Rumbun Qaya Page 48

Rumbun Qaya Page 48

Rumbun Qaya Page 48

RQ  

Page  48

****Tashi Ya Nabeela tayi bayan fitar Aryan din tace Raihanan ta taso ta nuna mata dakin ta. Tashi tayi ta bi bayan ta zuwa wani madaidacin daki me kyau da ya sha gyara na musamman saboda zuwan nata, hade yake da dan karamin toilet a ciki sai wardrobe a jikin bango me guda biyu. 

"Dakin mijinki ne, anan zaki yi zaman ki har sai mun gama abinda ya kamata muyi, ki saki jikinki dani dan Allah, ni yar ki ce dan dai ba zaki iya tuna lokacin ba, baki da wayo shiyasa."

"Nagode Anty."

Tace cike da jin dadin karamcin ta. Ta taimaka mata sosai dan ba karamin tsoron yanayin Aryan din take ba wanda yake abubuwan nasa babu ko digon nauyi bare kunya. Fita ya Nabeela tayi tace mata tana zuwa, ta zauna a gefen gadon kamshin turaren sa da ya riga ya kama dakin taji yana shigar mata hanci. 

***Ransa a dagule ya fito daga gidan, gaba daya sai yaji kamar an zare masa dukkan kuzarin sa, ba hakan yaso ba duk kuwa da dama be niyyar wuce iyakar da ya gindaya wa kansa ba, amma kuma shi an katse shi gaskiya. A dan lokacin nan yake son ta saba dashi ta saki jikinta domin har yanzu akwai tsoron sa a tattare da ita. Shi be ga amfanin zaman ta wajen Ya Nabeelan ba tunda dai an riga an daura shi baya bukatar komai a bar shi da matar sa zai san yadda zai yi. Main house dinsu ya wuce kai tsaye dan yaji tukin ma duk ya fice masa a rai kuma zai shiga gari sosai gwara kawai yaje ya dauki Driver su fita. Gidan shiru kasancewar babu kowa sai masu aiki dake kaiwa da komowa a cikin gidan suna gudanar da aikin su. Niyyar sa yau ya dawo gidan tare da Raihana amma sai gashi Ya Nabeela tayi masa shigar sauri ba zai kuma iya ja da hukuncin ta ba. Kamal ne ya fado masa ya dauki waya ya kirashi dan yana da yakinin da saka hannun sa a wannan decision din da Ya Nabeela ta yanke domin yaga alama gaba daya sun hade masa kai suna acting kamar wasu iyayen sa, da sauki idan Ya Nabeela ce kawai amma banda Kamal da shi har yanzu a matsayin aboki yafi jin sa kuma dan uwa fiye da wai wa da ya girme shi. Parking yayi a kofar gidan nasu daidai lokacin da Kamal din ya daga wayar yana kokarin fita daga office domin yaje gida ya dauki Khadija ya kaita gidan Ya Nabeela.

"Tare da kai aka hada baki aka karbe min mata?" Yace kai tsaye ko sallama be bari Kamal din ya amsa ba.

"Karbe mata kuma? Ban gane ba."

"Baka san shirin Ya Nabeela na rike min mata ba? Daga zuwa sai tace wai tazo kenan sai an neme ni."

"Hahaha... Tsakani da Allah fa? Haka Ya Nabeelan tace?"

"Ka rantse baka sani ba?"

"No Allah ban sani ba, bamu yi maganar da ita ba wallahi, amma me yasa zata karbe ta, ko dai taga rawar kan ka tayi yawa ne?"

"Oho, nima ban sani ba."

"Wannan tsarin yayi min dadi, bari na karasa gidan naji kanun labarin."

"Wai ni har nawa ka biya min sadakin nan ne? Naga alama dan kun karbo min aure juya ni zaku dinga yi."

"Gaskiya sai abinda ka gani kawai, kayi biyayya mu baka mata kaki mu barka da hamma wallahi. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kaga sai ka bada himma sosai wajen aikin office ka daina zama distracted har rigar ka na baci."

Kit Aryan din ya kashe wayar yana jan tsaki, cike da takaicin maganganun Kamal din. Horn ya danna a gate din da karfin gaske, maigadin ya taso da gudu ya zo ya bud'e gate din, shiga ya shiga a guje ya samu gefe yayi parking, sannan ya fito. Yahya ne ya tashi da sauri ya karasa wajen sa. Cilla masa key din yayi ya chafe yace fita zamuyi, sannan ya juya ya shige cikin gidan.

  Dakin sa ya wuce kai ya cire kayan jikin sa ya sauya zuwa wasu daban ya saka socks da sau ciki sannan ya fito ya samu Yahya ya fito da motar da yasan Aryan din na nufi daga rumfa ya kawota tsakiya. Gaba ya bud'e gefen Yahyan ya zauna hannun sa rike da wasu files.

"Ina zamu oga?" Yace yana saita motar akan babban titin

"Chamber." 

 Yace a gajarce ya cigaba da duba takardun har suka karaso chamber din su Barr Awais din. Sauka yayi yace ya maida motar inuwa ya jirashi ya shiga ciki. Suna zazzaune a wani round table Aryan din ya shigo, ya samu waje ya zauna suka gaisa sannan Barr Awais ya turo masa file din gabansa yace

"This is a sad news."

"Me ya faru Barr.?" Yaja takardar gaban sa yana dubawa

"Menene ma be faru ba? Mutanen nan ta karfi da yaji suna kokarin sauya dokar nan, ko nace ba sauya ta zasuyi ba, kawai bata aiki ne akan masu arziki."

"Ban gane ba?"

"Duba a hankali." Yace yana mikewa tsaye. Ran Aryan din ne ya baci sosai bayan ya gama karantawa, ya mike shima yana kallon Barr. Awais din.

"Me suke nufi?"

"Zasu bada belinta a zaman da za'a yi next."

"Innalillahi, haka k'asar tamu ta zama? Kisa fa ta aikata,duk shaidu sun bayyana, me yasa zasu sauya komai?"

"Wallahi tallahi, at first da na samu labarin ban yarda ba, sai gashi na samu waya daga Barr namadina ya kuma tabbatar min da zargin da ake yi, yanzu haka kotu ta hana hukumar DSS kama Justice Mandawari duk da dama ya fice daga k'asar tunda aka kama Hajiya Zeenat. Ashe shiri yake yi sosai akai, domin gaba daya saman tasu ce, yana da manya sosai a k'asar nan. Anya wasu alkalan zasu gama da duniya lafiya kuwa? Sune suke Sawa ayi mana kudin goro gaba daya."

Shafa kansa Aryan yayi da ya daure masa tamau saboda abinda yake shirin faruwar wanda be taba kawowa ba, yace

"Yanzu menene abun yi?"

"Dole zamu jira zaman da za'a yi jibi, anan zamu tabbatar da gaskiyar abinda yake yawo akan maganar."

"Ya Allah!"

Ya zauna a hankali ya dafe kansa, me yake shirin faruwa? Dafa shi Barr Awais yayi ya tsaya a gabansa ya dago yana duban sa

"Menene alakar Alhajin ku da Adam?"

"Adam? Babu wata alaka face ta auren mahaifiyar sa da Daddyn yayi."

"Ok, ya shigar da kara kotu ne, yana bukatar kotu ta bi masa hakkin sa a matsayin sa na d'a wajen Alhajin."

"Wannan maganar banza ce."

"Yana da support sosai, dan haka ne ma nake tunanin akwai wani gagarumin abu da mu bamu sani ba, alakar Hajiya Zeenat da Alhaji. Am sorry to say amma akwai abinda mu bamu sani ba."

"Na gaji wallahi, na gaji da duk wannan abubuwan dake faruwa. Inaga zan yi nisa da kowa na bud'e sabon shafin rayuwata. A sanda nake tunanin komai ya wuce a lokacin wani sabon al'amarin yake budewa."

"Ba zaka ce haka ba, dole sai anyi hakuri sannan za'a kai gaci, sannan muna bukatar tabbatar da gaskiya domin a samu yiwa kowa adalci. Sai dai ina da yakinin a yanzu muna da bukatar support din Alhaji, domin a bayanin da na binciko, akwai wani babban al'amari da yayi matukar bani mamaki."

"Menene?" 

"Tabbas Hajiya Aisha matar Barrister Nasir tana nan da rai, kuma tana wani waje a killace wanda nake kyautata zaton Alhaji yana da masaniyar komai."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun."

"But bincike na ne ya sanar dani hakan, bani da tabbacin gaskiyar maganar, ina tunanin Hajiya Zeenat tasan abinda ya faru."

"Ta sani, dan duk abubuwan da ya aikata tana da masaniya itace dai bata bari yasan nata."

"Yanzu me ya kamata muyi?"

"I don't know, ban sani ba wallahi. Kaina ya kulle gaba daya."

"We have to figure out abinda ya kamata if not duk effort dinku zai tashi a waste."

"Ya ma tashi." 

Ya mike dan be kuma sai me zai ce ba

"We have to wait zuwa ranar muga abinda zai faru, idan yaso sai muga action din da ya kamata mu dauka."

 Barr auwal ya fada yana kallon Aryan din. Be ce komai ba, ya juya kawai ya fice daga wajen. Yana fita suka saka dariya gaba dayan su Barr Awais ya dauki waya ya yi kira sannan ya ajiye yana murmushi.

***Bayan motar ya bud'e ya shige dan gaba daya ya rasa me yake shirin faruwa dashi, wacce irin rayuwa mutanen mu suke yi? Tabbas be yarda da maganar Barr Awais ba, dan duk wani abu ma da yake faruwa dole da saka hannun sa. Shikenan babu wanda zakayi trusting a duniyar nan kowa ya lalace ya zama mutumin banza? Gidan sa ya ce Yahya ya kaishi dan ko magana baya son yi sosai, da k'yar ma ya iya bud'e baki ya amsa masa da in da zai kaishin ganin ya nufi main house din su dashi. Suna isa ya balle murfin motar ya fice ya shiga ciki ko bi takan Baba me gadi da ke masa magana be yi ba, be ma jishi ba kwata kwata saboda yadda hankalin sa baya tare dashi. Be san yadda Kamal zai ji ba, abinda yayi sacrificing dukkan time dinsa akai, cikin dan kankanin lokaci wasu mutane marasa daraja sun lalata komai. Saukin ta daya gaskiyar waye shi ta bayyana ga mutanen da ya kamata su sani din, amma bayan wannan babu wata nasara. Shiyasa tun farko Aryan be so aka yi ta daga zaman nan ba, domin yasan yadda k'asar take ya kuma san mugun connection din Hajiya zeenatun zata iya komai, tunda ta riga ta bar hannun DSS ta koma hannun kotu in da suke da damar yin abinda suke so domin alkalan nan ba kirki ne dasu ba. 

  Kasa zama yayi ya dinga zagaye a dakin cikin yanayin bacin rai me tsanani. Ji yake kamar ya juyar da rayuwar sa ya chanja ta zuwa wani bangare na daban ba wanna din ba, ya manta kowa da komai ya fara rayuwar sa sabuwa ba tare da kowa a tattare dashi ba.

  Karar wayar sa ta dawo dashi cikin hayyacin sa, ya kalli me kiran Kamal ne, yana kallo ta gama burarin ta, ta katse sai kawai ya duka ya kashe wayar baki daya ya juya ya bar dakin.

***Fita sukayi bayan Kamal ya kawo Khadija gidan ya tafi. Ya Nabeela tace su fito suka nufi wani hadadden beauty spa and salon da tayi ma Raihanan booking jiya da daddare. Me wajen kawarta ce shiyasa ma suka karbi Raihanan duk da ana booking ne kusan wata guda kafin nan in dai bridal treatment ake so. Cike da kwarewa receptionist din ta karbe su ta basu wajen zama sannan tayi waya aka kawo musu ice tea kafin ta zo kansu. Kallon wajen Raihana take cike da burgewa kad'an kad'an suna hira har aka ce su taso aka shiga dasu ciki Ya Nabeela kuma ta nufi office din kawarta da tazo saboda Ya Nabeelan amma ba ko yaushe take shigowa ba ma. 

  Cike da kwarewa aka shiga wanke musu kafa dukan su daga ciki kuma ana shirya kayan da za'a soma mata gyaran jikin na alfarma irin na manyan mata yan kwalisa. Ita aka fara gamawa wankin kafar aka ce ta taso, kafar tayi wani irin kyau da taushi ta dinga kallon kafar kamar ba tata ba saboda yadda tayi kyau kwarai. Ciki aka shiga da ita wadda zata mata gyaran jikin ta soma aikin ta bayan ta sauya kayan ta zuwa rigar da ake amfani da ita idan zaa ma mutum gyaran.

   Sai la'asar likis sannan suka gama da wajen dan ma dai akwai ma'aikata itama Ya Nabeela an gyara kai da kafa haka ma Khadijan Kamal. Wani irin kyau fatar Raihanan ta fara tun a yau din kuma a kalla zasuyi kwana biyar zuwa sati daya suna zuwa ta tabbatar idan aka yi kwanakin nan ita kanta ba zata gane kanta ba. Har suka isa gida Khadija na ta koda ta Ya Nabeela na dariya suna zuwa sallar magriba sukayi suka ci abinci. Sosai Raihana ta sake da Khadijan dan tana da sakin fuska da wasa da dariya sosai a dakin da aka bawa Raihanan suka zauna suna hira har Kamal yazo daukar ta. Duk sai taji babu dadi kamar kar ta tafi haka dai ta rakota falon in da Kamal da Ya Nabeela suke maganar Aryan din da kiran da Kamal yayi masa be d'aga ba daga baya kuma wayar tasa a kashe

"Na zata ma zai dawo wallahi."

"Ai yana jin nauyin ki, da dai nine marainin wayon sa. Amma bansan me yasa ya kashe waya ba gaskiya, haka kawai baya kashe waya sai dai idan akwai yar matsala."

"Ko fushi yake na dauke masa matar sa?"

"Anya? Zan dai biya ta gidan na same shi idan yana chan."

"Ok." 

Tace a sanyaye. Gaishe shi Raihana tayi sannan ta yi wa Khadijan sai da safe ta juya ciki. Duk sai taji ta kasa nutsuwa da ta ji suna maganar ya kashe wayar sa kuma shiru be dawo ba duk da Ya Nabeelan ce tace kar ya dawo amma ai da wasa take masa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post