Rumbun Qaya page 63

Rumbun Qaya page 63

Rumbun Qaya page 63

 ***RQ***

   

   63

*****Har suka isa gida babu wanda ya sake daga maganar da Malam din yayi, dukkannin su kowa da abinda yake sakawa a ransa. Sau daya Hydar yayi magana bayan ya daga wayar Babbo daga nan kowa yayi shiru. Daki Raihana ta wuce da ita suna zuwa ta kwanta saboda ciwon kan a hankali kuma sai bacci ya soma daukar ta, gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi raihana tayi sannan ta dan karo mata ac dakin ganin tana zufa ta goshi sannan ta jawo mata kofar dakin ta dawo falon. Shirun da taji yasa ta gane sun fice daga gidan sai ta fara tunanin abinda ya kamata tayi musamman dasu Dadah zasu zo ya kamata tayi girki ba sai Ya nabeela ta kawo ba. Kitchen din ta wuce ta duba abinda zata bukata babu kayan miya sai kayan abincin a store kawai. Mayafin ta, ta yafa ta fito zuwa bq sai taga malam Yahya tare da baba maigadin yana ganin ta fito ya taso da sauri.


“Hajjaju Kina bukatar wani abu ne?”


“Eh malam Yahya, wai da cefene nake so ayi mana.”


“Sai naje ai, me ake bukata?”


“Kayan miya.”


“Toh ba damuwa, zaa samo hajjaju.”


Kudin da ta dauka ta mika masa yace 


“A ah Oga zai bada kudin ai, kiran sa kawai zan.”


“Toh,Nagode.”


Ta juya zuwa bq su gaisa da Hajara shi kuma ya dauki mota ya fita. Sai da ya isa kasuwar sannan ya kira Aryan din ya sanar dashi yazo cefene.


“Wa yace ayi cefene?”


“Hajiya ce, ta bada kudin ma nace ta barshi zan gaya maka.”


“Ok, ka siya duk abubuwan da muka saba siya, zan tura maka kudin sai a siya.”


“Ok gani ma a kasuwar.”


“Ok! Bari na saka maka.” 


Ya ajiye wayar ya tura masa kudin ya siyi komai da komai har abubuwan da raihanan bata ma san suna existing ba ya kai mata. Mamaki ne ya kusan kashe ta ganin uban kaya kamar zasu dawwama a gidan. Ta riga ta dafa white rice tuni dama sai kawai ta hada kayan miyan da chicken tayi stew ta hada musu hadin salad πŸ₯— me salad cream ,baked beans da egg. Ta gama ta dora su akan dinning sannan ta sake komawa ta duba Ammy still tana bacci. Dawowa falon tayi ta zauna shiru har aka kira laasar sannan ta tashi ta yi alwala tazo ta yi sallah a falon tana idarwa sai gasu Ya nabeela sun dawo. Dadi taji domin zaman dama ya isheta shiru ita kadai. Abinci ta kawo musu suka ci suna hira itama sai a lokacin ta dan ci kadan sannan ta koma kitchen din ta dora ruwa ta dafa spaghetti dan ba lallai kuma rice din ta ishi kowa da kowa ba, ta dora kenan Ammy ta tashi sai ta tafi wajenta ta barwa khadija ta karasa mata. A zaune ta samu ammyn tayi wanka tana gyara daurin dan kwalin kanta, mamaki Ya kama raihanan ta karasa da sauri wajenta ta tabbatar da abinda idanun ta suke gani. 


“Menene kike kallo na haka auta?”


“Ammy? Kin sanni? Kin ganini dama?”


“Kaji min yarinya, ni kike tambaya ko na gane ki? Tabbin jam.”


“Wayyo dadi, wallahi ammy na zata kin manta ni, dan Allah ammyna kin tuna ni?”


“Ikon Allah, kin taba ganin uwar da ta haifi da ta manta shi? Duk girman da zakiyi auta ba zan manta ki ba, duk kuwa da shekarun da yawa amma ke din dai kece.”


Rungume ta tayi tana kyalkyalewa da dariya, sai kuma ta d’ago cikin tsananin farin ciki tace


“Sannu Ammy, kan naki Ya daina ciwo?”


“Um da sauki, sai a hankali. Ina yayannaki, banga Abubakar ba, Allah yasa yana raye.”


“Kowa yana nan ammy, Abby, Dadah, babbo da su Hamma na, duk suna nan, su Dadah ma daf suke da karaso wa.”


“Masha Allah, ashe ina da rabon sake ganin su dama?”


“Kwarai da gaske, al’amarin Allah!”


“Lallai kuwa al’amarin Allah, Alhamdulillah Allah shine abun godiya.”


“Wallhi ammy.”


“Ina Aryan? Ina Nabeela?”


“Shi ya fita, Ya nabeela tana falo.”


“Tashi muje falon toh.”


Ta mike tsaye, rike hannun ta Raihana tayi har sun kai kofa sai kuma ta tsaya


“Auta, nan gidan waye?”


Kallon ta Raihana tayi da sauri, sai kuma tace


“Gidan Ya Aryan ne.”


“Duk da sauye sauyen da gidan ya samu, be chanja min ba ko kadan daga yadda na sanshi.”


Sai idon ta ya cicciko gaba daya.


“Muje kiga su Ya nabeela .”


Tace tana jan hannun nata, suka fito falon. Da sauri Ya nabeela ta taso ta tare ammyn a hanya ta karaso da ita falon suka zauna tana kallon ta


“Nabeela ta, kece kika sauya haka?”


“Nice ammy.”


“Masha Allah, Allah abun godiya.”


“Ina wuni ammy? Ya jikin kuma?”


“Alhmadulillah, an gode wa Allah. Sannun ku da kokari Kunji? Allah ya saka da allhairi.”


“Amin Ammy.”


“Ina maigidan naki ina yaran?”


“Duk lafiya kalou, yaran sun tafi islamiyya.”


“Masha Allah, Allah Ya raya su. Zan ga jikokina ashe, Masha Allah.”


Yadda ammyn take furucin kasan zuciyar ta a karye take, dauriya ce kawai amma ji take kamar ta fashe da kuka, musamman idan ta kalli yadda Raihanan ta, ta girma sosai, ba a gaban idon ta ba, sai dai a yadda ta ga yanayin su dukka suna cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali. Hakn ya sakata kwantar da hankalin ta. Abinci Raihana ta zuba mata taci, tana cin su Hydar suka shigo tare da Dadah, Abby da Babbo Sadeeq, Adda maimuna da Muhammad da Amina. Nan fa falon Ya kaure da murna Dadah ta rungume Ammyn a jikinta suka fashe da kuka me cin rai, Abby kuwa kamar an dasa shi a wajen idanun yaran da kasantuwar Dadah a wajen ya hanashi zuwa ya rungume matar tashi, sai kallon ta kawai yake, tana nan da kurciyar ta da kyan jikinta da ya santa dashi, sai da suka nutsu sannan sai Dadah ta tuno da Abby yana falon. Sai kuma duk kunya ta kamata, suka shige daki baki daya har su Ya nabeela suka bar ammyn a falo tare da Abbyn.


“Aisha!”


Ya kira sunan ta cikin wani yanayi na son gasgata abinda yake gani din.


“Naam.”


“Ashe rai kan ga rai? Ya Allahu ya rahmanu, nayi bakin ciki nayi kuka da na samu labarin babu ke, nayi tunanin yadda rayuwar yaran nan zata kasance babu mu dukkan mu, sai Allah ya nuna mana ikon sa, na gane ba wayon mu ko dabarar mu bace, komai da kowa yana karkashin kulawa da ikon Azza wa zalla.”


“Haka ne, ni kaina nayi mamaki yadda yaran suka zama. Alhamdulillah!”


“Alhamdulillah, Allah ya duba mu, yayi mana abinda bamu taba zato ba, duk kuwa da zaluncin da akayi mana. Wannan kadai be isa mutum ishara ba?”


“Ya isa!”


“Ya bayan rabuwa?”


“Alhamdulillah! Abinda kawai zan iya cewa kenan.”


“Toh Alhamdulillah! Alhamdulillah!”


Yace yana murmushi. Murmushi tayi itama, ta kasa misalta abinda take ji a zuciyar ta!***Ya dade sosai a Office din sai da ya tabbatar ya kusan gama komai sannan ya raba sabbin mukamai wadanda yake tunanin zasu iya kula da company idan baya nan. Yaso ya saka zainab dan tasan Aiki sosai amma kuma yana so ya fara nuna mata matsayin sa domin be yi sanyin da har zata fice tayi tafiyar ta haka kawai ba. Wake ya fito rike da takardar ya tara su a dakin da suke yin meeting baki dayan su sannan ya shiga yi musu bayanin sabbin mukaman na rikon kwarya daya bayan daya, sai da ya gama dasu sannan ya bar office din ya wuce side din da Adam yake kula dashi nan ma yayi irin abinda yayi a dayan sannan ya bar office din gaba daya. Office dinsa ya wuce ya shigar da abubuwan da zai shigar ya gama ya fito sai ga kiran Lawwali. Parking yayi a gefen hanya ya daga wayar da sauri amma sai yaji muryar sa a dan tashe


“Ya akayi Lawan?”


“Akwai matsala alhaji, matar nan ce take ta hauka da ife ife wallahi, tamkar ma ta zare ne ko menene wallahi bamu sani ba mun samu mun dai rufe ta a daki amma muna ji yadda take hauka tsaf zata iya balle kofar.”


“Subhanallahi! Me ya sameta?”


“Wallhi Allah bamu sani ba, bayan mun dauki maganar nan ta jiya bata ko nemi fitowa ba saboda tsoro, yau dai Ladi ta je ta kai mata abin kari da safe har sunyi magana ma, dazu kuma kawai ina kwance dakin zaure naji wani irin ihu, na taso da gudu na shigo gidan kawai sai ganin ta nayi suna kokawa da Ladi har ta shake Ladin tana kakari.”


“Yanzu zaku iya kula da ita zuwa safiya? Zaku iya?”


“Toh wallhi abun ne akwai tsoro, ina jin yanzu haka yadda take kokarin bude kofar, idan muka bari ta bude zata fice ne.”


“Kuma kuna ganin ba pretending take ba?”


“Naam?”


“Oh sorry, kuna ganin ba karya take ba?”


Idan lafiya lafiya, bata isa taja da Ladi ba.”


“Toh kuyi kokarin kula da ita, zan yi kokari na shigo gobe da safe in sha Allah, tunda mun samu abinda muke so cigaba da rike tan ma babu wani amfani.”


“Toh shikenan, Allah ya kaimu.”


“Amin, idan wani abu ya taso ka sanar dani kuma. “


“In sha Allah, Nagode.”


“Nima Nagode.”


Be tashi motar ba yayi shiru yana tunanin abinda yake faruwa, ganin ba zai samu amsar tunanin sa ba yasa shi hakura ya tada motar ya dauki hanyar main house dinsu. A waje yayi parking ya dan abu kawai zai dauka ya wuce, ya kashe motar ya fito ya nufi gate din, kafin ya karasa yaji alamun taku a bayan sa,

πŸ™πŸΎπŸ™πŸΎπŸ™πŸΎπŸ™πŸΎπŸ™πŸΎπŸ™πŸΎπŸ™πŸΎπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯ΉπŸ₯Ή

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post