A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 16

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 16

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 16

 *H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*


*_A RUBUCE TAKE_*

       (K'addarata)

            Part 02


Page 16           "Subhanallahi, garin yaya?" Bayan ya iso yana duba kayan,komai ya tarwatse ya hade waje daya,saita duqa da hanzari jikinta yana dan rawa tanason boye hadiye tashin hankalinta,ya duqa shima yana tayata tattare wajen sannan yace


"Qanwarki ta haihu......" Ya fada yana tattare wajen ba tare daya ko kula da yanayin da fuskarta take ciki ba


"Ta samu d'a namiji ba......abinda ni hafsat na gagara baka har kaje ka qara aure don ka sameshi,burinka ya cika" ta fada da wata irin shaqaqqiyar murya sai kuma ta saki tarkacen data fara kwashewa ta wuce daki tana sakin boyayyen kuka mai bala'in cin rai,komai ya qarasa lalacewa kenan,yaushe akayi cikin?,yaushe harya girma?,sannan data tashi haihuwa ma ba mace ba?,namiji?,saita quma kanta da bangon dakin wanda har tsakiyar kanta taji zafin buguwar da tayin,amma radadi da zafin dake cikin zuciyarta ya zarta wanda taji.


          Da kallo ya bita sanda take wucewa dakin,mamakinta yana kasheshi,banda yasan bata da aljanu da tabbas wasu lokutta sai yaga ruqiyya ce tafi dacewa da ita,yanzun a batun haihuwar widad din meye abun daga hankali?,harda qirqirar batun d'a namiji da 'ya mace?,bashi karan kansa ba,ko a cikin danginsa ba wanda ya taba zancan mata take haifa,hakanan tsahon zamansu bai taba kawo wannan tunanin a ransa ba banda yanzu data furta,don shi a wajensa d'a duka d'a ne,yadda ake haifar namiji haka ma mace,sai wanda Allah ya sanya yafi wani albarka kawai.


         Yadda yaran sukayi carko carko suna kallonsa yasa bayan ya gama sharar wajen ya wuce dakin nata bayan ya zaunar dasu a falon,kuka ya sameta tanayi sosai hadi da safa da marwa,ta kasa zama waje daya,ya isa tsakiyar dakin a nutse hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta


"Hafsat,ki nutsu mana,duka wannan abun na meye?" Sosai tayi qoqarin saita kanta, batason ya karanci yaron da aka haifa takejin buri da muradin mutuwarsa yana ratsata


"Na nutsu fa kace,wai meye ka maidani abbas?, yarinyar tayi ciki harta haihu ban sani ba sai ranar data haihu din?" Mamaki ya sake kamashi,lallai idan mutum bashi da abun fada to fada yakeyi da kowa ma


"To naji,amma relax please,kin saka yara duka hankalinsu ya tashi,yanzun dai tunda ta haihu ai ya wuce ko?,sai kiyi haquri" ya rufe da bata haquri duk don bayason tashin hankali.


            Kuka ta sake fashewa dashi ganin wani lafiyayyar nutsuwa da walwala shinfide saman fuskarsa


"Ko yaushe cutata kake abbas,ko yaushe zaluntata kakeyi" abinda ta fada kenan,kalmomi biyun da ya tsana kenan a rayuwarsa,ko zai yarda da komai amma bazai dauki kalmar cuta ko zalunci ba akan wani,babban dalilin da yasa yake da abokan adawa sosai akan aikinsa, don baya yarda a zalunci kowa,mai gaskiya ne kai ko mai laifi,kowa sai an tabbatar masa da hakkinsa.


          Ganin yadda ta birkice ba bisa gaskiyarta ba sai kawai ya juya ya fice daga dakin ba tare daya sake bi ta kanta ba,ta sake tunzura ainun sanda tashin motarsa,data leqa falon ba kowa duka ya tattara yaran ya fice dasu banda yusra da tayi bacci ya kwantar mata da ita saman couch ya tareta da pillow don kada ta fado,saita sake rushewa da kuka,a fili tana cewa


"Widad ta haihu?,kuma d'a namiji?" Ta fadi hakan ya kusa sau biyar,tanason idan wai mummunan mafarki takeyi Allah ya taimaketa ta farka,saidai still sake samun tabbacin cewa idanu biyu take tayi,musamman da taji muryar sagir dan yayansa daya dauko yake zaune a gidan,saboda samun security na gidan idan suna kaduna.


          Yana tuqi a hanya amma tunani barkatai yana zuwan masa,lamarin hafsat ya fara sakashi a kokwanto,ko a labari bai taba ganin mace mai baqin kishi irinta ba,ya maida dubansa gasu mimi dake ci gaba da murnarsu ta samun dan uwa,wanda a gidan basu samu sukuni ba saboda gargadin da hafsat din tayi mata,yaran fici fici dasu,ko wanka babu amma haka ya daukosu saboda yasan idan ya barsu a gidanma akansu zata huce idan ba'a yi wasa ba.


          Yana tsaida motarsa gaban gidan hajiya ya bude yace su shige ciki,da gudunsu kuwa suka fella,ya dauke idanunsa daga kansu yana murmushi bayan sun shige din,wayarsa ya ciro ya sake trying number widad amma taqi shiga, shikam bayajin yau zai iya kwana bai sanyata cikin idanunsa ba,don haka ya shiga kiran number din suraj karo na biyu


"Yaya dai angon qarni"


"Don Allah idan ba wani muhimmin uzuri gareka ba,ka ajjiye komai kazo kayimin rakiya kano"


"Da zafi zafi haka?"


"Kaima kasan bazan iya jurewa ba" ya amsa masa yana murmushi


"Bani nan da awa daya"


"Godiya mai kima" ya fada yana jin dadi,suraj din aboki ne na gari dake tsaya masa cikin kowanne irin yanayi.


            Suna gama wayar mimi ta fito da gudu tana kiransa


"Wai ka shigo inji hajiya" 


"Gani nan mimin daddy" ya fada yana dariya hadi da kashe motar,ya fito suka jera zuwa cikin gidan tana riqe da hannunsa tana gaya masa zasuyi party dasu nawwara da qawayenta


"An gama mimi na" ya bata amsa yana murmushi hadi da shafa kanta.


         Da waya a hannu ya samu hajiya,ya tsugunna yana sake gaidata duk da sun gaisa dazu ta waya.


         A nutse ta amsa masa tana kallonsa,cikin muryar nan dak cike da dattijantaka tace


"Wai meye yake faruwa a gidanka Abbas?" Tayi maganar cikin qosawa,sai ta kasa jira yace komai ma


"Me dame kake boyewa matarka" sosai ya dubi hajiyan,yasan kwanan zancen


"Hafsat ce ta kawo qara ta hajiya?" Ya tambayeta a sanyaye,saita gyada masa kai,tana jin tausayinsa yana kama ta,ya hadiye wani abu mai tauri sannan yace


"Wai na boye mata cikin widad,ni kaina ban dauka lokacin haihuwar yayi ba,saboda duka scanning dinta da awon da ake mata bata cemin komai" yayi maganar da sound na damuwa da takaicin dabi'ar hafsa.


           Zama hajiyan tayi a gefansa sabanin dazu da take zaune,sannan ta fara masa magana da harshe irin na uwa,tana tausarsa da kalamai masu kwantar da hankali da suka sanya jikinsa mugun sanyi,saboda yadda hajiyan ke masa magana kamar wadda ke bashi wasiyya ne


"Kaci gaba da haquri,ibada kakeyi,kuma nasan tabbas Allah bazai taba wofantar da kai ba,bazai kuma tauye maka ladanka ba,wataran sai labari,kuma wadan nan abubuwan da dukka nake gaya maka ko bayan raina zaka tuna,nidai abu daya da nake godewa Allah,widad da Allah ya baka,ko babu ni nasan zata kula dakai....in sha Allah"


"Hajiya ki daina fadin bayan ran nan don Allah" ya fada yana son katse zancan,sai tayi murmushi kawai


"Bara'atu harta kirani tayimin zancan zuwa kano"


"Eh nan da awa daya zamu tafi ni da suraj in sha Allah,su kuma ina ganin saisu bari ko bayan kwana biyar ne ko shida ko ranar suna"


"Ba laifi hakan yayi,Allah ya tsare"


         Kaye kaye ta masu uban yawa hajiya ta hadama widad din,a yau tana jin zuciya da ruhinta fes,tana sake godewa Allah da ya bata iko tayi wannan hadin,ko ba komai abbas din ya samu wani sassaucin rayuwar gidansa ta wani gefen.


             Sun dauki hanyar kano a lafiyayyar motar abbas din,daga shi sai suraj,wanda suraj ke tuqin,hira sukeyi sosai a junansu,wanda kusan fiye da rabin zancan na widad ne, zaiyiwu wuya kawo yanzu muddin akwai shaquwa da aminci irin wanda yake tsakaninsa da suraj kuyi dogon zama baiyi maka maganar widad ba


"Ka godewa Allah daya baka wani bangere da zaka dinga samun sassauci,amma koni.ina ganin qoqarinka,tabbas inda nine keda hafsat,da tuni na jima da qara mata mai" murmushi abbas yayi sannan ya miqe ya zauna sosai,ba daga bakun suraj kadai.yake jin wannan maganar ba,sai ya dan dubeshi kadan sannan ya maida dubansa ga titi


"Saki ba shine hanyar maslaha kadai ba,bai kamata saki ya zama wani abu mai sauqi ga kowanne magidanci ba,idan hakan kuwa ta kasance al'ummarmu zata zama bata da wata makoma,tunda kowacce al'umma gidan aure shine tushenta,tunda daga can ake samar da nau'i na dan adam,nagartacce ko gurbatacce,wanda daga baya shi zai fito ya zama madubi na al'umma,imma malami jagora ko shugaba,mun ruguxa gidajen aurenmu da aure aure da sake sake,me muke tunanin zamu tsinta a gobemmu?,idan kayi qoqarin gyara ko canza matarka hakan bata samu ba,ba saki bane kawai hanyar da zaka samu gyara,infact idan ma bakayi wasa ba,sai ya bude qofar wata barnar,wani lokaci ya kamata mu dinga duba da wasu abubuwa kafin afkuwar saki,kamar makomar yaranmu,da wanne ido zamuyi musu bayani sanda suka budi idanu sukaga babu iyayensu a tare dasu?,wanne alkhairi matar nan ta taba yi maka a rayuwarta komai qanqnatarsa?" Kai suraj yake jinjinawa,ya jima baiga mutum kamar abbas dinsa ba,ko yaushe yana gayawa kansa da kansa abbas din na dabanne,samun irinsa sai an tona,inda hafsat zata gane waye take aure,lallai ba shakka zata fahimci a duniya tana cikin mata masu sa'ar da ba kowa ke samunta ba.


            Misalai kala kala yaci gaba da bashi,wadanda suka fahimtar da suraj abbas ya fishi gaskiya da kuma hangen nesa,saidai a halittarsa bazai fa iya daukan abinda shi yake dauka ba.


            Wayarsa da tayi qara ita ta katse zancan,ya daukota daga inda ya zurata yana duban me kiran, al'ameen ne abokin aikinsa,sai ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da sallama


"Oga.......kasan an saki signal kuwa?" Abinda ya fara cewa dashi kenan bayan sun gama gaisawa


"Ah.....haba,yaushe?"


"Jiya cikin dare,ban kwanta ba sai dana duba list,saiga sunanka a farko farko,You have been promoted to DSP.....congratulations" sosai labarin ya tabashi,saboda baisan ma abinda ke faruwa ba banda al'ameen din ya gaya masa yanzun.


           Hajiya ya fara kira ya gaya mata,tayi masa addu'a sosai cikin zallar farinciki da fatan ci gaba da samun nasara,widad itace tazo ata biyu,don a yanzun a duniya bayan hajiya widad itace number two dinsa,ya gaza haquri har sai ya isa,tayi amsa addu'a sosai data burgeshi, shigen addu'ar da hajiya tayi masa,sai yaji zuciyarsa tana qara sanyi tare da samun nutsuwa a ransa.


"Lallai muhammad yazo da alkhairi da albarka" suraj ya fada yana murmushi,kai abbas ya jijjiga sosai,yana tuna sanda ya samu promotion sanda maganar aurensa da widad din ta taso,haka Allah yake al'amarinsa,yana tsara komai bisa yadda yakeso ya kasance.


            Daga sanar masa haihuwar zuwa isarsu kano duka duka ba'a cika awanni uku ba, lokacin da sukayi ido biyu da widad din sai yaji gaba daya duniyarsa ta dawo sabuwa,tausayi girma da kimarta suna sake ratsashi,ya sanya hannu biyu ya karba yaron idanuwansa suna qishirwar ganinsa.


            Wata irin qauna da soyayyar yaron mai qarfi ta saukar masa sanda idanunsa suka sauka akan fuskar da marabarta da tashi shekaru ne kawai


"Subhanaka rabbi.....maa a'azama sha'anik, Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fadi zuciyarsa na bugawa da soyayyar yaron,ya daga kai yana duban widad da wani irin narkakken murmushi


"Yau wannan babyn ta zama uwa.......wannan babyn ta zama maama,babyn uncle ta zama maman baby" kunya sosai ta kamata,ta kama hannunsa ta kifa fuskarta a ciki tana dariya qasa qasa.


          Tamkar abbas bazai bar gidan ba,yana jin kamar yayita zama yana kallon yaron nasa dama widad din gaba daya,saidai abisa tilas yayi musu sallama saboda tafiyarsa sokoto da dole ta koma washegari.


        Bai bar garin kano ba sai da ya tabbatar hatta da magi da widad zatayi amfani dashi ya tanadar mata,duk da cewa bata rasa komai ba a gidan,ga jibge mata komai na amfani,banda kayan sawa na barka nata dana baby wadanda musamman ya sake sabuwar siyayya banda wadda sukayi a saudiyya,wanda kowa ya gani sai ya shaida irin soyayya qauna da kuma yadda take da muhimmanci cikin rayuwarsa.


            A ranar ya yiwa yaron huduba da suna muhammad muhsin,wanda zabi ne ya baiwa widad kuma ta zabi sunan uncle muhsin din


"Hakan yayi miki?" Saita gyada kai tana murmushi


"Uncle muhsin ya bani komai a rayuwa da yayi silar wanzuwar rayuwata tare da taka,ya bani komai da ya bani kai" ta furta kalaman da wani irin sanyi,har cikin zuciyarta tana jinta cikin mata masu sa'a data samu abbas.


          Kalamanta sun sake gina mata matsayi mai girma cikin jiki da zuciyarsa cikin qanqanin lokaci,ya saki wani tattausan murmushi


"Ni zan fadi haka widad,ya kawowa rayuwata alkhairi,ya kuma yarda ya kawowa rayuwata dauki a sanda take gab da dulmiyewa,samunki wani babbar tagomashi da baiwane daga Allah, ubangiji na ya gama yimin komai,babu abinda zance dashi sai godiya mara yankewa har ya zuwa qarshen numfashi na".


********JEGO widad takeyi sosai,irin jegon da ake kira jego ja ainihi,don hajiya umma kakarta ta wajen mahaifiya wadda ta haifi mommynta ce ta taso takanas daga katsina ta taho yi kata zaman dabaro,tace damar da ba'a basu ba lokacin bikinta ba yanzu zasu nuna tasu bajintar.


          Nan sashen ummu ta sauka cikin dakin da aka warewa widad din,zamansu gwanin sha'awa,gurin sai ya zama majalisar gidan,abinda ya qarawa widad dadin zaman gidan kenan,sai 'yan qananun abubuwa dake damunta,rashin sabo da raino,da kuma shayarwa da sai an tsaya a kanta take shayar da yaron saboda tsoro da rashin sabo.


          Gyara iya gyara widad tana shansa,jego take irin na da wanda a wajenta yake kamar takura ce,har sai da anty madeena tace da ita


"Ki godewa Allah,ke yar gata ce gaba da baya,irin wannan gyaran da kulawar mata da yawa suka rasa,wanda daga ita ne kika samun sbauwar daraja da kima idan kin samu kula da gyara me kyau,daga itane kuma komai yake qwace miki ki kasa fahimtar inda mijinki ya dosa idan kinyi sakaci da ita".


           Ta sake yarda da haka bayan hajiya fanna tazo mata barka,daga cikin abinda ta kawo matan itama kayan gyara ne 'yan maiduguri masu shegen kyau,ta kuma jadda mata lallai lallai tayi duk abinda tsaffin suka ce mata,domin sun fita sanin me sukeyi,yadda taga kuma suna kula da ita itakam hakan ya burgeta.


         Fadin irin alkhairin data dinga samu ma bata baki ne,abun sai ya zamana kamar lokacinne aka yiwa abbas din haihuwar fari,abokan aikinsa kota ina,basajin tafiya daga bauchi zuwa kano ganin jariri,abun har mamaki ya dinga bawa kowa.


        To amma ba abun mamaki bane,duba da dabi'a da halayyar abbas din,mutum ne mai tsananin kirki kyakkyawar mu'amala da kuma budadden hannun alkhairi ga kowa,haka suka yita karbar jama'a,har akayi kwana biyar,aka fara shirin gagarumin suna.


*********Ita kadaice a zaune a falon nata tana yankan farcenta da wannan karon da kanta tayi amannar yayi datti yadda ya kamata,don babu ko sirkin jan lalle a kansa ko baqi balle ya taimaka ya boye datti ko tsahon da yayi.


          Gaba daya tunda akayi haihuwar takejin wani gagarumin sauyi yana tunkarar rayuwarta,tana fuskantar motsin kowa,kowa cikin family kamar rawar jiki yake da haihuwar,abbas kuwa duk da dama can nutsatse ne,komai nasa kuma bisa tsari da dacewa da kuma mutuntaka yakeyinsa......amma walwalarsa ta qaru dari bisa dari,jifa jifa tana tsintar hirarsa da yaransa akan sabon qaninsu,abinda yake matuqar quntata mata,ya kuma jefata cikin baqincikin da yake sake sakata cin alwashin da takejin muddin ranta ba zata sauke ba,sai taga abinda ya turawa buzu nadi.


         Ko a yanzun ma da take zaune ita kadai a gidan sai yusra,ya kwashesu suna wajen tailor dinsu karbo dinkunan suna,sunan da batajin ko sama da qasa zata hadu zata bar yaranta suje,badai a gobe zai wuce kaduna ba saboda tasowar wasu ayyuka masu matuqar muhimmanci?,taga wanda zai tareta da maganar zuwansu kano.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post