Wa ya Kashe Rukayya? Page 4


Health College

Wa ya Kashe Rukayya? Page 4

Wa ya Kashe Rukayya? Page 4

*WA YA KASHE RUKAYYA*

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.



4️⃣


Amal ce a gaba tafiya ta ke ko ina na jikinta na kaɗawa duk da kasancewar doguwar riga ce a jikinta amman saboda kirar jikin da Allah yai mata ko batai niyya ba sai hakan ya kasance.

Gaba ɗaya kallo ya koma kansu su kuwa ko a jikinsu tafiyar su suke hankali kwance tamkar su kaɗai ne a duka filin ɗakin karatun, kokarin zama suke bisa  kujerun da ya zame tamkar dan su aka yishi su biyar ɗin nan babu wanda ya isa ya zauna dan suna da masu goyan bayansu duk yanda su ka kai da makara basu zo da wuri ba babu mai hurumin zama a kujerun nan dan kuwa kowa yasan su waye taurari biyar.


Wani wawan tsawa ya daka masu, cikin harshan turanci ya soma faɗa ta inda ya ke shiga bata nan ya ke fita "Su waye ku da zaku shi go min aji yanzu har kuke koƙarin zama dan bakuda kunya, bayan kun d'aukewa kowa hankali daga sauraron abu mai mahimman ci, kuna hauka ne? Maza ku fice kafin ku ƙarasa bata raina in maku rashin mutunci".


   Cak suka ja suka tsaya sunai masa wani k'ask'antaccan kallo, kafin Amal taja wani dogon tsaki da k'wafa tamkar harshan ta zai fita, ta doka masa wata uwar harara da manyan idanuwanta tamkar zasu fad'o k'asa tace "ku muje"


Suka fice a d'akin karatun cikin wannan tafiyar tasu mai d'aukar hankali, har suka  bace daga cikin d'akin baibar kallon inda suka bi ba, zuciyar sa tamkar ta fasa k'irjin sa tafito, lallai yazama dole yayi maganin yaran nan babu ma kamar Amal da ya fi jin zafinta tun ba yau ba shi kansa bazai ce ga dalili ba shi dai yasan yana bala'in son yarinyar haɗe kuma da bala'in jin zafinta wanda bai san ko kishinta ya ke ko me ba ya tsani Ahmad ɗin nan da kullum yake manne dasu kamar wani ɗan daudu cikin mata.

A duk fad'in jami'ar nan su k'adai ne ke ta ka shi suke taka dokarsa son ransu but lokaci yayi daya kamata ya nuna masu iya karsu ya nuna masu cewa su ɗin fa ba kowa bane".


  Hankalinsa ya maida kan abinda ya keyi, gaba d'aya ajin kowa yasha jinin jikinsa dangane da abinda ya faru yanzu.


  Awa d'aya ya bata yana koyar dasu kafin ya rubuta masu test, hankalin yan kanzaginsu ne yayi bala'in tashi dan ganin an kori mutanan nasu gashi ya rubuta test wanda sun san  da gangan yayi hakan saboda wannan shine test d'in shi na k'arshe y har nanata masu yayi duk wanda yarasa wannan test d'in to kada ya saka ran zaici jarabawar sa.


Minti ashirin kacal su kayi yasa a k'arbar masa, ana gama had'awa ya fice abinsa.


  Zaune ya iske su bisa wani had'add'an Carpet mai kama da jikin damisa sai d'aukar ido yake, masu tsaronsu suna zagaye da su  kowanne ya doɗe ido cikin bakin tabarau kallo d'aya zakai masu ka tabbatar basuda mutunci zasu iya aikata komi akan aikin su.

  Ƙa'ida ne duk inda zasu tare suke tafiya suna tsaron lahiyarsu sai dai idan fitar sirri sukai kota satar hanya kamar dai na daran ranar.


  Manyan idanuwan ta ta watsa akan sa tare daja masa tsaki, kallo d'aya yai masu ya d'auke kansa daga barin kallonsu, ya wuce abinsa, d'aya daga cikin guy's d'in nasu yayi k'ok'arin binsa saboda tsakin da yayi, a take Amal ta dakatar dashi da fad'in "barshi ba Yanzu ba akwai sauran lokaci!".


   Ɗalibai ne suka suma fitowa daga d'akin karatun kowanne na surutu akan test d'in da Malamin nasu ya yi.


 Hamida ce ta nufosu rannan nata a had'e ta zauna kusa da su ta soma basu labarin abinda Malamin nasu ya yi sai kace sun tambaye ta kullum cikin like masu take suna gwasale ta saboda sam basu so kowa ya raɓe su sunce su biyar ɗin nan sun ishi kansu komai da komai.


Tsaki kawai Amal tayi ta ɗauke kai.


Rahma tace "karki damu Hamida indai kud'i suna aiki a duniya zamu saye Malamin nan dashi da y'an gidansu gaba d'aya, dan haka ki ta shi kije kawai mun gode".


Jiki a sanyaye Hamida ta tashi da salubabben guiwa.


Harara Rukayya ta watsawa Rahma tace "To meye na wani koranta ne ni banson wulakanci wlh".


  Murmushi Ahmad ya yi yace"zaku fara ko? Kamar wasu masu ganin hanjin juna".


Amal tace "Wlh gayen nan baida mutunci fa ji fa yanda ya disgamu na shaƙa sosai wlh".


"Kema ai kin masa tsaki wanda bai kamata ba".

  Cewar Ruky tana hararar Amal.


Hira suka ci gaba dayi abinsu cikin k'wanciyar hankali harsanda wani malamin ya shiga ajin kafin suka mik'e suka shiga suma.


  Tsawon wani lokaci malamin nayi masu darasi kafin ya fara watso masu tambayoyi,  tsit ajin yayi dan kuwa tambayar tad'an yi masu wuya, tsawon minti uku babu mai alamar mik'ewa, tambayar malamin yak'ara nanatawa cikin bacin rai amman tsit kake ji, ajin ya d'auki shuru.


 Can dai Amal ta miƙe cikin hadaddan turancinta mai dad'in saurare ta soma watso amsar tambayoyin cike da yakini da zazzaƙar muryarta.


Abin burgewa a wajan bayin Allah nan shi ne suna da matukar kokari babu ma kamar Amal din shi yasa mallaman su suke ji dasu da alfahari da su banda Malan Aliyu Haydar da duka duka watan shi shida kenan da fara koyarwar a makarantar kuma dama shekara ɗaya kacal zaiyi ya tafi.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post