Wa ya Kashe Rukayya page 2

Wa ya Kashe Rukayya page 2

Wa ya Kashe Rukayya page 2

WA YA KASHE RUKAYYA*?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.

2️⃣

Kukan jariri suka fara jiyowa daga cikin dajin wanda yasa su tsayawa cak daga tahiyar da suke a ta ke suka fara kallon-kallo zuciyoyinsu na bugawa cike da fargaba.

Amal ce ta fara nufar dajin kai tsaye ba tare da tace dasu komai ba, suma rufa mata baya su kai zuciyoyinsu na bugawa ba ma kamar Rukayya da ke ji kamar ta kurma ihu ta arta a guje.

  Baby ce wacce bazata wuce wata shida ba nannade a zani tana ta tsala uban ihu tana wulla ƙafa da hannu ruwan saman ya jiƙata sharkaf gwanin ban tausayi.

A hankali Amal ta kai hannu zata ɗauke ta tana sake haske ta da fitilar wayarta da ta kunna. 

"Amal! Badai ɗaukar ta za ki yi ba? Dan Allah ki rufa mana asiri kizo mu wuce, ki ka sani ko aljana ce?".

   Rahama ta ƙare maganar tana zaro ido.

Ba tare da Amal ta kulata ba ta ɗauko babyn haɗe dayin bisimillah.

Gaba ɗaya kallon babyn suke yi babu mai bakin magana.

Ahmad ne ya yi karfin halin cewa "Amal me yasa?


Tace "Bangane me yasa ba, so ku ke mu barta ta mutu? ko ban faɗa ba dai kunsan cewa uwarta ce muka kaɗe ta mutu har lahira muka yar da ita, to kuma sai mu bar ƴar kuma ta mutu itama? Gaskiya bazan iya tafiya in bar yarinyar nan ba".

Sororo suka tsaya suna kallonta da mamaki ruwan saman na sake yi musu duka.

Haka sukai ta jayayya amma Amal ta kafe kai da fata akan ita baza ta bar ƴar nan a nan ba sai dai su tafi da ita. Daga ƙarshe ma da suka nace akan barin ƴar sai cewa tayi su tafi kawai ita zata zo da kanta idan ma su suna tsoron tafiya da babyn ne. Haka dai suka gama jayayyar suka nufi mota tare da babyn dan kuwa Amal tafi su kafiya da naci.

             *****

"Annah! Annah!! Annah!!!"

   Firgigit ta farka daga baccin da ya ɗauketa bata shirya ba tana gadin uwar da ƴar.

"Annah ina Zainabu ban ganta ba"

  Ta ƙare maganar a ruɗe cike da kaɗuwa.

"Bangane baki ganta ba Mero ita Zainabun allura ce da za a ce ba a ganta ba?"

Matar da ke gadon kusa da su ce tace "ni fa naga wata nurse ta ɗauke ta ina ganin wani abin zasuyi mata kila dan taga kuna bacci ne bata tada ku ba nima cikin bacci na buɗe ido dai-dai lokacin tana barin ɗakin".

Hankalin Mero dai bai kwanta ba nan ta bazama niman ƴarta abu kamar wasa karamar magana ta zama babba.

           ***

Kai tsaye Danƙareren gidansu suka nufa wanda mallakin mahaifin Rahma ne ya mallaka masu suke zama a ciki tun fara karatunsu har zuwa yanzu da suke matakin ƙarshe. Ƴan aiki har uku ya aje masu suna ɗawainiya da su.

A palo suka baje inda Amal ta cirewa baby jikakkun kayan jikinta ta naɗeta da tawul tana ta jijjigata amma still babyn kuka ta ke jikinta na rawa tana ta jera attishawa akai-akai.

"Ƴan mata yanzu ya zamu yi da babyn nan kenan? Ni ina ga yunwa mafa ta ke ji gashi dare yayi ni banma san meye abinda zamu iya mata ba yanzu".

 Ahmad yayi maganar yana kallon Amal wacce ta hakikance akan babyn.

Kallon shi ta yi da kyau tana bata fuska tace "Wanka zan mata da ruwan zahi nasan danai mata bacci zatai da safe sai mu kaita Asibiti".

"Wai ke Amal kina da hankali kuwa? Taya zamu iya rainon ƴar yarinyar nan makarantar fa? Kuma ma duka duka nan da wata shida zamu gama gaba ɗaya sai muyi yaya da ita kenan? Hutu ma fa za ai da zaran an gama exams to wa zai tafi da ita gidansu a cikinmu? Mu ce kuma a ina muka samota?"

"Ke Rukayya nifa bance kowa ya so yarinyar nan ko ya ɗauke ta ba, ni ina sonta kuma ni zan tafi da ita gida kar wanda ya sake magana akan babyn nan ya isa haka nan kowa yaje ya kwanta gobe mu kaita Asibiti".

Haka suka watse kowa ya nufi ɗakinsa Ahmad ma ya nufi site dinsa da ke ta waje.

Bayan sati ɗaya tuni dukkansu sun bala'in shakuwa da babyn nan wacce suka sawa suna Amatullah bayan tayi kwana uku a Asibiti saboda zazzaɓi mai zafi daya kamata a sakamakon ruwan saman da yai mata duka inda likita ya shaida masu cewa yarinyar sikila ce, gaba ɗaya sun tausayawa Amatullah in da suke ta tattalin ta da nuna mata kauna idan zasu tafi makaranta sai su barwa masu aikin nasu su tafi inda suka shaida masu cewa babyn Laila ce ta ɗauko abarta tunda sun san Lailar tana da aure.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post