*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
A RUBUCE TAKE
(K'addarata)
Part 02
Page 09
Yana zaune saman kujera sanye da uniform din nan nasa dake qara masa kyau da kuma kwarjini,ko boots din qafarsa baikai ga cirewa ba,hafsat na tsaye daga gefansa,hannayenta goye a qirjinta,fushi ne kwance saman fuskarta.
Idanunshi a kanta,wani abu daya kasa tantance meye yana tsinkulin zuciyarsa,mabanbantan abubuwa guda biyu daketa faman gogayya da juna,har ta iso ta zauna gefan kujerar dake daura dashi tana masa sannu da zuwa.
"Me ya hadaki da hafsat.....har kikayi mata rashin kunya?" Maganar tazo mata a bazata,mamaki ya kamata,ta dubi hafsat din suka hada ido,sai hafsat din ta aike mata da saqon harara,ta daure ta shanye sanann tace
"Ni bansan yaushe nayi mata rashin kunya ba"
"Kina nufin bakisan maganar kayan da kika kwashe ba?" Ta tambayeta kamar wata diyar cikinta,sai abbas din ya daga mata hannu
"Ya isa.....me yasa kika kwashe kaya da aka dawo dasu daga laundry?" Cak ta tsaya ta zuba masa idanu,mamaki yana kasheta,duk yadda taso hana taruwar qwalla a idanunta amma ta gaza,saita gyada kai tana hadiye wani abu mai tauri daya tsaya mata,cikin rawar murya ta fara masa bayani
"Baba mai gadi ne ya kawo su,tana.bacci yace a kwashe maka kada yara su tattaka,don ma debe shine nayi laifi?,ina cewa kusan kaso uku cikin hudu na kayanka suna dakinta a wajenta,na taba magana?" Sosai ta taba zuciyarsa yadda hawaye ke sauka saman fuskarta,tana kuma maganar muryarta tana rawa cikin sautin kuka,yanason yace ta tashi taje,tayi dai dai amma kuma kamar ana ingiza zuciyarsa,kamar kuma ana hura masa bacin rai haka yakeji.
"Tashi kije ki debosu!" Yadan fada a kausashe,idanunta ta sanya cikin nasa mamaki yana sake daskarar da ita,totally uncle abbas din canzawa yakeyi cikin kwanakin,ba yau ya fara ba amma na yau yafi qona mata rai da tsaya mata a rai,ba yau ya fara ba,cikin kwanakin ko meye hafsat din tayi gaskiya yake bata,yana kuma qoqarin goyuwa da bayanta,sai ta miqe tsam cikin matsanancin bacin rai,ta dauke idanunta daga kansa ta maida ga hafsat,sai taga tuni yanayin fuskarta ya sauya zuwa madaukakin farinciki.
Janye idanunta tayi daga kan fuskokinsu gaba daya,ta kuma juya da sauri ta nufi dakinta, abbas ya rakata da idanu yana jin kamar ya bita amma kuma wata zuciyar na gaya masa yayi dai dai,sai yaci gaba da kallon qofar da kuma tsammanin fitowarta.
Cikin bacin rai ta fara tattara dukka wani abu da tasan nashi ne cikin daki,bata bar komai ba koda kuwa agogo ne,tana hade kayan hawaye na fita a idanunta,ta tsani rashin gaskiya,ta tsani a bata rashin gaskiya a rayuwar ta,ta tsani batayi abu ba ace tayi,tana jin kamar ta mutu idan akayi mata haka.
Debo kayan ta fara yi hannu bibbiyu,ba ruwa ta da wadanda suke zubewa ta riqosu zuwa falon,tana zuwa batayi wata wata ba ta watsar dasu a wajen ta juya da sauri taci gaba da debo sauran tana zubarwa a wajen,ran hafsat ya sosu sosai,wanne irin raini ne wannan?,ta tsammaci zaice wani abu,sai taga bai ko motsa ba yana kallonta ne kawai,yana karantar zallar fushin dake fuskarta,wanda bai taba ganin irinsa ba a tattare da ita ba
"Wai baka ganin abinda yarinyar nan takeyi?,kaga fa yadda take watso mana kaya?" Maganartata yayi da gama kwaso kayan,ta juya abinta da nufin komawa dakinta
"Widad" ya kirata a tausashe,bata ko waiwayo ba bare ta saurareshi,don kuka takeyi sosai ta wuce daki abinta.
Cikin qarfin ikon Allah ya miqe da wani irin zafin nama,zuciyarsa yaji kamar zata fashe da kukan da widad din keyi,ya tuna meye a jikinta,ta yaya zai barta tana irin wannan kukan?,sai ya nufi dakin da wani irin sauri wanda yasa hafsat ta zaci zuwa zaiyi yayi maganinta,ya dauki mataki akan abinda tayin yanzu,don haka ta saki wata qaramar dariya cikin nishadi da jin dadi,ta tako cikin rashin damuwa ta fara tsince kayan tana dibansu zuwa dakinta,sai a sanann ta lura da mimi dake sharar qwalla
"Ubanki kike a wajen?,wato an saka uwarki kuka shine kikazo kika rabe a nan kina naki kukan,zaki tashi ki wuce ciki ko sai nayi ball dake?" Ba shiri yarinyar ta zame ta wuce daki tana tura baki gaba hadi da ci gaba da goge qwalla.
Rub da ciki takeso tayi kukanta yadda takeso ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma tudun da takeji a cikinta ya hana,dole sai saman pillow ta dora fuskarta tana sakin kuka sosai.
Jiki a matuqar sanyaye ya qarasa shigowa dakin,sai ya kasa qarasowa ya tsaya daga bakin qofa yana kallonta,shi kansa baisan me yake damunsa ba,baisan me yasa yake wasu abubuwan ba,duk da abinda yakeyi din bata taba nuna damuwarta ba,koda ta nuna mintuna kadan take sakin fuskarta kamar ba'a yi ba,sai ayau data nuna fushinta har haka.
A nutse ya qaraso ya zauna gefanta,tunda ya buda mata qofar daki tana jinsa amma bata nuna tasan da shigowarsa bama,hannu yasa a tausashe ya zare pillow din ya maye gurbinsa da tattausan tafin hannunsa,sai tayi saurin kawar da fuskarta daga wajen kamar ya dora mata wuta,yasan halin kayarsa,ta iya rigima a duk sanda taso ko aka tabota,don haka yayi amfani da dukka qarfinsa ya azata saman jikinsa.
Dukka qarfinta ta sanya ta zame a jikinsa,bai gaji ba ya sake maidota yana kiran sunanta tare da qoqarin son su hada idanu amma taqi bashi wannan damar.
Kin zama tayi bare ta saurareshi ba,haka ya gaji da son yin magana da ita ya haqura ya fice yana sauke ajiyar zuciya,ransa gaba daya a jagule babu dadi.
Da kanta ta lallashi kanta,saidai a ranar ta yiwa kanta hukunci qauracewa abbas din da dukka abinda ya shafi hafsat dama cikin gidan,ba zata iya gani ba bazata iya jura ba,duk jarumtar ta abun ya taba ranta,tana iya bakin qoqarin bashi farinciki da son ganin walwala da nutsuwarsa.....gefe guda yana bawa hafsat go ahead tayi duk abinda yake shine dai dai,yana kuma mara mata baya,ta yaya ita tata zuciyar zata samu nutsuwar bashi nutsuwa?.
Washegari ranar girkinta ne,tun safe tana kwance a dakinta wanda tun dare ta saka muqulli ta rufe abinta,tana da abubuwan ciye ciye da yawa a dakinta da bata rabo dasu,don a lokacin abbas da ya shafe babin fita da iyalinsa zuwa wasu guraren shaqatawa a baya,a yanzu widad din ta dawo masa da wannan dabi'a tasa,ko rana daya hafsat din bata taba yunqurin binsu ba,sai mugun haushi da takaicin da take fama dashi,har zuwa sanda zasu dawo cikin gidan,takan ce ita tafi qarfin zuwa nan wajen.
Zamu iya cewa borin kunya ne takeyi,don tun sand yake marmarin kaita take watsa masa qasa a ido,take nuna tafi qaunar ya bata abinda za'a kashe a wajen ta adana,har abun ya fita a kansa,ko ssnda ta haifi su mimi yana son kaisu amma bai samu wannan qwarin gwiwa daga wajenta ba,don haka sai a jima bai fita da yaran ba sai sanda ya samu hutu mai tsaho,gaba daya ita din opposition na rayuwarsa ne totally,bata kuma taba sawa a ranta ta sauya wani tsari yanayi hali ko dabi'a tata saboda shi ba,saboda a samu dai daito da zama me dorewa.
Tana jin motsinsu daga parlor din amma bata ko motsa ba bare tayi yunqurin fitowa,ciye ciyen da tayi a daki ya dauketa fes,don dama bata iya cin abinci me yawa,yana zaune dining area amma hankalinsa yana kan qofar dakinta,jiya da abun ya kwana dashi ya tashi,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin mantar dashi da wasu salo da sam baibi jikinta ba bare ya dace da ita,don ba dabi'arta bane.
Ya kammala shan tea din da babu qamshin komai a ciki saina Lipton da milo,ya ajjiye cup din ya miqe yana sauka daga wajen,hafsat din na zaune tana kallonsa batace komai ba,tanason ganin ya za'a qare,ya isa qofar dakin nata ya tsaya a nutse ya fara knocking yana amsa wayar data shigo masa a lokacin.
Taso ta shareshi taqi bude qofar,saboda Wani mugun zafinsa da takeji har cikin ranta,amma sai taga hakan bai kamata ba,tunda tasan a lokacin kowa yana parlor,ta kuma tabbatar hafsat din tana ganin komai da zai faru,don haka ba'a son ranta ba ta miqe a hankali tana gyara zaman yaloluwar rigar jikinta ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofar.
Tana bude masa ta saki qofar ta koma,yabi bayanta da kallo tsigar jikinsa tana zubawa,ko kadan baya gajiya da ita,baya qosawa da ita,kwanaki biyun da basu tare mugun yunwar ta yakeyi,yaci gaba da kallonta yana dan hangen cikinta daya turo kadan,wanda sai ka saka ido da tsananin kula zaka iya ganinsa.
Guri ta samu ta zauna ta gaidashi ba tare data kalli fuskarsa ba,yanata qoqarin su hada ido amma taqi
"Ya jikin naki?"
"Lafiyata qalau" ta amsa masa a shashance,ya sake duban fuskarta sosai yadda taketa basarwa,sai ya ajjiye mata kudin cefane yayi mata sallama ya fice.
Dashi da kudin gaba daya tabi da kallo, zuciyarta ta tsinke kuka yaso qwace mata amma ta danne,ta kalli agogo sannan ta miqe ta shiga bandaki ta watsa ruwa,ta fito taa shirya cikin dinkin doguwar ruga bubu gown ta yane kanta da madaidaicin mayafi ba tare data daura dankwali ba,fuskarta tayi kyau,ta sake wani fresh da haske mai daukan idanu,inda ya ajjiye kudin cefanen ta isa ta dauki kudin,sannan ta qarasa inda wayarta take ita dauketa tare da daukan wasu abubuwan masu amfani sannan ta fito falon.
Babu kowa,sai ta zarce kitchen,ta dan samu abinda zataci wanda bazai mata wahalar narkewa ba,don yanzun matsalar da take fama da ita kenan.
Ta gama ta dauraye cup din ta maidashi inda ta dauko tana kallon yadda kitchen din ya hargitse,kamar ba kwanaki biyu baya ya koma hannun hafsat din komai fes bisa tsari,saika dauka watanni aka dauka ba'a gyarashi ba.
Baki ta tabe ta fice abinta,yau daga kitchen din har Parlor din babu inda zata sama hannu,itama tasan dadin jikinta,kawai dai tanayin komai ne don samun walwala da nutsuwarsa,tunda ta fuskanci babu abinda ke daga masa hankali a rayuwa irin qazanta,amma tunda bai gani itama ba zata dinga wahalar da rayuwarta ba,zata barsu shida hafsat din tasa.
Tana isowa falon sukaci karo da mimi
"Ina kwana anty?"
"Oyoyo mimin daddy,kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau anty,yau duka baki fito ba"
"Banajin dadi ne,ungo wannan ki kaima mommynki kice kudin cefane ne inji ni" ta hada dukka kudin da abbas din ya bata ta sanyashi a hannun mimi,sai da taga ta shiga dakin sannan ta fice abinta harabar gidan.
Kai tsaye boys quaters ta nufa wajen maari matar baba mai gadi,sosai taji dadin ganinta kuwa,don bata taba zuwan mata ba,ko yaushe widad din tafi ganewa zamanta daki tayi kallo ko chart,ta marabceta sosai suka fara dan taba hira,tun widad din bata sake ba har ta saki jikinta suka shiga hira sosai,kasancewar hajiyan bata nan,babu wani aiki cikin gidan haka suka wuni tare.
Maari din saita tuna mata da latifanta,cikin awanni kadan ta gane tana da kirki matuqa da jan mutum ajiki,har tafi tsohuwar me aikin hajiyan data dinga tayata kwana sanda abbas yake tafiya bauchi ba tare da ita ba.
Tayi musu faten tsakin masara da yasha gyada da yakuwa,batayi zaton zata iya ci ba,sai gashi taci sosai sunata hira,kirkin widad da yadda take girmama kowa cikin rashin nuna qyama ya sanya maari ma taji ta shiga ranta,ba kamar hafsat din ba,dake dagawa izgilanci da wulaqanta na qasa da ita.
Hafsat na tsaka da barci taji mimi na qwala mata kira saman kanta,da qyar ta bude idonta tana jan mugun tsaki,kafin daga bisani kuma ta buda hancinta sosai saboda warin bayan gida da take jiyowa,dole ta wartsake ta miqe sosai ta zauna tana duban mimi
"Ban hanaki idan ina bacci ki dinga tashina ba don ubanki?" Kebe fuska yarinyar tayi kamar zata saki kuka
"Ai ban tasheki ba harma su nawwara sukayi kashi,yanzunma anty ce tace na kawo miki kudin cefane"
"Kudin cefane kuma?"ta tambayeta da mamaki,saita jinjina kai,ta miqa mata hannu ta saka mata kudin,ta waresu tana irgawa.
To me yarinyar take nufi?,nufinta ta ajjiye girki kenan saboda abinda ya faru jiya?,aiko ba zata sabu ba,ita dinma ai ba jaka bace da zata zauna tayita girka musu suna ci.