Daudar Gora Book 2 Complete Document


Health College

Daudar Gora Book 2 Complete Document

 

Daudar Gora Book 2 Complete  Document

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

........A matuƙar razane Iffah ta shiga girgiza Tajwar Eshaan jikinta na rawa, gaba ɗaya ta daburce jin jikinsa ya saki ma gaba ɗaya a kanta, hannu ta kai saitin hancinsa, ƙirjinta ya sake girgiza tamkar zuciyarta zata ɓallo daga cikinsa ta faɗi. Cikin fita hayyaci ta cigaba da ɗan girgiza kafaɗunsa dake jikinta da faɗin, “Karka min haka, dan ALLAH ka tashi, ka tashi ka faɗamin, ka faɗamin wanene kai, wanene Ajmaal? Minene alaƙarka da shi? Idan ka mutu nima wlhy mutuwa zanyi... wayyo Ummu wayyo Babiy na shiga ukuna....” kuka ta fashe da shi mai tsuma rai tana mai ɗaura goshinta kan nasa da cigaba da ambaton “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Shike nan ni Fhareedah, shike nan na kasheshi Ummu, Ummu na kashshi na shiga ukunaaaaa!!”.

      A tare Miran Jasim da Miran Arshaan dake shigowa suka ɗauki salati, yayinda Malikat Bushirat da kalaman Iffah sukai matuƙar cakar ƙirjinta tamkar saukar mashi juwa ke neman zubar da ita a ƙasa, cikin sauri Daneen Ammarah dake bayanta ta riƙota itama jikinta na rawar. Jasrah dake bayansu kam tuni tayi kukan kura akan Iffah da ruɗani ya hanata sanin shigowarsu duk da salatin da su Miran Jasim ke faman jerawa har yanzu. A birkice ta janyo Iffah baya ta shaƙeta, faɗi take itama sai ta kasheta, sai ta rabata da numfashinta. Ganin Jasrah na neman yin kisa da gaske Daneen Ammarah tai saurin zaunar da Malikat Bushirat a kujera ta nufesu. Da ƙyar ta iya ɓangare Iffah da taimakon Miran Arshaan da sai da yaga Daneen Ammarah ta zaburo sannan shima ya zabura. Yaraf Iffah ta zube ƙasa tana jan numfashi da ƙyar, yayinda Jasrah ke cigaba da zabura cikin kuka akan ita sai fa ta kashe Iffah. Ƙoƙarin tanƙwarata Miran Arshaan yake yi amma sai ta sake kufce masa. A wannan karon kam da ƙyar Daneen Ammarah ta ɓanɓare Jasrah ta hanyar sauke mata mari itama.

        Ɗifff kowa ya ɗauke wuta a ɗakin sai kakarin wahalar da Iffah keyi, dai-dai nan kuma Sayeed Aashiq Ali ya iso da likitoci, kasanwarsa uba a gare su a tsawace ya basu umarnin duk su fice. A kaikaice Miran Jasim da Miran Arshaan suka dalla masa harara kafin su fice, Daneen Ammarah ta taimakawa Malikat Bushirat da bata tofa ko kanzil ba har yanzu, Miran Arshaan kuma ya kama Jasrah. Iffah kasa tashi tayi dan da gaske ta shaƙu, dole sai da aka taimaka mata itama. Da ƙyar aka iya ɓanɓare hannun dake cikin na Tajwar Eshaan har yanzu tana kuka kamar ranta zai fita. Sashenta aka maidata, tare da sake zagaye sashen Shahan-shan ɗin da tsaro na musamman. Likitansa da wasu ƙwararrun likitoci biyu dake a kansa domin ceto rayuwarsa tuni bincikensu ya gano musu dafin macizai da guba da ya sha. Sun sami nasarar kashe kaifin dafin macizan, sai dai sun tabbatar da gubar ta fara ma jikinsa illa, idan kuma ba'a gaggauta yin wani abu ba zai iya rasa ransa duk da a yanzu ma dai sai abinda ALLAH yayi.

       Hankalin su Malikat Bushirat da gaba ɗaya ta gama fita a hayyacinta ya sake tashi, dan gani suke ma Tajwar Eshaan ya rasu ne likitocin na ɓoyewa ne kawai. Saboda duk wanda ya ga a halin da aka samesa bazai taba sakankancewa zai rayu ba. Malikat Haseena tsohuwa mai ƙarfin hali da jarumta, duk da yanayin da nata jikin yake bata gaza nuna ƙoƙarin ta ba. 

     Da taimakon Daneen Ammarah aka maida Iffah dake matsanancin kuka tamkar wadda ta zautu sashenta, suna shiga ta riƙo kafaɗunta cikin tashin hankali tana mai girgiza ta, “Ibnati kice min ba haka bane kar zuciyata ta buga, dan ALLAH ki faɗa mana gaskiya miya samesa, minene ya faru?”. 

   Babu alamar Iffah zata kare kanta, sai ma wani irin karkarwa da jikinta ya farayi hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta. Sai ma kawai ta tafi luuu ta zube ƙasa....

      ★A firgice Iffah ta farka daga barcin da likita ya sakata na dole. Dan tun bayan shafa mata ruwa ta farfaɗo yanda take kuka da surutai sai tai kamar wadda ta zautu. Daneen Ammarah da ke kallon al'amarin nata matsayin ruɗani ne suka saka doctor danƙara mata allurar barci gudun kar wani abu ya samu brain ɗin ta. Saurin riƙota tai cikin muryarta data sha kuka ta shaƙe take faɗin, “Ibnati kwantar da hankalinki...”

      “Mamy hankalina bazai taɓa kwanciya ba. Dan ALLAH a wane hali yake? Ya rasa ransa ko? Ku kaini na sake ganinsa karki ce a'a dan ALLAH Mamy”. Duk wanda ya ga yanda Iffah ke jero waɗan nan tambayoyi yasan har yanzu a birkice take, dan tuni hawaye sun sake ma fuskarta kaca-kaca. Riƙota Daneen Ammarah tai ta rungume itama tana nata hawayen...

    A tsawace Jasrah data faɗo musu babu zato ta bama jami'an dake a bakin ƙofar izinin shigowa ɗakin. Daneen Ammarah tai saurin dakatar da ita itama a ɗan zafafe.

      “Jasrah!! Ki dawo cikin hankalinki, idan kin manta bara na tuna miki. Ita ɗin Zawjata-almilk ce, ba hadimar daular ruman ba, ba ɗakin barcinta ba koda falonta haramunne shigarsu.....”

        Itama Jasrah cikin rufewar idon ta tari numfashin Daneen Ammarah “Nima idan kin manta bara na tunatar dake Daneen Ammarah. Ada wannan abar ke amsa sunan da kike tunanin zai bata waccan darajar da kariya, a yanzu ko sunanta ƴar ta'adda, mai kisan kai, kisan kan ma na Shahan-shan.....”

    “Kin tabbatar da ita ta aikata?”.

Ta katseta itama a fusace.. “Mikike buƙatar ji bayan wanda kunnuwanmu sukaji? Da wanda idanunmu suka gani?”.

        Rikici ne yake neman ɓarkewa a tsakaninsu, kowanne na ƙoƙarin ganin ya tabbatar da gaskiyarsa akan Iffah. Abune da bai taɓa faruwa ba, dan akwai girmamawa tsakaninsu musamman kasancewar shekarun Daneen Ammarah sama dana Jasrah. A yanda suke a fusace su duka ya sake hargitsa kan Iffah da gaba ɗaya ta daina gane komai, sai ma hajijiya da ke neman son sake zubar da ita a ƙasa tai nasarar jingina da bango.....

    Domin sauke complete book 2 din danna wannan hoton da ke kasa.


Daudar Gora Book 2 Complete  Document

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post