Asalin kalmar Hausa Fulani

Asalin kalmar Hausa Fulani

Asalin kalmar Hausa Fulani

 ASALIN KALMAR HAUSA FULANI


Hausa-Fulani kalma ce da ake siffanta wata al'umma a arewacin Najeriya, wacce kuma ta daɗe ta na jawo muhawara a kafofin sadarwa na zamani, wato 'social media.' 

Tambayar da ake muhawara a kai dai ita ce, "Shin ku Fulani ne ko Hausawa ko Hausa-Fulani?"

Wasu masana dai sun yi tsokaci a kan cewa, babu wata ƙabila mai suna Hausa-Fulani, ko da yake sun amince cewa mutum na da damar ya siffanta kansa yadda ya so.

Farooq Kperogi mataimakin Farfesa ne a Jami'ar Kennesaw da ke Atlantar Jihar Georgia ta Amurka, kuma mai bincike a kan asalin ƙabilu, a wata hira da ya yi da BBC ya ce, har yanzu ba a iya samun taƙamaiman asalin kalmar Hausa-Fulani ba.

Ya ce, "Abin da na sani shi ne jaridun Legas da Ibadan ne suka sa kalmar ta shahara."

Tun a shekarar 1920 aka fara ambatar kalmar Hausa-Fulani. Kuma a cewar Farfesa Kperogi, ɗalibai irin su Ahmadu Bello sun yi amfani da ita a kwalejin Barewa sakamakon samun mutanen da a ƙabilance Fulani ne amma da Hausa suke magana.

Kansancewar an rasa yadda za a siffanta su sai aka kira su da Hausa-Fulani. Farfesa Kperogi ya ƙara da cewa, "Ina ganin ƴan siyasar Kudu maso yammacin Najeriya ne dalillin shaharar kalmar."

Ya ci gaba da cewa, hakan ya faru ne saboda wahalar tantance asalin arewa saboda addini ya yi tasiri a wanan ɓangaren.

A kwana a tashi kalmar Hausa ta zama wata kalmar da ba ƙabila take alamtawa ba.

Kamar yadda Dakta ya bayar da misalin cewa, za a iya samun Bayarbe ko Ibo wadda ya koma arewacin Najeriya da zama ya hayayyafa. Idan ƴaƴansa suka rungumi Musulunci suka kuma iya harshen Hausa sosai, shi ke nan sun zama Hausawa.

Fulani da yawa sun zama Hausawa a harshe, kamar wasu mutanen da dama.

Farfesa Kperogi ya yi bayanin cewa, a yunƙurin siffanta kaka-gidan da ƴan arewa suka yi a fagen siyasa, da farko an za ci cewa, ba Hausawa ba ne, saboda a kan ba su suna Hausa Fulani.

Ya ce, "Amma kalmar ba ta na nufin dunƙulewar Hausawa da Fulani ba ne".

A haƙiƙanin gaskiya abin da ake nufi a yanzu shi ne Musulmi ɗan arewacin Najeriya mai amfani da harshen Hausa.

Sai dai kuma wasu masanan sun ce, akwai Hausawa da Fulani waɗanda ba Musulmai ba ne.

Farfesa Kperogi ya tabbatar da hakan, sai dai a cewarsa ba su da yawa. Kuma saboda yawansu bai taka kara ya karya ba, mutane ba sa lura da hakan.

Kasancewar ƙabilar Hausa ta ɗamfara da Musulunci kuma hakan ne ma ya sa a cikin al'ummar Hausawa, waɗanda ba Musulmi ba sai ake kiransu Maguzawa.

Duk faɗin Afrika babu wani misali na mutanen da suka cuɗanya ta fuskar harshe da al'adu kamar Hausawa da Fulani.

A Rwanda ƴan ƙabilar Hutu da Tutsi sun gauraya ta hanyar auratayya, amma yawan hakan bai taka kara ya karya ba, shi ya sa babu wani abu kamar Hutu-Tutsi, saboda ko wannensu bai bar asalinsa ba.

Amma a ƙalla a Najeriya duk in da Fulani suka je, ban da kudu maso gabas, su kan ajiye Fulatancinsu su ɗauki al'adu da harsunan mutanen da suka samu.

Kuma kasancewar Hausa ƙabila ce da ta fi yawan mutane a Najeriya da ma Afirka ta yamma, Fulanin da suka shiga cikinsu sun sarayar da harsunansu da al'adunsu.

A Afirka, al'ummar Fulani su ne suka fi kowacce ƙabila yaɗuwa a yammacin nahiyar, ana samunsu a ko ina, amma ba su da rinjaye sai a Guinea. Kuma a ƙasar Hausa ne kawai suka yi cakuɗuwa ta ƙut-da-ƙut har suka sarayar da harshensu da ma ƙabilarsu.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post