihun nan......ki fahimta?" Nan ma kai ta gyada masa,ya jijjiga kai,shuru ya ratsa na second biyu


"Kin yini lafiya?"


"Ina wuni" ta maida masa da gaisuwa da muryarta dake dan rawa har yanzu


"lafiya lau" ya amsa mata yana miqewa


"Ga saqo can daga kano" fadin kano din da yayi ya sanyata warwarwwa ta farat daya,ya bita da kallo sanda yaga ta doshi kedar fuskarta na haske da murmushi,sai ua juya ya fice daga dakin,yanata juya al'amuranta a ransa,raino ne hajiya ta bashi,raino kuma me wuya da baisan sanda zai gamashi ba.


          Sanda ya isa sassan hafsat yayi mamakin ganinsa a tsaftace,zai iya cewa ya manta lokaci na qarshe da yaga komai a muhallinsa a sassan nata,baiyi dai magana ba,amma kuma hakan ya masa dadi, zuciyar sa kuma ta sauka,akaci sa'a a yau din ta danyi wankan dare,ta kuma qure adaka da daya daga cikin tsadaddun suturun da yake mata,don tana son ta sake amintar dashi,ta kums kore kowanne zargi daga ransa,uwa uba kuma akwai kudaden da takeson karba daga wajensa a daren.


*********To tsahon kwanaki ukun da sukayi a bauchin widad ita kewa hafsat din dukkan wasu aikace aikacen sassanta,kama daga wanke wanke shara da wankan yara da dyk wata lalurarsu,koda bata shigo sashen ba zata shigo da kanta ta fiddota,idan abbas yana gida yafi zama sashensa,takanntattara ta bishi can,bata fita sai idan yasa qafarsa yabar gidan shima.


        Baisan meke faruwa ba,tunda ya sani akwai alamun tsoronsa sosai tattare da yarinyar,bayason ya dinga matsa mata ko takura mata,ganin yadda taje sakewa walwalarta take qaruwa idan tana tare dasu mimi sai ya saki komai shima,wuni take hidimar sassan hafsat din,girki kawai hafsat din keyi,itama widad din taje tayi nata.


       Quruciya qarancin shekarunta da rashin wayo ya sanya bata dauki hakan a bakin komai ba, saidai wasu lokutan tana jin aikin kamar yayi mata yawa,amma bata fasa yi mata ba,don a ganinta gaba take da ita,sannan tana samun sassaucin mugun tsoron da hafsat din ta dasa mata a ranta,tsoron abbas din da koda yaushe take zayyana mata abu kaza babu kyau....abu kaza babu kyau,ki tsare mutuncinki,dukka wani halali ta haramta mata shi,tayi amfani da wayo da dabararta da shekaru data daranma widad din.


           Ranar lahadi da yammaci suka tattara suka bar bauchin,kamar wancan karon,wannan karonma wani abune ya tsaya mata a rai,ta zubawa motarsu idanu sanda take fita daga gidan,zuciyarta a mugun quntace,saidai taci alwashin tafiyar tasu babu abinda zata bari ya sauya,data koma cikin gidan kuma ta sake qarewa sashenta kallo taga yadda ya fara komawa hayyacinsa,sai taji inama widad din a kadunan take,ta tuna gobe fa itace zatayi dukkan hidimar da widad din ke mata,ga shirin makarantar mimi,ranta sai ya baci,haka ta wuni tana qunci tana kuma jibgar yaran,saboda kwanaki biyun bata saka hannu a hidimarsu,duk wata lalura tasu widad dince,wanka tsarkin kashi abinci da sauransu,su kansu yau din duk sai suka zama sukuku,kada ma mimi taji labari,minti daya biyu saita kira sunanta,saida hafsat din ta fara doke mata baki sannan ta samu salaama.


         Tun a mota widad in ta dinga bacci,baccin gajiyar data debo a kaduna na ayyukan wahalar hafsat,koda suka isa gida ma sai daya tasheta,ta murza idanunta ta buda motar ta fito a kasalance tayi sassansu.


          Sallar magariba da isha'i kawai tayi ta sake kifewa a dakinta,sanda ya shigo gidan tayi nisa a duniyar bacci,sai ya maida mata qofar dakin nata ya rufe kawai ya sanya ledar takeaway din a fridge don kada ya lalace,mamaki yana dan kamashi da irin baccin da takeyi,kamar wadda bata samun baccin kirki.


          Washegari da zai miqa ta makaranta ma kusan a makare suka fita,don sai daya shiga dakin ya tasheta sannan ta samu ta shirya a gurguje,don ko gyaran gidan bata samu yiba sai da aka taso daga makarantar,samuel ya aika ya daukota a motarsa ya ajeta gidan,tana shigowa suna cin karo da maami matar gidan,wadda yaranta duka maza ne,shi yasa ba wanda ke shigowa sashen


"Yaushe kuka dawo haka babu sanarwa?" Ta tambayi widad tana qare mata kallo cikin uniform din da suka bala'in karbarta


"Jiya da daddare ne,uncle yace na shigo na gaisheki ma daman idan an taso daga makaranta"


"Oh....makaranta kenan aka fara zuwa,aji nawa?" Ta sake tambayarta


"S.s one" kai ta gyada,lallai namiji,shan koko daukan rai,banda qalata irin tasa,itadai bataga abun daukarwa kai wannan dawainiyar ba,amma wataqila kyan yake rudarsa


"To Allah ya taimaka"


"Ameen,a dawo lafiya" ta fada tana yin gaba zuwa cikin gidan,ita kuma ta amsa tana shigewa motarta,idanuwanta akan widad din,kamar zata gayawa hafsat sai kuma ta share,don bataga abinda yarinyar tayi mata bama,kawai dai hali irin na mata,taya kishin da bai shafeka ba.


          Sallar azahar kawai tayi ta fara gyaran gidan,duk da muguwar gajiyar da tayi,ta tuna sanda take dawowa daga makaranta,ummu tasa an hada mata komai,saidai tayi wanka taci abinci tayi shirin islamiyya,take qwalla ta kawo a idanunta,taji kamar ta watsar amma ba zata iya zama a datti ba,tsahon rayuwarta ko kadan batasan dauda qazanta ko datti ba,ummun nada wata irin mugu muguwar tsafta,kowa ya shaida,hakanan duk matan gidansu babu qazama.


          Tana gama mopping taji ana saka key za'a buda qofar sashen,ta tsaya a dan tsorace tana kallon qofar,har ya kammala budewa ya tura ya shigo.


          A kanta idanuwansa suka sauka,yayin da kuma ta sauke ajiyar zuciya tana jin tsoronta na zagwanyewa,baisan yadda akayi murmushi ya subuce masa ba,don ya gane tsoron nata taji da taba qofar da yayi,itama sai murmushin ya kubcewa fuskarta,ta kuma ji yar kunya ta kamata,tayi qas da kanta tana tambayar kanta me yasa ta fiya tsoro haka


"Matsoraciya kawai" ya fada a hankali,murmushi ta danyi sannan ta turo qaramin bakinta gaba a shagwabe,kwatankwacin irin yadda takewa ummu,sai ya samu kansa da binta da kallo,batace komai ba shima haka,ya zauna hannun kujerar falon yana goye da hannayensa a qirji,lumsassun idanunsa nakan dan qaramin bakinta


"Me kika ci?" 


"Ni?" Ta tambayeshi tana fidda idanu waje hadi sa taba lips dinta kamar mai tsoron wani abun, murmushi ya sake subuce masa


"Eh me kikaci baki ajjiyemin ba?" Fuskarta ta narke a shagwabe


"Nifa banci komai ba uncle,yunwa ma nakeji" ta fada tana shafa cikinta,shafaffen cikin nata yabi da kallo, idanuwansa suka kai har kan qugunta daya fito sosai ta cikin skeet din material na jikinta,ya janye idanunsa yana sauke numfashi,hirar da abokan aikinsa moses jackson da  andrew sukayi yau ta fado masa a rai,har a lokacin suka cika shi suka kuma dameshi ya nemi tashi ya basu guri,sai suka dinga masa dariya suna tsokanarsa,ya sansu sarai,su din mayun mata ne,daya daga cikin abinda yasa ko kusa baya bari sukai ga ganin iyalinsa


"Ina zuwa,bari na fito sai naga yau me za'a koya" sosai taji dadi,don har hakan ya bayyana saman fuskarta,tana son taga ta iya kalolin girke girke,saboda zumudi a falon ta zauna tayi jiransa,ba jimawa sai gashi ya fito.


           Sauri tayi ta dauke kanta sanda ya fito din,boxer ne a jikinsa sai wata armless shirt farare,kayan sun masu kyau sosai,saidai sun fidda qirar jikinsa.


        Har ya kusa isa kitchen din yaji bata biyoshi ba,sai ya waiwayo yana dubanta,tayi hanzarin sake dauke kanta gefe tana turo baki,shi wasu abubuwan idan yayi kamar baijin kunya wai?.


"Ko baki shirya ba?" Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa da suka rusuna yau din qwarai,kai ta girgiza ta kuma amsa masa ba tare data kalleshi ba


"Na shirya.....amma.....amma" sai kuma ta kasa qarasawa


"Amma me?" 


"Ka saka kaya don Allah mana" murmushin da bai shirya bane ya qwace masa,ya kalli jikinsa sannan ya dawo da dubansa kanta


"Wannan meye a jikina idan ba kaya ba?"


"Amma uncle,kalli gafarka kalli hannunka fa,ummu idan su yaa ma'aruf suka fito haka fada take musu fa" ta fada a shagwaben nan nata kamar zata saki kuka.


          Lallausan murmushi ya subucewa fuskarsa,for now yana ganin ya kamata ace ta fara sanin bambancin mutanen gidansu dashi,wannan yasa ya fara takowa a hankali cikin lallausan carfet din falon,bata lura dashi ba sai ganin mutum tayi dab da ita.


         Gabanta ya fadi,sai taja baya kadan,bai damu ba ya zauna a gabanta saitin qafafunta yana kallon idanunta dake cike da quruciya,ta kuwa bata fuska sosai,gabanta yanata faduwa


"Akwai bambanci tsakanina dasu yaaya ma'aruf da sauran duk 'yan gidanku,ni mijinki ne,na biya sadaki an daura min aure,ni dake ya halatta muga komai na junanmu,mu taba juna,mu kwana guri daya....muci abinci tare,na ganki a duk yanayin da kike....koda tsirara kuwa....." 


"La ilaaaaa" ta fada da qarfi hade da wani irin kuka,idanunta a kansa, tsoronsa yana shigarta,ta kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar kamar mai shirin zurawa da gudu.


        Wata dariya ta bashi,wadda a wannan karon ya kasa riqeta sai daya dara,hannunsa saman bakinsa yana qoqarin controlling na dariyarsa,he don't know what to do next kuma.....he don't know how to explain her, tabbas goyon kakace ta gaske,kuma symptoms ne na cewa ta samu tarbiyyar qwarai.


"Shikenan,is okay,ya isa,bazan kalli jikinki ba,amma sorry for saying that.... shikenan?" Da qyar ya shawo kanta suka shiga kitchen din,yana hada girkin yana nuna mata kamar yadda suka saba,saidai sam taqi sakewa dashi,yana matsowa take komawa baya,gashi shi ba gwanin hira ba,biyu ta hadu,da haka dai ya dinga nuna mata har suka kammala.


          Ita ta zuba abincin a warmers takai dining,ta gyara kitchen din,ko kafin  ta fito har yayi alwala ya leqo yace mata ya wuce masallaci,don haka itama tana gamawa alawar tayi,tayi sallah sai kuma ta dawo falon ta zauna, maimakon taci abincin amma sai taji ba zata iya ci ba har sai ya dawo,hakanan ta zauna zaman jiransa,wayarta na hannunta tana game tana dakon shigowarsa.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Aslm Allah ya kara bassira.

    ReplyDelete
  2. Widad din mu yaushe zatayi wayoo?

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post