Ki Kulani Hausa Novel page 1 by Mss. Xoxo


Health College

Ki Kulani Hausa Novel page 1 by Mss. Xoxo

 

Ki Kulani Hausa Novel page 1 by Mss. Xoxo

K I   K U L A  N I

(MALLAKIN ZUCIYA)💕

N A N A  H A F S A T

       MSS XOXO

_Wannan littafin kirkirarre ne, Wasu sunayen ciki dama garuruwa da wasu abubuwan na ciki kirkirarru ne. Don haka ban yadda wani/wata su yi amfani da wannan littafin ba. Batare da masaniyata ba. Sannan idan labarin yayi shige da rayuwar wani/wata... To ba da sani ba ne. Don haka ayi hakuri. Akasi aka samu. Ban yarda wani/wata su canza mun littafi ko daukar wani bangare daga cikin sa batare da izini na ba. Ha ka ma ban amince a dau mun littafi a yadashi a wata kafaba (YouTube da sauran kafafe) Ba tare da an biyo ta kai na ba. A kiyaye...!! Wannan littafin na kudi ne akan nera 400 pages har zuwa kammaluwar su in shaa Allah. Hakama baki dayan pages din books din na wannan tafiyar na zafafa ba documents ba suna kan nera 1,200.... 🙏💕_

_بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ_

_Da sunan Allah mai rahama, Mai jin kai… Mamallakin kowa da komai!!_


_F R E E - P A G E :001_

______



*LT 'O' AVENUE.....*


  Kallon su baki daya kawai ta ke .. Daya bayan daya. Dukkanin fuskokin su na tariyo ma ta baya. Ta sauke katuwar bahaguwar ajiyar zuciya kana ta tallabo kumatun ta da hannun ta daya..


A tare suka shiga tambayar ba'asin shigar ta yanayin damuwa. Cikin dimuwa da son sanin abunda ya jefa ta cikin yanayin da ta shiga cikin kankanin lokaci...


"Hajiya.... Ko kunnen na ki ne? Kin saka abun kara jin Hajiya ?"


"Oh okay hearing device din baya kunnen ta?"


Ita dai bata ce da su uhm ko um um ba. Tana jin su ras.  Ganin baki daya sun jefa kawunan su cikin damuwa hakan yasa ta dan murmusa. Kafin ta mike dakyar cikin dogara yar sandar hannun ta tayi corridor inda dakin ta ya ke..


Duk wanda ya taso acikin su don temaka mata. Sai ta dagaa masa hannu kawai. Har ta shige cikin dakin ta. 


Kai tsaye ta wuce bakin gado ta zauna.. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Hade da lalubo addua ta karanta.. 


Farin ciki ne dankare a cikin zuciyar ta. Ta shiga yi wa Allah godia tana mai daga hannun ta sama kafin ta shafa a fuskar ta. 


"Alhamdulillahi... Alhamdulillahi Ala Ni'imatihi... Allah banida bakin godiya agare ka. Allah ka karawa annabi daraja, Karama da kuma karamci. "


Haka ta jima tana yan addu'oin ta da istigfari kafin daga bisani ta shige bandaki ta dauro alwala.


Ana kiran sallah ta mike tayi kana ta zauna tana addu'oi har ya zuwa sallar ishai. Bayan ta idar tayi karatu sosai. Sannan ta mike dakyar ta koma gefen gado ta zauna.


Dakin aka fara kwankwasawa. Ta daga kai ta dubi agogon dake bangon dakin. Duk da kasancewar girman shekarun ta ganinta yana nan., Jinta ne kawai yayi karanci. Lokacin da wani ibtila'i ya fada mata. Sai ya zamto da kunne daya take ji. Dayan kuma ya tabu sai da temakawar hearing device ..


"Hajiya abinci ne dama an kammala. Zaa shigo miki da shi "


Tamkar ba zata ce komai ba. Sai kuma ta tashi ahankali da temakon yar sandar ta ta isa kofar ta zare mukullin da ta saka. 


Masu aiki ne har biyu suka shiga cikin dakin na ta .


Bakunan su dauke da sallama suka rissina suna gaishe ta . Ta amsa da fara'a . 


Plate ta janyo ta dan zuzzuba yadda zata iya ci. Sannan ta rufe kulolin da marufan su. 


Ta karasa ci tana hamdala. Kafin ta shige cikin bandaki ta watsa ruwa hade da dauro alwala. 


Ta sauuya kayanta zuwa marasa nauyi Wanda zatayi bacci da su. Daga nan tabi lafiyar gado ta kwanta bayan tayi adduoin ta.


Ta kwanta zuciyar ta na saka mata abubuwa da dama. Nan da nan kwakwalwar ta ta shiga tariyo mata baya. Yadda rayuwar ta dana yaranta suka kasance kafin canzuwar rayuwar su daga halin rashi zuwa na samu..


*TUNA BAYA ..*


*RUMBUN K'AYA*🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post