Rumbun Kaya page 69

Rumbun Kaya page 69

 

Rumbun Kaya page 69

**RQ**

     *69*

***A cikin mayafi ta rufe fuskarta sanda suka zauna a cikin jirgin, kukan take sosai wanda take jin kamar idan ta dawo ba zata ga ammyn ta ba, bata wani samu time da ita ba kwata kwata, tana so su zauna sosai suyi hira ta bata labarin kuruciyar ta zuwa girman ta. Mayafin ya gyara mata da hannun sa yana kallon saman kanta, ta bashi tausayi ainun saboda ba abu bane me sauki a rabaka da kowa naka. Sanarwar tashin jirgin aka bayar da daura belt ya matso daf da ita ya daura mata belt din, rike hannun sa tayi kam yayi murmushi sannan ya sakè matse hannun nata sosai a cikin nasa yana jin yadda take motsa shi. Addua ce a bakin ta da take yi a hankali har jirgin ya daidaita a sama, sai ta dan rage rikon da tayi masa, ta janye veli din fuskar ta, ta bayyana bayan ta goge hawayen.


“Sorry.” Yace mata yana sakar mata murmushi. Murmushi yake tayi ya girgiza mata kai yana nuna mata wayar sa,bata gane me yake nufi ba tabi wayar da kallo, be ce uffan ba, ya ajiye ta ya jawo kanta ya dora a saman kafadar sa ba tare da yace komai ba. 

    Sun sha matukar wahala musamman raihana da ta galabaita saboda bata taba doguwar tafiya irin wannan ba, dan daga Nigeria zuwa New-Zealand tafiya ce me nisan gaske, tafiyar kusan kwana biyu. Qatar airways suka hau sukayi transit a Qatar bayan some hours suka sake daukar hanya sai New Zealand. Bata gane komai har suka gama duk process din da ake airport daga nan suka samu shiga kasar. Shi Aryan ya galabaicen yake musamman da ba wai cikakkiyar lafiya ce dashi ba, dauriya ce kawai irin ta maza kuma baya so ya kashewa Raihana guiwa, be san dalilin da yasa Daddy zabar kasa ba of all the kashashen duniya ya Kawo su karshe wadda take kusa da bangon duniya. Tsiran hours da Nigeria awa kusan goma sha daya ne. 

   Shi yake janye da kayan nasu dan raihana bin sa kawai take wai kuma a sunan kazo da mara lafiya fa kenan, tana tafe tana karewa birnin Auckland kallo , yayi masifar haduwa sai wani uban sanyi da yake kada ta duk da ta saka babbar rigar sanyi da suka saka tun a jirgi bayan sun baro Qatar. Uber Aryan yayi musu zuwa Hilton Auckland hotel wanda Daddyn yayi musu booking tun suna gida.

   Duk da gajiyar da Raihana take ciki bata bari kanta ya kulle ba bare har ta kasa morewa kallon duniyar da suka zo. Hannun ta sarke dana Aryan din suka wuce 5th floor in da dakin nasu yake bayan sun bar kayan su a reception zaa hawo musu dashi. 

  Wani sanyayyiyar ajiyar zuciya Raihana ta sauke bayan da suka shiga cikin katafaren dakin da yake a gyara tas tas cikin adon fari komai na dakin white ne tun daga kan furnitures har zuwa duvet da labulaye. 


“Sannu.” Yace mata yana wuce ta zuwa wajen heater ya dan karo ta saboda yadda dakin ya dau sanyi ga sanyin da suka kwaso a waje gashi ana ta sanarwa da zasu shigo akan kowa ya zauna a gida snow za’a yi me yawa. Temperature din ya duba yaga kusan -minus 7 ya tuno zafin da ake a Nigeria sai kawai ya girgiza kai, Allah daya gari ban ban kenan. 

   Akan sofa ta zauna tana mike kafarta da take jin kamar ta kumbura saboda yadda ta sage. Door bell aka danna ya karasa ya bude wani baturen saurayi ya shigo da kayan su ya ajiye Aryan yace nasa thank you sannan ya fice.


“Na gaji.” Tace tana jan muryar ta, waigo ta yayi yana janye da trolley din ya ajiye a gefe sannan ya karaso wajen da take zaune ta zauna a gefen ta


“Sannu, dole ki gaji akwai nisa.”


“Kamar kafata zata cire fa.”


“Sorry, taso kiyi wanka da hot water zaki ji dadi.”


“Sanyi fa ake yi.” Tace tana marairace masa dan har cikin kashi da bargon ta take jin sanyin na ratsa ta. 


“Shine zai tafi da gajiyar kinji? Daurewa zakiyi kiyi, ki huta sai ki taimaka min nayi.”


Sai a lokacin ma ta tuno ashe fa wai shi bashi da lafiya, amma ta barshi da wahalar tazo kuma tana narke masa. 

   Mikewa tayi tana karfafar jikinta, sai ya mike shima ya nuna mata toilet din da hannu


“Akwai new towel nasan a ciki, use it.”


“Ok.” 


Tace tana yin gaba, shi kuma ya koma bakin gadon ya kunna datar sa yana kokarin daddy yace masa suna hotel din sun sauka. Magana sukayi sannan yace su huta sai su fito gobe yana so a fara duba shi a goben, sallama sukayi ya ajiye wayar sai ya kwanta rigingine yana kallon zaman dakin. 

   Tsayawa tayi tana kallon tsarin toilet din da ya gaji da haduwa, komai na zamani ne a ciki, gaban sink din ta matsa sai dai ta rasa ta ina ruwan yake fitowa dan babu alamun wajen fitowar sa haka kuma babu wajen kunnawa. Tana tsaye tana tunanin yadda zatayi sai ta dan gwada kai hannun ta jiki kawai sai ga ruwan ya fito, tana matsar da hannun ta ya dauke. Dariya tayi ma kanta ya ciré kayan jikinta sannan ta duba instruction din dake jikin shower din ta danna ta saita ruwan zafin da na sanyin tayi wankan a hankali bayan ta kulle gashin kanta da yake a gyara tsaf. Alwala ta dauro ta fito yana kwance ya rufe idonsa kamar me bacci, wajen kayan su ta wuce da sauri ya bude idon da suka dan kada saboda gajiya Ya kalli bayanta,wasu kaya masu nauyi riga da wando ta dauka ta saka sannan ta dauki Hijab da sallayar da suka zo da ita ta shinfida. 


“Ji rani nayi wankan.”


Yace yana mikewa, ok tace ta karaso ta zauna a wajen da ya tashi shi kuma ya wuce toilet. Tashi tayi da ta kintaci ya kusan fitowa ta dauko masa kayan shima masu dan kauri sannan ta fito da magungunan sa ta ajiye ta fito da cake din da khadija tayi musu ta ajiye shima. Fitowa yayi daure da wani towel din sabo ya zauna a gefen gadon saboda kan da yake masa ciwo tun a toilet din. Taimaka masa tayi ganin yanayin sa, ta dauko cream din ta shafa nasa sannan ta taya shi yasa riga ta mika masa wandon, karba yayi ya tashi zai saka tayi saurin juyawa. Murmushi ya samu kansa da yayi ya koma toilet din ya sake alwala sannan yazo sukayi sallolin da ake binsu.  

   Bayan sun idar suna zaune Daddy ya kirashi yace yayi musu order abinci idan delivery guy din yazo zai kirashi. Godiya yayi masa ya ajiye wayar sukayi shiru sai kawai ta zame a wajen ta kwanta saboda tsabar gajiyar da take ji da bacci. 


“Gajiya ko?”


“Um bacci nake ji.”


“Bari ki ci abinci sai ki kwanta.”


“Idan na tashi zan ci.”


“Um um, ban yarda ba.”


“Zanci cake toh.”


“Cake ba abincj baje ba, duk tafiyar nan me kika ci?”


“Naci Burger a jirgi.”


“Look at you, burger abinci ne?”


“Allah bacci nake ji.”


“Zo kiji.”


Tashi tayi ta matso kusa dashi, ya jawo ta jikinsa sannan ya cire mata Hijab din, ya kwantar da kanta akan kafarsa. 

   Daga reception aka kira ya sauka yaje ya karbo sakon ya dawo. Abincin suka ci sannan ta haye gadon ta kwanta idanun ta na rufewa saboda tsabar baccin da take ji. Babban duvet din ya rufa mata, ya dauki magungunan sa yasha sannan ya kwanta a gefenta bayan ta kashe hasken dakin ya maida shi kadan.

    ***Longer night sukeyi gashi sun kwanta da wuri ga yanayin lokacin ba daya da namu ba, hakan ya hana Aryan din yin bacci yayi ta juyi yana kallon Raihanan da take ta baccin ta hankali kwance. Matsawa yayi jikinta sosai yana mamakin yadda ta saki jiki ta kwanta sosai tare dashi ba tare da tsoron da ta saba nunawa ba. 

  Fuskar ta ya zubowa ido da kallo zuwa saman wuyanta, a hankali ya dinga zagaya idonsa zuwa sauran sassan jikin nata. Yayi hakuri ma kadan ba, sannan yayi sakaci ya kuma kusan yin wasa da damar sa, da su zainab sun samu nasara a kansa da tuni ba wannan maganar ake yi ba. 

   Zuciyar sa ce ta shiga saka nasa abubuwan da take ta saka masa a dan zaman da yayi a asibiti. Yana bukatar ganin dansa shima ko yarsa a duniyar nan, tunda harin rayuwar sa ake yi be san menene zai faru gobe ba kuma. Ada ya cire tsammani da tunanin duk wasu kyale kyalen duniyar nan, yana jin ko be samu komai ba be damu ba. Amma a yanzu yana jin ko shi ba zai rayu ba yana son dan sa ko yarsa su amsa sunan sa domin ya dade ana tunawa dashi a doran kasa.

   

“Babyna.” Yace a daidai saitin kunnen ta yana kai kasa kusa sosai. Bata ji shi ba, sai dai jin mutum a kusa da ita yasa ta yin juyi cikin jin dadin baccin hade da sanyin da ake yi ta rungume shi tana shigewa jikinsa sosai kamar mage. Numfashi yaja ya sauke da dan karfe yana jin wani abu me kama da mayen karfe na fizgar shi zuwa gareta. Fatar ta me matukar taushi ya sa hannu ya taba tun daga sangalalin hannun ta zuwa saman wuyan ta, ya dire akan gyarareren gashin kanta da ya dan barbaje saboda kwanciyar da tayi.


_”baka da lafiya fa.” Zuciyar shi ta tuna masa ganin kamar ya manta 


“Wa ya sani ko silar warakar ce tazo.” Wata zuciyar daga chan gefe ta rada masa. Nan take ya aminta da ita ya kuma hau ya zauna akan hujjar da zuciyar tashi ta bashi ya kuma yi kudurin a yau ba sai gobe ba, zai yi abinda ya dace duk da yana matukar tausaya masa musamman saboda uwar gajiyar da ta kwaso sannan zai katse mata daddadan baccin ta da take yi hankali kwance.


Daga kanta ya fara yana shafawa a hankali yana zuwa hannun sa cikin gashin nata da yake fitar da kamshin hadadden conditioner me dadin kamshi. Daga nan ya sakko zuwa saman fuskar ta ya shiga zagaya hannun sa a hankali har zuwa zaman bakin ta. Sake kokarin shigewa jikinsa take yi ya rike ta yana yin baya da ita, abinda ya sakata farkawa a dan gigice ta kalle shi da shanyayun idanunta da suke nuna nauyin da baccin yake akanta


"I can't hold it anymore." 


"Naam?"


“Yes, please allow me kinji? I promise you ba zan yi hurting dinki ba.”


“Na shiga uku.” Tace a ranta, sai kuma hudubar Ya nabeela ta fado mata, da kashe din da tayi mata akan hana miji hakkin sa idan har ya nema, ya ma yi kokari matuka. A yadda ake cewa mazan yanzu suke, dan haka bata da ikon hanashi, sai dai tasan zata ji jiki, amma ya zatayi? Duk daren dadewa dama dai tasan ranar zata zo, sai dai bata kawo ta a yau yau ba duba da yadda suka dauko doguwar tafiya gashi ba wata ishashiyar lafiya ce dashi ba. Da ka ta amsa masa hawaye na biyo wa kuncin ta, ya rungume ta yana kissing din saman goshin ta zuwa karan hancin ta, kafin ya hade bakin su waje daya.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post