Ta fita Zakka book 1 complete


Health College

Ta fita Zakka book 1 complete

Ta fita Zakka book 1 complete

TA FITA ZAKKA..!

_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*

*Mallakar:Janafty❤️*

*BOOK 1*

*Wannan Labarin tundaga farkon sa har karshensa Tukwaici ne kuma Sadaukarwa ne zuwa ga HALIMA YUSUF GWARZO(Besty) Amincin Allah  su tabbata a gareki Allahu ya iya miki Halima Allah ya jibanci Lamuranki Duniya da Lahira Ameen*


_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_


*Intelligent Writer's association


*🅿️01*


*GUMEL:Jigawa_Dutse*

_Area:Zango Street_

Friday 5:30pm

Ta jikin get din ta fara lekawa so take tagani ko da wani a Haraban gidan duk da tasan ba lalle ta samu gilmawar wani ba yau jumma"a kuma adaidai wannan Lokacin Duka mazan yara da manya suna masallaci inda Baba Mallam ke musu karatun yammah Matan kuma Kowacce tana cikin gida a irin wannan ranakun na Alhamis da jumma"a suke samun Damar Taimakama iyayen nasu Tunda Ranakun makaranta basa samun Lokaci da sun dawo makarantar Boko abinci kadai suke ci sai sallah da Haraman tafiya islamiya in suka dawo kuma Dare yayi sai Sallar mangariba sai zama yin karatun Tsakani mangariba da Isha"i,sannan in an gama sallar Isha"i kowa zai yi aikin makarantarsa,ko kuma wankin kayan makaranta ko Guga da Sauran aikin karfe 10na Dare kowa yake neman makwanci Saboda Kada a makara Sallar asuba da Shirin makaranta ba atashin mutum sau Biyu sau Daya na biyun kuma Da Duka ne zai sa ya tashi wannan Dokace ga Duk wanda yasan Daya Daga Cikin Dokokin gidan BABA MALLAM da BABA SA"IDU.!

Hankalinta ta Dawo dashi tana kare ma anguwan nasu kallo Shuru ba wani Hayaniya ta Mutane yara duk suna gida Manya kuma suna wajen aikinsu Kofar wani masallaci take Hanga Daga inda take tsaye Fuska ta yamutsa ganin Takalma nan Birjit a kofar Hadadden masallacin mai kama da aljannar Duniya.

Daman tasan yau Dole ne akwai karatun yammah shiyasa bata yarda ta Biyo ta gaban masallacin ba ta yanko Hanya duk da nisanta ta gwammace nisan da Haduwa da Zaluman dake cikin masallacin nan yau suyi bandashenta kamar yadda suka Saba..

Karamin tsuka taja tana gyara zaman Bakar Jakar bayan Dake makale a bayanta wacce ta Sagala Hannu Daya Hannun Daya kuma ta sakeshi.

Yarinya ce wacce ashekaru akallah bazata gaza shekaru sha biyar aduniya ba Doguwace wankan Tarwada mai Dauke da wasu manyan Idanuwa da Doguwar Fuska,kallon Farko Zaka mata ayadda take Motsa baki zakasan tana da Surutu da Tsiwa Sanye take da kayan makaranta na Wando mai Ruwan kuka da Farar riga sai Farin Hijabi da Farin Dankwali kafarta Cikin Takalmin makaranta na Combas samfarin na mata da Safa.

Akallon Farko in kayi mata zaka Fahimci yadda ta jigata,Tun daga yadda Fuskarta Duk ta Kode bakinta ya Bushe yadda kuma take tsaye bakin karamin get din gidansu mai kalan brown zakasan tana tantantaman Shiga gidan ne ko kuma tana Tsorom ta tarar da wani da bataso acikin gida.....

Domin sauke wannan littafin danna Download Now dake Kasa. Zaku iya yin tambay ta hangar yin comment da abinda ya shige muku duhu.


DOWNLOAD NOW

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post