Wa Ya Kashe Rukayya? Page 5

Wa Ya Kashe Rukayya? Page 5

Wa Ya Kashe Rukayya? Page 5

 *WA YA KASHE RUKAYYA*?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.



*KAWATA KUMA UWAR ƊAKINA INA MIKO GAISUWA. WANNAN SHAFIN NA KI NE MY AUNTYSIS*🥰



5️⃣



Mummunar mafarkin da Rukayya ta yi ne ya sata farkawa a firgice bakinta ɗauke da addu'a.

  Sanye ta ke da riga da wando na bacci marasa kauri kanta sanye da hula jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Amal ta nufa ta ɗan kwakwasa tare da sanya kai ciki ba tare da ta jira an bata izinin shiga ba.


"Amal! Amal!! Amal!!

  Firgigit Amal ta farka tana rungumar Amatulla a jikinta.

  

"Gaskiya Ruky kin ɗau hakkina wlh mafarki na ke mai Bala'in daɗi ki ka katse min gashi banga yadda za a kare ba......"


"Amal anya bamu tafka babban kuskure a rayuwarmu ba kuwa?" Cikin rawar murya Ruky ta kare maganar tana mai kure Amatulla da ido wacce Amal ke ta sake runguma tamkar zata shigar da ita cikinta.


"Meye ya faru ki ke wannan maganar wai? Kalli agogo fa ƙarfe biyu da rabi wani abin ne ya faru?"


"Amal mun kashe uwar Amatulla mun wullar da ita, sannan kuma mun ɗauke babyn gaskiya abin yana damuna Amal wai dan Allah me zai hana mu miƙa yarinyar nan ga hukuma muce tsintar ta mukai in yaso sai a nimi family dinta ko za a samu......"


"What......."

  Amal ta katse ta cikin garaje.

  Baki da hankali Ruky, hakan ya na nufin duk sai mun tafi gidan yari idan zancan nan ya fito, baza a taba yarda cewa bamu muka kashe matar nan ba cewa za ai mu muka kashe ta muka ɗauke babyn sai da komai ya jagule muka kawota, wanda hakan zai bata sunan iyayanku mutane zasu yi cahh akan maganar nan zai iya zama babban abinda baki tunani iyayanku duka yan siyasa ne suna da abokan hamayya komai zai iya faruwa".

  "Amma Amal har azumi fa ya kamata kiyi tunda kece ki ke tuka motar sanda abin ya faru kuma........."


"Ruky! Dan Allah fitar min a ɗaki bana son jin wannan bayanin naki da dukkan alamu kin samu matsala a kwakwalwar ki....."

  "Ni da ke ai kowa yasan mai matsala a kwakwalwa kuma tabbas ni zanyi abinda ya kamata a lokacin da ya dace".


Da mugun kallo Amal ta bita har ta bar ɗakin.


"Babu wanda ya isa ya rabani da yarinyar nan ƴa tace ina sonta ni ce uwarta ni ce ubanta".


Cak Ruky ta ja ta tsaya daga ƙofar ɗakin Amal, idan ba gizo idanuwanta suke mata ba kamar Ahmad ne taga ya shiga ɗakin Laila a cikin tsohon daran nan.

  Meke faruwa ne da rayuwarmu haka? Ta yiwa kanta tambayar tana mai tsare kofar ɗakin Laila ɗin da kallo.

  "Kai kila dai idanuna ne me zai kai Ahmad ɗakin Laila a cikin daren nan matar aure ce fa, kuma kowa yasan yadda ta ke tsananin kaunar mijinta".

  Ta karyata kanta da kanta tana mai nufar ɗakinta.


    

           ***

Yauma course d'in Aliyu Haydar gare su, kamar koda yaushe d'akin karatun ya cika ya batse, jiran shigowar sa kawai su ke yi, Rahma ce ta dubi Amal tace, "yakama muje muga gayen nan fa akan test ɗinmu dan bana son abinda zai kawo mana tsaiko Allah Allah nake mu gama karatun nan in Amarce dan wlh Fahat ya matsa lamba nima kuma na gaji ina so in shige daga ciki".


"Eh yau nake so muje mu same shi dama da ya fita sai muje ayi wacce za ayi......"


Basu k'arasa maganar ba,  k'amshinsa ya tabbatar basu cewar ya iso, a hankali Laila ta furta, "Kurin banza kawai!, wannan turaran da yake kuri da shi da gani kunsan gaba ɗaya tattalin arzikin shi ya ke sawa ya saya kila ma harda  maula ya ke haɗawa dan wannan turaran yafi k'arfin albashin sa wallahi!," 

Ta k'arasa maganar cike da takai cin disgasu da ya yi rannan.


Ƙaramar dariya Amal ta saki tana sake kai dubanta gare sa, a take idanuwanta suka shige cikin nasa a take taji gabanta ya faɗi da sauri ta ɗauke kai.

Shima ɗauke nasa kan ya yi a dai-dai lokacin da ya ƙaraso gefen su dan hayewa sama. 


  A ƙasan zuciyarsa ya furta ƴar kyakkyawata

  Yau zan takalo rigima na sani sarai baku san komi ba in banda gigiwan tsiya da rawar kai, harda wannan ɗan daudun da ke manne da ku.


   Sanye ya ke cikin manyan kaya yayi bala'in yin k'yau tamkar a sace a ruga, cikin k'warewa sosai ya keyi masu darasin, gaba d'aya Sun natsu suna sauraran sa.


Tsawon awa d'aya yana koyar dasu, kafin ya shiga watso tambayoyi yana nuna wanda ya keso ya amsa masa wasu ɗalibai biyu ya fara tadawa kafin ya tada Ahmad ya watso masa tambaya yana mai tsare shi da idanuwansa.


Cike da natsuwa Ahmad ya soma  bashi amsa ko gargada babu wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba.


Rahma ya kuma yiwa wata tambayar itama ta mik'e ta bashi amsa kamar yanda ya buk'ata, daga k'arshe ya tada Amal yana mai watso mata tambaya mai zafi dan kawai ya ƙureta.

Amal wacce sam hankalin tama baya kansa yana kan wayarta da take ta latse latse a ciki, Ruky nata d'an taba ta tabayan ta amman ina hankalin ta yayi nisa.

 Da k'arfi ya kira sunan ta, " *AMAL UMAR ALIYU*"


  Da sauri ta d'ago manyan idanuwan ta tana kallonsa mamakin yanda akai ya san sunanta take, lallai ma gayen nan d'an rainin wayau ne!, sunana dana uba na yake kira haka.....

 Sake kiran sunan nata ya yi had'e da k'ara jefo mata tambayar tasa.


 Tsaye ta mik'e ba tare da tace komai ba.


Sake maimaitawa ya yi yana kallonta ko kiftawa baya yi.


Baki ta turo gaba tana ƙunƙuni ba tare da kowa yaji mai take fada ba. 

  Tsawon minti biyu zuwa uku bata ce komai ba shi ma baice ba ya dai tsareta da idanuwansa yana kallonta. Sai da ta mula ta sha iska kafin ta shiga shayar da shi ruwan mamaki wajan bashi cikakken amsar tambayarsa harma da karin bayani akan wanda bai tambaye taba.


Haka ya gama ya fice jikinsa a sanyaye da wani irin kaunarta da ya sake baibaye shi. 

  

Dama yau shi kaɗai su ke da shi dan haka yana fita kai tsaye suka fice ba tare da sunje sun same shi ba kamar yadda Amal din tace.

Wajan 

had'add'un motocin su masu azabar kyau suka nufa waƴanda suka gaji da haɗuwa baƙaƙe wuluk sai ɗaukar ido suke.

Ɗaya ne suke hawa dukkan su basa raba mota ɗaya kuma ta masu tsaron lahiyarsu ce.

Da sauri suka  bud'e masu kofofin suka shishiga Ahmad ya jasu suka fice a guje duk da gidan nasu yana kusa da makarantar ne.


Motoci biyu ne a harabar gidan bayan wayanda suka fita da su.

 Da sauri masu tsaron nasu suka sauko daga tasu motar suka bud'e masu k'ofar motar nan suka fito cikin tafiyar nan tasu ta tak'ama suka shige gidan harda Ahmad ɗin.

A palo suka baje gaba ɗayansu ko wacce ta cire mayafinta suna sake maida yadda akai.


Gaba ɗaya ƴan aikin nasu suka zube suna kwasar gaisuwa ga iyayan gidan nasu.


Da murmushi a fuskokinsu suke amsawa tare da tambayar su ko babu wata matsala .


"Babu matsalar komai" babban cikin su ta amsa ta ƙara da faɗin "Abincinku na bisa dinning ko nan za a sauko da su?"


Amal ce ta amsa da cewa "A barshi acan ɗin ni wanka ma zanyi ina Amatulla banji motsinta ba"


"Ranki ya ɗade tana ɗakinki tana bacci tunda akai mata wanka tasha kununta ta koma bacci ".

  Ba tare da ta sake cewa komai ba ta shige ɗakin nata dan duba ƴarta da kuma yin wanka.


 kai tsaye gadon ta nufa ta mannawa ƴar tata kiss a goshi ta tabbatar da lahiyarta kafin ta wuce toilet ta watsa ruwa ta fito d'aure da tawul,  gaban madubi ta wuce, ta yi tsaye tana k'arewa surar ta kallo,  iska ta shak'a haka nan ta ke jin wani nishadi ba tare da tasan meyasa ba.

 Murmush tayi wanda ya k'ara fitowa da k'yawun fuskarta a zahiri.


  Tafi minti sha biyar gaban madubin tana ta kalailaita, ta shafa wannan ta murza wancan ta fesa wannan ta gurza wancan, a haka dai har ta gama,  ta sanya wata had'add'iyar doguwar riga, ta fice daga d'akin kanta ko d'an k'wali babu sai wata y'ar k'aramar waya a hannunta mai bala'in kyau.

A bisa dinning ɗin ta iske su sunfara karyawa itama ta zuba nata ta soma ci kafin a hankali ta kallesu ɗaya bayan ɗaya tace "idan muka gama zamuyi magana akwai bukatar yin hakan saboda Rukayya ta zo da wata bidi'a......

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post