Wa ya kashe Rukayya page 3

Wa ya kashe Rukayya page 3

Wa ya kashe Rukayya page 3

 *WA YA KASHE RUKAYYA*?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.

3️⃣

Ɗakin ɗaukar karatun a cike ya ke taf da ɗalibai duka-duka ƙarfe takwas ne na safiya amman kowani ɗalibi ya halarci lecture ɗin kasan cewar sam mallamin babu wasa bare ɗaga ƙafa a tattare dashi, gashi yau ɗin suna saka ran zai masu test, duk kuwa da ba wai ya faɗa cewa zai yin bane, amman da dukkan alamu suna saka ran zaiyi ɗin, dan shi haka ya ke badai yace zaiyi abu ba, saidai ya shammace ku yayi ɗin. 

Hayaniyar ɗaliban ne ya cika ɗakin karatun, wasu na hira, wasu na karatu wasu na bacci, yayinda wasu keta faman cece kuce.

  Lokaci d'aya d'akin ya d'auki shuru, tsit ka keji tamkar ba sune keta hayaniyar nan ba, masu bacci tuni sun tashi, kowa ya kama kansa ya shiga taitayin sa.

Matashin malamin ne ya shigo, wanda k'amshin turaransa ya sanar wa d'aliban nasa ya iso.

Kyakkyawan matashi ne wanda shekarun sa na haihuwa bazasu haura 38 ba, wankan tarwad'a ne dogo sosai ga fad'i, yanada manyan idanuwa had'e da yalwataccan gashin gira dana ido, ga wani had'add'an sajensa wanda ya k'ara fitowa da k'yawun da Allah yai masa, hancin sa dogo mai k'yawun gaske.

  Sanye yake cikin k'ananan kaya, bak'in wandon Jeans ne had'e da wata jar riga mai azababben k'yau,  rigar ta d'an matse shi kad'an saita k'ara fiddo shi, k'afar sa sanye cikin wasu had'add'un takalma na maza, dagani kasan masu tsata ne, wani dank'areran agogo ne d'aure a tsintsiyar hannun sa mai kalan bak'i sai wani shek'i yakeyi tamkar diamond.

*ALIYU YUSUF ALKALI WAZIRI* kenan, matashin malamin dake lokacin sa a jami'ar ta AMADU BELLO UNIVERSITY ZARIYA,  cikin takunsa ta k'asaita ya isa gaban d'akin karatun, inda ya k'arasa sama inda ya dace ya tsaya d'in,  tsawon minti uku ya d'auka a tsaye yana k'arewa d'aliban nasa kallo d'aya bayan d'aya, idanuwan sa suka fad'a gun zamansu su biyar ɗin inda yaga wayam basu zo ba,  amma kuma babu wanda ya zauna a wajan. murmushi yasaki wanda ya tsaya a fatar bakin sa,  gaba d'aya d'aliban nasa sunyi mamakin ganin murmushin nasa dan sabon abu ne agare su, wannan ne yasa kowa ya k'ara shiga taitayin sa, dan a cewar su murmushin mugunta ne wannan.

 Cikin k'warewa ya shiga koyar dasu daki-daki, gaba d'aya hankulan su nakan sa ko motsi mai k'arfi babu maiyi a cikin su, tsawon minti talatin yanai masu darasin. 

K'was!! K'was!! K'was!! K'arar takalman nasu ke bada sauti, kasancewar wajan ya yi shuru shi yasa k'arar ya karad'e ko ina, shi kansa malamin nasu Aliyu Haydar cak ya tsaya daga bayanin sa yana kallon ikon Allah, shi dai ya san cewa babu d'alibin daya isa ya shigo mashi aji bayan shi d'in ya shigo, dan wannan rainin wayau ne babba acewarsa.

Hankalinsu  k'wance suka ci gaba da takunsu suna k'arasowa cikin d'akin karatun.

Tafiya suke cikin yanga da tak'ama,  kallo d'aya zakai masu ka tabbatar da cewar manyan yara ne su ɗin kuma ƴaƴan wasu ƙusoshin gwamnati ne masu faɗa aji a ƙasar, zaka gane hakan ne ta yanayin shigar su da kuma yanayin yanda suke tafiyar tamkar bazasu taka k'asa ba Ahmad da ya kasance namiji a cikinsu yana ta ke masu baya.

 kyawawa ne ajin farko, tsayawa  kwatanta  kyawunsu kamar bata lokaci ne.

  *RAHMA HASHEEM MATAWALLE*

   Ƴar gidan gwamna.

*LAILA FARUK MIJIN YAWA*

   Ƴar gidan deputy governor. 

*RUKAYYA HAMZA MAJI DADI*

   Ƴar gidan kwamishinan ilimi

*AHMAD TAHEER SHATIMA*

  Ɗan gidan sarki.

   Sai ta ƙarshan su ita ce *AMAL UMAR ALIYU* 

    Ita ɗin ba yar kowa bace sai ƴar babanta amma kuma ita ce ogar su mai faɗa aji a cikin group ɗin nasu sam basu cika tsallake maganar taba haka kuma duk tafi su kyau da kokari, haka kuma dukkansu saboda ita ne suke zaune a ƙasar nan suke kuma karatu a ABU saboda abotarsu tun daga primary school ta samo asali tunkan iyayan nasu su zama wani abu.

 Matasan ƴan matan da babu kamar su a cikin jami'ar, wajan k'yau da ilimi tak'ama da kuma nuna isar cewar su d'in fa wasu ne.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post