Rumbun Qaya Page 49

Rumbun Qaya Page 49

 

Rumbun Qaya Page 49

RQ


   Page 49

***Kwantawa tayi lamo akan gadon cikin tunanin ko lafiya? Juye juye ta dinga yi har Ya Nabeela tayi knocking ta shigo ta sameta a kwance ta tashi zaune bayan ta shigo.


"Kin gwada kiran Aryan kuwa?"


Tace tana zama a gefen gadon. Girgiza kai tayi tace 


"A ah."


"Call him please, na fara jin babu dadi, ko maida ke zanyi? Wai so nake yadda akayi auren nan urgent a kalla ki samu gatan da kowa ta samu, amma idan hakan zai takura masa gwara ki koma, bana son abinda zai taba lafiyar sa an samu ya fara warewa"


Shiru Raihana tayi bata san me zata ce ba tunda har lokacin nauyin Ya Nabeelan take ji sosai. 


"Kira shi kinji? Bari naje naji shigowar Daddyn su Amna xan dawo."


"Ok tam."


Tace a sanyaye ya Nabeelan ta fita ita kuma ta dauki wayar ta, ta yi dialing number tasa. Kunna wayar sa kenan bayan ya tashi da k'yar daga wajen da yake zaune tun da ya idar da sallar isha. Ji yayi yana son kiran ta a kalla zai dan ji saukin abinda yake ji din a zuciya da ruhin sa. Sai ga kiranta ya shigo a daidai lokacin. Kallon number yayi kafin ya daga cike da mamakin co-incidence din da aka samu dan har ya hau kan number tata zai kira kiran ta ya shigo masa. Mikewa yayi sakale da wayar a kunnen sa ya koma saman gadon ya kwanta rigingine yana jin tayi sallama ya amsa a chan k'asan makoshin sa. Shiru ya biyo bayan amsa sallamar tasa saboda rashin sanin abinda zata ce masa, muryar kadai ta isa ta tababtar mata ba lafiya ba. 


"Ya Nabeela ce tace na kiraka dama."


"Ok." Yace ya sake yin shiru. Sai ta rasa me zata ce masa kuma. Tana jin yadda yake sauki numfashi da dan karfi dan tana jin sound din sa. Kusan minti biyar suna a haka sai kudin ta ya kare. Kiran ya biyo a take ta d'aga jikin ta a sanyaye.


"Raihanaaa." Ya kira sunan ta cikin jan sunan. Har cikin kwakwalwarta taji yadda ya kiratan. 


"Kina so na?" 


"Na'am?"


"Tell me, kina so na? Zaki zauna dani duk tsanani duk runtsi? Ba zaki gujeni ba?"


"Menene ya faru?"


"Just answer me please, did you love me?"


Hadiye yawu tayi jin yadda ya tsare ta, muryar sa kuma a chunkushe alamun ba da wasa yake ba. Sake maimaitawa yayi a karo na uku ta tashi tsaye tana tattaro kalaman bakin ta da take jin sun mata nauyi tace


"Yes, ina sonka. Amma me ya faru? Me ya same ka?."


Wata irin ajiyar zuciya ya sauke me karfi sannan ya k'ara gyara kwanciyar sa ya dora wayar a saman kirjin sa a hankali yace


"Nagode sosai, babu abinda ya faru inaso kawai na sani ne."


"Ok, but muryar ka..." Katse ta yayi yace 


"Missing dinki nake, inaso na ganki. Nazo?"


"Eh kazo." Tace zuciyar ta na wani irin harbawa da sauri.


"Ok, I'm coming right away." 


"Ok." Tace a sanyaye suka ajiye wayar. Sai ta kasa tashi daga in da take zaune kirjinta na cigaba da dukan uku uku, yanzu idan yazo ya zatayi dashi? Daga jin yadda yake magana rigima kawai yake nema,kar Ya Nabeela tace ma so take ta tafi, amma kuma ya zatayi masa? Ba zata iya hanashi zuwan ba dan tana son ganin shi ta kuma san halin da yake ciki. 

   Dawowa Ya Nabeela tayi dakin ta tambaye ta sunyi waya? Eh tace mata amma sai ta kasa fada mata yace zaizo yanzu. Sai da safe tayi mata ta ja mata kofar ta nufi part din Dr Farouk saboda lokacin kusan goman dare. 

  Da kansa yake driving din duk da jikin sa babu kwari sosai amma kuma yasan idan ya ganta zai samu wani kaso daga cikin energy din nasa, duk da yasan Ya Nabeela zata masa tsiya amma kuma bashi da wani option idan ba zuwan ba, yana so ya rik'e ta a jikinsa yana shak'ar kamshin jikinta me dadi da yake saka shi manta dukkan damuwar sa. A waje yayi parking motar ba tare da ya shigo ba, ya kwankwasa kad'an gate man din ya leko ya ganshi sannan ya bud'e masa da sauri. Haske sosai a harabar gidan ba zaka ce daren yayi har haka ba. Suka gaisa ya zaro wayar sa ya kira Raihanan ya ji tana ina. Sai da kirjin ta ya buga da karfi da taga kiran nasa wanda ta tabbatar da ya karaso kenan. Dagawa tayi jiki a sanyaye yace tana ina, ta fada masa tana dakin sa. Murmushi yayi da ya tuna da kofar baya ta dakin da yake amfani da ita idan baya son shiga cikin gidan. Ce mata yayi ta bud'e masa back door din, ta tashi ta bud'e masa ya shigo ya maida kofar ya rufe. Taku daya tayi da nufin komawa tsakiyar dakin ya riko ta da sauri ya sakata a jikinsa yana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke itama dan ba karamin nutsuwa take ji ba a duk lokacin da ya rungume ta a jikin sa. Hancin sa ya kai saman wuyan ta ya shiga shinshinawa a hankali kamshin da jikin ta ke fitarwa na gyaran jikin da akayi mata ya shiga fizgar shi. Hadadden kamshi ne me aji da sanyin dadi wanda be taba jin irin sa ba. 


"I love this scent!"


Yace yana kara kai kansa sosai ya zura a jikin wuyan nata wanda take jin hakan tamkar tafiyar tsutsa. Kankame shi tayi yayi murmushi yana raba jikinsa da nata ya zaunar da ita sannan ya durkusa a gabanta ya rike hannun ta.


"Wani abu zai faru dani wanda ni kaina bansan menene ba, abu daya na sani shine, sai na cika alkawarin da nayi wa kaina, ko da kuwa hakan na nufin katsewar numfashi na. Ina fatan zaki zauna dani duk runtsi duk wuya, ba zaki gujeni ba."


gid'a masa kai tayi idon ta na cicikowa da kwalla. Hannu ya kai ya share mata saman idon yana girgiza mata kai


"Karki zubar da hawayen ki akan abinda be chanchanci zubar su ba, zan yi komai da kaina ba tare da kowa ba, kuma sai na tabbatar da duk wanda yake da hannu ya fuskanci hukunci me tsanani."


"Su waye menene suka yi maka?"


"Karki damu, just pray for me."


"Tom, please karka saka kanka a wani abun dan Allah."


"Ba abinda zai faru kinji? Na miki alkawari amma karki sanarwa kowa, sirri ne tsakanin mata da miji."


"In sha Allah." 


Tace a sanyaye. Mikewa yayi daga gabanta ya zauna a gefen ta yana jawo ta jikin sa. Ya lumshe idon sa yana jin saukin abinda yake ji a ransa na bacin rai. Abinda ya rasa a baya da har ya bari bacin ransu yayi masa mummunan tasiri a rayuwar sa. Amma banda yanzu da yake jin yana da abu me muhimmanci da zai yi protecting, yana kuma da burin tara family nasa na kansa. Yayi musu irin tarbiyyar da yake so. Su rayu cikin so da kaunar junan su. 

Ba zai kyale duk wanda ya shiga gonar sa ba a wannan karon, idan har ya tabbatar da Barr Awais amanar su suka ci, sai yayi maganin su da duk wanda suke yiwa aiki, zai aje rigar hukuma ya saka wadda ta dace dasu zai kuma yi amfani da abinda Hajiya Zeenat din take ji da takama dashi wato dukiya wajen yakar ta. 

    Baya yayi dasu suka kwanta akan dan madaidacin gadon da yafi kama da na mutum daya, ya kara jawota sosai jikinsa har kusan rabin ta na saman sa. Hannun sa ya kai saman gashin ta yana shafawa a hankali, yana sauraron heart beat dinta take tafiya kusan daidai na nasa bugun zuciyar. 


"Inason babies Raihana." 


Da sauri ta yinkura zata tashi ya matse ta yana murmushi


"Ba yanzu nace ba, kawai nace inason yara ne, da yawa da yawa kinga mu bamu da yawa, ina sha'awar naga mutum da yara masu yawa."


"Ni ba ruwana." Tace tana turo baki.


"Da ruwanki, kece zaki bani dukka kuma."


"Ka tashi ka tafi kar Ya Nabeela ta dawo."


"Um um ba in da zani, idan tazo ma shikenan kinga"


"Dan Allah ni dai ka tafi."


"Kora ta kike?"


"Eh." Tace tana tashi zaune.


"Ba in da zani, ai daki na ne nan din."


"Yanzu ai ya zama nawa."


"Aro dai aka baki."


"Toh ka tashi ka tafi." Ta ture shi ganin yana matsowa gareta. 


"Kinaso in tafi?"


"Eh."


"Ok zan tafi, amma har yanzu b3 na a low yake, dazu ma 30% kawai yayi kuma ya zuke nan da nan, yanzu 50 nake so yayi kawai sai na tafi."


"Toh ba sai ka saka charjin ba, ai akwai wuta." .


Tace pretending bata gane me yake nufi ba. Murmushi yayi yana mata wani kallo me dauke da ma'anoni. Bakin ta da yake maganar ya bawa attention dinsa sosai. Kunya taji ta rufe fuskarta da sauri ganin yadda yake kallon ta.


"Kinga yanzu ma ya koma 0, anya ba bari zanyi yayi 100% ba kawai?"


Mikewa tayi ta hau yunkurin sauka daga gadon cike da dana sanin cewa yazo, ita wai ta tausaya masa ne amma ashe ba haka bane ba. Riko ta yayi ya dawo da ita kan gadon ya yi mata rumfa da jikinsa ya dora mata baki daya nauyin sa. 


"Kin yarda in samu full charge din?"


Girgiza masa kai tayi alamar  a'ah da sauri tana matso kwallar jin yadda ya danne ya hanata kwakkwaran motsi.


"Dan Allah kayi hakuri."


"Dan Allah kiyi hakuri." Ya ciji lips dinta na k'asa ya kwaikwayi muryar ta. Runtse idonta tayi ganin ya saka kansa a jikinta yana bin jikin nata da wani irin salon kiss. Jikinta ne ya dauki rawa ta rikice tsoro ya shigeta tayi kokarin ture shi amma ta kasa kwata kwata, numfashin sa yake sauke mata yana cigaba da abinda yake matan yana kuma saka idon sa a nata yana kallon reaction dinta. Hannun sa ya shiga zagaya a jikin nata zuwa saman cikin ta da yasa hannu ya yaye rigar t-shirt din dake jikinta ya zura hannun zuwa in da batayi tsammani ko tunani ba. 


"Wayyo Daadah." Ta furta da dan karfi jin yadda ya kaiwa b***b dinta riko, saurin hade bakin ta da nashi yayi waje daya ya cigaba da yawo da hannun nasa a saman kirjinta yana mata kamar tafiyar hawainiya. Sosai ta rude jikin ta ya hau rawa ta rasa in da zata saka kanta sai jujjuya kanta take saboda abinda yake mata ba karamin rudata yayi ba. Romancing dinta ya shiga yi sosai yana cigaba da kissing din bakinta cikin salon da ya sata fashe masa da kuka. Kukan tane ya ankarar dashi abinda yake aikatawar, da kuma abinda yake shirin zarmewa idan har ya biye wa mahaukacin feeling din da ya taso masa a lokacin. Cikata yayi ya dagata ya kwanta a gefen ta yana maida ajiyar zuciya ya jawota jikinsa ya manne ta yana lumshe idon sa da yake jin kamar kansa zai fashe saboda yadda ya yi masa nauyi. Be san me ya hau kansa ba, duk da abinda yayi din ba haramun ya aikata ba amma ba yanzu bane right time din. Dan light romance yaso sai gashi ya zarme da yawa har yana neman wuce gona da iri. Zafi sosai bakinta yake mata da saman kirjinta, haka ya saka ta kuka k'asa k'asa yana jinta ya hanata tashi duk da attempt din da tayi na son tashin. Bacci ne ya soma fusgarshi bayan wasu mintuna ya sake kankame ta yana jin baccin sosai na rinjayar sa. Tashi tayi ganin yayi bacci ta zubawa fuskar sa ido zaka rantse ba zai aikata abinda ya aikata a yanzun ba, innocent face gareshi da wani irin shariya wanda zaka dauka irin su rike hannun mace ba zasu iya ba bare har su iya hada jiki da ita. Ita gaba daya ma tsoro ya bata dan yadda ya sauya mata lokaci daya. Saukowa tayi daga gadon ta dan harare shi kad'an tana cije bakin ta da lips din suka dan yi ja kad'an ta wuce toilet tana gyara rigar jikinta da ya maida mata ita sama.

  

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post