Abban Sojoji (Takun Karshe) hausa novels complete - Novels Elite

Abban Sojoji (Takun Karshe) hausa novels complete - Novels Elite

Abban Sojoji (Takun Karshe) hausa novels complete - Novels Elite

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

Zagayeta su kayi gaba ɗayansu,su jahad na ambatar sunanta,fawan ne ya ɗauko masu ruwa a fridge ya dawo ya miƙa ma uncle ɗinsu,kar6a yayi tare da buɗe murfin ya ɗebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskarta,nan take ta farka tana faman yin atishawa,Alhamdulillah suka shiga faɗi suna kallonta,yunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido,

   Muryarta na rawa tace"jaj..jahad hos...sana...ku ne?ko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba?

  Ba ƙaramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane su,atare suka faɗa jikinta suka rungume juna suna kuka,

  Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaɗae ba ma fuskar kowannansu na ɗauke da murmushi,musamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka hajiya azeemarsu har cewa take yi"yanzu nan waɗannan ƴan ukun duka namu ne?ƴa'ƴan mu ne?Allah abun godiya,yau dole in yi nafilar dare don miƙa godiyata ga Allah S.W.A daya nuna mun ƴa'ƴan abusufyan ɗinmu da ranmu kuma da lafiyarmu,Ashe dae da rabon yara suga danginsu,bayin Allah sun sha wahalar rayuwa,amma bakomai har yanzu lokaci bai ƙure mana ba,zamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarku,Zamu baku duk wani jin daɗi na duniya da kuka rasa,zamu gatanta ku,sai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani ƙunci da kuka ta6a fuskanta arayuwarku,waɗanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sunji dama ba'a halicce su cikin duniyar nan ba,


Abbansu junaid ya kar6e da cewa"Ae daga rana irin ta yau su fara ƙirgen kwanakin mutuwarsu,saboda ƙarshen su yazo,sun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEIN!Wallahi thumma tallahi ɗaya daga cikinsu bazai sha ba!' ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar,

   Abbas yace"Abba ina ganin yakamata yaran nan suje su kwanta dare yayi sosai,suna buƙatar hutu,in yaso koma menene gobe zamu ida tattauna akai,'

   Jinjina kai Abbansu yayi tare da mayar da idanunshi kansu sehrish dake manne da juna suna kuka,

   Gyaran murya ya ɗan yi masu,atare suka ɗago suna kallonshi da idanunsu dake zubar da hawaye,

  "Kuyi kuka yara bazan hanaku ba,dole kuyi kuka domin kuwa an cuci rayuwarku,an zalunce ku,an ƙuntata maku,an rabaku da mahaifinku na asali kuma an rabaku da danginku,duk akan laifin da baku kuka aikata ba,saboda son zuciya irin na mutanan nan su rasa akan wa zasu ɗauki fansar su sae akan waɗannan bayin Allahn....  'Shiru ya ɗanyi yana faman sauke ajiyar zuciya,

  abusufyan na zuƙunne akusa dasu ya sunnar da kanshi ƙasa,hakanan ya dinga jin kunyar yaran yana ji aranshi tamkar duk shi ne silar jefa su cikin halin da suka shiga,

  Su fawan kuwa dasu twins irfan jabeer da sauransu duk suna atsaye kowannansu jikinshi asanyaye kamar waɗanda aka zare ma lakka,lokaci guda sukaji tsananin Son yaran ya kamasu,

Domin saukewa  dannan Download now da ke kasa. Dan Allah kuyi comment, share sannan kuyi following din blog namu.

DOWNLOAD NOW

15 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

 1. Gdy muke sis nidai a page 71 natsaya na kasa samun cigaba bansan yazanyi ba wlh

  ReplyDelete
  Replies
  1. Ki bude wanna har karshe zaki sami in sha Allah

   Delete
 2. Gky bana ganin posting dinshi idan anyi

  ReplyDelete
 3. Nidae takun karshe nake nema

  ReplyDelete
  Replies
  1. Natsaya dadai inda aka dauramuso sure cigaba

   Delete
 4. Nidai daga 64 na tsaya bana ganin sauran saidai takun karshe Naga ana Sawa shikuma bana ganewa

  ReplyDelete
 5. Ni dai Banga book 3 ba

  ReplyDelete
 6. Dan Allah ni ina daidai inda za'ayi auren su husana da jahad ne

  ReplyDelete
  Replies
  1. Ki yi downloading wannan zaki sami har karshe

   Delete
 7. Dan allah cigaban takun karshe daga 81

  ReplyDelete
 8. Na tsaya agurin da tayima babban yaya bye bye

  ReplyDelete
 9. I love Rafayet with all my heart

  ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post