A Rubuce Take (K'addarata) page 49 Hausa Novel - Novels Elite
Health College

A Rubuce Take (K'addarata) page 49 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 49 Hausa Novel - Novels Elite

*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*

      (K'addarata)


Page 49



       Awanni kusan hudu kenan tana abu guda,baya ga kitchen din data yiwa kaca kaca kota ina,kamar wadda ke girkin mutum ashirin,sannan daga bisani ta samu ta kammala tuwon shinkafa miyar kubewa iya yadda taga latifa tana yi,ta zuba cikin sabbin warmer masu kyau da aka hado cikin siyayyar cefanen da aka kawosu jiya.


          Dafe bayanta tayi bayan ta kammala gyare kitchen din


"Shi tuwo dama haka yake da wahala?"ta fada tana yatsina fuska,duk da can qasan ranta farinciki ne fal,wai yau itace da yin girki cikin kitchen dinta,ba kwaba ba hantara babu bakiyi dai dai ba,ta juya ta soma diban warmers din takai saman dining,ta jeresu da  kyau,tana kallonsu tana murmushi,har cikin ranta dadi take ji idan ta tuna wai yau ance tayi girki.


           Dakinta ta koma tayi wanka,ta shafa powder a kyakkyawan fuskarta mai santsi da sheqi dauke da tambari na quruciya,dubai abaya wine color da tasha adon duwatsu masu walwali ta fidda  ta sanya,ta daura dankwalin saman kanta,ta kuma shafa turarukanta kamar yadda ya taba gwada mata yadda ake sanyasu,tun daga ranar kuwa ta dauke tsaf,yadda ya kwatanta matan haka take sakawa,ita kanta sai taji tafi jin dadinsu.


            Sosai abayan ta haska jar fatarta,kamanninta suka fito sak na ainihin tushen yankin data fito,ta koma gefan gadonta bayan ta dauko wayarta dake saman madubi,ta bude ta shiga wata game da taketa daukan hankalinta ta fara bugawa cikin qwarewa.


           Hankalinta yayi nisa sosai a game din,har bataji qarar motarsa zuwa shigowarsa cikin gidan ya kuma tura qofar dakinta ba,sai ya tsaya riqe da handle din qofar dakin,zai iya lissafa adadin shigowarsa dakin,idanunsa saman fuskarta,tattausan siraran labbanta sunata qyallin lips balm,tana ta juyi saman gadon,duk sanda taci game din sai tayi dan tsalle kadan na murna sannan taci gaba.


         Idanunsa ya dauke sannan yayi gyaran murya kadan ya hada da sallama,daga idonta tayi daga kan wayar zuwa kansa,saita aje wayar gefanta tana masa sannu da zuwa,sannan a dabarance tana laluba maballan gaban rigarta taji sun rufu da kyau?,ta kuma tsareshi sosai da ido taga ko.yana kallonta?.


          Sarai yaga abinda takeyi,amma sai ya kauda kai ba tare da yakai idanuwansa kan qirjin nata da yake ganin basu da maraba da qirgar dangi a wajensa ba


"Tare da baqo nake,ki kawo abincin" kai ta gyada masa,ya saki handle din qofar ya juya zuwa falon,yana duba wayarsa daketa ringing.


          Ba kowa ke kiransa ba sai hafsat,tunda satin ya wuce taga baizo weekend ba hankalinta ya gaza kwanciya,gaba daya zuciyarta cike take da wasi wasi da kuma fargaba,duk kuwa da bayanin da yayi mata na cushewar aiki da ya samu a kaduna fiye da dukka garuruwan da yake zuwa aiki,amma zuciyarta ta kasa aminta da hakan,duk inda yake baya wuce satin nan dai baizo bauchi ba ko don hajiyarsa,sai wannan karon?,sai wannan lokacin daya tafi da wannan sadakar yallan?,anya ba holewarsa yakeyi ba?,anya bai samu wani abu bane daga gareta?.


          A kullum kwanan duniya kira uku zuwa hudu ne sai ta yiwa widad shi,ta tambayi ya suka kwana?,ya suka tashi?,ya suka yini?,ya dawo gida kuwa?,me ya faru a tsakaninsu?.


           Sam widad din bata boye mata komai,rashin wayo da qarancin shekaru yasa bata dsuki wannan din a mazaunin komai ba,face ma qauna soyayya da kulawar da mommy hafsa din ke nuna mata,wannan yasa ta sake ganin kimarta,ta kuma sake ganin girmanta,hakanan taji tana qaunarta,shi yasa dukkan abinda zata umarceta dashi take aiwatarwa kanta tsaye,wannan dalilin ne kuma yasa tayi riqo da hudubarta yadda ya kamata,don ya zame mata kamar tishi ne akan tarbiyyar ummu,sai faduwa tazo dai dai da zama,tana nisantarsa iyakar iyawarta,tana kuma qauracewa duk wani abu da tasan mommy hafsa ta gargadi akai.


        Ta sani ta kuma fuskanta,sam qarya bata cikin dabi'ar widad,da gaske haka take tun a gida,duk da samun wannan tabbacin,hakan bai sanya zuciyarta da ruhinta sun aminta sun kuma kubuta daga zargin abbas ba, don haka taketa kiransa,tanason taji yaushe zai zo din.


           Ajiyar zuciya ya sauke,yau inda ace buqata ce da hafsat din dole.ya ajjiye dukkan abinda yakeyi yaje ya sauke mata ita,to amma yafi kowa sanin wacece ita,tana iya share wata guda koma fiye bata buqaci komai daga gareshi ba,saidai shi din ya nema,a yanzun ma.ya tabbatar ba wani qwaqwaqwaran dalili ne da ita ba na kafewar ya taho din,ya bata dukkan wata dama da zata fadi uzurinta amma amsa daya ce


"Kawai son ganinka nakeyi"


"Kiyi haquri,indai ba babbar buqata ce dake ba......akwai aikin da nakeyi a nan din,banason kuma na matsa daga kaduna sai na kammalashi,aikin yana buqatar sirri kula da kuma takatsantsan" amsar daya bawa hafsan kenan,ta furzar da iska dgaa bakinta,zuciyarta na raya mata ta shirya ta tafi Kaduna kawai,to amma sanin girman laifin data aikata masa wanda yayi silar haramata mata Kaduna kwata kwata yasa ta sake jaddadawa kanta wannan ba mafita bace,zata bi ta hanyar da tasan dole yazo gida koda baiso ba.


             Sai data nema yalwataccen mayafi ta yane jikinta dashi sannan ta wuce falon,idanun abbas din a kanta,hakanan yaji abinda tayin ta burgeshi,bai gaya mata ta yafa din ba,amma tasan ya kamata,ta tsugunna har qasa ta gaida ameen abokinsa,sannan ta wuce ta soma dauko warmers din tana jera musu bayan ta shimfida table mat a qasan.


         Ta tsara komai yadda ya dace,har cikin ransa yaji abinda tayi ya burgeshi,ruwan sha dana wanke hannu duka akwai a wajen,abinda hafsat bata taba yi ba,dai dai da tissue daya dace ko yaushe a sameta saman dining sai ya nema,ita kuwa ta koyo hakanne daga wajen ummu,haka taga tana yiwa alhaji.


          Har ta juya zata wuce daki,sai taga ana hasko wani cartoon da take mugun so,fasa shiga dakin tayi,ta dawo ta zauna fuskarta cike da fara'a,kadan abbas ya waiwaya ya kalleta,kamar zaiyi magana saiya fasa,ganin irin excitement din dake kan fuskarta na ganin cartoon din,ya maida kansa ga warmer din,ya bude ya sanya hannunsa ya dauko malmalar tuwon farko.


          Tun baikai ga budeta ba ya fahimci an samu babbar matsala,duk da haka bai fasa ba,ya wareta yana sakinta saman plate,take kuwa tuwon ya dare biyu,suka hada ido da ameen din,sai abbas din ya basar,ya bude warmer din miyar,koriyar kubewa shar,wadda aka qarantawa kayan hadi ta bayyana,bama kayan hadi ba,harda kayan dahuwa,wake yayi tsuru tsuru yaja gefe,ga danyan manja a sama ya hade rai.


        Serving spoon yasa ya kwaso musu ita da qyar ya zuba akan plate din,ya maidata ya rufe ya saka musu cokula yana cewa da ameen


"Bismillah" dukka dauriyarsa amee din ya gayyato,ya matso ya dauki cokalin,suka sanya lomar farko a tare da abbas din.


         Spoon din ya ajjiye sannan ya miqe yana duban abbas


"Kasan nayi mantuwa a office,zan koma,daga can gida zan wuce" yadda ameen din keta rattaba bayani ya bawa abbas dariya,amma sai.ya qushe abarsa,gulma ce da ganin qarshen mutum tasa yace zaya biyoshi


"Okay....sai na fito" ya amsa masa,sai ameen din ya juya yana cewa


"Amarya,ni zan koma ko,ina godiya sosai,sauri nake.ban samu naci abincin ba,amma...... next time"


"Ka gaida gida" ta furta a sanyaye sanda ta kalli abincin taga kamar babu abinda ya dandana,idanunta nakan plate din har ya fice a gidan.


        Dukkan alamu sun nuna.girkin nan nauyi dadi ko ma'ana ba sam,jikinta a sanyaye,ta tabbatar shima ajiye mata abincinta zaiyi,ba iya ci zaiyi ba,musamman data hangi yadda tuwon ya baje abinsa,ya koma kamar shinkafar da bata samu wadatacciyar dahuwa ba.


         A mamakance ta maida dubanta ga fuskarsa,sai kai abincin bakinsa yake,kamar babu wani abu da baiyi dai dai ba a girkin,karo na uku suka sake hada idanu tana masa kallon mamaki


"Zonan" ya fada a tausashe yana yafitota da hannunsa,saita aje filon data dora saman cinyarta,ta miqe a sanyaye ta nufeshi.


           Idanunta na tara ruwan hawaye.


        Gabansa ya nuna mata,ta zauna a hankali tana sake ja baya kadan,qaramin murmushi ya subuce masa yana kallon qwayar idanunta,sannan ya tsame hannunsa daga abincin bayan yaci wani adadi mai yawa


"Tuwo yayi fa dadi,gyaran kadanne" da farko shuru tayi tana dubansa,fuskarta dauke da alamun mamaki,daga baya kuma sai murmushi ya subuce mata,cikin wani irin zumudi da sakewar da bata tabayi dashi ba


"Allah?,ashe dai na iya girki" ta fada cikin murna,kai ya gyada mata yana kallonta


"Kin iya,amma na fiki iyawa ai" ido ta fidda waje tana dubansa


"Namiji dama ya iya girki?" Ya jinjina mata kai qaramin murmushi na fita daga fuskarsa


"Iyawa kai,ki shirya daga gobe zan fara koya miki irin nawa"  sosai taji dadi da fadin hakan da yayi,ita din tanason taga ta iya girki irin na anty madina da anty deena.


         Cikin ransa yakejin dole haka zai samu lokaci cikin lokutansa ya ware ya koya mata wasu abubuwan kafin ya laluba makarantar koyon girki ya sakata,at least koda girkin ta iya zai rage wani abun.


          Washegari da safe shi yayi mata knocking ta fito,ta rusuna ta gaidashi tana sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando da wando,tana biye dashi suka isa kitchen,ya sama mata kujera yace


"Zauna a nan ki gani" murmushi ta sake tana kallonsa,sanye da wani wando na sojoji da farar shirt,ta zauna din sannan ta jefa masa tambayar dake cinta tun daxu


"Wai kai police ne kuma soja ne?" Sai daya juyo ya kalleta da manyan idanunsa,sai tayi tsuru tsuru kuma tana dafe bakinta,tana jin kamar tambayar tayi yawa,kai ya girgiza yana sakin fuskarsa


"Ni police ne me kama masu laifi" saita jinjina kai tana murmushi kawai.


           Cikin kitchen din taci gaba da zama,kome zaiyi sai ya nuna mata,saidai tana daga gefe tana d'ari d'ari dashi,bata bari tazarar dake tsakaninsu tayi kusa,ya lura amma dariya kawai take bashi,daga baya bayan ya gama hada komai,ya bata yanke yanke yace tayi masa tana daga zaune.


           Cikin awa daya da rabi suka hada breakfast mai kyau tare,ta dinga murna tana jin dadi,shi kam saidai ya bita da ido,bayan sun kammala yabar mata kitchen din ta gyara,shi kuma ya wuce dakinsa yin wanka,ta gyara ta kwaso komai ta kawo falon,saita zube saman kujera tana maida numfashi,don tadan gaji,sai data huta sannan ta wuce itama dakin don yin wankan.


         A ranar ma ya samu sauqin aiki,don haka da rana ya dawo gida,ganinsa a gida da rana ba qaramin dadi yayi mata,ashe mutum rahama ne,cikin zuciyarta ta dinga jin wani dadi,duk da babu abinda ke hadasu daga sannu da zuwa zai wuce dakinsa ne,bayan ya fito suka sake shiga kitchen tare,ta dinga murna da zumudin son ganin me zasu dafa,abinci sassauqa sukayi,itadai tana ta mamakin yadda namiji ya iya girki haka,bayan sun gama kowa yaci nashi ya sake shiryawa ya koma.


        To da daddare ma haka,sabon girki sukayi,duk abinda yakeyi idanunta na kanshi tana biye,haka ce taci gaba da kasancewa,cikin satin gaba daya aiki biyu ya dinga yi,yayi na office ya dawo gida ya koya mata abinda ya sawwaqa,wani lokaci idan bai samu dawowa da rana ba,to da daddare akeyi.


          Cikin satin sai gashi an samu ci gaba,ta riqe wasu abubuwan,da yake widad din badai kai ba,kuma tana da qaunar yin girkin,sai gashi a satin ta iya hada breakfast,hakanan abincin duk daya koya mata ta fara gwadawa,yana kuma yi,saidai hannun baikai ga fadawa sosai ba.


             Ranar wata alhamis bayan sun gama girkin dare ya fiddo foam yace ta matso ta bashi bayananta zai cike,foam ne na wata makarantar secondry ta 'yammata daya samar mata zata ci gaba da zuwa,tsananin murna yasa ta fada jikinsa ta qanqameshi tana godiya,sai kuma ta sakeshi da sauri taja baya,jikinta nayin wani irin sanyi,kada fa mommy ta gane ta rungumeshi,tayi tsuru tsuru,har sai daya fahimta,ya dade da fahimtar wannan,koda a kitchen da suke ayyuka tare duk abinda zai kawo haduwarsu waje guda tana daga baya baya,ko abu zai bata sai ya ajjiye take dauka,hakanan suna gama komai take qulewa daki ta kulle abinta,shikam dariya take bashi,kamar yanzun,baisan me take tunani ba,shikam indai abinda take tunani ne idan yayishi yace yayi me?,saiya girgiza kai kawai yana boye murmushinsa cikin fuskarsa ya fara cike mata foam din,bayan ya gama ya miqa mata yana cewa


"Idan zan fita gobe zan karba na fita dashi,and....ki shirya jibi zamu je bauchi" ta karba foam din jikinta a mace,sai taji inama ace kano yace mata zasuje?, tabbas da ranar ba zata iya bacci ba.


*Arewabooks: Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63



*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post