Daudar Gora book 2 page 59

Daudar Gora book 2 page 59

 

Daudar Gora book 2 page 69

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (59)

.......“Labarin ya fara ne tun zamanin iyaye da kakanni da ya kasance akwai ƙarancin ilimin addini. Ba a daular ruman kawai ba hatta da sauran dauloli da ma talakawan ƙasar RUMAN kowa yasan anyi matuƙar imani da tsafe-tsafe a ƙarnikan da suka shuɗe. Zaki samu duk talaucin mutum duk yawan arziƙinsa yanada wani boka da ke faɗa masa motsinsa ko wani abu dake tunkarosa, ko bashi Sa'a a abinda zai yi ko yake yi. A lokacin da addinin musulunci ya fara kutsowa cikin wannan ƙasa tamu idan akaji ka amsa sai an halaka ka, idan kuma kai shugaba ne to fa za'a tuɓeka a koreka kai da duk ahalinka. ALLAH sarki, masu shiga musulunci da masu hidimar ganin an shiga sunsha matuƙar wahala a wancan ƙarnin. Komai ya canja da cajawar labarin wannan ƙasa dalilin wani fari da akai na tashin hankali, ruwan dake zagaye da wannan tsuburi da ƙasar RUMAN take ya zagaye komai hadda gidaje da dukiyiyi har ma da rayuka. Ba ƙasar ruman ce kawai ta girgiza ba, Africa da ma duniya baki ɗaya wannan al'amari ya matuƙar girgizasu, inda aka shiga kawo mana ɗauki ta kowane ɓangare. Wannan shine mafarin fara samun canji, domin a cikin wannan yanayin ne tarin bayin ALLAH mabiya addinai daban-daban suka fara yaƙin ganin sunja ra'ayoyin mutane da dukiyoyi da wasu abubuwan ƙyale-ƙyale na duniya, harda masu yimusu tayin binsu ƙasashensu suyi rayuwa. Babu mai son yabar ƙasarsa tushensa dan haka mutane suka fara bijirewa, sai ko wani bawan ALLAH ya basu goyon baya mai suna SHEHU UTHMAN ƊAN-FODIYO da ga ƙasar NIGERIA. shine ya tabbatar musu ƙasarsu itace ƴancinsu, itace gatansu, itace martabarsu, su tashi da ƙarfin ƙwanji su gyarata yayi alƙawarin tallafa musu da ƙarfin jiki da ga tawagarsa. Zantukansa sun ƙayatar da kowa sun saka karsashi a jikin mutane, musamman yarima mai jiran gado Miran Aliy Qutb. Ganinfa Miran Aliy Qutb ya amshi wannan tunatarwa tuni ya samu mabiya. Abu mafi ɗaukar hankalin mutane SHEHU UTHMAN ƊAN-FODIYO ya kasance MUSULMI ne, hakama almajuransa da sukayi masa rakkiya, amma sai bai taɓa cema wani dole sai ya shiga addininsa ba ko masa tayi da wata dukiyar da zai shigan, ya dage dai tuƙuri da taimakonsu yana ibadarsa. Hakan sai ya shiga birge mutane tuni suka fara karɓar musulinci. Sai kuma cikin ƙanƙanin lokaci ƙasashen musulunci manya irinsu Saudi Arabia suma suka fara yunƙurowa, mabiya addinin islam suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen hidimtawa wannan ƙasa ta RUMAN ta sake ginuwa ta komawa kan ƙafafunta. A cikin abinda bai wuce shekaru ƙalilan ba abubuwa suka cigaba da canjawa kasancewar munada tarin tattalin arziki kashi daban-daban. An ɗauki babban mataki akan ruwan dake zagaye da mu, aka kuma ƙara faɗaɗa ƙasar ilimin addini ya yawaita, kafirci ya fara nisa a cikin al'ummar mu. Masu bautar gumaka da yin imani da bokaye duk suka fara janye jiki, wasu bokayen ma da kansu suka dinga ajiye kayan tsafe-tsafen suma suka koma ga ALLAH. Masu taurin kan cikinsu kuwa sai suka bijire da jan tunga, wasun su suka koma dazuka wasu kuma suka koma yi a ɓoye.”

       Ta ɗan ja ajiyar zuciya da ɗaukar ruwa takai bakinta. Kafin ta cigaba da faɗin, “Uwa ɗiyar wata bokanya ce  babba a wannan masarautar, bayan mahaifiyarta da ake kira bokanya Ta-bunu ta mutu itace ta gajeta. Shekaru masu yawan gaske da suka shuɗe itake tafiya da jan zaren yi da hani na wannan gida harta mutu ƴarta ta gajetan (wato Uwa). Ta kuma gajeta ne ana gab da samun wannan iftila'i da ya faru, lokacin da abun ya faru tana farkon fara jin daɗin karfin ikonta dan tafi mahaifiyarta hatsabibanci. Domin kuwa komi za'ayi sai an sanar mata tace ayisa, idan ko ta hana akan dakata koda ana sonshi. Hatsabibiya ce matuƙa. Dan duk da mahaifin Miran Aliy ya yarda ƴan ƙasarsa suyi addinin da suke so shi ya kasa rabuwa da Uwa har ALLAH ya masa rasuwa Miran Aliy Qutb ya zama Shahan-shan. Shi dai yaso bijirewa da farko, amma babu wanda yasan miya faru hakan ta gagara ya cigaba da mata biyayya akan abinda ta shardanta kota hana. Na takaice miki zance fa ikon Uwa sai da ya kasance itake kamar mulkar ƙasar ruman dan har shi Shahan-shan ɗin sai da cewarta yake cewa ga talakawansa. Haka yay mulkinsa ya shuɗe Miran Abdul-majeed ɗansa, mijina ya karɓi ƙasar ruman. Muma mun cigaba da kasancewa a ƙarƙashin say na UWA, sai dai abun na matuƙar damuna kasancewar nayi ilimin addini mai zurfi. A lokuta da dama idan tace ai abu nakan ƙalubalanta har sai na fahimtar da Tajwar Abdul-majeed illarsa. Duk bayan wata uku takan saka ayi yanka na baƙaƙen shanu da karnuka da raƙuma wai tsarine na wannan daula. Takan tilasta ɗaya daga cikin ƴaƴan Shahan-shan a aura mata wani talakan ƙasa ko bawa ta samu ciki ta haihu, da zaran ta samu cikin dole kuma ya saketa. Shi kuma abinda aka haifa zai cigaba da rayuwa a cikin masarautar bashi da wani ƙarfin iko da shi. Sai dai kin san wani abun mamaki da ya fara jan ra'ayina harna bijirema wannan al'amarin?”.

       Jiki a sanyaye Iffah ta girgiza mata kai. Nisawa Malikat Haseenat tayi da cigaba da faɗin, “Duk waɗan nan yaran da aka haifa ta wannan hanyar basa zarce shekaru bakwai a duniya suke rasa ransu. Na fahimci hakane ta hanyar bibiyar tarinhin wannan masarautar kasancewa mutum mai son sanin tarihi. Lokacin dana fara ƙalubalantar yankan da akeyi duk bayan wata uku na baƙaƙen shanu da karnuka ne tasa Abdull-Majeed ya auro mahaifiyar su Jasim. Ban damuba dan wannan bashine gabana ba, ban kuma canja daga bijirewata ba da cigaba da nusar da su akan sanin ma'anar yankan nan. Alhamdullah naci nasara, naci nasarar dawowar hankalin wasu jikinsu akan hakan aka fara ja'injar a daina a canja da wani abu na sadaka bakwai sai yankan ba. Yayinda wasu kuma ke faɗin ai yankan ma sadaka ne tunda raba naman ake wa talakawa da hadimai. A cikin tsaka da wannan dambarwa na haifi Haysam. Mahaifin mijinki kenan. Haysam yaci wahala sosai da cututtukan da aka gagara gane kansu, sai dai ALLAH ya ƙaddara kwanakinsa basu ƙare yana yaro ba. Bayansa na haifi Ammarah, Ammarah ta zo da wasu abubuwan ban mamaki a rayuwarta tun tanada ƙarancin shekaru. Sai Waheeda, auta Nayyar, zuwa lokacin matan Abdul-majeed mu huɗu ne, kowacce kuma ta haihu da shi, akwai maza kuma akwai mata. Bari na sake dawo miki akan yanka, bijirewata da mabiya dana samu yasa aka daina a zahirance, ashe a ɓoye ana cigaba da yi batare da sanin Tajwar Abdul-majeed da ni ba. Sai da wata ranar juma'a da yamma faɗan yara ya haɗa Jasim da Haysam shi da ƴan uwansa suka masa taron dangi Ammarah ta shiga, dukan mata kai da akai ta yanke jiki ta faɗi, abinka da yaro sai duk suka haɗu kanta suna ihu ganin jini ta hancinta. An kinkimota an kawomin tana zubda wannan jini, cikin ikon ALLAH sai ban ruɗe ba na fahimci haɓo ne. An bata taimakon gaggawa jini ya tsaya har tai barci, sai dai lokacin da take farkawa bayan sallar magriba sai ta tashi a firgice. Koda na tambayeta bayan na mata addu'a ta samu nutsuwa sai ta sanar min mafarki tayi ana yanka shanaye da yawa baƙaƙe da karnuka da raƙuma. Ga mahaifinsu cikin ɓacin rai an ɗauresa da rufe masa baki. Da farko ban ɗauki wannan mafarki nata a komai ba, sai kawai nace tai addu'a mafarkine kawai. A'a bayan kwana biyu da hakan tai wata faɗuwa nan ma sai haɓo, akai mata magani dai ta kwanta sanda zata farka a firgice, nan ma na tambaya ta maimaita min wancan dai mafarki da tayi. Abin ya ɗan fara damuna sai dai ban maida hankali ba. Da ga ranar kuma bata ƙarayi ba har ta cika shekaru kusan goma sha biyar a duniya. Da ga lokacin kwanaki ɗai-ɗai ne bazaki samu Ammarah ta tashi a firgice a barci ba, idan ka tambayeta tace ba komai. Ban taɓa matsa mata ba duk da abun na ɗan damuna, sai dai ina binta da addu'oi akoda yaushe ita da sauran ƴan uwanta. Abu ya cigaba da faruwa daban-daban daga Ammarah naban mamaki, bamu fara tsarguwa da ita ba sai a randa aka samu gawar Nayyar a cikin ruwa. Abubuwan data dingayi sai da ya tada hankalin duk wani mai numfashi a cikin masarautar nan, inda ta dinga ihu da jadada sai ta ɗauka fansar jinin ɗan uwanta. Anyi-anyi kuma ta faɗa miya faru take irin wannan magana taƙi cewa komai, harma abin ya ban haushi na tattarata na ƙyale, a kuma lokacinne ita kuma ta tattara ta tafi makarantar koyan aikin likitanci a ƙasar America, Sai lokaci-lokaci take zuwa mana hutu ta koma. Ta maida hankali sosai saboda tana so, gashi kuma makarantar da aka sakata makarantace ta musamman. A shekarar da take kammalawa a shekarar yayansu Haysam yay aure, hakama ƙanwarta Waheeda, anyi-anyi ta fidda miji itama tace a barta ba yanzu ba, ita akwai wanda take jira. Sam bamu takurata ba, dan tanada karamin jiki sosai, shekarun nata ma dai ba wasu bane masu yawa, in bama mun faɗa ba zaka ɗauka Waheeda ce babba gareta. Anyi bikin Haysam da Waheeda Ammarah ta cigaba da aikinta a cikin clinic ɗin masarautar nan da kuma karatunsa a cikin wannan ƙasa ta ruman, a sati kuma takan zagaya jahohi biyu sau biyu domin bada gudunmawarta ita da wata ƙungiya da suka haɗa. Tsahon shekaru huɗu babu haihuwa da ga matar Haysam, tadai samu ciki sau ɗaya ya lalace bama ya haura wattani uku ba, hakama Waheeda itama acan bata haihu ba. Nata bai damu kowa ba, amma na Haysam an fara kanan magana akan sai ya ƙara aure kasancewar shine Miran mai jiran gado. Bai son ƙara aure, amma mahaifinsa ya takura masa, ya nema damar a basa lokaci zai nemo da kansa. Anan kam sai ya bashi dama. Ba'a rufa watanni uku ba kuwa ya kawo sunan Bushirat, ta kasance ƙanwa ga wani abokinsa da sukai karatu, amma suma ƴan nan ƙasar ruman ɗin ne, sannan kuma manyan mutanene dan mahaifinta babban malami ne masani sosai. Ƙyaƙyƙyawar nasabarta yasa bamu wani tsananta bincike ba akai biki. Sai dai me itama shiru, dan garama Ashwaq ta taɓa ɓari sau ɗaya. Shekarar Bushirat biyu a masarautar nan itama babu labari sai ma Ashwaq ɗin ce dai ta ƙara ɓari, dan haka aka sashi ya ƙara auro Danish-Ara, cikin ikon ALLAH Danish-Ara bata rufa wata guda ba sai ga ciki da ga Bushirat. Kowa yayi farin ciki sosai musamman ma shi da ita da mu kammu, hakama Ammarah kai kacema ita keda cikin, dan gaba ɗaya ta tattara ta koma sashen ɗan uwanta tana kula da Bushirat. Bamu hanata ba, duk da rashin aurenta na damunmu, sai dai mun fahimci akwai matsalar junnu tattare da ita, dan haka muka dage da addu'a gareta kawai”..........✍️



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post