Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 98

Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 98

Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 98

"Bayan komawarsu hannun kishiyar babata,Sai hankalin mu ya dawo kan tunanin a ina zamu ga uwar yaran nan,Nemanta muka bazama yi acikin unguwar nan ruwa A jallo,duk wasu gidajen masu unguwanni na kewayen mu mun cigita haka ma ofishin yan sanda,tsawon lokaci ana nemanta bamu same ta ba,Hankalinmu ya tashi,Saboda sanin cewa Yarinyar nan bata da kowa,Gashi tabar gida a wani yanayi na ta6in hankali,Ga ƴa'ƴanta dake buƙatarta,hakan yasa bamu yi kasa a gwiwa ba ni da baban umari muka kai cigiya awani gidan Redio amman shiru kake ji ba Abu babu dalilinta Allah kaɗai yasan ina ta nufa don kasan garin kano da faɗi,aƙarshe muka fara zullumin anya Abu na'a garin nan ma kuwa,hakan yasa muka hana idonmu bacci wurin rokon ubangijin sammai da kassai da ya bayyana mana ita cikin aminci ya kareta aduk inda take,tsawon lokaci muna ta rokon Allah ba tare da gajiyawa ba,Ana haka kwatsam wata rana muka samu labarin bayyanar Abu ta hanyar Sanarwa a gidajen radio dana talabijin cewa Ana neman danginta,tare da adireshin asibitin da aka kwantar da ita sakamakon motar wani bawan Allah da ta bugeta a saman titi tana gararanbarta shine ya kaita asibiti ya kuma bada ayi cigiyar danginta,koda sanarwar nan ta isar mana jiki na rawa,Ni da Maman sadeeq tare da yaron nan ɗan wurin makwabcinmu muka kwasa muka tafi asibitin,ba ƙaramin daɗi muka ji ba da muka samu abu zuciyoyinmu suka cika da farinciki,duk da babu hankali atattare da ita,A lokacin likitan dake kula da ita ya buƙaci akawo wani makusancinta,wata'ƙil adace ta dawo cikin hayyacinta idan tayi ido biyu da ƴa'ƴanta da take yawan ambaton sunansu,jin haka yasa na yanke shawarar zuwa katsina domin in taho da yaran nan,ko Allah zaisa adace abu ta dawo cikin hayyacinta,alokacin nayi kokarin kiran lambar tsohuwa don in sanar da ita game da zuwa na don a shirya ma yaran amman a kashe,hakan baisa nayi tunanin wani abu ba,don dama mafi yawancin lokutta wayar tata na kasancewa a rufe sai anyi sa'a ake samu,ahanzarce na shirya zuwa katsina,Sai dai kash!wani mummunan labari ya riskeni a lokacin da naje unguwar da suke,Na rasuwar ita mariƙiyarsu Kishiyar babata tsohuwa,Sannan kuma naji cewa an liƙa masu ƙazafin maita,wai sune suka kashe ta saboda an ga kumfa a bakinta kamar taci guba,Hankalina yayi mugun tashi saboda ina da tabbacin cewar yaran abu bazasu ta6a aikata hakan ba,Ni shaida ne akan yaran,nayi baƙin ciki sosai kamar zan haɗiyi zuciya in mutu lokacin da Makwabcinsu ya rakani police station ɗin da aka kulle yaran,ƴan sandan da muka samu a wannan lokacin sun tabbatar mana da cewa,a nan police station ɗin aka kawo case ɗinsu,sai dai daga baya sun bar hannunsu sakamakon ciwon ɗaya daga cikinsu daya tashi aka kaisu asibiti Anan ne wani babban Jami'en Soja ya kashe Case ɗin gaba ɗaya,Shine silar barinsu asibitin,kamar zanyi hauka alokacin,Saboda tsabar takaici,na nace akan dole ƴan sandan nan su haɗani da mutumin daya kar6i yaran,Amma suka sanar dani cewa su kansu basu san wanene ba,Saboda basu bane asalin waɗanda case ɗin ya mutu ahannunsu ba,waɗancan anyi masu canjin wurin aiki,A ƙarshe dana takura masu na dinga zarya a police station ɗin akan su faɗamun waye wannan jami'en sai su kayi mun barazanar idan na ƙara zuwa zasu ɗaure ni,Tun daga wannan lokacin,jiki a mace nadawo kano alokacin aka sallami Abu bayan likitan dake kula da ita ya bada shawarar amaida ita asibitin masu ta6in hankali amman muka dawo nan gidana da ita da tunanin yi mata addu'oi don alokacin ina ganin kaman harda sihiri atare da ita,haka na dukufa yi mata addu'oi ba dare ba rana amman sauki dai sai wurin Allah,yadda taga rana haka take ganin dare sam bata bacci,sai sambatun Babanta da ya'yanta,in takaice maku dai Abu buge buge ta fara tana kokarin guduwa,Babu yarda muka iya muna ji muna gani haka muka dauki Abu muka kaita Asibitin mahaukata......"daƙyar ya ƙarasa maganar saboda kukan daya zo mashi,yana kai ƙarshen maganar ya fashe da kuka,tuni hawaye sun wanke fuskokinsu gaba ɗaya,Musamman Sehrish sosai take kuka,

  Muryar Abusufyan na kerma yace"Ya..yanzu...a wani psychiatric ne aka kaita,"

  Maman sadeeq ce ta bashi amsa da cewa"Tana a Dawanau Psychiatric Hospital,ko watan daya gabata sai da muka je gano ta,baiwar Allah tana cikin halin ha'ula'e,gwanin ban tausayi,duk in muka je kai mata ziyara,haka zamu sameta tana ta kuka tana sambatun Ya kashe mata mahaifinta,Ƴa'ƴanta Suna ina,akawo mata ƴa'ƴanta,kada ya kashe mata su,"

Jin wannan maganar yasa Sehrish ta ƙara sautin kukan nata sosae,

  "Inason ganinta yanzu,"Abusufyan ne yayi maganar tare da miƙewa jikinshi na rawa yace"dan Allah idan ba damuwa,Ku taimaka ku jagorance mu izuwa asibitin,"

  Miƙewa suka yi gaba ɗayansu,Baban Sadeeq yace"nafi kowa farin cikin wannan ranar,duk da ina da uzuri a makaranta,Zan iya dakatar da komai,dan In raka ku muje a tare,"

  Ɗaga hannu Abusufyan yayi sama yana godiya ga Allah,Ita kanta Sehrish tsantsar farin cikine ya rufe ta,

  Atare suka fito daga cikin gidan,a ƙopar gidan suka tsaya,Abusufyan ya ɗauko wayarshi tare da dannawa Sgr kira,Bayan ya amsa kiran anan yake sanar dashi cewa Zasu wuce Dawanau Psychiatric Hospital,Sgr yace su haɗu acan,"


A back seat na motar Baban Sadeeq tare da Maman Sadeeq suka shiga suka zauna,Yayin da Abusufyan ya shiga mazaunin driver,Sehrish na a gefenshi,ganin yadda hannunshi ke ta kerma wurin ƙoƙarin tashin motar yasa tace"Daddy,Anya zaka iya driving ɗin nan"?

  A ruɗe yace"Daughter,ki ganni kawai,ba zaki gane halin da nake ciki ba,Am so eager to see her,Kamar nayi fiffike,"

Murmushi ta ɗan yi,Ita kanta ji take da ace tana da fiffike da ta tashi sama don ta ƙarasa asibitin da wuri,


da gudun gaske ya fisgi motar kamar zasu tashi sama,cikin ƙankanin lokaci suka ƙarasa asibitin,


*DAWANAU PSYCHIATRIC HOSPITAL*


A dai dai lokacin da Abusufyan yake ƙoƙarin shigar da motarsu cikin asibitin,Sai ga Motocin Sgr da jiniya mai sautin gaske,sun shararowa a jere,Jibga jibgan sojoji ne a saman motocin bana wasa ba,ko shugaban ƙasa albarka,tuni mutane suka dare aka bar masu hanyar su kaɗae,

A daidai bakin gate din aka tsaida jiniyar,kafin motocin suka shiga cikin Asibitin, Motar Abusufyan ce ta fara shiga sannan nasu suka rufa masa baya,wasu daga cikin sojojin dake a motar ƙarshe ne suka diddiro suka ƙame a bakin gate din shiga sai faman mazurai suke yi kowannansu hannunshi na riƙe da ƙatuwar bindiga gwanin ban tsoro,parking ɗin motocin su kayi,buɗe motar Abusufyan yayi tare da fitowa daga ciki,ya zagaya ya buɗema Su Baban Sadeeq motar suka fito,Sannan itama Sehrish ta fito,tana ƙarewa asibitin kallo,tun kafin ma su shiga ciki,ta fara ayyana yadda zata samu mahaifiyarsu,duk da tana cikin damuwar halin da zasu same ta,


Fitowa Armstrong yayi daga cikin Motarsu,ya zagaya tare da bude mashi,A hankali ya zuro ƙafarshi daga cikin motar,Kafin ya ƙarasa saukowa daga cikinta Masha Allah,Open shirt ce sanye a jikinshi white colour,rigar ta bayyana Ƙirar faffaɗan ƙirjin nan nashi,Cos bai sanya button ko ɗaya ba,a buɗe yabarta sai farar vest,Dogon wandon jikinshi black colour ne,Wankan black & white ya ɗauka,ƙafarshi na sanye cikin oxfords shoes,daga saman sumar kanshi kuma ya sanya facing cap black,Eyes ɗinshi na manne da Sunglasses,Wa'iyazubillah Ya haɗu iya haɗuwa,kamar a buga a jarida,

Duk da yanayin da suke ciki hakan baisa sun ƙi kallon wankan nashi ba,Musamman Babban sadeeq da kuma Maman sadeeq,tare da sauran jama'ar dake zarya a cikin asibitin,Yayi matuƙar jan hankalinsu,Ita kanta Sehrish sai da ta girgiza da irin wankan da ya ɗauka,


Kama hanyar shiga ciki su kayi,Baban sadeeq ne agaba shi da Maman sadeeq,Abusufyan da Sehrish na abayansu,yayin da Sgr tare da Armstrong suke a biye dasu,sai wasu daga cikin security,mutum biyu dake ruƙe da jibga jibgan bindigogi,suna take mashi baya,a bakin OPD suka ƙame,yayin da Sgr da Armstrong wanda ƙugunshi ke manne da bindigu pistol guda biyu suka shiga ciki,batare da sunsha wahala ba saboda su Maman Sadeeq sun san asibitin,suka nufi wurin da nurses suke,wato nurses station,Anan suka taras da Nurses ɗin dake Duty,koda nurses ɗin nan sukayi arba dasu,gaba ɗaya hankalinsu ya koma akan Sgr,kallon ƙurulla suka shiga binshi dashi,

Gyaran murya Abusufyan yayi masu hankalinsu ya koma akanshi,A natse ya soma magana"Sannunku da aiki,"

  Atare suka haɗa baki wurin amsa mashi"Yawwa yalla6ai,munayi maku barka da zuwa,"

   gabatar masu da kanshi yayi tare dasu Sehrish kafin yace"akwai patient ɗinmu dake anan asibitin,munzo dubata ne,'

  ɗaya daga cikinsu ce,ta kai hannu gaban drawer chest ɗin dake a jikin table ɗin gabansu,tana ƙoƙarin zaro roster ɗinsu,tace"Zan iya sanin sunan mara lafiyan naku,"

Abusufyan yace"Sunanta Zainab ibrahim buzuwa,"yayi maganar tare da kallon baban Sadeeq,don yaji idan ya faɗa dai dai,jinjina mashi kai yayi alamar eh,

  A saman table ɗin gabansu ta ajiye patients roster ɗin,tana dudduba sunan marasa lafiyan,

  "Last week,an canza ma wasu daga cikinsu wurin zama,bansan ko kuna da masaniya akan hakan ba,"acewar nurse ɗin 

  Kallon juna sukayi hankalinsu aɗan tashe fargabarsu kar ace,an ɗauke abu daga asibitin,

  "Yawwa,itace Zainabu ibrahim buzu ko"?

Har suna haɗa baki wurin cewa "eh,itace,

Murmushi Nurse ɗin tayi tare da cewa"Zainab tana a female ward B,"kallon abokiyar aikinta dake a gefenta tayi tare da cewa"kiyi masu jagora izuwa ɗakin da Zainab buzuwa take,"Amsa mata tayi da toh,sannan ta fito tare da nufar wani corridor,gaba ɗaya suka bi bayanta,kowa da abunda yake saƙawa aranshi,jikin Sehrish dana Abusufyan sae kerma yake yi,duk sun sha jinin jikinsu,


Tun kafin su ƙarasa ward ɗin,mahaukatan dake a killace suka fara kwala masu kira,

  "Yalla6ai,yalla6ai,"Sehrish ba ƙaramin tsoro taji ba,gasu nan gwanin ban tausayi,sae faman zuru hannuwansu suke yi daga cikin bars ɗin,

  "Baiwar Allah!"wata mahaukaciya ce ta kwala ma Sehrish kira,tana nuna ta da hannu,a firgice Sehrish ta juya tana kallonta,Washe mata haƙora tayi tana kashe mata ido ɗaya tace"ki ce wa mijinki ya dinga sanya Niƙabi a fuskarshi,in ba haka ba wlh za'ayi maki kwacenshi,Don mu nan da kike ganin mu ba cikakken hankali ne damu ba,"

 

  Ba sehrish ba,hatta Sgr sai da ya ɗan murmusa,ba ƙaramin dariya ta basu ba,

  Suna cikin tafiya wata mahaukaciyar kuma ta ƙara kwala masu kira tana fadin"Wayyo Allah,Farin namiji ko maye ne nidai inaso,Ya Allah ka bani fari dogo kyakkyawa,kalan yan kasan waje,In biya sadakin shi ayi mana aure,"tana magana miyau na zalala a bakinta,

  A rude Sehrish tace"Nashiga uku,Wannan wani irin kyau ne da har mahaukata ma suke santinshi"?acikin zuciyarta tayi maganar,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,tajiyo wata mahaukaciyar kuma tana tambayar wai nawa ne farashinshi,

  "Yalla6ai..."hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,jin yadda suke ta kwaɗa mashi kira,duk da jikinta yayi sanyi,tsananin tausayin mahaukatan ne ya kamata,nan take ta shiga tunanin ko awani hali zasu samu oummansu,

  Tana cikin wannan yanayin na damuwa taji hannun Sgr a cikin nata,ɗan juyawa tayi tare da kallonshi,adai dai lokacin shima idon nashi na akan fuskarta,kallon juna suka shiga yi,bakomai ne ya faɗo mata aranta ba,face irin haukan da yayi mata adaren jiya na sauraye,yayin da shima abunda yake tariyowa kenan acikin kanshi,yadda ta tsaya kore mashi saurayen nan,ta ba shi kyakkyawar kulawa har ya samu bacci,ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba,

  Gaba ɗaya sun shagala da kallon junansu,

  Muryar wata mahauciyarce ta kuma katse su da cewa"Ranka shi daɗe,Amma dai sabon aure ne ko?Wlh kunyi kyau kun dace da juna sosai,Wlh har kun tunamin da mijina...."tana faɗin hakan ta fashe da kuka mai sauti,atare suka kai idanunsu wurinta suna kallonta,Cikin shessheƙar kuka tace"Yalla6ai dan Allah ka kula da matarka kuyi zaman lafiya,kada ka wulaƙantata,ka bata kyakkyawar kulawa,Musamman in tasamu ciki,"ta ƙarasa maganar tana matsar kwalla,

Wata irin kunyace ta rufe sehrish,

Maman sadeeq ce ta kalli mahaukaciyar tare da cewa"baiwar Allah,meya faru da mijin naki?baki bamu labari ba,". 

  Hannu tasa ta ɗan share hawayenta kafin tace"Naso shi sosai,Munyi aure har mun haifi ƴa'ƴa dashi,babban abun takaici,A wurin haihuwarshi mahaifiyarshi ta mutu da cikinshi,"tana kai ƙarshen zancen nata ta rushe da kuka,.  

  Gaba ɗaya suka fashe da dariya,hatta Abusufyan dake acikin damuwa sai da ya ɗan yi murmushi,Haka Sgr shi kanshi baisan ya saki wannan kyakkyawan murmushin nashi ba,Zuba mashi ido Sehrish tayi tana kallonshi,dimple har biyu suka lotsa asaman fuskarshi,abun yayi matuƙar tafiya da hankalinta,koda ya gane cewa shi take kallo,nan take ya ɗauke murmushin ya tamke fuskarshi,

  A dai dai lokacin da suke ƙoƙarin karya corner su shiga wani ward ɗin,kwatsam suka ji hayaniya na tunkarosu,da sautin takalman mutane,hankalinsu a matuƙar tashe suka kai idanuwansu wurin don suga meke wakana,

  Wata mahaukaciya ce,ta 6allo daga wurin da aka killaceta,da gudun gaske,blue uniform din jikinta duk sun yayyage sun fita hayyacinsu,ƙafafunta ba takalma,gashin kanta duk ya hargitse ya rufe fuskarta gaba ɗaya,a bayanta kuwa likitoci ne da wasu ma'aikata suka biyota suma a guje,suna ƙoƙarin dakatar da ita,

  "Ki tsaya!ki dakata anan!dan Allah ataimaka ataro mana ita,mara lafiya ce ta kufce mana,"ɗaya daga cikin likitocin dake biye da ita ne yayi maganar,hannunshi na ruƙe da syringe,yayi annoucement ɗinne don asamu wanda zasu taimaka wurin damƙo masu ita,

  Duk tabi ta firgita ta ruɗe,ko kallon gabanta batayi,da dukkan ƙarfinta take yin gudun gashi sumar kanta duk ta zubo ta rufe mata har idanuwanta,ita kanta batasan wurin da zata dosa ba,burinta kawai tabar hannun masu fararen kayan dake biye da ita,

  Sai gara likitocin takeyi duk sun galabaita,gadan gadan ta tunkari wurin da su Sehrish suke,Naɗe hannun riga Abusufyan ya shiga yi,haka Sgr ma he's ready to help,ba'a maganar Armstrong da yayi shirin yi mata ɗaukan jariri, jira kawai suke ta ƙaraso wurinsu,su cafke ta,

  Tunkan ta ƙarasa wurinsu,ƙafafuwanta suka harɗe gaba ɗaya ta tafi a karkace zata kife ƙasa,da sauri Abusufyan ya damƙota,ta faɗa ƙirjinshi ta tsorata sosai,ƙankame shi tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,jikinta sai kerma yake yi,

  Ƙarasowa likitocin su kayi suna faman sauke ajiyar zuciya,

  "Yalla6ai,mun gode sosai,ba ƙaramin taimako kayi mana ba,baiwar Allah nan,daga shiga yi mata Allura ta kubce mana,ta bamu wahala sosai,"ɗaya daga cikin likitocinne yayi maganar,

   Ɗayan doctor ɗin dake a gefenshi yace"Allah ya taƙaita wahala,Da bamu son inda zata dosa ba,"

..su uku ne likitocin sae Nurse ɗaya dake a biye dasu,

  Hannu Abusufyan yasa yana ƙoƙarin 6an6arota daga jikinshi,ae kuwa a tsorace ta ƙara ƙankameshi tana faɗin"dan Allah kada ka bari su tafi dani,wlh ni ba mahaukaciya bace,da hankalina,ƴa'ƴana nake nema,dan Allah ku kaini wurin ƴa'ƴana kar a kashe mun su suma,koda sau ɗaya ne in sanyasu acikin idanuwana,"

  Rasss! yaji gabanshi ya faɗi,Hatta Sehrish sai da gabanta ya faɗi,saboda jin muryar Mahaukaciyar da tayi maganar,"

  Ƙarfi yasa ya ɗaɗɗago da kanta,daga saman ƙirjinshi,Hankalinshi a matuƙar tashe yake kallonta,ta runtse idanuwanta jikinta sae faman kerma yake yi,

    Bazai ta6a mantawa da fuskar abunshi ba,haddar da yayiwa fuskarta bamai gogewa bace,Bazai ta6a mantawa da ita ba,duk irin canzawar da zatayi,

  Muryarshi na kerma ya ambaci sunanta da ƙarfi"ABU"!gaba ɗaya hankalin Sauran ya dawo kansu,

   da ƙarfi Sehrish ta Ambaci sunanta"OUMMA!!"a firgice mahaukaciyar ta juya tana kallon Sehrish da tayi magana,duk tabi ta ruɗe,hannu tasa ta dafe kanta wani irin jiri ta dinga gani acikin idanuwanta,Nan take jikinta ya soma kerma,sumewa tayi gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa,da sauri Abusufyan ya dawo da ita jikinshi sosai ya ƙanƙameta,Lokaci guda hawaye suka shiga wanke mashi fuskarshi,Sehrish kuwa tuni ta fashe da matsanancin kuka,Na farin cikin ganin Oummansu,

   Kowa fuskanshi ɗauke da farin cikin ganinta da su kayi batare da sunsha Wahala ba,likitocin da suka biyota,duk jikinsu yayi sanyi,musamman yanayin da suka ga mutumin ya shiga,tare da yarinyar dake a gefenshi,ta wani 6angaren kuma fargaba suka fara yi kada ace wa'adin zaman abu ya ƙare a asibitin,Saboda sun saba da ita,ko acikin mahaukatan dake a Gidan,

  Gyaran murya Sgr yayi tare da cewa"We don't ave time to waste here,Uncle zamu wuce da ita gida ne,idan yaso Dr ɗin dake kula da ita,Sai ya bi mu can,"

  Hankalin ɗaya daga cikin Dr ɗinnan ba ƙaramin tashi yayi ba,yanayin yadda ya furta"tafiya za kuyi da Zainab"?

  Jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"Zamanta acikin asibitin nan ya qare,"ya ƙarasa maganar har lokacin hawayen basu daina sauka akan fuskarshi ba,gashi ya ƙanƙameta ajikinshi,ko warin jikinta baiji,

  A ruɗe Dr ɗin yace"Haba yalla6ai,mezai hana ku barta anan acigaba da duba ta,har Allah ya Bata lafi......."kasa ƙarasa maganar yayi ganin irin kallon da Sgr yake yi mashi,duk sai ya sha jinin jikinshi,

Sai lokacin Baban sadeeq ya tsoma baki,

  "Doctor,Wannan da kake gani Mijinta Ne!wannan kuma ƴarsu ce,yaran da take yawan ambato acikin bakinta,To wannan ɗaya ce daga cikinsu,Ƴan ukune gare ta,ƙaddara ce ta rabasu da ita,Yanzun kuma Allah ya haɗasu da ita,"

  Yana kai ƙarshen maganar,likitocin suka haɗa baki wurin cewa"Allahu akhbar!Amma mun tayata Murna sosai,Allah yasa silar samun saukinta kenan" gaba ɗaya suka amsa da Amin,

  Sun jima suna magana,a tsaye kafin daga bisani,Abusufyan ya ɗauketa asaman kafaɗarshi,Sai da suka fara shigar da ita medical room likita ya duba ta sosai,tare da yi mata allurorin da aka saba yi mata,aciki hada na bacci,Tsayawa suka yi acikin asibitin suna ciccike wasu mahimman bayanai da ake bukata a wurinsu,harda Malam nura su da suka kawo ta asibitin,kafin Aka mallaka masu ita, 😍


*Boss Bature*


  *Hayaaam*


Tun da Aunty babba tabarta a asibitin nan magashiyan rai hannun Allah,Sai yau ta dawo cikin Hayyacinta,duk ta bushe ta dishe ta ƙanjame,jikinta duk faci,kamar wadda tayi hatsarin Mota,Komai nata ya ƙare,tayi mamakin ganinta a asibiti kuma babu kowa atare da ita,daƙyar ta iya miƙewa zaune,jikinta sae kerma yake yi,lokaci ɗaya ta shiga tariyo abunda Haroon yayi mata,fashewa tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,duk taji ta tsani kanta kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu,cikin shessheƙar kuka take faɗin"Meyasa na farka ban mutu ba?me yayi mun saura acikin duniyar nan,Natsani kaina,Natsani komai ban sha'awar cigaba da zama  acikinta!bazan ta6a yafe mashi ba,mugu azzalumi ya cutar da rayuwata,hannu tasa ta yaye farin yadin da aka rufeta da shi,riga ce ƴar dai dai guiwa aka sanya mata blue colour kamar uniform,yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin ƙoƙarin ɗage rigar don taga menene a wurin,don tana jin kanta kamar ba dai dai ba,

  Slowly ta tattare rigar,ta dage ta,koda tayi arba da gabanta,A rikice ta mayar da rigar ta rufe tare da fashewa da wani kukan mai cin rai,

  Tana cikin kukan nan,Dr ya shigo tare da Nurse abayanshi,

   Lallashinta suka shiga yi har suka samu ta lafa,Sannan Dr ɗin ya soma magana a tsanake,

  "Baiwar Allah,Ya jikin naki"?_

Cikin shessheƙar kuka tace"da sauƙi,dan Allah ku faɗamun wanene ya kawo ni asibitin nan,yaushe aka kawoni,"tana magana hawaye na wanko fuskarta,

  "ƴar uwarki ce,ta kawoki asibitin nan,Tun last week,Sai dai tun ranar da ta kawoki,Ta gudu tabarki anan bamu ƙara jin ɗuriyarta ba,Mun nemeta sosai ba mu same ta ba,A ƙarshe sai muka samu wannan wasiƙar a gefen gadon ki,bamu karanta abunda ke ciki ba,"ya ƙarasa maganar tare da miƙa mata wasiƙar,

Tunkan ta kar6a gabanta ya shiga faɗuwa rasss!rass!buɗe paper ɗin tayi ta soma karanta abunda ke cikinta,tun da ta fara karantawa tafin hannunta ɗaya ke rufe da bakinta,hawaye sai shararowa sukeyi daga cikin idanuwanta,ƙiris ya rage zuciyarta ta buga saboda tsabar takaici,Ba ta ta6a tsammanin cewa Aunty laila zata iya guduwa tabarta a asibitin ba,Taji ciwon kalmar nan da ta kirata,Wato karya wadda ba'a rabata da maza,ta yanke mata hukunci batare da tasan ainihin abunda ya faru da ita ba,"

Dunƙule takardar tayi ta cukuikuyeta a hannunta,sai faman matsar kwalla take yi,wasu nabin wasu,

  "Lokacin sallamar ki bai yi ba,Amma ya zama dole muyi discharge ɗinki saboda kuɗin gado da aka biya sun ƙare,Sannan akwai wasu bayanai masu mahimmanci game da lafiyarki,da muke so mu samu wani makusancinki mu sanar dashi,Gashi baki da kowa,Bayan wannan akwai alluran da kike buƙata da kuma magunguna domin bunƙasa lafiyar jikinki,Ko kina da wani wanda zai iya taimaka maki"?

  Kuka sosai hayaam take yi,tunani ta shiga yi wa zata kira yanzu don ya taimake ta?Waye take dashi wanda zaiji tausayinta,A iya saninta bata da kowa,in ma akwai babu wanda zai agaza mata saboda sanin Mugun halinta,Shiyasa a koda yaushe akeso mutun ya kasance yana aikata abun kirki a rayuwarshi,ba ka son awani hali zaka tsinci kanka ba a nan gaba ba,duk wani abu da kake taƙama dashi,Walau kyau ko dukiya ko mulki,wata rana Allah zai iya kwace abunshi,Hayaam tayi dana sanin rayuwarta gaba ɗaya,abun ya tsaya mata arai,Wai har ƴar uwarta wadda suka fito ciki ɗaya,Zata iya guduwa tabarta a gadon asibiti rai hannun Allah,ta rayu kota Mutu wannan badamuwarta bace,Wannan wace irin rayuwace?ɗan uwa na gudun ɗan uwanshi,koda yake ɗa ma ya kashe ubansa,Sau nawa akayi?


"Baiwar Allah,kin yi shiru ba kice komai ba"?Dr ɗinne ya katse mata zancen zucin da takeyi,

  Cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah,ku taimaka mun da waya,inaso na kira ƴar uwata ne,"_

Hannu Dr ɗin yasa a aljihun wandonshi ya zaro wayar shi,Infinix ya miƙa mata,jiki na rawa ta kar6i wayar,sai da ta ruƙeta a hannunta ta shiga tunanin wa zata kira,Bakowa ya faɗo mata aranta ba,Fa ce AMANI,duk da tana jin fargabar kada Amani,ta balbale ta da faɗa sakamakon irin wulaƙancin da sukayi masu,daƙyar ta iya danna numbobin wayar Amani,da yake ta haddace numbarta a kanta,Danna mata kira tayi,nan take ya shiga,gabanta sai faɗuwa yake yi,almost 3 times Amani bata ɗaga ba,


A lokacin tana a kitchen tana shirya lunch,tajiyo muryar Amaal tana kwala mata kira,fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin ta tunkarota tana tambayar wanene ke kiranta a waya,

Amal dake saukkowa downstairs,tace"New number ce,bansan wanene ba,ta ƙarasa maganar tare da miƙa mata wayar,zuba ma numbar ido tayi tana kallonta,a ƙa'ida bata cika ɗaukar bakuwar number ba,amma tunawa da yadda Amal tazo hannunta,ta hanyar kira da bakuwar number,yasa tayi tunanin ɗaga kiran kada ace wani abu mai mahimmanci ne,Sanya wayar tayi a kunnanta bayan ta amsa kiran,sallama tayi"Assalamu alaikum,"

  On the other hand Hayaam na jin an ɗaga kiran,jiki na rawa ta kara wayar a kunnanta,cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunanta"Aunty Amani,"

  Cike da mamaki Amani tace"To fa,kamar muryar Hayaam nake ji,"

Murya na kerma tace"Ni ce,"shiru amani ta ɗan yi kafin tace"Lafiya kika kirani?fuskarta a ɗaure tayi tambayar kamar tana agabanta,

  Cike da fargaba hayaam tace"Aunty Amani ina gadon asibiti,nayi fiye da sati a kwance,babu wani a kusa dani,"

   Murmushi Amani ta saki tare da cewa"Sai akai yaya kenan?menene amfanin kira na?ina Laila ne?inasu Abrah?

  Jiki asanyaye Hayaam tace"Duk basu atare dani,Aunty laila itace ta kawoni asibitin,Amma ta gudu ta barni ni kaɗai,gashi ina cikin mawuyacin hali,kamar zan mutu,"

  tana kai ƙarshen maganar Amani tace"Oh Allah sarki,Allah ya baki lafiya,"

  "Dan Allah Aunty Amani ki taimaka mun,Nasan kina da kyakkyawar zuciya,"

  Fashewa Amani tayi da dariya mai sautin gaske,hada yin shewa kafin tace"Sai yau kika san inada kyakkyawar zuciya?Kin manta irin rashin mutuncin da kuka shuka mana?Ashe akwai rana irin wannan da zaki nemi taimako a wurina?bakiyi tunanin hakan ba?Saboda tsabar rashin kunya a haka kike tunanin cewa zan taimake ki,Koda yake dama ae ba kunya gare ku ba,"guntun tsoki taja mtswww kafin ta ɗaura da cewa"Karki kuskura ki ƙara kiran layina da sunan taimako,don da in taimaki Mugaye masu kafirar zuciya irin taku,wlh ƙwara na tattara duk wani abu dana mallaka,na kaishi gidan marayu,ko Allah ya bani Lada,Amma taimakon irinku,bakomai zai janyomun ba,fa ce Zunubi!"tana kai ƙarshen maganarta,tun kan taji me Hayaam zata ce mata,Nan take ta katse kiran,

  "Aunty Amani meyasa zakiyi mata haka"?Acewar Amal,wadda tuni tausayin hayaam ya kama,

  Harara Amani ta watsa mata tare da cewa"Oh harkin manta irin Muguntar da su kayi mana kenan!waɗannan mutanen da baƙin cikinsu mahaifiyar mu ta mutu,Sannan sune su kayi silar Da mahaifinmu ya Zauce,yake rayuwa tamkar mahaukaci,Bayan wannan Sune suka wulaƙantar da rayuwarki suka mayar dake tamkar dabba a haka kike tunanin zan iya taimakonsu!"?

   Cikin sanyin murya Amal tace"Aunty Amani be kamata kina tuna abunda ya faru ba,wannan su da Allah,Tunda har hayaam ta kira a waya tana neman taimakonki,Yakamata ki agaza mata,koba komai ita ƴar uwarmu ce,bai kamata mu juya mata baya a irin wannan halin na neman taimako ba,Wata'kil ya zamto silar shiriyarta,dama kuma shine abunda muke fata,duk wani wanda ke aikata badai dai ba,ya gane kuskurenshi ya koma ga Allah..."sosai Amal ta shiga tausar Amani,har ta ɗan fara saukowa,


Tunda Amani ta katse mata kira,ta fashe da wani irin matsanancin kukan,mai cin rai,Hada majina,miƙa ma Dr ɗin wayarshi tayi batare da ta iya furta mashi komai ba,Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,shi da nurse ɗin dake atsaye suna kallonta,duk ta fita hayyacinta,

  "Am sorry sister,dukkan tsanani yana tare da sauƙi,Ki ci gaba da addu'a in sha Allah,Zaki samu wanda zai taimake ki,"ɗagowa hayaam tayi da idanuwanta waɗanda sukayi jawur tana kallon nurse ɗin da tayi maganar,cikin shessheƙar kuka tace"Allah bazai ta6a yafe mun zunubin da na aikata mashi ba,Sakayyace ke bibiyata,haƙiƙa Nayi danasanin zuwana wannan duniyar,"tana magana hawaye na zuba akan fuskarta,

  Nurse ɗin tace"Ki gode ma Allah da kika kasance araye har wannan lokacin da kika gane kuskuren da kika aikata,baki mutu kina mai aikata shi ba,Yanzu dama ce agare ki,da zaki tuba ki koma ga Allah,"

  Tana kai ƙarshen maganarta,Tabi bayan Dr ɗin suka fuce daga ɗakin,

Sosai hayaam ke yin kuka har kanta ya fara ciwo,Ga uwar yunwa dake cinta,kamar tayi hauka,zama tayi zugudum tana tunanin inda zata dosa idan likita ya sallameta,bata da kowa babu wurin wanda zata je,gashi bata da ko sisi balle ta doshi gida,ko da tana da kudin inama zata iya zaman mota zuwa maiduguri a wannan halin,saboda raunin dake a jikinta,Batajin zata iya taka ƙafafunta ma har taje wani wuri,uban tagumi ta zabga,tare da rufe fuskarta,tana cigaba da shessheƙar kukan,


Almost 30 mins bata motsa ba,tana cikin wannan halin,Ta jiyo sautin takalma,Kamar ana shigowa ɗakin da take ciki,

    "HAYAAM!"kai tsaye kiran ya shigar mata har cikin dodon kunnanta,a firgice ta ɗago don taga wanene,har sai da gabanta ya faɗi,Abunda batayi tsammani ba,Hannu tasa tana murza idanuwanta,don ta tabbatar da abunda su ke gane mata,

  Amani ce atsaye bakin ƙopar,jikinsu na sanye da jallabiya,sunyi rolling veils a kansu,Hannun Amani na ruƙe da Hand bag ɗinta,Amal kuma na ruƙe da Basket mai ɗauke da food stuffs,da suka zo mata dashi,

   Sakin baki hayaam tayi tana kallonsu cike da tsananin mamakin ganinsu,Lokaci guda kuma tasake fashewa da wani kukan na farin cikin ganinsu,

  Ƙarasa shiga cikin ɗakin sukayi,abayansu kuwa Dr Osman ne a biye dasu,likitan dake kula da ita,

   Ashe bayan fitarshi daga ɗakin Hayaam,ya wuce Office ɗinshi,bada jimawa ba,sae ga kiran Sabuwar numbar a wayarshi,Daya ɗaga kiran,suka gaisa da Amani,ta buƙaci ya bata address ɗin asibitin,Ba ƙaramin farin ciki likitan yayi ba,Saboda ya gane cewa ƴar uwar mara lafiyannan ce,Bayan ya tura mata address ɗin asibitin,After some minutes Motarsu Amani ta shigo asibitin,da kanta tayi driving ɗinsu a motarta,Bayan sun ƙaraso ta kira layin doctor ɗin,Da kanshi yazo inda suke,sannan ya jagorance su izuwa Room ɗin da aka kwantar da Hayaam,


  Wuri Amani ta samu gefen gadon ta zauna,Amal kuma ta zauna saman plastic chair ɗin dake fuskantar gadon,a ƙasa ta ajiye kwandon hannunta,

 a ruɗe Amani tace"Hayaam!meya faru dake haka?hatsarin mota kikayi ne"?

  Girgiza mata kai hayaam tayi alamar a'a,kasa buɗe baki tayi,saboda bata da amsar da zata basu ga kukan dake cinta,

    "Hayaam dan Allah ki sanar dani meya faru dake ne,Nayi mamakin ganinki ke kaɗai a asibiti a wannan halin,batare da Laila ba,"

  "Aunty Hayaam,Sannu ya jikin naki"?Amal ce tayi maganar fuskarta da alamun tausayinta,daƙyar ta iya amsa mata,Duk kunya ta rufeta,

   Cikin sanyin murya tace"Aunty Amani nayi danasanin rayuwata gaba ɗaya,Na tsani kaina,Komai ya fita raina,Ban yi tsammanin zaki zo ba,Har na fidda rai da cigaba da rayuwa acikin duniyar nan,Amma ganinku da nayi ba ƙaramin farin ciki nayi ba,"tana magana hawaye na zuba,

  Juyawa Amani tayi tare da kallon Amal tace"Ki jirani a waje,Zan kira ki,inaso muyi magana da hayaam,ki tafi da wayata,ko game ne ki buga,"

  Miƙewa Amal tayi tare da matsawa wurin Amani,ta kar6i wayarta,kafin ta kama hanyar barin ɗakin,

   mayar da hankalinta tayi sosai akan Hayaam tace"ina sauraronki,faɗamun meya faru dake?meyasa kike zaune a asibiti ke kaɗai batare da Laila ba?duk me ya jawo hakan"?a ƙagare Amani take da taji amsoshin tambayarta,

  Hayaam bata 6oye mata komai ba,Tun daga kan Abunda ya faru tsakaninta da haroon har izuwa farfaɗowarta da tayi a gadon asibiti,Hannu tasa tare da ɗaukar wasiƙar da ta cukuikuye agefenta ta miƙa ma Amani ita,kar6a Amani tayi a atsanake ta shiga karanta wasiƙar da Aunty babba ta rubuta mata,wasu irin hawaye ne suka soma shararowa daga kan fuskarta,Saboda tsabar ƙululun baƙin ciki kamar ta haɗiyi zuciya,

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!wannan wani irin rashin Imani da rashin tausayi ne?Anya kuwa laila tana son tagama da duniya lafiya?yanzu duk don saboda neman abun duniya ta tafi ta barki a gadon asibiti rai hannun Allah?Anya matar nan tana da Hankali kuwa?Ya salam"rai a6ace take maganar,abun ya ƙona mata ranta sosai,

  Hayaam tace"bata da imani,wlh duk rashin hankalina,banajin zan iya tafiya in bar Aunty laila a gadon asibiti,Amma haka ta haura ƙafa ta barni,Sai kace ba ciki ɗaya muka fito da ita ba......"kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata,

  Itama Amanin kukan takeyi sosai,cikin shessheƙar kuka tace"Ha..hayaam ki faɗamun sunan wanda yayi maki wannan aika aikar,inason nasan Wani mara imanin ne"?

  Daƙyar hayaam ta tsagaita da yin kukan tace"HAROON ne ɗan gidansu Ya Abbas,Mijinki,"

  Saboda tsabar kiɗima a razane Amani ta miƙe tsaye hankalinta a matuƙar tashe take maimaita sunan haroon abakinta,

  Hannu ta aza akai tana faɗin"Nashiga Uku!Hayaam kina nufin haroon shine yayi maki wannan ɗanyen aikin"?ɗaga mata kai hayaam tayi Alamar eh,

   "Wlh bazan ta6a ƙyaleshi ba,Sai na tona mashi asiri wurin Abbas!Fasiƙi kawai mugu,dama ni bai ta6a kwantamun araina ba,Allah kaɗai yasan abunda yake aikatawa"ta ƙarasa maganar tare da komawa gefen gadon ta zauna,

  "Aunty Amani ki ƙyaleshi kawai,kada kice zaki tona mashi asiri,koma me ya faru dani laifina ne,Da ace tun farko na kama mutuncin kaina,da babu namijin da zai nemi aikata fasiƙanci dani,Zan yi haƙuri in rungumi ƙaddarata,Kibarshi kawai,Allah shi zai sakamun,"

  girgiza kai Amani ta shiga yi tare da cewa"Wlh bazan ta6a ƙyaleshi ba,Shikenan yaci bulus kenan?wannan mutumin fa,ba ƙaramin mugu bane,bai kamata a dinga ƙyale irinsu ba,Suna aikata abunda suka ga dama,batare da an yanke masu hukunci ba,Yanzu kika san irin matan da ya lalata ta ƙarfi ta tsiya kamar yadda yayi maki?shiru hayaam tayi tana sauraronta,

  "Dole ya gane kuskurenshi,kuma ni bazanso duk wani abu da zai 6ata sunan family ɗinsu ba,Yana so ya zubda masu mutuncinsu ne a idon duniya,Don haka dole na ɗauki mataki akanshi,"ranta a 6ace tayi maganar,tare da kai hannunta cikin food basket din da suka zo dashi ta zaro plate tare da warmer,Buɗe kular tayi,Soyayyan naman kaza ne acikinta wanda yaji uban kayan haɗi,sae ƙamshi ke tashi,tuni jikin hayaam ya soma rawa sai faman haɗiyar yawu take yi,kamar ta kaima warmer ɗin wawura haka take ji,.  

   Acikin plate Amani ta zuba mata naman tare da miƙa mata,Sannan ta dauko mata ruwa mai sanyi na roba,tare da fresh milk,ta shiga tsiyaya mata su acikin Cup,

   ganin yadda hayaam ke taunar cinyar kazar hada ƙashin duka take haɗawa,yasa Amani cewa"Ki ci a hankali mana,kada kija ma kanki wata matsalar,"kasa natsuwa tayi saboda yunwar da take ji,

  Sosai hayaam taci naman nan,tasha fresh milk ɗin mai sanyin gaske,sai da taci ta ƙoshi,sannan ta samu natsuwa,

  "Itama Laila bazan ƙyaleta ba,nasan cewa zata nemi Abra ne don ta rakata wurin bokan,wama yasani ko har sun tafi,Kuma ina da tabbacin cewar,bazata ta6a sanar ma wani cewa tabarki a asibiti ba,don kada a tuhume ta,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar kafin taci gaba da cewa"muguwar ashe ko ƙannenta da suka fito ciki ɗaya bata iya raga mawa,inajin tsoron tace zata kai Abra wurin fasiƙin Bokannan,don muddin takaita,zaiyi wuya bai nemi ya kusanci ɗaya daga cikinsu ba,"

  Jin wannan maganar yasa hankalin hayaam ya tashi,don ita yanzu tayi nadama,kuma tana jin tsoron halin da Aunty babba zata jefa Abra,kamar yadda tayi mata,


   "Yanzu ya zamuyi mu dakatar da Abra daga zuwa wurin bokan nan"?hayaam ce tayi maganar,

  "Ina ganin idan muka kira Abra muka sanar da ita abunda laila tayi maki na barinki a gadon asibiti,zata fasa bin ta ne,"

  Zama suka yi suna yanke shawarar yadda zasu dakatar da Abra,a ƙarshe suka yanke shawarar kiranta a waya,


*Boss Bature*


*JUNAID*


Tsaye yake a gaban dressing mirror,ya ɗauki wankan pakistan ajikinshi masu kyan gaske farare sun ƙara fito da hasken fatarshi,Fuskar nan har wani kyau ta ƙara,ya gyara sumar kanshi sosai ta kwanta luf a bayan wuyanshi,Slowly ya miƙa hannu gaban mirror ɗin ya ɗauki kwalbar turarenshi,yabi ko ina na jikinshi ya feshe shi,bayan ya mayar da ita,ya ɗauko wrist watch ɗinshi ta diamond da Hajiya azeema ta bashi,Yana ƙoƙari sanyata a hannunshi,Wayar shi ta soma ringing,da sauri ya ƙarasa sanya agogon,tare da tunkarar saman gadonshi inda ya ajiye wayar yakai hannu ya ɗauketa,tare da kollon screen ɗin wayar,Sunan Mommyn su ne ya bayyana akai,tur6une fuska yayi kafin ya ɗaga wayar,cike da shagwa6a ya soma magana"Mommy,ni fushi nake yi dake,"

On the other hand,Alexandra tace"haba romeo ɗina,why are u angry wit me?laifin me na maka da kake fushi dani"

   "Mommy,u forgot about me,tunda na dawo baki kira layina ba,babu wanda ya damu dani,"

  Cikin lallashi tace"Sorry my own son,pls kadaina fushi dani,"

  Bubbuga kafarsa yayi cikin shagwa6e yace"Nidai Mommy indai kina son farin cikina,Ki dawo gida kawai ke da daddy,dasu yaya Fawan,kowa ya dawo gida,nayi missing ɗinku sosai,"

   Alexandra tace"shi ne kawai abunda kakeso,"

  "Eh,adawo gida,acigaba da rainon baby junaid"yanayin yadda yayi maganar ba ƙaramin dariya ya bata ba,yana jiyo muryarta ta cikin wayar tana dariya,

Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Calm down ur mind,This week zamu dawo,"

  Fuskarshi ɗauke da farin ciki yace"Mommy pls,Ki tursasa daddy,ko da baya son dawowa,ni dai ku dawo gida kowa da kowa,tare da su yaya fawan,Twins su irfan and sister hafsat,inason ganin kowa a kusa dani,"

  "Don't worry ur self,my romeo kowa zai dawo saboda farin cikinka,"

Ba ƙaramin daɗi yaji ba

  Sun jima suna waya kafin daga bisani,su kayi sallama,ajiyar zuciya ya sauke tare da yin wurgi da wayar saman gadon,kwankwasa ƙopar bedroom ɗinshi akayi,da sauri yace wanene

  "My Romeo,its Me ur juliet,am ready for the outing,"wani irin ƙayataccen murmushi ya saki jin muryar jahad,

   A ƙagare yake daya ga wankan data ɗauka,jiki na rawa ya ƙarasa tare da buɗe mata ƙopar,Gabanshi ne ya faɗi rass,Tun daga kan takalman ƙafarta ya fara kallonta,High heels ne ƙafarta,farare,abun ya bashi mamaki ganin tayi shigar white gown,launin kayanshi daya sanya,tayi rolling veil akanta,lips ɗinta kuwa Red ta sanya masu,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga jikin ko wannansu,


  Ruƙo hannunta junaid yayi tare da janyota cikin bedroom ɗin,lumshe idanuwanshi yayi tamkar maijin bacci,da wata irin kasalalliyar murya,yace"Jahad,You look so beautiful,kayan nan sunyi maki kyau sosai,"

  Hannu tasa tare da shafa side face ɗinshi"Duk kyawuna ae bankai ka ba,kaifa na dabanne,ta ko'ina Allah ya baka,".  

  Aɗan shagwa6a yace"Amma ni bana jin kaina a matsayin cikakken mutun,"

  A ɗan ruɗe tace"Saboda me,'?

Hugging ɗinta yayi tare da kai lips ɗinsa saitin kunnanta sannan yace"Saboda,ban mallake ki ba,sai dake ne zan zama cikakken mutun,'

  Wani irin matashin murmushi jahad ta saki,taji daɗin kalaminsa sosai,

   "Nikaina junaid,bana jin kaina amatsayin cikakkiya,har saina mallake ka,"

  kalaman soyayya suka shiga gayawa junansu,

Duk wannan abunda da suke yi akan idon Haroon wanda ke la6e,ya ɗan buɗe kopar ɗakin ya zuro kanshi yana kallonsu,

  Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Ta kwana gidan sauƙi,"yana faɗin hakan,ya rufo masu ƙopar ɗakin,hannu yasa tare da zaro wayarshi,Contact ya shiga,Tare da rubuta wasu numbobi,ya danna kira,tare da manna wayar asaman kunnanshi,

  Muryar wani kakkauran mutunne yace"Ya haroon,Ya ake ciki ne?ina fata kazo mana da labari me daɗi,"

  ƙasa ƙasa da murya haroon yayi don kada wani ya juyo shi,

   "Ka saurare ni dakyau,Yanzu junaid zasu fita tare da ƴar wurin uncle ɗinmu,Abunda nakeso daku,Karku kuskura ku ta6a lafiyar jikin yarinyar saboda ba akanta zamuyi aiki ba,Junaid kawai nakeso,Ku bi ta kan motarshi da truck,Yadda ko fuskarshi ba'za a gane ba,idan tayi dameji,"

  Fashewa mutun yayi da wata irin Mahaukaciyar dariya,hhhhhhhh kamar zai fasa screen ɗin wayar,Bayan ya tsagaita da yin Dariyar yace"AN GAMA OGA,SAI DAI UWARSHI TA HAIFI WANI,"

Jinjina kai haroon yayi tare da sakin shu'umin murmushin nan nashi yace"ku kasance a ankare,Yanzu zai fito da motarshi,banaso yaron nan ya dawo gidan nan araye,Gawarsa kawai nakeson gani,jaga jaga da jini,"


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post