Daudar Gora Book 2 page 60

Daudar Gora Book 2 page 60

Daudar Gora Book 2 page 60

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (60)

.......“An haifi ciki lafiya, kuma ɗa namiji sanɓalele da yaci suna *_Eshaan_*, Eshaan ƙyaƙyƙyawan yaro mai lafiya da ban sha'awa ga kowa, ga shiga rai. Wata irin makauniyar soyayya Bushirat ke nuna masa har takai Ni kaina sai nayi da gaske nake ganinsa, hakan da take yasa Waheeda yimata tas kafin ta ɗan canja aka dinga kawomin shi nan. Ya taso yaro mai wayo, miskili da baka iya gane abinda yake so ko baya so sam. Shi ko irin abokan wasan nan na ƙuruciya Eshaan bayayi, yafi so ya zauna shi kaɗai shiru ko yayta karance-karancen abubuwa musamman na litattafan tarihin wannan daula da suka shuɗe. Sai dai yana matuƙar son wasan doki da basket ball, da wasan takobi, idan kuma yana tare da Kakansa ko mahaifinsa zaki dingajin maganarsa ko babu yawa. Al'adar wannan masarauta da Miran mai jiran gado ya kai shekaru bakwai zuwa goma ake kaishi can wani ɓoyayyen waje ya rayu har sai girmansa, ko kuma sarki ya zaɓi murabus kafin ya mutu shi ya ɗaurasa, idan kuma bazaiyi murabus ba za'a dawo da shi cikin masarauta da iyalansa dan su basa wuce shekaru ashirin basuyi aure ba gaskiya. Shiyyasa sai kiga yaro ya taso mahaifinsa bai wani tsufa ba. Da farko Bushirat ta tsaya tsayin daka akan baza'a raɓata da ɗanta ba, nima kuma na bata goyon baya dan banji daɗi ba sanda aka rabani da Haysam, sai dai wasu tsurface-tsurfacen tsafi da Uwa ta fara kawowa a kansa yasa nace a kaisan, ta nuna baƙin cikinta sosai akan hakan da nayi, har tai gargaɗi mai girma akaina da cewarta ni na cika shiga mata hanci ni da zuri'ata. Sam wani kurarinta da tsubbace-tsubacenta basa bani tsoro, dan da UBANGIJI NA na dogara akoda yaushe. Dan haka na cigaba da dagewa har sai da Tajwar Abdul-majeed ya yarda aka kaisa ƙasar Cuba. Haukane kawai Uwa da Bushirat basuyi ba, sai dai kamar ALLAH ya saka tsorona ne a zukatansu ni ban sani ba. Dan duk hatsabibancin uwa iyakarta borenta a kaina a bayan idonane, taci alwashi sosai a kaina dalilin ɗauke Eshaan har ma abin ya dinga ɗaure mun kai amma sai na ɗaukesa aikin banza dan bata isa mun abinda bai kasance jarabawata ba. Komai ya lafa kowa ya cigaba da harkokinsa aka shiga watan azumin ramadan. Azumi nada kwanaki bakwai sai Tajwar Abdul-majeed ya sameni akan zan masa rakkiya ya duba Eshaan da ga can muje umrah da shi bayan salla sai mu maidasa Cuba mu dawo gida. Ban kawo komai a raina ba na shirya mukai wannan tafiya har da Haysam. Munyi-munyi Ammarah ta bimu taƙi, ashe lokacin ta samu wani saurayi ne ya kuma mata alƙawarin dinga zuwa shan ruwa wajenta. Sai da na nuna ɓacin raina kan rashin son binmu a zatona bata son taje ne su haɗu da ƴar uwarta, sai da ta zauna ta fahimtar dani. Naji daɗi sosai, dan tace tana son bashi damane ta karanci halayyarsa anayin bikin sallah ai aurensu kawai. Munyi farin ciki da hakan, mun kuma mata fatan alkairi.”

       Malikat Haseenat tai shiru tana jan ajiyar zuciya, yayinda Iffah kejin ƙaguwa matuƙa da son jin cigaba, sai dai batayi magana ba har sai da Mammah ta cigaba dan kanta bayan tasha ruwan zam-zam dake gabanta.

     “Tafiyarmu itace mafarin ƙaddarar Ammarah, sannan itace mafarin yakice uwa da ga wannan zuri'ar, sannan itace mafarin yin kuka garemu dama duk al'ummar ƙasar ruman, sannan itace mafarin hawan Haysam karagar mulki matsayin madadi ga mahaifinsa. Bayan wucewarmu umarah, bisa yarjewar Jasim UWA ta sakasu yin yankan nan dai dana sa Tajwar Abdul-majeed bijire mata akansa, ta kuma basu umarnin ɗaura auren ɗaya daga cikin ƙannensu da wani bawa ko cikin talakawan gari. Son zuciya da sanin makomar ɗan da ake so a samar ko ƴa ta wannan hanyar suka aurar da Ammarah ga ɗan mai ɗinka kayan dokin masarautar, domin a ranar sunzo kawo kayan kwalliyar dokuna na bikin al'ada dake tunkarowa. Babu waya a lokacin balle ta sanar mana ko wani ya sanar mana, hasalima sunyi auren ne a sirrance sai ita da suka ɗauka suka kai wa yaron bisa tirsasashi ya kusanceta in ba hakaba zasu kashe dukkan ahalinsa da shi kansa. Dolene ya tsorata ya aikata abinda suke buƙata yana kuka itama tanayi. Shi UBANGIJI mai hikima ne, sun taya ya kuma isar musu bisa ikonsa, badan baya son Ammarah da wannan bawan ALLAH bane, ba kuma dan yana son nuna Uwa a saman ƙoƙarin mu bane. A'a wannan itace ƙaddararsu. Kuma ALLAH ya rubuta sai an samar da wannan abun haihuwar ta wannan hanyar. Sai dai alhmdllh, ina godema ALLAH da sake gode masa, dan kuwa koba komai ta hanyar biyan sadaki da sheda aure abinda ya farun ya faru. Mun dawo muka tadda Ammarah a wani irin yanayi, dan kuwa ta birkice musu matuƙa, a lokacin kowa ya sake tabbatar da iska a tare da ita. Munyi kuka ni da Mahaifinsu da ɗan uwanta sosai, mahaifinsu kuma ya fusata a wannan karon har ya kulle Jasim a kurkuku tare da duk wanda suka goya masa baya akan aikata aikin, yayi kiranyen uwa amma taƙi zuwa, an sa malamai domin mata kiranye nanma taƙi zuwa. Har takai an haɗa da bokaye irinta amma amsa ɗaya suke bamu tafi ƙarfinsu. Hankalinmu ya tashi matuƙa, musamman bayan wasu watanni da ciki ya bayyana ga Ammarah, gashi lafiya taƙi samuwa gareta, tama koma wata iri kamar mai ciwon hauka, ta daina magana da kowa, sai kuka, abinci ma sai an tsaya kanta take ci. ALLAH ne kawai ya zama kariya ga wannan ciki har zuwa ranar haihuwarsa. Tajwar Abdul-majeed ya saka a nemo masa mijin da suka aura matan, sai dai anje ba'a dace da samunsu ba, wai sun bar asalin ƙauyensu a wani dare. Iya nema da bincike kuma ba'a dace ba dole aka haƙura. A daren wata juma'a ALLAH ya sauki Ammarah lafiya, sai dai tasha matuƙar wahala kafin ALLAH ya kawo haihuwar. Ta haifo yarinyarta mace ƙyaƙyƙyawa, sai dai babu ta inda take kama da ita sai tambarin tabon tawadar ALLAH da zuri'ar wannan gida ke da ita, bamu san mahaifinta ba kuma balle musan ko da shi take kamar. Mun amsheta hannu biyu, sai dai zagaye take da addu'ar neman kariyar UBANGIJI da ga sharrin uwa. A randa aka haifi yarinyar a ranar ALLAH ya kawo wani mai magani....”

      Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ciwo. Tare da faɗin “kin san wani abu?” kai Iffah da ke sharar hawaye ta girgiza mata. Malikat Haseenat ta sake sakin murmushi. “Mai maganin nan hatsabibin kansa ne, dan kira ɗaya yayma uwa a randa ya cika kwana uku a masarautar nan a take ta bayyana gabansa gaban kowa wujiga-wujiga. Ya tabbatar mata shi ba azzalumi bane, da sai ya wahal da rayuwarta ta yanda bata isa sake numfashi a duniya ba, amma ko'a yanzu bazai ƙyaleta ba sai ya nakasa rayuwarta ta yanda bazata ƙara tunanin cutar da wani ba. Ya sakata ta warware duka wani tsafi data aikata zagaye damu batare da mun sani ba, sannan ya buɗe dukkan surukanta a gabanmu yay mata korar wulaƙanci da gargaɗi mai tsaurin gaske. Sosai ta dinga kuka da neman gafara da tabbatar masa ta zubda makaman yaƙinta bazata sake ba a barta taci gaba da rayuwa damu amma yaƙi saurarenta. Majiya ƙarfin hadimai aka saka suka kwasheta zuwa can tsakkiyar dokar jeji mai tsananin rintsi da haɗari suka jefar da ita. Wannan shine mafarin barin uwa tare damu, sai dai kuma a wannan dare ALLAH yay ma jaririyar da Ammarah ta haifa rasuwa, washe gari shima Shahan-shan Abdul-majeed yabar duniya sakamakon bugawar zuciya da saran macijin da aka rasa tushensa, sai kuma ya kwana da tashin hankalin abubuwan da Uwa ta dinga sakasu sunayi na shirka da yanda bayan ya tsawatar wasu suka zagaye sunayi ciki harda ɗansa Jasim. Abdul-majeed ya rasu, uwa ta shuɗe, jinjirar Ammarah ta koma. Haysam ya zama Shahan-shan. Bayan duk faruwar waɗan nan abubuwa da shuɗewarsu zukata suka hakura abubuwa suka fara komawa dai-dai. Saurayin nan da Ammarah ta shirya gabatar mana matsayin miji ya dawo da burin aurenta duk da ba'a ɓoye masa komai da take ciki ba. Yace yaji ya gani, dan ko a baya da ya janye jikinsa Jasim ne ya samesa da gargaɗin karya sake zuwa an mata aure. Bayan kuma yaji an saketa dan auren kwata-kwata na sati biyu ne ya sake dawowa amma aka hana mishi ganinta ma kwata-kwata. Ammarah taso bijirewa, dan har lokacin bata dawo dai-dai ba, amma naita lallaɓata da mata nasiha ni da ƴar uwarta hatta haƙura aka ɗaura aure. Sai dai sam auren bai wani je ko'inaba ta fito, sakamakon wata sabuwar ƙaddarar data afka mata, a duk sanda mijinta zaije gareta sai a sauya halittar matancinta ta koma ta namiji. Dole babu yanda zaiyi ya rabu da ita ta dawo gida, daga nan bata sake aure ba, daga nan bamu sake jin labarin uwa ba, daga nan bamu sake jin labarin bawan ALLAHn nan da ya taimake mu ba akan Uwa ba, daga nan Jasim ya nuna mana ya tuba, sha'anin mulkin Haysam ya cigaba da tafiya a tsaftace dan na masa gargaɗin nisantar duk wani mushiriki akan al'amurin mulkinsa..”

         Hawaye sosai Iffah takeyi na tausayin Daneen Ammarah, da tausayin su Malikat Haseenat dan labarin nan ya matuƙar girgizata, al'amari haka kamar a wasan kwaikwayo, wannan wace irin duniya ce mai cike da son zuciya. Kowa burinsa ya kasance a sama, mai nasara bisa nasarar ɗan uwansa, kai kai rayuwar gidan sarauta dabance, dabance a cikin duk wani rikicin gidaje da zuri'arsu. Yanda Iffah ke kuka sai Malikat Haseenat ce ta koma lallashinta. Sai da ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta miƙar da ita. “Hafida-ti, kinga tashi ki tafi dare yayi  maybe ma mijinki nacan na jiranki”.

       Cikin share hawaye Iffah tace, “Ai bai san ma na taho nan ba”.

   Idanu sosai Mammah ta waro da faɗin “Ya ALLAH, aiko kinyi laifi, maza wanko fuskarki muje na miki rakkiya to”. 

        Bata musa ba taje ta wanko fuskar, Malikat Haseenat ta miƙa mata wata ƴar ƙyaƙyƙyawar jaka tana murmushi. “Kije da wannan, duk abinda ke ciki kiyi ƙoƙarin dinga amfani da shi kamar yanda na rubuta, ki yawaita shiga ruwan zafi har ki saba da daina jin ciwon”.

     Kai Iffah ta sunkuyar cike da jin kunya, sam batai tunanin Mammah ɗin zata gane ba yau, musamman yanda take dauriyar dai-daita tafiyarta duk da zafin da take ji.........✍️     _Hummmm babu abin cewa kam yau🥱🚴_   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post