H U G U M A
Arewabooks:Huguma
A RUBUCE TAKE
(K'addarata) Book 02
Ta hadu da mutane masu karamci,don haka bata wani jima ba ta sake sosai a cikinsu,zamu iya cewa tafiyar ta zame mata wani mabudi na alkhairi tare da sake sanin wacece ita,wanne aiki ne a gabanta?,wanne muhimmanci abbas ke dashi a rayuwarta wanda abaya duka hankalinta bai taba mata hasashen hakan ba,duk kuwa da yadda take jinsa sosai a jikinta zuciyarta da ruhinta.
Abun ya fara ne daga yadda suka maidata kamar qanwarsu,koda a aikin hajjin kowa qoqarin tallafarta tare da nuna mata abubuwa yakeyi,musamman daya zamana ita daya ce farkon zuwa wajen,cikij taimakon Allah sukayi hajjinsu lafiya suka gama,sai ya zaman lokacin komawa gida nigeria kadai ya rage musu.
A sannan taga kowacce hankalinta ya tattaru kan mijinta da sukazo tare,a lokacin suka lura da yadda ita din bata maida hankalinta sosai akan hakan kamar yadda su sukeyi,hajiya sha'awa ita ta fara fahimtar hakan,wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,tuntuni suka gane quruciyar dake dawainiya da ita,wadda wasu abubuwan take gaza yinsu,babu wadda taji kunyarta acikinsu,dukka suka hadu kamar yadda zasu yiwa qannensu uwa daya uba daya suka fara dorata akan sabon saiti.....sabon karatu da sabon darasi.
Bata taba jin kunyar wasu mutane kaf rayuwarta ba irin yadda suka sanyata jin kunya,amma ta dole sukayi mata ta sake ta kuma soma bin karatun nasu.
Abinda bata sani ba kusan kowannensu tasan halayyar hafsat ciki da bai,wannan yasa hatta gidan babu wadda tayi masa zuwa uku, lokacin da sukaga widad din a mazaunin kishiyar hafsat qaunarta da tausayin yadda zata iya zama da ita ya shigesu,wannan yasa suka samu qarfin gwiwar dora mata abubuwa masu nauyi da yawa,wadanda sukasan koda bayan rabuwarsu zai zauna a kanta ya kuma bi jikinta.
Ranar farko kuma karo na farko da taji itama tanason kasancewa da mijinta kamar kowacce mace,ta dauki waya ta kirashi,a sannan suna tare da sauran abokansu da basu taho da matansu ba,saidai dukka kewarta ya isheshi,bayason ya fiya takura mata ko matsanta mata ne kawai,duba da situation din da take ciki,amma he really needs her,kullum kwanan duniya sake shigewa rayuwarsa takeyi.
Cikin karsashi ya daga kiran,saidai muryarta kawai ya kashe masa jiki,ya jingina da kujerar yana saurarenta sanda take magana dashi cikin narke murya
"Bakayi kewata ba ko uncle?" Maganar tata tadan tabashi,har sai daya murmusa
"Har bansan yadda zan misalta miki ba babyn uncle,kawai dai baison takurawa maman baby dama babyn" har ranta taji dadin amsarshi
"Indai hakanne to kazo mu tafi,yau a wajenka zan kwana" mutuwar zaune yayi yana mamaki,widad dinshi ce ke fadar haka da bakinta?,ya rasa amsar da zaya bata har sai data sake cewa
"Hello"
"Than you baby,gani nan zuwa" abinda ya iya fadi kenan jikinsa yana dan rawa kadan,wanda ba lallai ne kai ka fahimta ba
"Ina zuwa" kawai yace musu yana barin wajen.
Kiran wayarsa ya shigo wayarta sanda ta fito daga wanka,tana tsaye jikin madubin dakin nasu tana mulke jikinta da wasu oil perfumes da hajiya fanna ta bata sanda zasu fice subar mata dakin,hajiya khairi ke tsokanar hajiya fanna
"Allah dai yasa ba kyautar turaren banza kikayi mata ba,wala'alla ki dawo ki sameta nade a gado ma tayi baccinta"
"A'ah ai ba za'ayi haka ba,na tabbatar karatunmu yana shiga,nidai ina ganin canji" qas tayi da kanta tana murmushi,dukkaninsu kunyarsu takeji,tunda sun girmeta,tana jinsu suna tsokanarta har suka fice.
Wayar ta daga tace masa gata nan fitowa,ta gama shirinta a nutse,ta dauki duk wani abu da takega ya dace da wanda taga suna dauka suma idan zasu fita din,ita kanta tana jin banbanci da canji a tattare da ita,ta kammala komai a nutse ta fito.
Ko sau daya baiji ya qosa da jiranta ba har ta iso,kasa magana yayi sanda qamshinta ya gaurayeshi,sai ajiyat zuciya mai nauyi daya sauke kawai,suna shiga dakin ya maida qofar ya rufe da wani irin zafin nama,ko ina na jikinsa yana daukan rawa.
Zaucewa ya kusa yi sanda widad din ta miqa masa kanta yadda yakeso,ta kuma hada da bashi gudunmawa,sai kansa gaba daya ya kunce,jikinsa ya dauki rawa tako ina ya fita mata a hayyancinsa.
Bawai shi ba,ko ita din a yau ta gane da banbanci,ta fahimci kuma maganganun su hajiya fanna,bayan komai ya kammala wata kunya ta kamata,yayin da shi kuma ya hanata sakat,bakinsa kuma ya kasa yin shuru,ya dinga zuba sumbatu ya kasa tsuke bakinsa,domin kuwa ta shammace shi fiye da kima,ta kuma kaishi wata duniya da tunda hajiya ta kawoshi sararin duniyar nan bai tana zuwa can din ba,ko sanda yake kidansa yayi rawarsa shi kadai yaya ya qare?,bare yanzu data bashi tallafi ta kuma miqa masa kanta kacokam.
Wannan canji na widad ya tabashi fiye da kima,ya sake kuma cusa wata irin zazzafar soyayyarta a zuciyarsa,ya sake susucewa,har abun yake bawa widad din mamaki,yadda ya dinga cire kudi yana mata siyayya abun sai ya dinga daure mata kai,wanne irin so uncle din nata yake mata haka?.
Ranar da suka fita siyayyar data sake sanya widad sallamawa abbas rayuwarta da jikinta......ta sake yaqini da yadda yake yawan fadin yana sonta,cikin shagon gold ya mallaka mata wata sarqa da farashinta yakai naira dubu dari tara da hamsin.
Kanta ya daure sosai,a wauta da quruciya irin tata tace ba zata karba ba,sai bayan taje dakinsu da ita su hajiya sha'awa suka dinga mata dariya
"Karki qara cewa ba zaki karba ba,tunda ya siya baifi qarfinsa bane,kuma tukuici ne tabbas yake baki,lallai soyayyar da yake miki tana da girma da fadi,saiki sake kula ki kuma tabbatar duk abinda yakeso kina aikatashi sau da qafa,tabbas gaba saikin mallaki abinda yafi haka muddin zaki sallamawa mijinki tare da tsare duk wani abu da yakeso,ki kuma guji wanda bayaso" ta jima a kwance tana tariyo rayuwarta ta baya,da kuma abubuwa da suka faru a yanzu,ko addu'a ce da ummu da mommynta suka yita jaddada mata ta yiwa kanta mijinta da kuma rayuwar aurenta?,ba shakka akwai tasirin addu'ar data dinga yi tuquru,sai gashi tanata ganin abubuwan da ada bata iyasu ba batama san dasu ba.
Ranar da suka qara fita siyayya gefe ta koma kawai tana kallonshi,yadda ya zage yana siyan kayan babies kamar yasan me za'a haifa,har sai data gaji da ganin yadda yake diban kaya kamar baisan ciwon kudinsa ba tayi magana
"Uncle" ta fada a narke
"Baby" ya amsa bayan yabar dukkan abinda yakeyi ya waiwayo yana duban idanunta farare masu haske sosai,wanda suka dan qara girma kadan
"Wai don Allah bakajin kunya?,ciki fa ka yiwa mace" dariyar da bai shiryawa ba ita ta kubce masa,nutsatstsiyar dariya mai wani irin siririn sauti da tasa fararen haqoransa bayyana,sakalci da shirmen quruciya dai a cikin jinin widad qilan yake,sai tayi kaman ta daina sai wataran ta sakankance ta yanko maka wata wautar,kallonta yake kawai yana dariyarsa,yama rasa wacce amsa zai bata.
Turo baki gaba tayi ganin yadda yaketa mata dariyar yana kuma kallonta
"Kaiko a jikinka,ka yiwa mace ciki kuma kana siyan kayan jarirai,bakajin kunya ma mutane su gane". Takowa yayi gaba kadan ya tsaya a gabanta yana kallonta,ko yaushe qara kyau takeyi tana zama wata balarabiya,ba wanda zai kalleta ya yadda ta iya hausa,hakanan babu wanda zai kalleta ya yarda akwai ciki a jikinta
"To ko mutanen duniya zasu fara boye kawunansu ne?" Kai ta daga ta kalleshi don bata gane me yake nufi ba,saiya kashe mata ido daya
"Ai kowa ma ta yadda wannan cikin ya samu ta haka yazo,ciki harda ni dake da......." Da sauri ta rufe masa bakinsa bayan ta danyi dage kadan,saita janye hannunta da sauri
"Kuma me ya kawo wannan maganar?"
"Kece mana" ya amsata yana qunshe dariyarsa
"To naji,amma bakasan fa me za'a haifa ba kake diban kaya"
"Ko meye kika haifa wuud(qauna/soyayya matsananciya) inaso,idan ana haifar rabin mutum ma kika haifamin zan karba hannu bibbiyu" ido ta zaro tana kama haba
"Rabin mutum?,wai?" Yadda tayin ta bashi dariya,sai.ya janyeta cikin hikima sukaci gaba da zaban kayan unisex a tare,ya kuma tura mata option na zabar favourite colors dinta a dabarance,ta zaba din sosai,duk da tanayi tana waiwaye kamar wadda ke aikata wani abu ba dai dai ba.
**************Karfe sha biyu da mintuna na dare motarsu ta tsaya qofar gidansu na bauchi,a sanyaye widad din ta maida bayanta jikin kujera tana kallon gidan,wani mugun tsanar gidan na shigarta sosai,tana jin kamae ta balle murfin motar ta fice ta kama hanyarta,inda zai bata zabi....da salin alin zatace masa ya kaita gidan hajiya ko gidan uncle muhsin,to amma koda ta fada din tasan ba lallai yayi hakan,don zaice mata ne dare yayi,ko baya ga haka ma.....iya kusancin da suka samu a yanzu a tsakaninsu,bata tunanin zai bari tayi nesa dashi.
Shi ya fara fita daga motar yana cewa
"Ina zuwa" saita gyada kai kawai,tana jin yadda qirjinta yake bugawa,tana iya hangensa daga inda suke zaune a motar ita da umar qaninsa daya daukosu,yanata knocking.
Tun yana qwanqwasa a hankali har ya koma bubbugawa da dan tsauri,wasa wasa sai gashi sun kwashe mintuna masu tsaho yana bugawa,amma qofar ko gezau,babu alamun za'a bude musu gidan,har umar dake zaune cikin motar ya miqe ya fita ya soma tayashi bugun.
Tun ransa bai baci ba har ya soma baci,don ba cikin gida ba......muddin dai ba wani abu bane ya samesu ba a irin bugun da yakeyi yasan har maqota sun jishi,sannan ma ba ita daya bace a gidan,idan ita bata ji ba saboda tayi ciki......shi kuma lawal fa dake kusa kusa?(dan dan uwanshi daya dauko sanda zaiyi tafiya).
"Kira number lawal ka hadani dashi" ya fada yana duba agogon hannunsa,umar ya fidda waya ya fara kiransa,amma wayarsa na a kashe,sabanin ta hafsat daketa ringing kuma ba'a daga ba,a handsfree take don haka yaji me computer ta fada, kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sunji motsi ana tambayar waje,abbas ya tsaya kam yana riqe da qugunsa yana kallon qofar,umar ne ya amsa mata da
"Mune" sai aka fara buda qofar gidan a hankali kamar mai ciwon hannu