Rumbun Qaya page 71

Rumbun Qaya page 71

Rumbun Qaya page 71

RQ

     Page 71

**** Karo na biyar kenan tana taka Qaya a kafarta, tayi tafiya sosai bata san ashe nausawa take kara yi ba, babu ruwa babu abinci, duk kafar ta, ta yayyanke saboda azabar da tasha. Tayi dana sanin fitowa daga gidan da ta zauna duk ma abinda zasuyi mata suyi mata. Bata san yadda akayi ta fito ba, gashi babu ko takalmi bare dankwali a kanta. Ta kasa tuna komai da ya faru har ta samu ta fito din gashi nata san yadda zatayi ta koma ba.


“Bani da mara ba da mahaukaciya.” Tace tana kallon kayan jikinta da sukayi wani irin baki da daudar datti. Cigaba da tafiya tayi sai gata ta iso wani dan karamin gari. Safiya ce yara sun fito waje suna wasa, suna ganin ta suka mike da sauri suka fara ihun ga mahaukaciya ga mahaukaciya. Nan da nan aka taru ana kallon ta, wannan wacce iriyar rana ce a gareta? Yara ne fa suke yi mata ihun mahaukaciya. Duwatsu taga sun tsuguna sun dauka, da farko bata gane me zasuyi ba, sai da daya daga cikin yaran ya saita ta, ya jefe ta da dutsen a daidai goshin ta.


“Kai kai, kuna da hankali kuwa?” Wani Babba da ya fito daga cikin gidan yace, da gudu suka watse ita kuma ta rike kan da ya soma jini.


“Sannu Baiwar Allah.” Yace daga dan nesa nesa dan batayi masa kama da me hankali ba.


“Yawwa, aina nake nan?”


“Kina kauyen Yalwa ne, daga ina ke kuwa Baiwar Allah.”


“Nima ban sani ba.” Tace jin gaba daya ta kasa tuna daga ina take ma.


“Lafiya Ilu?” 


“Wallahi babà wata Baiwar Allah ce, yaran nan na wasa suka jefa da dutse.”


“Subhanallahi, maza kira iliya me kemis yazo ya duba ta.”


“Bana so, ku kyale ni. Sanda shegun yayan suka baibaye ni uban wa ya hana ku zuaa ku hana su, sai da suka ji min rauni sannan zaku nuna kun damu, dan baku san ni wacece ba.”


“Toh, Baiwar Allah daga taimako?”


“Bana so, duk kuma sai nayi maganin ku.”


Tayi gaba fuu ta wuce su tana rike da wajen da yake jinin, mamaki ne Ya kusan kashe su.


“Allah ya baki lafiya.” Ilu yace yana komawa cikin gidan.


    A wani kududdufi ta tsaya ta wanke fuskar ta bayan ta zagaya bayan garin, sannan tasha ruwan da bashi da kyau kwata-kwata, ta cigaba da tafiya a wahalce. Chan ta soma hango titi daga dan nisa, tayi saurin daga kafarta ta hau sauri sauri cike da murnan ta, ta karasa titin ta tsaya tana waige-waige. Motoci ne suke wucewa a guje saboda yanayin hanyar babbar hanya ce highway baa wani tsayawa. 


“Ina ma zance idan na samu motar?” Ta tambayi kanta tana kokarin tunowa amma sam ta kasa. Ji tayi kamar ana ingiza ta, ana tura ta sai kawai ta hau kan titin kanta tsaye ba tare da tunanin komai ba balle ta duba masu wucewa. Wani irin karar taka birki me karfin gaske ya shiga kunnen ta, kafin ta ji anyi sama da ita an watsa ta gefen titin, gaba daya jin ta da ganin ta ya dauke dip, ta sume a take.

   Be tsaya ba me motar, ya kara gudun motar sa ganin kamar ta mutu, Arne ne dama ba musulmi ba, kuma be san yadda zai da ita ba idan ya tsaya masifa zata zamar masa, ganin babu kowa a bayansa kawai ya take motar sa ya gudu. 

  Tana kwance a gefen titin cikin jini, wata motar yan sanda tazo wucewa, da farko basu ganta ba, sai da suka dan gota ta sannan suka lura ta cikin mirror, baya suka dawo suka tsaya suka fita da sauri.


“Wani ne ya bige ta ya gudu.” Daya yace 


“Ya Salam, bleeding take ta baki da hanci, mu taimaka mata.”


Daukar ta sukayi, suka sakata a motar su, suka dauki hanya sai cikin Kano, suna zuwa suka wuce Emergency unit da ita, aka karbe ta aka shiga duba ta. 

   Bayan likitocin sun duba ta, suka gano ta samu karaya biyu a hannu sai kafarta daya da motar tayi crushing kafar k’ashin ya dagargaje sosai. Hoton ta aka dauka sannan aka saka a social media dan gaba daya ma ta sauya kama numfashi kawai take yi amma ba karamin bugawa tayi ba.


****Ya nabeela na kwance bayan sun gama magana da Aryan a waya, ta shiga Facebook din ta zata duba newsfeed kawai sai ta ci karo da hoton da ya daga mata hankali ya sata mikewa da gudu tana kokarin jefar da wayar


“Na shiga uku, Hajiya?” Tace tana dafe kirjinta, rasa me zatayi tayi, ta juya nan ta juya chan sai ta dauki wayar ta kira Kamal, yana compound din gidan su yana zaune da computer a gaba kiran ya shigo, a rikice tayi masa sallama ya amsa yana dan matsar da system din


“Ya akayi Ya nabeela?”


“Hoton Hajiya na gani, Yanzu a fb wai ana neman dangin ta, tana Akth.”


“What?”


Ya mike tsaye da sauri


“Bari na tura maka ka gani, Itace wallahi.”


“Calm down, ki kwantar da hankali, zan duba Yanzu.”


“Ok, ka duba na tura ma a whatspp.”


“Ok.” Yace suka ajiye wayar, ya shiga whatspp din ya bude hoton, itace kuwa, sosai ya shiga shock, me ya faru da ita bayan ta gudu? Aryan? Noo ba zai yi mata komai ba. Ya jaddada sai kuma ya kasa hakuri, ya shiga kiran Aryan din duk da yace ba zai taba damun sa da duk wata magana da ta shafi nan ba tunda baya nan.

  Shirin fita suke zuwa asibitin Raihana ta riga shi shiryawa dan wuni a kwance yayi shi sai da kyar ya tashi da yaga 5 din ta kusa. Yana daura belt kiran ya shigo, yasan idan ba Ya nabeela ba toh Kamal ne dan su kadai ya kira da number din sai yan gidan su Raihana wanda su kuma yanzu basu dade da gama wayar da ita ba.


“Ya Kamal ne.” Tace tana mika masa wayar, maimakon ya karba kawai sai ya hada da hannun ta ya rike da wayar ya jawo ta sannan ya amsa wayar


“Kana jina?”


“Eh.”


“Baka samu wani labari akan Hajiya zeenat ba?”


“Na zata mun rufe wannan babin.”


“It’s very important ne.”


“Ok, ban samu ba. Har na taho babu wani bayani, ta gudu bayan ta musu pretending tana hauka, which nasan karya take.”


“We can’t say exactly abinda ya faru dai.”


“Akwai wani information ne?”


“A ah, babu.” Ya rufe masa


“Oh okh.”


“Later.”


“Ok.” Ya katse wayar


“Kinyi kyau?” Yace yana kallon ta da murmushi, shigar da tayi ta palazzo da riga ta dora babbar jacket akai sannan tayi rolling medium veil yayi mata kyau ainun


“Umm.” Tace tana murmushi. Peck yayi mata a kuncin ta, ya karasa gyara belt din shima ya dora rigar sanyin akai da katoton takalmin sa, suka fita hannun sa rike da nata. Uber sukayi zuwa asibitin wanda Daddy tuni ya isa yana jiran su. Suna shiga suka hange shi a zaune a reception, yayi haske sosai yayi fresh kamar bashi ba, ya samu lafiya sosai


“Welcome son.” Ya rungume shi yana jin soyayyar dan nasa na kara shigar shi, tunda ya samu lafiya yaje saudiyya yayi dawafi ya samu saukin abinda yake ji akan yaran nasa, wata irin soyayyar su yake ji da tausayin su musamman Aryan da ya kusan fin kowa shan wahala.


“Sannun ku da hanya.” Yace bakin sa yaki rufuwa saboda tsabar murna r ganin su, da kuma yadda yaga Aryan din ba haka yayi tunani ba.


“Daddy ina wuni?” Tace tana zame wa 


“Tashi da sauri yata, maza tashi.” 


A kunyace ta mike


“Sannun ku da hanya, kunzo lafiya?”


“Lafiya lou Alhamdulillah.”


“Masha Allah.”


“Daddy barka da rana.”


“How are you Aryan?”


“I’m good, ya karfin jukin?”


“As you can see, babu wani abu da yake damuna yanzu, na samu lafiya Alhamdulillah.”


“Masha Allah, Allah ya kara sauki.” Suka hada baki da raihana suka fada


“Amin, ya kake ji yanzu?”


“Da sauki.”


“Good, akwai excellent Dr anan, zasu duba ka sosai.”


“Thank you Daddy, Allah ya kara girma.”


“Amin.” 


Zama sukayi, duk sai suka kasa sakewa, Daddyn na lura da yadda Aryan yaki sakin jiki sam dashi, duk sai yaji babu dadi, duk da  shine ya jawo Amma still babu dadi, ace kai da yaran ka kamar Wasu strangers, yayi dana sani har ba adadi, kuma ya nemi gafarar Allah akan abinda ya aikata yana kuma fatan duk su yafe masa har Aminin sa, yana kwadayin su dawo yadda suke duk da ba abu bane me sauki ba.

  Time din appointment din ne ya cika, aka nuna masa dakin Dr din ya shiga kai tsaye. Daddy da raihana zaune duk ta takura, waya yake ta faman yi tana jin shi har ya gama sannan ya kalle ta


“Nagode sosai yata, Allah yayi muku albarka baki dayan ku kinji?”


“Amin Daddy, mun gode.”


“Sai na samu kyakkyawan labarin dawowar aisha, naji dadi matuka kuma na samu saukin abinda nake ji, a kalla zaku yi rayuwa kuma kamar kowa, tare da uwa da uba. Amma Aryan fa? Ya raga jigon rayuwar sa, yadda Aryan yayi rayuwa dashi da marayan da ya rasa uwa da uba bashi da maraba, da rai na da lafiya ta amma bani da wani amfani a gare shi, na kuntata masa, dan Allah kiyi min alfarma ‘yata.”


“Daddy…!” Tace tana zamowa daga zaman da tayi saboda yadda ta kasa sukuni gashi yana yi mata wasu irin maganganu da suka sake sakata jin nauyin sa


“Alfarma zaki min dan Allah raihana, ki taimaki rayuwar Aryan ki tallafe shi, Kisa ya manta duk wani bakin ciki da ya kunsa a baya, na tabbatar idan ya samu kulawa zai manta komai, yayi raywa kamar kowa.”


“In sha Allahu daddy, in sha Allahu zanyi iya kar iyawata, in sha Allahu.” 


“Nasan zaki iya, karki ji nauyi ne, dan ni ma tamkar mahaifin ki nake, duk abinda Kike bukata ki kirani a waya ki sanar dani kinji?”


“Nagode Daddy Allah ya kara girma.”


“Amin ya Allah, Allah yayi muku albarka, ya baku zuri’ah dayyiba.”


Kasa amsawa tayi saboda nauyin adduar a wajenta, sai yayi yake kawai ta amsa a ranta tana me cike da tausayin daddy da Aryan din ka gaba daya.

   Admitting dinsa akayi duk da ba wai yana cikin wahala sosai bane, amma suna bukatar rike shi na kwana daya suyi duk binciken da zasuyi kafin su dora shi akan magungunan da zasu raba shi da ciwon kan da yake damun shi. 



***Tare da Dr Farouk suka je asibitin, a matsayin yan uwan Hajiya zeenat din tunda tuni mutane da yawa suka gane ta aka fara kananun magangunu a garin. Bata farfado ba har sanda suka je, aka tabbatar da dangantakar su sannan aka bar su suka ganta, sukayi settling dukka bills din sannan suka fito suka zauna.


“Bata da dangi ne?”


“Tana dasu amma ba yan kano bane ba, ta rabu dasu tunda ta auri daddy, yadda ta raba shi da nasa familyn haka itama ta watsar da nata.”


“Yanzu ya za’a yi? Tana bukatar wani a kusa da ita.”


“Ban san ya za’a yi ba.”


“Ko ke zaki jinyar ne?” Yace cikin sigar tsokana


“Ni kuma?” Tace da sauri tana kallon shi


“Yes, ke din mana, ko ba zaki iya ba?”


“Ba zan iya ba.” Tace a sanyaye


“Wasa nake miki… Kinsan me?”


“Um um.” Ta girgiza kanta 


“Kina da zuciya me kyau, kinyi kokari idan wata ce ko zata rube anan ba zata taba damuwa ba,kinyi kikari sosai.”


“Bansan me yasa ba, bana iya daukar zafi akan duk abinda mutum zai mun, gashi ta bata min karshen batawa, tayi ahinda be kamata na kalle ta ba din, amma sai na kasa. Na barta da Allah duk cutar war da tayi mana.”


“Allah yayi miki albarka.” Yace yana jin dadi sosai.


***Wata tsohuwa aka samo mata a chan kasan unguwar su, ta biya ta kudi ta kwana ranar da Hajiya zeenat din, duk da babu abinda zaa mata dan har lokacin bata farfado ba, amma a kalla Ana bukatar wani a kusa, gida suka koma da daddare sai da safe zata dawo taji abinda Dr din zai je dan suna tunanin da kyar kafarta zata sakè moruwa da kyar idan ba yanke ta za’a yi ba.



****Da safe suka sake dawowa ita da Dr Farouk din kafin Kamal ya karaso dan ya taho yana hanya, Ya dan tsaya ne akan case din Adam wanda aka shigar dasu court za’a yanke musu hukuncin su.

   A Asibitin ya samu su Ya Nabeela ,zuwan sa yasa Dr Farouk tafiya ya bar su dan dama dan kar ya barta ita kadai ne. Zama sukayi ta fada masa komai abinda ya faru jiya, sannan suka shiga dakin da take. Suna shiga tana farkawa da wani irin ihu me karfin gaske, wanda sai da ya tsorata su, da gudu nurses din suka shigo suka tarar har ta fara fizge fizge tana jan kanta da hannun da babu karayar tana gunjin kuka. Danne ta sukayi amma sai da ta kusan zubar dasu, sai da sukayi da gaske sannan suka iya danne ta, akayi ma allurar bacci.


“Da kyar idan bata samu matsala a kan ta ba.” 


Nurse din tace ma dayar da suke tare


“Bari nayi ma Dr Ammar magana.” 


Suka juya suka fita da sauri

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post