A RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 02 complete Document

A RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 02 complete Document

A  RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 02 complete Document

H U G U M A

Arewabooks:Huguma

A RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 02

          Ta hadu da mutane masu karamci,don haka bata wani jima ba ta sake sosai a cikinsu,zamu iya cewa tafiyar ta zame mata wani mabudi na alkhairi tare da sake sanin wacece ita,wanne aiki ne a gabanta?,wanne muhimmanci abbas ke dashi a rayuwarta wanda abaya duka hankalinta bai taba mata hasashen hakan ba,duk kuwa da yadda take jinsa sosai a jikinta zuciyarta da ruhinta.

         Abun ya fara ne daga yadda suka maidata kamar qanwarsu,koda a aikin hajjin kowa qoqarin tallafarta tare da nuna mata abubuwa yakeyi,musamman daya zamana ita daya ce farkon zuwa wajen,cikij taimakon Allah sukayi hajjinsu lafiya suka gama,sai ya zaman lokacin komawa gida nigeria kadai ya rage musu.

           A sannan taga kowacce hankalinta ya tattaru kan mijinta da sukazo tare,a lokacin suka lura da yadda ita din bata maida hankalinta sosai akan hakan kamar yadda su sukeyi,hajiya sha'awa ita ta fara fahimtar hakan,wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,tuntuni suka gane quruciyar dake dawainiya da ita,wadda wasu abubuwan take gaza yinsu,babu wadda taji kunyarta acikinsu,dukka suka hadu kamar yadda zasu yiwa qannensu uwa daya uba daya suka fara dorata akan sabon saiti.....sabon karatu da sabon darasi.

              Bata taba jin kunyar wasu mutane kaf rayuwarta ba irin yadda suka sanyata jin kunya,amma ta dole sukayi mata ta sake ta kuma soma bin karatun nasu.

         Abinda bata sani ba kusan kowannensu tasan halayyar hafsat ciki da bai,wannan yasa hatta gidan babu wadda tayi masa zuwa uku, lokacin da sukaga widad din a mazaunin kishiyar hafsat qaunarta da tausayin yadda zata iya zama da ita ya shigesu,wannan yasa suka samu qarfin gwiwar dora mata abubuwa masu nauyi da yawa,wadanda sukasan koda bayan rabuwarsu zai zauna a kanta ya kuma bi jikinta.

           Ranar farko kuma karo na farko da taji itama tanason kasancewa da mijinta kamar kowacce mace,ta dauki waya ta kirashi,a sannan suna tare da sauran abokansu da basu taho da matansu ba,saidai dukka kewarta ya isheshi,bayason ya fiya takura mata ko matsanta mata ne kawai,duba da situation din da take ciki,amma he really needs her,kullum kwanan duniya sake shigewa rayuwarsa takeyi.

           Cikin karsashi ya daga kiran,saidai muryarta kawai ya kashe masa jiki,ya jingina da kujerar yana saurarenta sanda take magana dashi cikin narke murya

"Bakayi kewata ba ko uncle?" Maganar tata tadan tabashi,har sai daya murmusa

"Har bansan yadda zan misalta miki ba babyn uncle,kawai dai baison takurawa maman baby dama babyn" har ranta taji dadin amsarshi

"Indai hakanne to kazo mu tafi,yau a wajenka zan kwana" mutuwar zaune yayi yana mamaki,widad dinshi ce ke fadar haka da bakinta?,ya rasa amsar da zaya bata har sai data sake cewa

"Hello"

"Than you baby,gani nan zuwa" abinda ya iya fadi kenan jikinsa yana dan rawa kadan,wanda ba lallai ne kai ka fahimta ba

"Ina zuwa" kawai yace musu yana barin wajen.

            Kiran ayarsa ya shigo wayarta sanda ta fito daga wanka,tana tsaye jikin madubin dakin nasu tana mulke jikinta da wasu oil perfumes da hajiya fanna ta bata sanda zasu fice subar mata dakin,hajiya khairi ke tsokanar hajiya fanna...

Domin sauke complete din danna wannan hoton da ke Kasa.   

A  RUBUCE TAKE (K'addarata) Book 02 complete Document

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Aslm Danallh part 2 nake nema na rasa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post