Daudar Gora book 2 page 6

Daudar Gora book 2 page 6

 

Daudar Gora book 2 page 6

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      



  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)




            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻




𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (06)




........Sir Fawzan na ɗaya da ga cikin waɗanda suka tsinta kansu a wannan razanin. Hakama Azaan da Fhakir da suka kasance yaransa da duk inda ya saka ƙafa a ɓoyayyen yanayinsa suna biye batare da sun san ainahin wanene shi ɗin ba. Ire-irensu nada yawa da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ya mu'amulanta ta fuskoki daban-daban na alkairinsa da bibiyar al'amarin al'ummar ƙasar tasa batare da sun sani ba sai a yau da ya bayyana kansa a zahirinsa garesu.....


         ★★..... 


   A cikin masarauta wannan al'amari daya jagoranci motsin ƙasar a yau ya matuƙar sakasu a rudani da firgici, dan da gasken gaske Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ya musu duka irin na bayan ƙeya na cikin duhuwar da ko zaka tsinke wuyanka dan waige bazaka iya hango wanda zai maka ba sai bayan yayi idan yaso. Hankula da damar gaske sun tashi, irin tashin da sukejin ko wuta aka nuna musu zasu iya jagorantar jefa Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin a yau. 

     Shi mai mulki ne, mulkin kuma shine abin baƙin cikin mafi yawansu. Su da shi duk suna gwagwarmaya ne akan waɗanda yake mulka ne. Sai dai su ƙoƙarin wargaza kansu suke yi masa bore domin cikar burikansu, shi kuma son dunkulesu yake domin sauke nauyinsu da ALLAH ya daura masa duk da kasancewarsa mai shekarun da har yanzu basu cimma arba'in ba a duniya...


     Abinda zai sake birgeka ga wannan bawan ALLAH tun da ya gama fuskantar al'ummar sa babu wanda ya sake jin wani motsinsa a wannan dare sai likitocin da ke zagaye da shi, wanda a yau zasu masa aikin da ya rage insha ALLAHU kamar yanda ya buƙata......


       ★★..... ★......


   

    Duk jarumtarta da juriya a wannan gaɓar sai da nakasun ƙaddara ya kaita ƙasa. Ƙarancin cin abincinta da tsantsar damuwar da suka zame mata abokan rayuwa sun mata illa matuƙa. Ta fita a hayyacinta sosai tamkar ba Iffahr nan ba ƴar gayu mai bakin da kadata sai wanda ya gawurta. Duk da ƙarfinta ya ƙare, rashin yaƙinin cigaba da rayuwa bai sa ta sallama ba akan burin maida fansar ta ga su Miran Jasim. Babban burin da take fata a yanzu koda bayan ranta shine al'ummar ƙasar ruman su kasance masu tsananta bincike wajen sanin ainahin Tajwar Eshaan bin Haysam Abdul-majeed a zahirinsa da baɗininsa. Duhuwar ƙaddara da bin makauniyar hanya sun haska mata wasu muhimman abubuwa a wannan tafiyar, sai dai kash ita tata tazo ƙarshe, labarinta ya zama tarihi a gaɓar daya kamata ace itace mai rubuta tarihin abinda ya kasance burinta da sadakarwata. 

        Ta saki wani murmushi mai wahalar fassara ga wanda ya santa sakamakon ƙamshin turaren data ɗauka tsahon mintuna tana shaƙa a dinɗaɗɗen ɗakin kurkukun da take da yaƙinin yafi na kowa matsi da tsauri, sannan ita kaɗai ce mutum mai numfashi a wajen sai ko dakarun da ke zagaye da ita da sunan tsaro....


       (Kowanene Iffahn ta shin shino haka kuma? Ta hanyar turarensa, da alama dai wanda ta sani ne ko take hasashe🚶).

      

     Batai yunƙurin buɗe idanunta ba kamar yanda bata motsa ba. Ɗakin ya cigaba da zama shiru babu alamar wanda ke tare da itan zai tanka har tsahon wasu mintuna data fara jin gundira da kasancewar koma waye a tare da itan. Sai dai kuma da alama akwai wani farin ciki, dake kokawa da gargaɗin ba haka bane a tattare da yaƙininta. Kunya da tunanin idon da zata iya kallonsa in har ma shi ɗinne yasa taji bazata iya ɗagawa ta tabbatar ba. Duk da duhun ɗakin hasken dake leƙowa ta mitsitsin windown da wutar lantarkin waje ta hasko ya taimaka wajen ganin wanda ke zaunen. Sanye yake da kaya baƙaƙe hatta da yatsun hanunsa a cikin safar hannu suke. Fuskarsa kam na sakaye da norse mask daya sakaya ainahinsa, sai baƙin gilashi daya ɓoye idanunsa. Ga mutum mai hangen nesa da ilimin saurin ɗaukar haske kan abu zai kira kowanene da mace, dan ƙira da dirin jiki sam basuyi kama dana namiji ba duk da akwai maza masu ƙarancin girma ta ɗa namiji. Babu alamar damuwa da rashin ɗagowar Iffahr da ta tasa gaba ta na kallo, haka suke sake shanye adadin wasu mintunan babu alamar nuna gundira duk da kuwa tsakkiyar dare ne da shiru ɗin masarautar zai iya tabbatar maka da haka kai tsaye. Da alamar jiran cikar lokaci aka kai duba ga agogon dake a tsintsiyar hannu, batare da cewa komai ba akai saurin ɗaga yatsu biyu ga wanda ke baya tsaye da babu tantama shikam namiji ne. Cikin gyaɗa kawai ya zaro syringe dake jikinsa mai ɗauke da ruwan allura ya nufi Iffah da har yanzu bata ɗago ba, babu ma alamar zata ɗago ɗin. Zabura tayi da ƙoƙarin son sakin ƙara sakamakon jin saukar ƙarfen allura ta kusa da gefen wuyanta da ke tsakani da kafaɗa. Abinda aka manne bakinta da shi ya hana fitar ƙarar, cikin abinda kuma bai wuce mintuna uku ba sun fice dai-dai da shaƙar wani ɓoyayyen ƙamshi daya bambanta dana farkon data fara shaƙa data gama hasashen mai shi. Sai dai na yanzu ya sake tabbatar mata da an yaudareta da ƙamshin ne kawai ba Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin bane......


      Kammala theatre ɗin Tajwar Eshaan dai-dai da fiddo Iffah da mintuna kaɗan baya aka farga da halin da take a ciki ta dalilin jami'an dake zagayata a kowane dare domin tabbatar da lafiyarta bisa umarnin Malikat Haseenat. Da farko su sunma zata ta mutu ne, ruɗewarsu da kururuwarsu taja hankalin jami'an dake zagaye da sauran ɗakunan masu laifin dan waɗanda ke zagaye da Iffar har su huɗe duk suna zube alamar akwai abinda aka shaƙa musu suma. Sunyi gaggawar sanar da halin da take a ciki, cikin ƙankanin lokaci ƙwararren likitan dake a clinic ɗin masarautar ya isa gareta, sai dai a take ya fahimci abin babban al'amari ne, dan haka shima ya tabbatar da dubata bazai yiwu ba anan. Kai tsaye Malikat Haseenat ta bada umarni ɗaukarta zuwa clinic ɗin.

       An isa da Iffah clinic hankali tashe, yayinda likitoci suka rufu a kanta, sai dai abin mamaki iya bincike har na kusan awanni biyar basu gano komai ba, gata kuma a sanƙare babu inda ke motsi a jikinta sai bugun zuciyarta da na fitar numfashi kawai. Hatta abincin da aka kai mata a daren ranar dana safiyar duk anyi bincike kansa babu komai da aka zuba wanda zargin kowa ya karkata akai. Tofa wannan al'amari yazo da wani sabon hargitsi da yafi na lokacin Tajwar Eshaan, dan fa a wannan karon zukatan jama'ar masarautar ma kansu da bakunansu sun fara karkata da wani abu daban mai nuni da (anya kuwa babu wata a ƙasa?).

      Wannan kalma tayi wata irin amsa kuwa ga mafi rinjayen al'ummar cikin masarautar da zuwa yanzu komai yaje ga kowa. Dama gasu a cikin wata ɗimuwar da aketa faman ka-ce-na-ce da babu alamar zai ƙare anan kusa...


     (🤔nifa gaskiya🥱, tom🤫 bara dai nayi shiru🤭).


★★.....

    

     An sake wayar gari dai cikin tashin hankalin yanayin da Iffahr ke ciki wanda hankulan mutane suka rabu biyu. Dan duk yanda ake ƙunshe maganar a iya masarauta a washe garin sai da tai amsa kuwwa matuƙa a kafafen ƴa labarai dama na social media fiye da tsammani. Anan ne fa kowa ya shiga ƙara tofa albarkacin bakinsa. Malikat Haseenat tsohuwar alkairi, duk da abinda Iffah ta aikata ga jikanta ta kasance a jerin farko na masu zuwa su dubata bisa jagorancin Daneen Ammarah. Hankalinta ya matuƙar tashi, a take tausayin nan nata da zinariyar zuciya suka motsa ta nema ganawa da likitocin dake tsaye akan Iffahr. Sunyi zaman tattaunawa na kusan awa ɗaya, ƴan son suji mi zaman ya ƙunsa tuni sun baza hadimansu ƴan leƙen asiri, sai dai kuma basu sami damar jin mi'aka tattauna ɗin ba, sai labarin zuwan ƙwararren likitan da ake da yaƙinin yana da ilimi akan al'amarin na Iffah daga ƙetare domin dubata tunda su likitocin na nan sun kasa fahimtar komai, dan hatta da likitoci uku ƙwararru da suka zo daga baya suma basu iya yin komai ba a kai. Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara shirye-shirye zuwan doctor, abinka da masu ƙasa cikin abinda bai gaza awanni goma sha biyar ba komai ya kammala doctor ya iso.

        A wannan karon Daneen Ammarah ce tsaye kan komai, hakan sai ya bama Miran Jasim da Miran Arshaan damar kafa wasu ƴan ƙananun magana ga su Jasrah dangin Malikat Bushirat, acewarsu Daneen Ammarah ta nuna damuwa akan bare wadda ta shirya halaka musu jininsu, har takai wasu ma na danganta halin da Tajwar Eshaan ɗin ke ciki da ita har ma da Malikat Haseenat da wasu maganganun kan koma cikin kunenta amma tai kunnen uwar shegu....

     

★★★.......


      Ƙwararrun likitoci kuma manya ne suka rufu kan Iffah na tsahon lokaci. A ranar dai basu cema kowa komai dan gane da al'amarin nata ba, sai dai Daneen Ammarah nata ƙoƙarin ganin ta kwantar da hankalin Malikat Haseenat dake kiransu akai-akai dan hankalin tsohuwar da gaske a tashe yake, tashin hankalin da kowa ya gagara bama fassarar dalilinsa a gareta. Duk da a wannan ranar basu sami damar sake ganinta ba hankalinsu ya ɗan kwanta da ganin jikin Tajwar Eshaan yayi ƙyau shi kuma Alhamdullah, dan zuwa dare a bisa jagorancin likitansa doctor Afif sun sami shiga ɗakin da yake. Duk da bai furta da baki ba alamu sun nuna yayi farin ciki da ganin Daneen Ammarah ɗin, haka itama har da hawayenta na farin ciki ta kumayi sujudar shukur na nuna godiyar ta ga ALLAH. Baiyi magana akan Iffah ba, itama kuma batai masa ba duk da tanada tabbacin komai dake faruwa a masarautar yana zuwa masa kasanwar tun a safiyar yau ɗin ya farka kuma likitoci sun tabbatar da nasarar da aka samu kan aikin da akai masan a daren na jiya.........✍️







   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post