*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 46
Space ya bata,ya zauna daga nesa yana kallonta har sai data gamsu don kanta ta tsagaita kukan,don ya fuskanci kukan da take harda na sakalci ma,sanann ya miqe yana duba dakin ko zaiga abincin da yace a kawo mata amma baiga alamunsa ba,waiwayawa yayi yana dubanta
"Ina abincin da nace a kawo miki?" Baki ta tabe sosai irin na yaran da suka gwanance wajen shagwaba
"Naji ana knocking,inajin tsoro ne bazan iya fita ba" dan qaramin bakinta me dauke da jajayen lips yabi da kallo,wannan da alama ba abinda ta sani sai sangarta da sakalci,ya janye idanuwansa yana laluba aljihunsa ya fidda wayarsa,a nan ya samu tarin miscall na wanda ya aika din,yana kiransa kafin yace komai ya gaya masa yayita bugu ba'a bude ba
"Ba matsala,am back,zaka iya kawowa" ya fada yana nufar qofar dakin da zummar ficewa,saidai tun bai sanya qafarsa a falo ba ta miqe ta rufa masa baya.
Tsayawa yayi bayan ya zame wayar daga kunnensa sannan ya waiwayo yana kallonta,saita dauke kanta gefe tana turo baki gaba gami da tabeshi
"Ina zaki?"
"Ni binka zanyi,Allah ba zan zauna a nan ba" saiga hawaye yana biyo bayan maganarta
"Saqo zan karbo"
"Zan bika" ta sake fada wasu hawayen na sake zubowa
"Yanzu zan dawo,just a compound din gidan nan ne" wannan karon maqale kafada tayi saboda kuka ya riga da ya subuce mata
"Oh god" ya fada yana dan lumshe idanunsa hadi da budesu duka lokaci guda,kafin ya sake cewa wani abu anyi knocking,sai kawai yayi gaba,ta kuwa take masa baya yana dauke qafarsa tana saka tata.
Takeaway na abincin ya karba ya maida qofar ya kulle,daya juyo sai kuma tayi tsaye tana jin banbarakwai,ya tako taja baya hadi da yin gefe ta bashi hanya,ya isa tsakiyar falon
"Dauko plate a kitchen da spoon" ya fada yana ajjiye ledar,hadi da zama saman kujerar sannan ya fara qoqarin cire agogon hannunsa.
Jin shuru bata amsa ba,bata kuma motsa ba ya sanyashi dago kansa,tana tsaye ta marairaice fuska kawai tana kallonsa
"Bakiji bane?" Ya tambayeta da kaurin murya
"Tsoro...."
"Subhanallah" ya furta a hankali,sai kawai ya miqe ba tare da yace komai ba,nan ma batayi qasa a gwiwa ba ta rufa masa baya,tana tsaye ya dauko plate din,ya hado da spoons da bottle water da drink na kwali guda daya sannan suka rankayo suka fito.
Wannan karon a qas ya zauna sosai,ya bude ledojin ya hada komai da komai kowanne plates d'ai d'ai ya tura mata hade da ruwan da kuma lemon,ya sanyawa nashi palate din spoon ya fara diban abincin yana ci bayan yayi bismillah,hannunsa daya riqe da wayarsa yana dannawa.
Shuru tayi tana kallon plate din nata,tun asali ita din bata saba cin abinci ita kadai ba,tun tasowarta,saboda ta taso mutum ce mara son cin abinci,wannan yasa kowanne lokaci da ummu sukeci,suna ci tana hilatarta har sai taci me yawa,idan kuwa tana azumine ko kuma tana makaranta taci kafin ta dawo wanda zaiyi wuya ma ta rigata ci din,saita hada mata da wani cikinsu Aafiya,ko ta tafi sassan anty madina taci cikin jama'a,shine fa take ci da dan dama,ko zuwanta bauchi kullum da latifa sukeci,to a yanzun saita kasa tabuka komai,har yayi nisa da cin nasa abincin.
Bai kula ba sai da yayi nisa sosai,ya daga idanunsa ya kalleta,itama shi take kallo,ta narke fuska kamar wadda kukan da tayi bai isheta ba tana neman qari ne
"Dauki kici" ya fadi yana mata nuni da abincin da ido,saita girgiza kai
"Na qoshi" mamaki ya kamashi,baici ace bata jin yunwa ba,yasan tun sanda suka fito rabonta da abinci,saiya rasa yadda zai mata taci.abincin,don daga qarshe ma baya taja ta rungume qafafunta kamar wata marainiya.
Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye nasa plate din,shikam ya gamu da gamonsa,da alama rainon zaiyi da gaske,suraj da suke chart dashi a lokacin ya turawa gajeran saqon tambaya
_"If you want a child to eat and he refuses, what will you do for him?,ina buqatar taimakon,its urgent please"_. Sai daya tura masa sticker din dariya sannan ya amsa masa
_"yar rainon taka hala?,ka lallabata,malam ka kuma koyi magana,wannan ba hafsat bace,ita din ba zata gane shuru ba,be a child like her for a while,sannan ne komai zai daidaita"_
_"thanks,i will tray_" ya amsa masa sannan ya kashe data dinsa ya ajjiye wayar
"Oh God, give me courage" ya fada can qasan ransa yana kallonta
"Let's share the food,come closer" ya fada yans miqa hannu yaja plate din,makarantar da tayi mai tsada ce sosai,don haka ko a iya js data tsaya tana jin turanci fes tana kuma iya mayarwa,don haka taji sarai abinda ya fada,to amma fa ita tsironsa takeji,ta sani tun a gida cin abinci da maza ba abu bane me kyau,uwa uba hudubarta tana nan a kanta fes bata bace ba,ya zataci abinci da wani?,to amma kuma yunwa takeji,idan kuma bai tayata ci din ba tabbas tana iya kwana da yunwa
"Uhnnn,bismillah" ya sake fada yana juya spoon dinsa a ciki,jiki a mace,a kuma mugun darare ta matso,nesa da plate din ta zauna,saidai tana kai hannu tana diban abincin,tana yi kuma tana satar kallonsa,amma sai taga sam shi hankalinsa baya wajen,wannan yasa ta dan sake sakewa ta soma cin abincin a nutse.
Duk da ya qoshi hannunsa kadai ya zame amma bai tashi daga wajen ba,har sai da yaga ta cire nata hannun,takai goran ruwan mitsitsin bakinta ta fara sha,har cikin ransa yaji ya sauke nauyi,zuciyarsa tayi wasai,sanda ya dawo ya samu bataci abincin ba ji yayi kamar yaci amanar hajiya,ya kasa sauke nauyin amanar daya karba ya kuma dauka tun ba'a kai ga kwana ba.
Zaman kurame sukayi a falon,shi yana aikace aikacen sa a waya,ita kuwa tana takure gefe daya duk da tv tana aikinta,saidai ita hankalinta ya kasu kashi biyu,duk wani motsi da taji saita waiwaya da sauri taga meye,shi kuwa ya zauna ne don ya debe mata kewa ya kuma rage mata dare,duk kuwa da yanason tashi,yana nan a zaune sai kiran hafsat ya shigo wayarsa,abinda ya bashi mamaki kenan,ya kuma yi hanzarin dagawa yana tunanin ko wani abunne ya faru?,qila ita ko wani cikin yaranne babu lafiya,saboda sam ba dabi'arta bace ta kirashi don yayi tafiya,komai nisan zangon da zaiyi,koda da nufin jin yadda ya sauka,saidai idan shi din ya sauka ya kirata ya shaida mata ya sauka lafiya,ta kuma bashi yaransa suyi magana,indai kaga kiranta to wani abunne ya faru,ko kuma wata buqatar ce ta taso.
A tsanake ya daga wayar yana mata sallama da lallausar muryarsa data saukar mata da wani zazzafan kishinsa,zuciyarta nata ayyano mata kasantuwarsu da widad a dai dai wannan lokacin,duk kuwa da tana da wani yaqini da kuma qwarin gwiwa abinda ta dasa zaiyi tasiri sosai,saboda saran da tayi akan gaba.
Muryar data amsa masa sallamar da ita ta sake sanyashi a mamaki,ya manta rabon da yaji wannan tune din daga gareta,tun wani zamani can baya,suka gama gaisawa yana jiran yaji ta kawo complain ko wani damuwa sai baiji wannan ba,sai hira da taketa qoqarin jansa dashi.
To anan dai ya biye mata,don shima yana da buqatar irin wannan kulawar,yana yunwar samun kulawa irin wanann amma ta zame masa jidali a wajen hafsat din,ya kishingida kadan yana sauraren hirar da take masa,duk kuwa da cewa qarfin hali kawai takeyi,daga can harta gundura,bawai don ta gaji dajin muryarsa ba,muryarsa na daya daga cikin abubuwan da bata taba jin ta gaji dasu ba.
"Wai ina qanwata ne?" Ta jefa masa tambayar fa tun dazun so samu ta zama ta farko,to amma he is very smart,zai iya sansano wani abu,shi yasa ta kaita tsakiyar zancansu
"Bata mu gaisa mana,nayi mata ya gajiyar hanya?,ina fata ba zaka sake tara mata wata gajiyar ba" maida idanunsa yayi kan fuskarta da a yanzun ta bada hankalinta ga tv,saboda wani cartoon da suka juya haskawa,hasken tvn ya haske fara tas din fatarta da kyau,haka kawai zuciya ta d'arsa masa abinda hafsat din ta fada akan widad,ya danyi imagination akai na wasu sakanni,sai yayi sauri ya ture daga ransa yana fadin
"She's too young"
"Hello" muryar hafsat dake tawa ta ratsa ta tunaninsa,saboda raya mata da zuciyarta tayi tana jikinsa ne yana debe kewa da ita
"Ina jinki"
"Tana ina?"
"Bata kusa.....sai wani lokacin" haka kawai taji zuciyar ta bata yadda da abinda ya fada ba,don haka ta bishi da
"Okay" taja qaramar keypad dinta ta soma trying number widad din,amma aka sanar mata a kashe wayar take,take tajin hankalinta ya tashi,abbas baya son barin waya a kunne a sanda suka kebe,haka yake,koda tata wayar karba yake ya kashe,yakance
"I need a rest,ina buqatar kadaicewa da iyalina" bai fiya barinta kunna waya ba idan yana gida weekend a sanda suna tashen buga soyayyarsu.
Haka kawai taji hirar duka ta fice mata a kai,don haka ta nema suyi sallama,bai matsa ba,don yaga qoqarinta,abun shekara da shekaru,shi yayi mata sallamar,yama rigata kashe wayar ya ajjiye,abinda ya sake saka mata zargi a ranta kenan,tayi jifa da wayar gefanta,ta koma da baya yaraf ta kwanta tana duban ceiling,dole ta kira yarinyar taji.me ya faru a yau,dole ta kirata ta dora mata bita.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥