Rumbun Qaya page 64

Rumbun Qaya page 64

Rumbun Qaya page 64

RQ

   Page 64

***Juyowa yayi da sauri sai ji yayi an kwala masa abu akan sa, kara yayi wadda ta jawo hankalin gateman din yayi saurin fitowa a daidai lokacin da wanda ya kwala masa abun ya ruga da mugun gudu, bin sa gateman din yayj amma kfin ya cimmasa ya haye wani machine suka bar layin, da gudu ya dawo wajen da Aryan din yake rike da kan nasa da yake fidda jini sosai,rike shi yayi da sauri ganin jira na neman kayar dashi ya shiga dashi cikin gidan da gaggawa, tasowa su Bob sukayi da gudu suka tare su, suka taimaka masa aka saka shi a mota Malam yahya da Bob suka dauke shi zuwa  asibiti dan tuni har idanun sa sun rufe ruf. Asibitin da suka saba zuwa suka je suna zuwa drs suka karbe shi direct suka wuce dashi theater room aaka shiga kokarin tsaida jinin sannan aga yanayin wound din da yake kan. Sosai suka same shi domin sun fasa masa kan mummunar fasawa kuma ya zubda jini sosai ba kadan ba, dressing wajen akyi masa bayan an masa alluran rage Zafin ciwon sannan aka tura shi zuwa dakin da za’a kwantar dashi.


Sanda suka zo asibitin Dr Mahfouz baya nan yaje duba ammy, dawowar sa asibitinn kenan ya tarar da abinda Ya faru da Aryan din, zuwa yayi ya duba shi duk da har lokacin be farfado ba sannan ya fito ya koma gefe ya kira Kamal dan sanar dashi abinda yake faruwa tunda Alhaji baya gari.

  Ganin kiran Dr Mahfouz yasa Kamal ya dakata d abinda yake yi domin yasa magana ce me muhimman ci zai yi masa. Da sallama ya daga wayar suka gaisa a mutunce sannan yace


“Sir kana gari ne ko kana wajen aiki?”


“Ina wajen Aiki Dr, akwai abinda ake bukata ne?”


“Eh toh, dama Aryan ne!”


Tsaye ya mike chak cikin yanayin tsoro yace


“Me ya samu Aryan din?”


“I think thugs ne suka yi masa rauni akai, wanda yayi sanadiyyar sun ji masa deep wound a kan masa…”


Da sauri ya katse 


“Yaushe? Aina? Garin yaya? Subhanallahi!”


“Yanzu aka fito dashi an samu nasarar tsaida jinin kuma he’s stable now, but akwai bukatar ayi masa scan domin mu gano how deep ciwon yake.”


“Yanzu kenan abun ya faru? Waye ya kawo shi asibitin?”


“Daga gida ne kamar, naga driver da wani, but su chan gidan nasa I don’t think sun san me yake faruwa, cox daga chan nake na duba Hajiya Aisha, and banji wani magana akai ba.”


“Basu sani ba, ya Allah! Shikenan Nagode Dr, za’a zo daga gidan yanzu, duk abinda ya kamata ayi kawai, zan shigo gobe in sha Allah.”


“Ok ba damuwa.”


Zagaye dakin Kamal ya dinga yi hankali a tashe, ya ma rasa abinda zai yi, wa zai kira wa zai gayawa? Baya so hankalin raihana ya tashi amma dole ne a sanar da Ita, amma ba yau ba, sai dai zuwa safiya Kila ya farfado lokacin. Lamido ya yanke shawarar kira kawai, lokaci suna tare dukkan su a falon suna hirar yaushe gamo, Dadah da Raihana suna daki suna hirar su suma Amma rabin hankalin raihanan na wajen Aryan musamman da taji shirun yayi yawa, lokaci lokaci tana duba wayar ta tana ganin time. Ganin dai shiru jiran ba zai yiwu ba sai ta fito da niyyar kawo ma su Ammy ruwa ta shiga kitchen ta kira shi amma no answer, dauko ruwan tayi da juice ta fito a daidai lokacin abby na cewa zai tafi hotel ya kwana ba zai kwana a gidan nan ba, Lamido ma yana cewa shima daga chan zai wuce da asuba zai koma wajen aiki,ajiye ruwan tayi ta koma kitchen din ta dauko cups Kamal ya kira Lamido, suka gaisa sannan ya sanar dashi abinda yake faruwa, 


“Subhanallahi, yaushe hakan ta faru? Yanzu ina Aryan din?”


Tsayawa tayi chak bata karasa kitchen din ba jin an ambaci sunan Aryan, 


“Ok ok, Yanzu zamu je in sha Allah, Allah ya bashi lafiya.”


Ji tayi kafarta na neman janta zuwa kasa, da sauri ta dafe kitchen din tsoro na shigar ta, menene ya same shi?


“Wai wasu wanda ba’a san su waye bane suka kwala masa abu a Kansa,Yanzu haka yana asibiti ma.”


“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, toh Subhanallahi, abinda ya samu Aryan din kenan? Allah sarki Shiyasa shiru be dawo ba ina taso na tambaya .”


Ammy tace cike da alhini. 


“Yaron nan yana bani tausyai, wallahi yasha wahala sosai ya kamata ace zuwa Yanzu ya huta.”


“Hutun ya zo ma Abby in sha Allah!

Sadeeq, Hydar ku tashi muje.”


“Nima dole zanje ai, muje tare.”


Abby ya mike dan be ga zaman me zaiyi ha kuma.


“Ku duba shi dan Allah, Allah dai yasa ba Wani serious abu bane.”


“Toh Amin, amma yadda naji muryar Kamal.”


“Dan Allah Hamma Nima zan je.”


Raihana da ta fada kamar wadda aka tunkudo basu ji zuwan ta ba sam sai maganar ta.


“Auta ki barsu suje kinji.”


“A ah Ammy,mace da mijinta a hanata zuwa ganin shi? Dauko hijab dinki.”


Kallon Ammy tayi itama sai ta kalle ta, sai kuma Wasu ahubuwan suka shiga dawo mata a dan zaman da tayi dasu na kwana biyu, babu wanda ma ya tabo maganar auren raihanan tunda suka zauna. Kasa magana tayi har raihana taje ta dauko Hijab dinta tabi bayansu da sauri Dadah ta biyo bayanta tana bata baki. Suna fita ammy ta kalli Dadah


“Dama auta an mata aure Dadah!”


“Eh, an mata wallahi, babu wanda yayi miki magana r ko? Abubuwa ne da yawa sai a rasa abinda ma zaa fada, sai a hankali komai zai dawo daidai.”


“Ikon Allah, lallai shekaru sun ja.”


“Kwarai d gaske, sai dai muyi fatan gamawa lafiya.”


“Tafiya zamuyi Dadah, gwara na koma gidan Maimuna akan na zauna anan, ashe nan din gidan su ne, jaira dana tambaye ta sai cewa tayi gidan sa ne?”


“Toh zata ce miki an min aure ne ammy?”


“A ah, da Amma ai sai ta bani haske, mu jira su dawo gaskiya gwara na koma chan, ba zan kara kwana anan ba.”


“Toh mu jira su din, Allah yasa yaron kalou yake, yaro me hankali da nutsuwa kai.”


“In sha Allah zai samu lafiya.”



****Kuka take a boye a motar Hydar na jinta tunda shine a kusa da ita, tabo ta yayi ta kalle shi Ya girgiza mata kai, cikin kasa da murya yace


“Ki daina kuka.”


Share hawayen tayi da bayan hannun ta Amma still wani yana sakè zubowa, tsoron ta daya kar wani abu ya same shi, bata san yadda zatayi da rayuwar ta ba. Ko da suka isa asibitin tsoronta karuwa yayi har sai suka shiga dakin da yake, drip ne a hannun sa yana kwance sambal sai dan jinin da ya bata masa jikin rigar sa kadan sai ciwon dake kansa. A baya ta tsaya tana cigaba da kukan har suka gama duba shi suka fita zuwa wajen Dr. Karasawa tayi gaban kujerar dake gaban gadon ta zauna tana kallon fuskar sa da tayi ja sosai, hannun ta tasa ta gyara masa hannun da drip din yake jiki yadda zai dinga shiga sosai kamar ya dan taba shi, sannan ta goge masa gefen bakin sa tana cigaba da hawayen. Tana zaune suka dawo dakin ta tashi ta matsa gefe Dr Mahfouz ya sake duba shi sannan yace zai tashi zuwa safiya Amma dole sai an zauna an kula dashi da duk moves dinsa kafin safiyar idan an ga wani unusual abu a kira nurse. 


“Tunda ga amarya ma ai nasan zata kula dashi sosai.” 


Ya kara she maganar da sigar tsokana tana kallon raihanan


“Ko Hydar ya zauna.”


Lamido yace, 


“No a bar matar sa, zata kula dashi ai.”


Abby yace yana matsawa wajen kofa,


“Toh amarya sai d safe, ki kula dashi sosai please, duk da dai nasan va ma sai an fada va.”


“Muma tafiyar zamuyi, sai da safe Kanwata, Allah ya bashi lafiya.”


Lamido yace sannan ya fita, sallama Abby sukayi mata da Hamma hydar Abby yace tasa Key a kofar karta barta a bude sannan suka tafi. 

   Locking kofar tayi ta dawo ta zauna a gabansa tana kallon sa, ta dade a zaune sai ta mike ta shiga toilet din dake jikin dakin tayo alwala ta hau kan dan madaidacin carpet din dake dakin ta dora dan kwalin ta akai ta tada sallah, isha tayi sannan tayi shafai da wutri tayi masa addua sosai sannan ta zauna jigum tana kallon sa daga in da take zaunen.

    Yadda taga rana haka ta kusan ganin daren domin ko bacci barawo be iya sace ta ba, sau  biyu yana motsa wa idan ta rike hannun sa sai ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da baccin. Daf da za’a kira asubah ta sakè yo alwala tazo tayi raka’atanul fajri sannan ta hau saman sofa din ta dan kwanta tana facing din gadon nasa. 

  Da safe gateman ya fito sai yaga karamar waya a kasa, hannu yasa Ya dauka ya kunna ta, sai wani tunani yazo masa, ko dai wayar wanda ya kwala wa Aryan abu ne? Ciki ya koma ya dauki wayar sa ya kira Kamal lokacin har ya dauko hanya ma, ya sanar dashi abinda ya cinta, ajiye ta yace yayi sannan sukayi sallama. 

  Wajen bakwai da rabi Ya nabeela ta iso hankalin ta a tashe, sai a lokacin Kamal ya fada mata aikuwa tasha kuka tun kafin ta karaso tana zuwa ta rungume Raihana kafin ta karasa tana kallon yadda ya sauya a lokaci daya


“Ba zai yiwu ba, kuzo ku bar kasar nan raihana, rayuwar shi suke nema gwara ku tafi, zan kira Daddyyanzu,nasan Ya samu sauki sosai gwara ya dawo kawai, ayi muku Emergency Visa ku tafi, wannan masifar har ina?”


“Su waye suka yi masa hakan ?”


“Ban sani ba Raihana, amma Kamal yana hanya, zai kuma binciko ko su waye, kuma sai sun fuskanci hukunci. Amma tabbas ba zaku zauna ba, gwara ku tafi kafin su kassara shi, gashi da naci da kafiya idan ba tafiya yayi ba Shima ba hakura zai ba.”


“Allah ya bashi lafiya.”


“Amin Amin, Dr din sun shigo?”


“Wata nurse ta shigo da asubah, tace Dr Mahfouz zai shigo anjima kadan.”


“Ok.”


Ta zauna akan sofa din tana ciro wayar ta dan kiran Daddy din.



.


*

*RUMBUN QAYA🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾😂😂😂

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post