Ta Fita Zakka book 2 complete


Health College

Ta Fita Zakka book 2 complete

Ta Fita Zakka book 2 complete

Yana dafe da kansa kwata kwata baisan motar ta kwacemai ba sai da yaji ta fara yawo a kan titi sannan ya dawo hayyacinsa yana kokarin kamo Sitiyarin motar ne Amina Data ke kuka cikin karan sautinta taga wata babbar mota tayi kansu gadan gadan sai gabanta ya fadi,Kukanta ya Dauke da batasan sanda tayi tsalle sai gata jikin Danmallan cikin rawan jiki Ta kwalla kara tana Fadin"Wayyo Allah babbar mota...!

Wani bakinciki da takaici su kusa kasheshi,bai samu damar mata mgana ba sai da ya daidaita Motar sannan ya gangara gefen hanya yayi parking kafin ya juyo yana kallon Amina wacce ke rike dashi Saboda Tsoro ran sa bai kara baci ba sai da yaga gabadaya Hawayenta da majinanta ta gama gogemai saman kafada wani irin kallon kyama da Haushi yake binta dashi ita batama Lura ba saboda bata cikin natsuwarta ga Halin datake ciki ga Razanan da tayi na ganin babbar Mota ta nufesu gadan gadan.

Ganin sai zare ido take yi taki sakinsa yasa ya saki wani siririn Tsaki kafin ya Daka mata tsawa yana fadin"Ke...!

Sai alokacin ta dawo Tunaninta ta Dago tana kallonsa ganin irin yadda yake Hararanta ne yasa tayi saurin Sakin rigarsa data cukwikwiye da hannayenta ta koma kujerarta ta zauna da Duwawunta tana maida Nunfashi Lokaci daya da ruwan hawaye suna gudu Bisa kumatunta.

Ransa ya kara baci da ya kunna Hasken motar yaga yadda Maikon hannunta ya sakamai Shatin Datti ajikin Rigansa baisan sadda ya kalleta cikin bacin rai yana fadin"Ke wata irin kazamar yarinya ce mara natsuwa..?Ko sau daya tak a rayuwarki bazaki yi wani abu da zai nuna ke mace bace..? 


Download now

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post