*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 26
Hafsat da lawal ta hango tsaye jikin motar hafsat din suna magana,da alama fita zasuyi ko kuma sun dawo,ba kasafai takeson shiga sabgarsu ba,amma yanzun dole tayi tambaya taji ta inane wurin yake tunda ba garinta bane,saita sauya akalar tafiyarta zuwa wajensu.
Dif sukayi sanda suka ganta a wajen,hafsat ta dauke kai kamar bata ganta ba
"Don Allah lawal ta ina faaz hotels yake?" Tambayar data fusgi hankalin hafsat,saita waiwayo ta zubawa widad din ido
"Faaz hotel kuma?"
"Eh nayi baqi ne zan taho dasu"
"Okay" ya fada sannan ya fara mata kwantance inda yake ya qarashe da cewa
"Kibi ta nan ahmadu bello way"
"Aah,ta sa'adu zungur road kaman yafi" hafsat ta tsoma bakinta,bata kawo komai a ranta ba,cikin tsarkakakkiyar zuciya tace
"Yauwa na gode" kamar tace lawal din ya kaita ganin suna rufe motar sun gama uzurinsu da ita amma saita fasa,ta shige part dinta da sauri ga sauya kayanta zuwa abaya wadatacciya tayi rolling,saita saba affan a kafadarta ta dauki key dinta da kudin napep da zai kaita ta fita,tasan ba zata jima ba,duka duka da zuwa da dawowar ba lallai ta wuce awa daya tunda basu da wani nisa sosai.
Wani irin duumm yaji kansa yayi,ya sake daukan wayar jikinsa yana rawa ya kuma buda hotunan,itace dai..... widad dinsa ce dai babu canji, itace dauke da affan dinsa,yaron dake tsananin kama dashi
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ya fada wannan karon har bakinsa yana rawa,kansa ya sara masa yasa hannu bibbiyu ya dafe,wani sashen na zuciyarsa yanata qoqarin kawo uzuri da kariya a gareta,amma wani sashen kuma yana qaryata haka hadi da sukan duk wani hanzari da zuciyarsa ke badawa,sashe mafi qarfi kuma mafi rinjaye kenan.
A hankali sai zuciya ta fara ayyano masa irin abubuwan da suka faru a jiyan,ita tafara tashinsa a bacci,ta kuma shirya masa komai na tafiyar tun lokacin tafiyar baiyi ba,ta dameshi kuma ya tashi ya shirya kada yayi latti,hakan yana nufin dama akwai abinda ta shirya zatayi a ranar shiyasa take Allah Allah ya tafi?.
Bayan nan yayi kiranta da yammar kusan miscal uku,bata biyoshi kiran ba,har sai cikin dare bayan bacci ya daukeshi,sai da safe yaga miscal,bata kuma sake nemansa ba,me hakan yake nufi,duka wadan nan abubuwan da ido yake gani ya zama gaskiya kenan?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya sake fada kansa yana qara sara masa sosai yayi qas da kansa yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani masifaffen zafi.
Yafi awa uku cikin matsanancin halin da baisan dame zai kwatantashi ba,kafin daga bisani wata qaqqarfar zuciya ta yunquro masa,ya miqe ya fara hada kayansa,abinda sam baiyi shirinsa a sannan ba har sai zuwa gobe da safe.
Bashi da kuzari ko qarfin halin da zai iya tuqi daga sokoto zuwa bauchi,dole ya nemi daya daga cikin yaransa da sukayi tafiyar tare ya bashi driving din.
Tunda suka dauki hanya bai iya katabus din komai ba,sunci rabin tafiyar saiga kiran widad din ya shigo,ya kalli wayar sosai kamar widad dince a gabansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,wani sashe na zuciyarsa na bashi izinin dagawa,wani sashen kuma yana hanashi tare da tuna masa girman laifinta a gareshi,daga qarshe daya sashen yayi rinjaye,sai yayi rejecting kiran,yama kashe wayar gaba daya,ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa,kanshi yana ci gaba da sara masa
"Widad fa,widad" abinda zuciyarsa keta maimaitawa kenan cike da wani irin zulumi tashin hankali tsoro da kuma fargaba.
Cikin mamaki ta sauke wayar tana kallon fuskar wayar sosai,zuciyarta na gaya mata rejecting kiran nata yayi amma ta kasa gasgatawa,saita katse shakka da mamakinta ta sake yunqurin kiransa a karo na biyu,saidai computer ta gaya mata wayar tasa a kashe take.
Jim ta danyi,to kodai wayar tasa babu charge ne,ya qare sanda take kiran nasa?,bata sani ba,amma daga qarshe saita barwa kanta cewa hakanne,don baka ta miqe ta soma aikace aikacenta lokaci lokaci tana gwada sake kiransa,saidai babu wani abu daya canza,a kashe din dai take.