Wata sakayya page 29

Wata sakayya page 29

Wata sakayya page 29

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

😭😭😭😭😭😭😭

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*

 *Wattpad nusaiba* alkamawa 

 *AREWABOOK nusaiba* alkamawa 


 *Free page 29* 

*******

_______Kasa ta sakko  ta tarar da Al'amin yana kallo su kuma su Hassan suna zaune a kasa sunayin home work din da aka basu a makaranta, "Alamin kaine ka sauko daga sama yanzu?  " girgiza mata kai yayi alamar bashi bane, "to waye a cikin ku ya sauko yanzu daga sama?" jim yayi alamar tunani, "yauwa Umma na tuna, Asabe ce ta hau sama yanzun nan da tray din abincin ki zata kai miki, kuma yanzu naga ta sauko ta nufi bangaran su" cije dan yatsa Hassana tayi lallai kuwa Asabe ta jawo ruwan dafa kanta tunda kuwa tayi min labe kuma ta saurari sirrin dana dade ina boyewa shekara da shekaru, ta ayyana haka aranta tana komawa sama, wayarta ta dauka ta kira boka ringing daya biyu ya daga nan ta gaya masa abinda ya faru kecewa yayi da wata irin mahaukaciyar dariya,yace "yanzu zabi biyu gare ki kode a kashe ta ko kuma a haukatar da ita" dan shiru tayi kafin tace, "boka a dai haukatar da ita amma banda kisa","yanzu zan ba aljani dan 'kundalo ya kawo maki wata karamar randa sinadarin haukan Asabe zai kasance a ciki ki tabbatar kin boyeta inda babu wanda zai gani balle a fasa duk kuwa ranar da randar nan ta fashe tofa ina mai tabbatar maki hankalin ta zai dawo jikinta daganan kuma haukan zai dawo kanki","amma boka babu wata hanya sai wannan idan har aka fasa randar shikkenan nice zan haukace","kwarai da gaske saiki kula" yana gama fadin haka ya katse wayar, tana nan tsaye tana tunanin inda zata boye randar in an kawo mata, aljanni dan kundalo ya bayyana cikin mummunar suffar sa, randar ya bawa Hassana jikinta na kakkarwa tasa hannu ta karba, tana amsa. 

Bat ya bace daga dakin, wata dabara ce ta fado mata maizai hana ta sakata a karkashin gado anan ne babu wanda zai iya ganninta balle har a fasa ta, hakan kuwa tayi ta daga karkashin gado ta saka yar karamar randar sannan ta maida katakwayan sannan ta saka katifa ta shimfida zanin gado.

********

Asabe kuwa tunda taji abinda Hassana take fada kwanunkan hannunta suka tarwatse a wajan abincin ciki yayi faca _faca a wajan, da gudu ta sauko kasa bata tsaya ko ina ba sai cikin dakinsu, so take ta gayawa Jidda abinda taji Hassana na fada kuma ta gaya mata amma batada inda zata samu number gidan da  take aiki kuma gashi batasan gidan ba, yanke shawara tayi data bari sai jidda tazo ganin gida saita gaya mata da yake yanzu ta dauki kusan wata daya da fara aikin tasan tabbas tana dab da zuwa gida, amma ya zatayi da Hassana dan tabbas tasan itace ta labe a bakin kofar yanke shawara tayi da zata nuna mata bataji komai ba, tana cikin haka taji kanta yayi wani mugun tsara mata ga wani abu da taji kamar ya shiga jikin ta amma batasan mene ba, dariya ta fara kyalkyalawa tana jan gashin kanta farfasa abubuwan cikin dakin  tana ihu  sannan tayo waje da gudu, da sauri Garzali ya mike tsaye ganin yadda ta fito yana ambatan sunan Allah, duk yadda yaso ya riketa karta fita amma ina ya kasa saida ta fita, a dari ya rugo zuwa falo yana haki Hassana da sauko warta yanzu kenan taga ya shigo mata falo a hargitse, "kai lfy zaka shigowa mutane haka babu naiman izini babu komi" saida taja numfashi sannan ya fara magana, "Hajiya wllhi Asabe ta haukace yanzu ta ruga waje tayi bakin titi kuma fa babu hijab ajikinta, dan Allah Hajiya ki taimaka" wani irin kallo ta watsa masa, "kaga malam in zaka koma bakin aikinka ka koma in kuma ka gaji da aikin ne kasan inda dare yayi maka, Asaban uwarka ce da duk kabi ka tashi hankalin ka, ita kadai tasan lafin da tayiwa Allah daya maida ita haka, bace ka bani guri" jiki a sanyaye ya fito daga falon gudun karya cigaba da tsayuwa ta kore sa daga aiki, "amma matar nan sam batada digon tausayi a cikin zuciyar ta yaseen" ya fada a fili yana lekawa wajan ko zai hango Asabe amma ko keyarta bai gani ba, jiki babu kwari ya dawo kan benci ya zauna, Hassana na ganin fitar Garzali ta bushe da dariya, "ba ita tayi min labe taji abinda nace ba wato taje ta tona min asiri ai gashi nan nayi maganin ta, kuma a haka zata mutu a haukace ba, waya sani ma ko ta hau kan titi mota ta banke ta banza kawai","Umma lfy naji kina ta magana ke kadai?","babu komi Alamin cigaba da kallon Ka, shi kuwa al'amin yaji sarai abinda take fada, murmushi yayi yace bara naje nasharewa baba garxali tantamarsa, yafada cikin xuciyarsa, fita yayi yana tafiya yana wani kwalisa irin ta yaran nan marasa Ji, baba garxali barka da hutawa. 

"mamaki ne yacika baba garxali sbd a Iya tsaron rayuwarsu da aminu baitaba gaishe shi ba saiyau hasali ma ya rainashi, am sawa yayi cike da mamaki. 

Al'amin yace baba ashe inna Asabe rasuwa akayi mata ko naji sanda ake gaya mata awaya, yafada cike da makirci yana dariyar gefen baki"innalillahi wainnailahi rajiun haba nifa ince, shiyasa tafi to a birkice ashe rasuwa akayi mata, to Allah yajikan rai yasa aljannace makoma, amen al'amin yace wanda yake tsaye hannunsa cikin aljihun wandonsa, to shikkenan baba bara na shiga ciki, to Al-ameen idan asaben tadawo mayi mata ta axiyya tunda bamu San garin nasu ba, kuma bani da number wayar tata, to nidai na huce ya fara tafiya yana wani gwaggwale kafafu, wani farin cikine ya lullubesa ganin hakarsa ta cimma Ruwa, yanzu shikkenan babu wanda xaiyi zargin umman sace ta aikata wannan Al amarin. 

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post