Rumbun Qaya
Page 53
Hafsat Rano
***
TUNA BAYA
Kokarin daidai ta kanta Ammy tayi ganin bata da kowa da komai a yanzu sai Allah sai yaran ta dake biye da ita wadda gaba daya kulawarsu take karkashin ta. Idan ta nuna karaya dole suma zasu karaya har a samu matsala wadda ba zata so ba. Tashar Kano line suka nufa duk da bata da wani ishashen kudi a hannun ta dan babu wani abu da suka bar ta, ta dauka sai yan abinda ba za'a rasa ba. Motar Kaduna suka samu suka hau Lamido rike da Raihana da ta kwanta lamo a jikin sa sai Babbo Sadeeq da Hamma Hydar a gefen sa sai Ammy din. Bayan gaba daya ta siye musu dan idan aka ce za'a karo mutum daya zasu takura saboda haka nan da nan motar ta cike suka dauki hanyar barin Kano zuciyar ta a chunkushe da tayi mata wani irin nauyi. Bata neme dangin Abby ba sam dan su ma basu neme su ba tunda aka fara case din kuwa dan dama ba wani shiri suke sosai saboda babu idanun mahaifan su, tasan babu wani abu da zasu iya yi mata shiyasa ma ta yanke shawarar zuwa nata dangin kafin ta san abinda ya kamata tayi. Tunda suka dauki hanyar babu wanda yayi kwakkwaran motsi a cikin yaran har Raihana da ba wani wayo ne da ita sosai ba, sau daya tace ruwa wani bawan Allah dake gaba ya miko mata gorar ruwan dake hannun sa Lamido ya karba ya bata tasha ya maida masa yace su barshi ko zata bukata,godiya Ammi tayi daga nan basu sake magana ba har bacci ya dauke Raihanan a jikin Lamido, Hamma Hydar kuma ya kwanto jikin Ammy shima yayi baccin ya rage sai Babbo Sadeeq da Lamido kawai.
"Ina zamu Ammy?" Lamido ya furta k'asa-kasa yana kallon sashen da Ammyn take.
"Gidan Adda Fatima zamu Ibrahim."
"Ok." Yace ya sake yin shiru yana kallon hanyar yana tuna cin kashin da akayi musu wajen fitar dasu daga gidan.
***Shigar dare sukayi wa garin na Kaduna saboda yanayin tafiyar lokacin da suka taso ma yamma ce dan haka basu isa da wuri ba gashi sai da suka tsaya a hanya sau biyu ma abinda ya kara delay din kenan. A gajiya suke tikis Raihana ta tashi Ammy ta karbe ta daga wajen Lamido suka samu motor da zata kaisu unguwar su Adda Fatiman wadda ta kasance kanwa a wajen Daadah kuma wadda suka fi shakuwa sosai da Ammyn a kaf yan uwan su. Kasancewar ta san da zuwan su Ammy ta sanar da ita yasa tuni ta saka an gyara musu dakin da zasu zauna ana jiran isowar su. Jiki a sanyaye suka shiga gidan ga gajiya da wata irin yunwa da suka kwaso Raihana sai dan kuka take saboda wahala. Da fara'a ta tarbe su suka gaisa ta dauki Raihana ta rike ta cike da tausayin Ammyn da yaran. Abinci yaran suka fara ci ita kuma Ammy ta yi alwala ta hau ramakon sallolin da suka wuce ta, bayan ta idar sun gama cin abincin tasa Lamido ya jasu sukayi alwala sukayi sallar suma sannan suka kwanta.
Abincin Adda Fatima ta ce taci, duk da bata da appetite amma haka ta dan ci kad'an saboda karfin jikinta sannan suka koma dayan dakin ta shiga bata labarin komai tana kuka sosai. Sosai Adda Fatiman ta tausaya mata dan sai data zubar mata da kwalla sai dare sosai suka kwanta duk da babu wani baccin kirki da ammin zata iya yi a lokacin. Juye juye ta dinga yi ta saka wannan da kwance cikin son samun mafita ganin ba zai yiwu ba yasa ta mike ta kara dauro alwala tazo ta hau sallah domin kai wa Allah kukan ta.
***Kwanan su uku a gidan Adda Fatima suka hau shirye shiryen tafiya Adamawa domin Dadah tace ta taho gida zaman anan ba zai yiwu ba ga yara, dama itama tana da niyyar tafiyar a kwana daya ma dan dai addan ta hanata ne shiyasa ta hakura ta zauna din amma yanzu da Dadah tayi magana dole ta hakura ta barsu su tafin itama zata fi sakewa a gidan su kafin ta san abinda ya kamata tayi. Da asussubah suka dauki hanyar Adamawa saboda su samu su isa da wuri dan babu dadi tafiyar dare ga yara.
Zuwan su Adamawa ya dan rage wa Ammy abubuwa da yawa musamman na daga nauyin da take ji a kirjin ta da ya zo ya tokare ta ko ruwa ta hadiya sai taji zafi, Dadah ta tsaya mata sosai da ban baki da shawarwari sannan ta dauke mata duk dawainiyar yaran sai dai kawai ta zauna shiru tana tunanin yadda rayuwa ta sauya musu lokaci daya tayi tafiyar yaji da farin cikin su ya tarwatse ya barsu da tarin bakin ciki irin wanda yake da nauyi da wahalarwa. Ta ina zata fara ne? Haka zata hakura ta zuba ido ta bar Mijinta a irin wannan halin? Gashi bata da komai bare tace zatayi wani hubbasa wanda take ganin ko zatayi din ma ba zata iya karawa da Alhaji Ibrahim Mukaddas ba. Bata da zabi illa ta koma Kano ta je ta same shi, ta nemarwa mijinta gafara ta hanyar tunasar dashi dah da rayuwar su ta baya, wala Allah ya iya sauraron ta ya farfado daga ramin da ya shiga. Ire-iren wadannan tunanin take yi a ko da yaushe har tafiya ta soma mikawa. Basu da wani arziki dan ita kanta Dadah ma fama take da kanta dan ma mace ce me neman na kanta da kokari sosai. Dalilin da ya hanata waiwayen Kanon kenan ta maida rayuwar ta kachokam wajen kula da yaran ta da suke bukatar ta, babu batun maganar makaranta a yanzu saboda bata da kudin da zata iya sakasu a irin makarantar da suke yi a chan sai aka saka su islamiyya suka fara zuwa kafin komai ya daidaita.
Watan abby hudu da rufewa aka bada damar zuwa a ganshi dan ko barin ganin shi ba’a yi ba tun lokacin nan. Cikin tsananin farin ciki ammy ta hau shirye shiryen tafiya ganinsa sannan ta samu ta je taga Alhaji Mukaddas ta roke shi. Lamido yaso zuwa amma tace su yi zaman su ita kadai zata je wanda ba haka yaso ba dan yana so yaje yaga Abbyn amma kuma dole ya hakura dan raihana ma rigima zatayi idan suka tafi. Ita kadai ta shirya ta dauki hanya bayan ta dan masa siyayyar abubuwan da zata kai masa ta isa kanon ta sauka gidan wata yar uwar abbyn da suke shiri ta kwana sannan ta nufi prison din da safiyar asabar din domin ta samu ganin sa. Ta dade sosai a layi tana jira har layi yazo kanta aka bude mata ta shiga ciki aka bata tag ta saka a wuyanta sannan suka shiga ciki sosai har zuwa wani dan madaidacin daki me dauke da dogon benci. Zama tayi tana kallon wajen a hankali jikin ta a sanyaye tana cike da zulumin ganin sa. Tare da wani ganduroba suka shigo yana sanye da dark blue uniform na yan prison yayi wata irin rama da baki tamkar bashi ba. Da sauri ta mike tsaye hawaye na zubowa a idon ta, ya dan yi murmushi kadan cike da farin cikin ganin ta ya girgiza mata kai alamar kar tayi kuka sannan ya zauna itama ya ce ta zauna ta zauna tana cigaba da kallon sa.
“Ya yarana?” Yace tana zama dama kuma tasan su zai fara tambaya
“Suna Adamawa.”
“Adamawa?”
“Umm, chan muka koma ai.”
“Me yasa!?”
“Ba komai, kana lafiya?”
“Toh, kamar yadda kika gani dai, Alhamdulillah ala kulli halin.”
“Baka cin abinci ne?”
“Abinci Aisha?” Yace sai yayi wani irin murmushi kawai da yasan maanar sa shi kadai
“Kuna lafiya? Babu wata matsala dai? Me yasa kuka koma adamawa?”
“Lafiya lou.” Ta share wasu hawayen da suka sake sakko masa, bata son sanar dashi an kore su ne ta sake tashar masa da hankali amma ta ga alamar ba zai kyale tambayar ba
“IBRAHIM ne ya tashe ku?”
“Mu ne kawai muka tafi.”
“Karya ne, ban yarda ba.”
“Me yasa?” tace tana kokarin boye damuwar da take ciki. Girgiza kansa yayi sannan yace
“Nasan babi dalilin da zai saku tafiya, me yasa zai min haka? Me yasa?” Ya furta cike da bacin rai
“Ban sani ba nima.”
Shiru yayi be ce komai ba, sai wani irin harbawa da zuciyar sa take yi cikin tsananin bacin rai ya hadiya wani abu be ce komai ba, dan bashi da abinda zai ce din dama kuma dan a halin da yake ciki babu abinda zai iya yi.
“Karka damu dan Allah, muna nan lafiya suma yaran saboda nisan da kuma bana so suzo su tashi hankalin su shiyasa ban zo dasu ba, amma suna lafiya dukka.”
“Shikenan, ba komai. Akwai wata bakar jakata ina fatan kun dauke ta, akwai debit cards dina a jikin wata wallet dina sannan akwai dayar wayar nan tawa a ciki itama, zai muku amfani.”
“Basu barmu mun gama daukar komai ba, amma yanzu zanje gidan zan duba na gani.”
“Lokacin ki ya cika hajiya.” Ganduroban dake zaune a dakin yace yana mikewa tsaye. Kallon Abbyn tayi idonta na sake ciccikowa ta kalli kayan da tazo dashi tace masa gashi, gid'a kansa yayi ta mika masa kudin dake hannun ta da nufin bashi ganduroban yayi saurin fizgewa yana kalle kalle.
"Ba'a ce miki banda kudi ba? Idan ma zaki bayar dole mu zaki bawa." Yace yana muzurai gami da chusa kudin cikin aljihun sa, sannan ya nuna mata kofar fita da hannu
"Sai anjima."
Da wani irin sauri ta fice saboda kukan da ya taso mata gaba daya bata kuma son yi a gaban Abbyn.
***Abun hawa ta tsayar bayan ta fito daga prison din ya dauke ta zuwa unguwar tasu, duk da bata da tabbacin samun abinda taje nema din amma kuma dole zata gwada sa'ar ta dan suna bukatar kudin sosai. A gaban gate din gidan nasu ya ajiye ta, ta bashi kudin sa ta sauka tana kallon katoton padlock din da aka makala a jikin kofar. Matsawa tayi gaban dayan gidan ta saka hannu ta kwankwasa gate din tana daidaita kanta saboda gaba daya zuciyar ta tayi masifar yin weak kamar zata zube a wajen haka take ji. Gateman din ne ya leko ta dan opening din wajen kafin ya saki abun ya juya zuwa wajen su Hajiya zeenat da Daddy dake shirin fita ya duka cikin girmawa yace
“Hajiyan gidan chan ce tazo.”
“Hajiya? Ban gane ba?”
“Makotan dake dayan gidan da suka tashi kwanaki.”
“Aisha?” Daddy yace yana kallon Hajiya Zeenat
“Shigo da ita Moses.”
“Ok.” Yace ya juya da sauri.
“Me ya kawo ta?”
“Bari tazo muji.” Tace tana murmushi
Yana gaba ammy na biye dashi a baya suka nufo su, idon su a kanta da yadda tayi wata irin rama da baki, murmushi hajiya zeenat tayi tana da yakinin zuwa yanzu Ammyn ta gama tantance wacece ita.
“Kawata kece da tsakar rana haka?”
Motsa bakin ta, tayi ba tare da tayi magana ba dan ji tayi bakin yayi mata nauyi sosai.
“Muje ciki ko?” Daddy yace yana yin gaba.
“Muje Kawata.” Tace tana mata murmushi. Bin bayan ta ammy tayi cike da zulumi da tsoro dan ta gama tabbatar da rashin imanin Zeenatu ya wuce duk yadda take tunani
*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*
1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)* 400
2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)* 400
3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)* 400
4... _INAYAH_
*(Mamu gee)* 400
5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)* 400
_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_
*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥
_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_
_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_
_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_
_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_
1 _*IDON NERA*_
Mamuhgee
2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata
Billyn Abdul
3 _*RUMBUN QAYA*_
Hafsat Rano
4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata
Hafsat Miss Xoxo
5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata
Safiya Huguma
_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_
Guda 5 1200
Guda 4 1000
Guda 3 800
Guda 2 600
Guda 1 400
_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_
_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_
Saiku tura shedar ta👇
_*09033181070*_
Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇
09166221261
TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥
MUNGODE🙏🙏❤️