Rumbun Qaya page 65

Rumbun Qaya page 65

 

Rumbun Qaya page 65

RQ

    65

***Ta jikin tagar dakin Ladi ta zura kanta ta leka, tana tsaye a tsakiyar dakin duk ta yaga kayan jikinta kanta a barbaje tana ta jansa da karfi sai ta cizge shi, gwalalo ido Ladi tayi cikin tsoro ta juya ta samu Lawwali a dakin zaure zaune yayi tsuru dan baya jin zasu samu damar yin bacci a ranar. 


“Gashin kanta take cizgewa fa.”


Tace masa tana rike hab’a cikin alajabi 


“Akwai matsala ,Allah yasa ba abinda ta dade tana aikatawa bane ba ya dawo kanta.”


“Shi din ne ma, karshen shegiya ne yazo, mummunan karshe dan daga gani haukan nata babban ne, Allah yasa ba na yawo bane tsirara Innalillah.”


“Yanzu ya zamuyi? Na kira shi dai yace zai shigo da safe.”


Kafin ta bada amsa sai ihun balle kofar suka ji, sannan suka ji har ta fito tsakar gidan. Kusan gware sukayi da Ladi da Lawwali wajen fita daga gidan gaba daya, dan sun tabbatar ta zo ta cimmasu zata iya lahanta su. Suna fita ta karaso zauren a guje tana ife ife, tayo waje duk da duhun da garin yayi, ta yi gaba kawai tana tafe tana ihu da surutai tana jan gashin kanta, kusan minti goma suna labe jikin wata danga, sai da suka ji shiru suka fito zuwa lokacin tayi nisa ma, dan kamar iska haka suke kada ta, hanyar suka dan bi Lawwali na haska musu touch light dinsa amma babu alamun ta, dawowa sukayi kawai suka koma cikin gidan suka kulle cike da tsoron kar ta dawo musu cikin dare.

  Gajeren bacci suka yi a daren ranar da sun ji motsi sai su fito. Da gari yayi shaa suka dan sake fita neman ta tare da Malam sani Amma babu wani alamun ta ko in da tayi, dan ko sahun kafafunta babu a hanyar sam. 


“Ko dauke ta sukayi?”


Ladi tace 


“Wa ya sani ne,lallai sharri dan aike ne, kuma komai daren dadewa sai ya dawo duk kuwa in da ka aike shi, ji sakayyar Allah.”


“Yanzu menene abun yi?”


“Mu jira zuwan sa, duk abinda ma ya kamata ayi idan yazo din sai ayi.”


“Toh, Allah yasa ma ta tafi kenan, shegiyar mata jiya da ta shake ni wallahi na hango lahira, kai nasha azaba ba kadan ba.”


“Ai karfi ne dasu.”


“Naga alama.”


Juyawa sukayi suka koma gidan suna tattauna abinda ya farun.



*****Tashi tayi ta fita bayan sun yi magana da Daddy, tayi dana sanin fada masa abinda ya faru da Aryan din dan ya rikice sosai sai da ta kwantar da hankalin sa sannan ya hakura yace ta hada shi da Mahfouz din, a office ta same shi yana dora labcoat dinsa akan kayan sa, zai taho dakin Aryan din. Gaisawa sukayi ya tambaye ta me jiki sannan tace


“Daddy ne zakuyi magana , bari na kirashi.”


“Ok.” Ya zauna akan kujerar sa ta kira Daddy din ta bashi sukayi magana,yayi masa bayanin abinda ya faru.


“Muna tunanin going for MRI or CT scan muga ko akwai internal injury ko bleeding.”


Ya karkare bayanin


“Wanne zaifi?”


“CT scan is faster that MRI, but za dai mu duba tare da colleagues dina muga abinda zaifi.”


“Please just do the needful Dr, zan fara ganin yadda za’a yi processing komai within a week, sai su wuce, na dade dama Ina binsa yazo ya samu doctors anan musamman akan severe headache din nan nasa.”


“In sha Allah zamuyi iya kokarin mu kafin su wuce din.”


“Nagode Dr, thank you very much.”


“You are welcome sir.”


“He’s so worried, naji a muryar sa.”


Yace ma Ya Nabeela yana mika mata wayar


“Nayi regretting sanar dashi nima.”


“No dole ne ai, but in sha Allah ba wani serious case bane da zai fi karfin mu, dan dai yana so su tafi din ne kawai, but anan ma we can handle it.”


“Dama da akwai plan din tafiyar tasu, suje ya huta sosai abubuwan sun yi yawa.”


“Haka ne, nasha fada masa nima yana bukatar hutu, ko maganin sa baya samu yana sha yadda ya kamata, Shiyasa har bugun ma ya samu tasiri sosai akan sa.”


“Yanzu tunda yana da mata dole ta sashi ya sha ko baya so.”


“Yes zata sashi, bari na ga Dr Fredrick sai mu shigo dakin nasa.”


“Ok Dr, mun gode.”


Ta tashi ta fita. Ammy da Dadah sun karaso asibitin sun duba shi sai suka fito waje suka zauna duk da dakin babba ne kuma vip ne, zuwa Ya nabeela tayi suka gaisa suka yi mata ya mai jiki sannan ta shiga dakin. Raihana na zaune a gabansa, hannun sa cikin nata ya rike ta kam tun dazu tana so ta tashi amma bata so ta zare hannun sai ta hakura kawai ta zauna a gaban gadon tana gadin sa. Ya nabeela na shigowa tayi saurin cewa


“Ya rike min hannun ya hanani tashi.”


“Me Ya faru Raihana? Kunya ta kike ji ko? Karki ji komai Aryan yana bukatar kulawar ki fiye da kowa a yanzu, take good care of your husband kinji? don’t be shy.”


Nodding kanta tayi tana sakè yin kasa da kanta


“Tafiya zakuyi, za’a yi masa scan aga komai daga nan zaku bi daddy New Zealand.”


“Ok.” Tace a hankali 


“Bari naje wajen su Ammy.”


Juyawa tayi suka yi kichibis da su Dr Mahfouz, ta matsa musu hanyar suka shigo ta fice ita kuma


“Madam ya patient dina?”


Dr Mahfouz ya tambaye ta yana kallon drip din hannun Aryan din


“Alhamdulillah,ina kwana?”


“Lafiya lou, wanne ne drip na nawa da aka saka masa.”


“Uku, tace idan ya kare ba zaa saka wani ba.”


“Ok.” Ya taba gefen wuyan Aryan din


“He looks stable akan jiya, I hope he regain his consciousness very soon.”


“In sha Allah.”


“Dr Ahmad me kake gani?”


“I think we should go for the CT scan din.”


“Ok, Madam wannan shine Dr ahmad, head neurologist na kano gaba daya, zamu yi ma oga scan na kai saboda mu san iya in da ya samu injury, ba wai wani babban abu bane as baya ma daukar wani babban time,.”


“Ok, Allah ya bada sa’ah, ya bashi lafiya.”


“Amjn ya Allah, zasu zo su tafi dashi.”


“Ok, mun gode Dr.”


“Yawwa.”


Suka fita, ta dawo wajen zaman ta. Ta sakè rike hannun nasa tana kallon sa a marairaice, hawaye ne taji yana zubo mata ta yi saurin share wa bata so wani ya shigo ya ganta, Amma har ga Allah zuciyar ta a kusa take, ji take kamar ta zauna tayi ta kuka, daga wannan sai wannan su kenan? Shigowa nurses din da zasu tafi da Aryan din sukayi, tayi saurin mikewa tana goge fuskar ta, suka dora shi akan gadon da zasu tura shi suka fita dashi. Da sauri ta shige toilet ta rufe ta shiga rera kuka yadda ba zaa ji ta ba.

  Ammy ce ta biyo ta cikin jin bata fito ba, bata dakin ta karasa kofar toilet din ta kwankwasa 


“Auta?”


“Umm!”


“Ok Kina ciki.”


“Umm.”  Ta sakè cewa dan bata so tayi magana ammyn ta gane kuka take. Fuskar ta, tayi saurin wankewa sannan ta fito tana goge fuskar. Kallo daya ammy tayi mata tasan kuka tayi


“Addua zaki masa auta, ba kuka ba.”


Ai kmar wadda take jiran kiris sai ta sakè rushewa da kukan ta fada jikin ammyn, a kalla yanzu itama kamar sauran masu iyaye ne, zata yi kuka a jikin mahaifiyar ta har ta rarrasheta.


“Ya isa toh, kar kizo ciwo Ya kamaki kema, ki kwantar da hankalin ki kinji? Zai samu sauki in sha Allah.”


“Babu abinda zai same shi ko Ammy? Ya sha wahala sosai wallahi, shine kuma ya gano in da kike yayi risking life dinshi for my happiness, bana so wani abu ya same shi.”


“Babu abinda zai same shi, amma sai kin daina kuka, kin zama strong kinji? Kiyi masa Addua.”


Gid’a kanta tayi, ammyn ta share mata hawayen ta sata sakè wanko fuskar ta goge ta sannan suka fito wajen da su Ya nabeela da Dadah suke zaune. 



****Ba karamin gudu yayi ba, har Allah ya sa ya iso lafiya, shi kansa be san ya iya taka mota haka ba sai ranar, sanda ya iso an shiga dashi scan din, gaisawa sukayi da kowa Ya nabeela ta taso suka shiga ciki ganin yadda idanun sa suka yi ja babu walwala ko kadan a tattare dashi


“Kamal, ka ganka kuwa?”


“Na gaji ne Ya nabeela, hakuri na Ya kare, an kaini karshe wallahi.”


“Na sani, but dole mu zama strong, for Aryan, yana bukatar mu a wannan lokacin.”


“An samu wayar daya daga cikin yan iskan, tana mota na zan wuce station zan duba ta, duk ma wanda yake da hannu akai wallahi ba zan kyale shi ba, idan akwai abu da ake bukata call me please.”


“Ok, best of luck Kanina, babu labarin Hajiya?”


“Babu, and I don’t care tana Ina ma yanzu, I hope ko a ina take tana cikin bakar wahala.”


“Amin, Allah yasa.”


“Bari naje, call me please.”


“Khadija fa?”


“Bata ma san ma shigo ba, zan kirata idan na natsu.”


“Ok, sai ka dawo.”


Bayan kamar minti talatin aka dawo dashi dakin nasa, lokacin ammy da Dadah sun je gida saboda kan Ammyn dake mata ciwo, Ya nabeela ce sai khadija da tazo bayan Kamal ya kirata ya fada mata, akwai matar Kanin Daddy dai da tazo duba shi ta kawo abincj bata ma jira an fito dashi ba ta tafi, su kuwa dama dangin maman su ba damuwa sukayi da sabgar su ba dan babu ruwan su dasu. Shiga dakin sukayi suka zauna tare da Raihanan duk sukayi jigum har kusan azahar sannan ya fara motsawa yana son farkawa. Kansa Ya nabeela ta tsaya tana dan kiran sunan sa a hankali wanda yake jin kiran a chan cikin kansa da karfin gaske. Yanayin yadda yake motsawar kana gani ba na dade bane ba, yasa Raihanan fita da sauri ta kira nurse din, ita kuma taje ta kira Dr ahmad suka shigo a tare, fita sukayi suka rufo musu kofar hankali a tashe dan yanayin sa ya tsorata su sosai, kusan mintuna biyar sai ga Dr Mahfouz shima yazo ya shiga ciki, sai chan kuma suka fito ya karasa wajen su Ya nabeelan 


“Yana fama da severe headache ne wanda dama munyi tunanin zaa iya samun hakan, amma in sha Allah ba wata babbar matsala bace ba, amma dole sai da mukayi masa allurar baccin domin yana da bukatar ya cigaba da baccin dan tashin nasa zai iya zamar masa matsala musamman ciwon kan nasa.”


“Zai samu sauki ko Dr?”


“Kwarai kuwa, zai samu in sha Allah, Kiyi masa addua.”


“Me scan din yace Dr.”


“Babu wani abu aside ciwon kan nan gaskia, wanda yake da wahalar wa sosai musamman dama ciwon sa ne, but for better result muna tunanin yin MRI.”


“Ok, mun gode Dr.”


“Ba damuwa, madam karki damu fa, ango zai samu lafiya”


Kasa raihana tayi da kanta ya wuce yana murmushi. Baba ne yazo, Baban Kamal tare da matarsa da kannen sa su biyu daga rano, ciki aka shigar dasu suka duba Aryan din sannan suka dawo wajen.



****Daga chan Office din nasu main house din suka wuce tare da yaran sa su biyu, da normal police masu black uniform,wajen da abun ya faru suka dudduba sannan sukayi ma gateman tambayoyi ya amsa sannan suka wuce wajen gyaran wayar da suka bayar domin wayar da ta fadi ta dauke dan haka taki kunnnuwa, akwai yaron da yake musu irin wannan aikin dan haka da kansa Kamal yaje wajen ya karba sannan suka sakè komawa Office aka saka wayar a computer suka dauke komai na cikin ta har call log sannan suka bar wayar a kunne suna monitoring call din da zai shigo ko text message. Call log din Kamal ya shiga yana duba numbers din da akayi kiran da wadda sukayi magana last wadda itace number da aka fi kira a ranar gaba daya. Tura number yayj ya bada umarnin a duba masa me number, da adress da komai. Within 5min aka turo masa komai akan contact din. Tashi yayi yana kallon number da Address din cikin tsananin mamaki, tunani ko hasashen sa be taba kawo mishi ba, dan haka ne ma sai da ya sake dubawa sosai ya tabbatar da hakan ne babu mistake. Cikin shigar da suke idan zasu fita operation suka fita, zuciyar sa na faman wani irin tafasa yana jin kamar ya bude chest dinsa ta ya zare ta ya huta da tsananin bacin ran da yake ciki.




*

*RUMBUN QAYA🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post