A RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 2 Page 6

A RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 2 Page 6

A RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 2 Page 6

H U G U M A

Arewabooks:Huguma

A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

Part 02

Page 06

          Hannu ya miqa mata yana dubanta da idanunsa da sukayi laushi,saita noqe kafada alamun a'ah,ya sauke hannunsa muryarsa adan shaqe yana tambayar


"Waye?"

"Nice" kakkausar muryar hafsat ta bayyana,ya miqe cikin wata irin kasala hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya isa bakin qofar yasa hannu ya bude mata.

        Idanu suka zubawa juna shi da ita,ita din tanason karantar cikin wanne yanayi yake,yayin da shi kuma yakeson jin ba'asanin bugun qofar

"Tazo ta kwashe kayan nata" sai daya lumshe idanunsa ya lumshe ya budesu lokaci guda sannan ya amsa mata a nutse

"Meye damuwarki ne?,badai kinyi complain ba?" Mugun haushi ya cikata,yadda ya bata amsar sam shi bashi da damuwa ma kenan

"Eh.....amma dai kasan yau din kwana na ne da zakazo har cikin dakinta ku rufe qofa" sai daya dubi bayansa wato cikin dakin ta gefan idanunsa sannan ya maida dubansa kanta

"Stop it hafsat......kisan irin abinda zaki dinga fada,yara kin sani suna jinki"

"Eh ai.hakkin......"

"Dalla ya isa......bacemin agun" ya fada cikin bacin rai ganin bata da niyyar yin shuru,gasu mimi dake zaune daga falo ta fara calling attention dinsu.

         Ido ta zuba masa cikin bacin rai,saita jijjiga kanta da qarfi ta juya da sauri tana barin wajen saboda hawayen da suka ciko mata idanu,cikin bacin rai yaja siririn tsaki ya koma da baya cikin dakin,zuwa sannan har widad ta nema doguwar riga ta saka.

         Wani kyan yaga ta sake masa fiye dana dazu,yasa hannu ya dan shafi cikinta kadan wanda shima har yanzu yake mamaki idan ya tuna tuna akwai d'a a ciki

"Ki shiga dakina ki dauke abubuwanki masu muhimmanci,mamansu mimi zata aje kayanta" ido tadan lumshe sannan ta kauda kanta tana jin wani abu ya soki zuciyarta,a taqaice dai an koreta daga dakinsa mummy Hafsat din ta tare kenan

"To" ta amsa masa ciki ciki tana dan tura baki gaba,ya fahimceta sarai,qaramin murmushi ya kubce masa,yadda take kishin nan nasa yana nurgeshi sosai,sai ya.miqa hannu ya jawota jikinsa

"Bamu rabu ba babyn uncle,ko yaushe ina cikin gidan nan,ranar girkinki kuma zamu kasance tare anan har sai kince kin gaji" da sauri tadan tureshi tana dariya

"Nifa ba haka nake nufi ba,kuma ma bance komai ba uncle" dariya ya saki cikin jin dadi,Allah baya hadawa bawansa zafi biyu,idan ya rageka ta wani bangaren saiya sanyaya maka ta wani,sam bata daukar abubuwa da zafi,uzuri guda daya kacal ya isa ya wankeshi a wajenta.

           Shi ya taka mata har dakin gudun fitina,yana tsaye ta hada kayanta tsaf ta baro dakin,shima duk sai ya dinga jin ba dadi,har ya fara tunanin sauya muhalli wadatacce muddin hafsat din ta dage da zaman kadunan.

          Kamar jira take widad din ta fita a dakin ta fito daga bandakin data shige sanda taji motsin shigowarsu,gudun kada widad din taga hawayen da takeyi ta rainata, qorafi taso dasa masa kan wanda ta fara dazun amma bai bata fuska ba,hasalima sai ya fice daga gidan abinsa,dole ta tattara dukka wani quncinta ta adanashi waje guda,don ko widad dinma tana cikin dakinta tana sabgarta,bata ganta ba bare ta juye a kanta.

          Da dare shi ya kira widad din akan tazo suci abinci,hafsat din tanata wani cika tana batsewa kamar wadda tayi wani abun kirki,shinkafa ce da miya 'yar kullum,sai nama da bai gama rusuna ba cikin miyar.

            Wata armless chiffon gown ce a jikinta ruwan zama, tsahonta duka duka iyakarsa qauri,ko sauko mata batayi ba sosai,hafsat din ta bita da kallo ranta kamar zai fashe,ta cika tayi fam a rigar saboda cikinta da yabi jikinta sosai zuwa qirjinta,ita batayi don wata hafsat ba,tayine saboda sabo,ire iren shigarta kenan dama a kadunan,da wuya ka ganta da atamfa.

          Da qyar take zuba abincin,ta gama ta turawa kowa tabar widad da zuba nata,kadan ta zuba,don ko a ido ma ta dinga jin abincin bai mata ba tun batakai cikinta ba,aikuwa da qyar tayi loma biyu ta miqe,ya bita da kallo yana tambayar ba'asi

"Na qoshi ne uncle" ta fada adan shagwabe,yasan inda matsalar take,shi kansa da ya saba cin wannan collabo din nata yana ci ne kawai don babu yadda zaiyi,bare widad din da bata saba ba.

"Amma.....me zakici?" Tadan juya fararen idanunta cikin dan tunani

"Zan duba wani abun ko cikin fridge ne" kai ya gyada

"Make sure kinci wani abun kafin ki kwanta,karki sake ki kwanta da yunwa" ya fadi yana dan jin damuwa a ransa,ya dauko abinda ya zame musu damuwa duk su duka,kai ta gyada

"In sha Allah uncle" sai ta fara takawa zuwa cikin dakinta,yayin da hafsat ta kasa daurewa taja wani mugun tsaki mai masifar qara

"Ayidai mu gani" kallonta yayi baice komai ba yaci gaba da cin abincinsa ganin widad din ko waiwaye batayi ba bare tasan abun ya shafeta,sai yarinyar ta sake burgeshi,yasan ta tsani taja masifa aqi tanka mata,yanzu zata sake haukacewa

"Sai wani rawar qafa kake a kanta,idan banda daurewa qarya qarqashi,ayi abincin tace wani wai bataci,sannan kai ka biye mata da zancan ta nemi wani abun taci tsabar ciwa mutum fuska" tayi maganar muryarta tana rawa.

         Sosai ya kalleta kafin ya aje spoon din hannunsa

"Ki shiga taitayinki hafsat,ni ba haka na saba rayuwata a Kaduna ba,nutsuwa da kwanciyar hankali sosai nake samu,ba zaki zo ki hanamin wannan ba,indai kikace irin wanan halin zaki dauka to ki tabbatar ba zaki taba jin dadi na ba" daga haka ya miqe shima yabar mata wajen.

******Kwanakin girkinta guda biyun nan ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi,itadai widad bata fasa sabgoginta ba kamar yadda hajiya fanna ta bata shawara,illa iyaka ganinta ma wuya yakema hafsat din bare ta takaleta,wuni a daki baya yi mata wahal,tayi kallo ko tayi chart ko ta buga game,idan ta fita falo daukar abu tazo yi zata dauka ta wuce abinta,yaran suna son zuwa wajenta amma uwar ta kasa ta tsare,idan ta bari sun rabeta to uban yana gidan ne babu yadda zatayi tana shakkar hanasu.

         Abbas din yana ta qoqarin ganin tana fitowa ta sake a cikinsu amma taqi bada wannan damar,don ta sake sanin ciwon kanta zuwa yanzu,uwa uba kuma kishin hafsat din itama takeji sosai,musamman ta ganta ta fito daga dakin uncle din nata sai taji kamar zuciyarta zata fashe,tafi ganewa tayi zamanta a dakinta tayi sabgoginta,ko abincin darenma na washegari tsakura tayi tabar falon,hafsat din nata binta da harara kamar idanunta zasu fado,amma ita bata ma kalleta ba bare tasan me takeyi.

********Kwanansu biyu da dawowa widad din ta karbi girki,ranar tunda safe datayi wanka ta shirya cikin wata farar wide leg jumpsuit,sai baqar gatsby cap data dora saman kanta.

           Duk sa cewa tayi shigarta ne kawai normal bada wani manufa ba amma wani mugun kyau tayi,shigar ta karbeta sosai,saika dauka wata baturiya ce,musamman yadda sassalkan gashinta ya fita ta qasan hular kan nata.

          Ta lura da lalacewar falon kwanaki biyu kacal,saboda haka can ta fara fita bayan ta zura lallausan bedroom slippers dinta.

            Yadda take tsammani haka ta samu falon,a wargaje tarkace kota ina,haka ta dinga kawar da duk abinda tasan bai kamata ya zauna a falon ba tana killaceshi,cikin mintuna qalilan ya fara daukan saiti.

         Tana tsaka da aikin hafsat ta fito dauke da qaramin mug da plate dinsa,suka hada ido widad ta janye kallonta daga kanta tana ci gaba da aikinta,wata irin harara da widad din batasan tana yi ba ta zabga mata,taja wani dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,gaba daya yarinyar ta gama shige mata rayuwa,banda tsabar raini me ya hadata da taba mata falo?,ko tana tunanin itama tana da power ne irin yadda ita take da ita?

"Iyayin banza da wofi kawai" ta fada tana wuce widad din,wadda tabi bayanta da kallo,saita samu kanta itama da cillama bayan nata harara kafin ta maida dubanta ga qofar dakin uncle din nata,wanda a yanzu ya zama nasu shida hafsat din,wani zafi takeji a zuciyarta,tunda mommyn tazo komai ya sauya a tsakaninsu,a baya kullum suna manne da juna,amma yanzun ta shiga tsakaninsu,siririn tsaki taja data tuna uncle din nata yana dakin,tare suka kwana,kuma duk wani abu da yake mata itama mummyn yana mata kenan?,tana shaqar wannan daddadan qamshin nasa?,tana jin wannan lallausar fatar tasa?,yana bata wannan soft kiss din irin wanda yake bata?,sai taji ranta ya baci amma tayi saurin koren shaidan yadda anty madeena ta koya mata.

            A kitchen kuwa tsaki hafsat din tayita ja a jajjere,yau abbas din zai raba musu kwana da yarinyar?,saita zube cups din kawai ta fito tabar kitchen din.

           Wuceta ta sakeyi ta gefanta kamar zata gogeta,ko daga kai widad din batayi ta kalleta ba taci gaba da aikinta,ba jimawa aka turo qofar dakin,bata juya wajen ba,amma duk da haka lallausan qamshinsa ya gaya mata waye.

         Tsaye yake daga bakin qofar yana qare mata kallo cikin police uniform dinsa dake matuqar qara masa kyau da wani irin kwarji na musamman,hannayensa cikin aljihunsa fuskarsa ta wadata da murmushi,duk kuwa da cewa bata ma san da tsaiwarsa ba,tun tana basarwa hadi da qin kaon qofar har zuciyarta ta gaza,tana jin saukar idanunsa a dukka jikinta,yana kuma haifar mata da kasala sosai.

          A gajiye ta daga fararen manyan idanunta ta sauke masa,idanuwansu suka gauraye waje guda,sai shima ya gaza.....ya zaga da tsaiwa a nan ba tare daya iskota ba,ya fara takowa a hankali har yanzu ya kasa dauke idonsa daga kanta

"Good morning babyn uncle" fuska tadan narke kadan ta karyar da wuya,kishi nason taso mata amma tana danneshi,uwa uba kuma ya mata wani irin kyau me taba zuciya

"Morning uncle din baby" maganar tata ta sanya murmushi ya subuce daga labbansa,kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai hafsat din ta fito daga dakin,dauke da briefcase dinsa, idanuwanta a kansu har ta iso ta miqa masa jakar,ya karba yana gyara rufinta

"Ina kwana?" Ta fada tana russuna masa cikin girmamawa

"Lafiya lau baby,kin tashi lpy?"

"Lafiya uncle" ta amsa masa a narke tana karyar da wuya,ya gyara jakar yana mata duban tsakiyar ido,yana jin kamar ya jawota ya rungume cikin jikinsa,shi wani mutum ne da muddin yana so ba kasafai yake iya boyeshi ba,ba soyayyar mutum ba,soyayyar komai ma

"Ba wani matsala ko?" Kai ta gyada tana dan murmushi, idanunsa kawai sun wanke mata komai a ranta

"To shikenan sai na dawo"

"A dawo lafiya uncle,Allah ya tsare"

"Ameen babyn uncle" tsaiwar mashi cak sunan ya yiwa hafsat a tsakiyar ranta,wanann zallar iskanci ne da wulaqanci,a gabanta suke irin wadan nan abubuwan?,sai kawai tayi fuuuu tayi gaba,hakan ya bashi damar qarasa sallamarsa a nutse ya fice yana qorafin tayi masa qauro,ai ba irin wannan sallamar suka saba yi,tana ta masa dariya hadi dace masa aiba ranar girkinta bane,yayita juya zancan cikin ransa,wato har ta fara rarrabewa da wani girkinta da ba girkinta ba,yadan daki sitiyarin motar kadan,shikam wannan tafiyar da hafsat ta tauyeshi da yawa.

           Aikinta taci gaba da yi,saidai sanda ta shiga kitchen ta gane hafsat ta jiqa mata aiki,komai a qazance,sak dai yadda ta saba barin sassanta na bauchi,saita zage ta shiga gyara haiqan,wanda tun batayi nisa ba taji cikinta ya wani cure kamar an sakar mata dutse,ta miqe tana dora hannunta saman cikin,tana mamakin wani dan tudu da take iya ji cikin nata yayi,idan ta kalli kanta cikin madubi kuma bata iya ganin komai,saita koma da baya ta huta kadan sanann ta qarasa.

            Duka abinda akeyi hafsat tana falo ta kasa ta tsare,wata irin dakiya ce ta zoma widad din,bata fasa aikace aikacenta ba kamar yadda bata bi ta kanta ba,da taga bata ko lura da zamanta ba saita fara zirya tana qananun maganganu daga kitchen din zuwa falo,burinta yarinyar ta tanka,ta samu ta likideta ta fake sa rashin kunya tayi mata.

             Tana jiyo su mimi daga falo suna nemanta ta daka musu tsawa ta zaunar dasu waje daya,saida suka fara kukan yunwar da suka farka da ita sannan ta wuto kitchen din daukar musu abinci,sannan harta gama kintsa kitchen din,tana adana kayan cefanen da tun randa suka dawo hafsat din ta karbi girki abbas din yayosu masu yawan gaske,amma haka nan hafsat din ta barsu,komai saidai ta farka ta diba yadda ranta yakeso ta barshi a wajen,hatta da kayan miyansu haka ta wurgasj fridge babu gyara.

          Zuciya tazoma hafsat din iya wuya,me yarinyar ke nufi,duk abinda ta fita a girki ta barshi ta sauya masa fasali daga yadda yake wai ita zata karba girki,har tazo fita ta dawo baya a zafafe

"Ke nifa banason iyayin banza da wofi,duk kin kama abubuwa kin sauya musu waje kamar kinfi kowa iyawa?" Tana ware tomatoes din da suka lalace ta daga kai ta dubeta,ido tadan zuba mata ba tare da tace komai ba

"Dake nake magana kika zuban ido,ba zaki zo gidana kice zaki isheni da kinibibi bafa" sai a sannan ta janye idanunta,qasa qasa tace

"Gidanmu dai"

"Qunquni kikemin?,me kika ce?" Ta tambayeta a zafafe

"Gidanmu dai" ta amsa mata kai tsaye tana kallon qwayar idanunta.

          Wani abu ne ya saukar mata a kanta mai nauyi,mamaki yayi bala'in cikata,yanzu haka har tana da qwarin gwiwar maida mata magana haka kai tsaye?,lallai tayi sake,tayi kuma barci kwana biyu

"Zaizo me daure miki gindin ya gaya min idan shine ya gaya miki gidan nan kema gidanki ne" sai tayi gaba widad ta rakata da ido tana tabe baki,sai kuma ta gwada yadda tayi maganar sannan ta saki dariya,ita abinda ke bata mamaki,mummy hafsat din babba da ita,amma kullum aikinta tsaiwa taja magana tsakaninta da ita,taja tsaki tana sake tabe baki taci gaba da aikinta.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post