Daudar Gora book 2 page 53

Daudar Gora book 2 page 53

Daudar Gora book 2 page 53

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (53)

.........Wata shegiyar dariya ya saki idanunsa kan takardar da aka aiko masa ta sake zaman shari'ar yau. Ya kai hannu ya yarce ruwan wankan dake kan goshinsa zuwa fuska. Tun safiyar jiya basa gidan shi da Miran Jasim. Sai yau ne shi yake dawowa Miran Jasim kuma da daddare. 

        Wayar landline dake gefe gadonsa ya ɗauka, yay yan danne-danne yana da ga tsayen da yake. Ana ɗauka ya kwashe da dariya, sai kuma ya kai zaune a bakin gado. “Yaya dai kawun mai shari'a kaima an kawo maka takardar ne?”.

      Wani irin shegen tsaki Miran Jasim yaja da ga can. Ya ce, “Bar wawa ɗan wahala mana. Shifa gani yake kamar ya wani kai anan. Muje zuwa idan ya isa sake zaman wata shari'ar da ga wannan. Zamuyi maganinsa ne shida shegiyar yarinyar nan mai bakin akkunaye”.

          Sake kwashewa da dariya Miran Arshaan yayi, tare da faɗin, “Ai boka ɗan gurguzu yayi, tunda muka fita muka dawo masarautar nan babu wani shege da yay magana shima bai isa yinta ba yau”.

      Dariya suka kwashe da ita a tare kamar wasu mahaukata.....       _Tofa, mi Fir'auna da hamana suka shiryo ne haka🥱😂🚴🚴🚴🚴_


★★......


       Yau kam a tare suka fito zuwa dining room. Amintaccensa ya zube kansa a ƙasa yana gaishesu cike da girmama. Iffah ce kawai ta amsa masa cikin kulawa. Gogan nata kam lips kawai ya motsa ya wuce abinsa. Da kansa ya ja mata kujera, itama sai ta ja masa tana kallonsa da murmushi. Shi dai bai murmushin ba, amma ya juya idanu cike da salon birgewa. Koda amintaccensa ya taso domin haɗa masa abinci kamar yanda ya saba dakatar da shi tai. Sai ma ta sallamesa akan yaje idan sun kammala sai ya dawo. 

        Sai da ta gama bubbuɗe duk kwanikan wajen sannan ta kallesa alamar mi yake so? Kaifafan idanun nan nasa ya zuba mata, sai kuma ya ɗaga yatsarsa manuniya a hankali ya nuna ta. Baki ta tura gaba tana wani kyaf-kyaf da idanu. “Ni abinci nace fa”. Yanda tai ɗin sai ya bashi dariya. Amma sai ya gimtse abarsa ya ɗauke kai. Itama sai ta taɓe baki ta ɗauke nata kan ɗan ta fahimci yau kuma yan mislinacin ne da mulki a kansa. Zaɓar abinda taji tana so a ranta tai kawai ta zuba musu ta ajiye komai gabansa da faɗin bismillah. Abincin kawai ya zubama ido yana jinsa wani daban yau ɗin. A da sai dai amintaccensa ya haɗa masa, yau kuma gashi matarsa ce, abinda ya jima yana mafarki. Rayuwa kenan mai farko da ƙarshe.

        A nutse suka fara cin abincin, Iffah na satar kallonsa da jinjina mulki da ƙasaita. Yanda yake cin abincin ma kansa abin birgewa ne. Suna gab da kammalawa kanta yay wani irin sara mata. Da sauri ta kai hannu ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Kallonta yay shima da mamaki, sai kuma ya riƙo hanunta da ta dafe kan da shi. Ɗago idanunta da sukai wani irin jajaja cikin ƙanƙanin lokaci tai ta kallesa. Shi har sai da ma yaji tsigar jikinsa ya tashi, amma sai ya dake kasancewar shima akwai nasa abebaɗan a kansa. Da ido ya mata alamar minene? Dan da gaske yau miskilancin ne a kusa. Ji yake motsa lips ɗin ma yay magana babban aiki ne. 

         A hankali ta furta, “Kaina ke ɗan mun ciwo”.

     “Tun yaushe?”.

  Ya faɗa a fusge. “Da safen nan ne fa. Amma ba wani ya matsa bane karka damu. Dan ALLAH ka barni na fara tafiya kotun nan sai kai kuma ka taho da ga baya”. 

       Idanu kawai ya tsira mata. Ita kuma ta langaɓe kai gefe alamar roƙo. Ɗauke idonsa yay kawai da ga kanta batare da ya ce komai ba. Ya jima yana zargin akwai junnu a jikin yarinyar nan, yanzun ma kuma abinda yake zargin kenan. (Ya arrahaman, komai na yarinyar nan sake sakashi a ruɗani yake). Sai kuma maganar data faɗa masan yanzu ta shiga masa kaikawo a rai. Ya barta ta fara yin gaba kafin shi na nufin akwai wani abu kenan. Shikam yaga takansa da waɗan nan ahali nashi. Wani abu kenan wani ya sake masa ko kuma dai aljanun nata ne ke neman raina masa hankali. Cikin rashin bama abin muhimmanci ya cigaba da cin abincinsa, sai dai kuma abinda ta faɗa kuma ya faru a wacan ranar na masa kaikawo. Iffah dake binsa da kallo kamar zatai magana sai kuma ta haɗiye kayarta tana sakin nannauyar ajiyar zuciya da jan jikinta baya.

        Komai baice mata ba, sai da yaga ta miƙe. A can ƙasan maƙoshi ya furta “Ina zuwa?”.

     Agogo ta nuna masa. Kallon agogon yay ya ɗauke ido. Batare da ya sake kallonta ba ya ce, “Kina buƙatar masu rakkiya ne?”.

         “A'a”.

     Ta bashi amsa a taƙaice. 

“Amma kin san bazai yuwu kije ke kaɗai ba. Kije akwai masu jiranki a can ƙasa”.

            “Nagode”.

       Da kallo kawai ya bita ganin yanda ta sauya lokaci guda. Ga fuska ta wani ɗaure tamau babu alamar wasa. Shi sai ma ya fara jin ko dai itace aljanar da kanta.


     ★Yau kam da alama shari'ar zatai zafi. Dan kotun tacika fiye da zaton mai hasashe. Abinda kuma zai birgeka duk ahalin masarautar ne. Cikin wani irin takun ƙasaita da izza da ya jawo hankalin duk wanda ke cikin kotun Iffah ta shigo da shi. Ga hadimai na take mata baya. Tayi matuƙar ƙyau cikin shigar jikinta, ga wani irin ƙyawu da fuskarta ta ƙara sai shining takeyi fiye da hasken tauraruwa zarah. A zahiri ita tafiyarta takeyi normal, amma ga masu kallonta babu abinda suke gani tattare da ita sai tsantsar izza mai ban mamaki. Wani abin birgewa da tai ya ƙayatar da wasu a wajen shine kai tsaye inda Malikat Haseenat take ta nufa. Takai ƙasa cike da girmamawa ta kamo hanunta ta sumbata, kafin ta gaisheta. Malikat Haseenat da itama abinda Iffah tai yay matuƙar tafiya da ita fuskarta ɗauke da murmushi ta ɗaura hanunta bisa kanta tana amsa mata da tsantsar so da ƙauna da kulawa, tare da sanya mata albarka.

        Juyawa tai gaban Daneen Ammarah da ke gefen Mammah ɗin itama ta gaidata, kafin ta sake juyowa gaban Malikat Bushirat itama ta gaidata. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Iffah ta sakar mata wani makirin murmushi da ɗan kashe mata ido ɗaya. Batare da tako kalla su Malikat Ashwaq da ke binta da wani shegen kallo ba ta miƙe abinta. Kujerar da Sayeed Hanifud-Din ya nuna mata ta nufa cikin irin takun data shigo da shi tana ɗan satar kallon sashen da su Miran Jasim ke zaune har yanzu wuyarsa da abu. Wani malalacin murmushi suma ta sakar musu tana kaiwa zauna babu alamar wata damuwa tattare da ita. 

         (Zakici ubanki ne da ga yau shegiya) Miran Arshaan ya faɗa a zuciyarsa yana hararta. Sarai Iffah taga hararar, dan haka tai ɗan murmushi, a zuciyarta ta ce, (kwantar da hankalinka ban iso kanka ba ai ɗan kaɗafi). Miran Jasim kam idanu ya lumshe wani abu na tsarga masa game da Iffah. Shi kam dai yana matuƙar kwaɗayin yarinyar nan, duk da babu wanda ya tsana yanzu bayan Tajwar Eshaan da Malikat Haseenat sama da ita a duniya.....

   

      Shigowar mai gayya mai aiki tasa tunaninsa katsewa.. a take kotun tai tsitt kowa ya miƙe domin girmamawa. Taku yake cikin tsantsar ƙasaita da izza data zame masa jinin jiki. Ga wani irin kamshinsa mai kaɗa zuciyar mai shaƙa na tashi. Yammatan wajen da suka daɗe da folawa a sonsa tuni zukatansu suka shigar narkewa, duk da babu abinda ake gani bayyane a fuskarsa. Dan ya sakayata hatta da idanunsa saye suke cikin eyeglasses dake nuna blue da ga waje. Addu'ar neman tsarin ALLAH da ga duk wani abin cutarwa ya karanto lokacin da yake kaiwa zaune a hadaddiyar kujerar da ke a mallakin zamansa. Ya ɗan saci kallon sashin da yake tunanin ganinta. Tana a wajen kuwa, sai dai abin mamaki ita sam bama shi ɗin take kallo ba. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke a hankali wadda ko amintaccensa da ke gefensa da masu tsaro guda huɗu haggu da damansa basu isa ji ba.

      Bayan an tabbatar da kowa ya natsa Sayeed Hanifud-Din ya miƙe ya dubi jama'a. “Alhamdullahi muna godiya ga ALLAH da ya sake dawo damu zama na uku akan wannan shari'a. A zaman daya gabata wadda ake ƙara ta amsa laifinta, sai dai ta Bama wannan kotu mai adalci damar bincike mai zurfi akan tushen samuwar madara data shayar da adalin shugaba na wannan daula. Inda wannan kotu mai adalci ta amshi ƙorafinta har ta bada dama ga masu bincike. Matsala ta ratsa ta yunƙurin son halaka Zawjata-almilk da akai, inda dalilin haka aka samu tazarar ɗaga wannan zama har sai da ta samu lafiya. To yanzu dai alhmdllh, wannan zama a wannan gaɓar duka zai ta'allaka ne ga jin bayani da ga bakin shugaban jami'ai da aka danƙa wannan bincike garesa. Shugaban jami'ai bismillah”.

        Sai da ya miƙa gaisuwa ga Shahan-shan cike da girmamawa kafin ya juya ga jama'a. “Assalamu alaikum kamar yanda aka bamu damar bincike a gaban wannan kotu mai adalci mun gudanar. Mun bibiyi tushen samuwar madara da kaita sashen Zawjata-almilk. Inda bincikenmu kuma ya kaimu har ga wanda ya shigo da wannan madara mai ɗauke da dafin macizai a ciki. Karna cikaku da surutu waƙa bakin mai ita tafi daɗi. Ina roƙon alfarmar wannan kotu da ta bani damar gabatar da Dafiq ibn Ghalib a gabanta”.

       “An baka”.

   Cewar Sayeed Hanifud-Din. 

Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai suka saki murmushi. Sai kuma sukai saurin duban wanda jami'ai ke ƙoƙarin shigowa da shi ƙirazansu na wani irin mummunan harbawa. Ƙoƙarin miƙewa Miran Arshaan yayi da sauri Miran Jasim ya danne masa hannu jikinsa na rawa. Iffah da ke kallonsu ta saki murmushi, cikin Sa'a kuwa suka haɗa ido da Miran Jasim. Ido ɗaya ta kashe masa da ɗauke kanta tana ɗan wani cizar lips cike da salo.

      Dattijo da jami'ai suka shigo da shi bazai wuce shekaru hamsin da takwas a duniya ba. Cikin nutsuwa ya gurfana gaban Shahan-shan yay gaisuwa, bai ko motsa ba da ga zaman ƙasaitarsa. Dattijo Dafiq ibn Ghalib ya gyara tsaiwarsa yana fuskantar kotu. Dubansa Sayeed Hanifud-Din yayi ya ce, “Dattijo waye kai?”.

     Cikin ɗan rawar harshe ya ce, “Dafiq ibn Ghalib. Ni masanine akan macizai. Ina zaune a ƙauyen Bansh”.

   “Miye alaƙarka da daular ruman?”.

    “Alakata da Daula ruman alakace irin ta kowanne ɗan ƙasa. Wato fadan shugaban ƙasata adali”.

              “Amma duk da haka ka iya bada dafin macizan da za'a cutar da shi?”. 

        “Ko kusa ba haka bane, ko wani naga zai cutar da hadimin wannan daula bama shugabana ba sai inda ƙarfina ya ƙare ai. Ni dai a ranar daren wata laraba wani bawan ALLAH ya sameni akan shi ɗin jami'in ne na hukumar bincike akan sanin nau'in dabbobi masu dafi. Yazo kuma wajena ne da buƙatar samun kalolin dafin macizai zaiyi bincike a kansu. Da farko naso naƙi, dan nasan dan adam na wannan duniyar ba abin yarda bane. Amma sai ya nuna min katin shaidar aikinsa. Hakan yasa na yarda da shi na ɗauka na bashi”.........✍️   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post