Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 97

Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 97

Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 97

 Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥

Am really sorry,🙏

Tayi matuƙar tsorata dashi,kasa ɗagowa tayi daga jikinshi,jikinta sae kerma yake yi,lokaci guda daddaɗan ƙamshin turarenshi ya daki hancinta,nan take ta ruɗe tana ƙoƙarin gano a ina tasan ƙamshin nan,duk duniya mutun ɗaya ne ta sani mai irin wannan ƙamshin turaren mai matuƙar ratsa zuciya,Ruɗewa tayi tana so ta canko wanene,kuma tana kokwanton anya hakan zai iya kasancewa gaskiya?zame hannayenta tayi daga saman waist ɗinshi da ta ruƙe,ta matsar dasu har izuwa mid back ɗinshi,Gabanta ne ya faɗi rass jin ta shafo doguwar sumar kanshi,muryarta na kerma ta furta sunanshi"BABBAN YAYA..!"tana ambaton hakan,Wutar ɗakin ta dawo nan take haske ya gauraye ko'ina tamkar da Rana,zuba mashi ido tayi tana kallon kyakkyawar fuskanshi wadda ke sanye cikin face mask black colour,Launin rigar jikinshi ya lumshe idanuwanshi,slowly ya ɗan waresu akan fuskarta,Ae tana ganin blue eyeballs ɗin nan nashi,Ta ƙara tabbatar da hasashenta,abun yayi mugun ɗaure mata kai,kallonta yake yi from head to toe,fuskarta duk tayi zufa saboda tsabar firgicin da ta shiga,ga hawaye jaga jaga a fuskar,duk don saboda an ɗauke da wutar nepa ta ganta acikin duhu,


Sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,hankalinta har ya kwanta da ta tabbatar cewa shine,Tayi tunanin wani mugunne yazo don ya cutar da ita,tayi farin cikin ganinshi sosai kamar tayi ihu,Amma ta wani 6angaren tsoran hukuncin da zai yanke mata take yi,duk a tunaninta yazo ne don ya hukuntata,tunda ya bata Command taƙi bi,

   Ganin irin kallon da yake yi mata ne yasa tayi saurin sunnar da kanta ƙasa,tana wasa da yatsun hannunta,

    Hanky ya zaro daga cikin trouser pocket ɗinsa,Ya miƙa mata tare da cewa"Take it,"hannu tasa ta kar6a,ta shiga goge fuskarta sosai,

   "In kawo maka ruwa kasha"?cikin sanyin murya ta ambaci hakan,

   Girgiza mata kai yayi alamar a'a,kafin ya wuce cikin falon,Ya zura hannayenshi biyu acikin aljihun wandonshi,

  juyowa tayi tana kallonshi,A dai dai lokacin suka jiyo sallamar Abusufyan"Assalamu Alaikum",

   Amsa mashi su kayi da"Wa'alaikum salaam,"

  Shigowa cikin falon yayi,hannunshi ruƙe da key ɗin Motarshi,

  Koda yayi arba da Sgr,cike da mamaki yace"Rafayet!Ashe dagaske ne,Abban ku ya sanar dani cewa,zai yi wa Omar magana ko shi ko kai wani yabiyo bayanmu don yaso yana nan muzo dashi,Banyi tsammanin cewa kaine zaka zo ba,Yanzu kawai ina karyo kwana da motata naga sojoji zagaye da gidan nayi ta mamaki cikin raina,Gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba," ya karasa maganar a yayin da yake ƙoƙarin rungumarshi,da alama Abusufyan ba ƙaramin daɗi yaji ba,Sai murmushi yake yi,

   "Na same ku lafiya,"?

"Lafiya lou Alhmdllh,Naje masallaci ne,na biya naga wani Abokina daga can kuma na wuce wani store zanyi mana siyayyar kayan abinci,Inata fargabar nabar yarinya ita kaɗai acikin gida",

  Sgr yace"nayi mamakin ganinta ita kaɗai zaune acikin gidan,time ɗin dana shigo kuma bansan meya faru ba,duhu ko'ina,so sai daga bayane hasken ya dawo,"

  Abusufyan yace"Ae ɗaukewa su kayi da wutar ne,yanzu nima ina kan hanyar dawowa naga sun dawo da ita,"

  wurga idonshi yayi kan Sehrish dake tsaye hannunta ruƙe da hanky dinsa,ta kammala goge hawayen,

  "Daughter,zonan mana,"ya kirata da hannunshi,wurinsu tazo ta tsaya tana facing din Abusufyan,

   "Faɗamun meya faru?bayan na tafi"?

 murmushi ta ɗan yi,batare da tace komai ba,

   Mayar da idanuwanshi yayi kan Sgr yace"Amma dai ba  nan zaka kwana ba ko"?

   "I will spend the night here,"

Abusufyan yace"ba ka ga yadda gidan yake ba ne?Ni nasan bazaka iya bacci acikinsa ba,Yakamata ka wuce hotel kawai,ina ganin zaifi maka daɗin zama,"

  Girgiza mashi kai yayi"No,i wanna stay here," gyaɗa kai abusufyan yayi tare da kallon sehrish yace

  "Sehrish ki kaishi bedroom ɗin da kika gyara,ya zauna acan,Amma dai banso ba wlh,Don nasan cewa zaka takura sosai,Ga zafi ga sauro duk da na siyo maganin sauron,Amma bana tunanin zai iya dakatar da saurayen dake acikin gidan nan,"

  Amsa mashi tayi da toh,Sannan ta juya tare da kallon Sgr tace"Mu shiga ciki,"

  Gaba tayi yabi bayanta,daƙyar yake iya taka kasan palourn,saboda daudar dake a wurin duk da sun gyara shi,

  Shiga cikin bedroom ɗin su kayi atare,Wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana ƙarewa ɗakin kallo,

  "Kana bukatar wani abu,in kawo maka,"

   "No need"ya ambaci hakan a yayin da yake zaro wayarshi daga cikin aljihun wandonshi,

"Sehrish!"Abusufyan ne ya kwala mata kira,da sauri ta juya ta fita daga ɗakin,

  Komawa tayi cikin palourn A tsaye ta same shi,Ga kayan da yayi masu siyayya hada gass cylinder saboda yin girki,Sojoji ne suka shigo dasu,A cikin buhu guda biyu,sae cylinder ɗin da suka ajiye nan,

  Ƙarasawa tayi wurinshi,"Gani Daddy,"

   "Kunyi magana dashi ya fada maki ko yana buƙatar wani abu?"

   "a'a bai bukaci komai ba,"

Shiru Abusufyan ya dan yi,ganin damuwa akan fuskarshi yasa tace"Meya faru daddy," hannu yasa ya ɗan shafa sumar kanshi kafin yace"Daughter,bazai iya kwana acikin gidan nan ba,Ni nasan waye rafayet,Wlh nayi mamakin ganinshi banyi tsammanin cewa shi zaizo ba,Kalli fa gidan nan ki gani,babu wani shiri da mukayi,yanzu da zarar an ɗauke da wutar nepa,Shikenan zafi zai rufe mu,kuma ko kaɗan baison zafi,Gashi da ƙyankyami toilet idan bana bedroom ɗinshi ba,baya shiga na kowa,Kuma dole ya buƙaci yin wanka,Ni bansan ya zamu ƙare dashi ba,"

  Murmushi Sehrish tayi,ita kanta ta jinjina ma ƙarfin hali irin na Sgr,yadda yake da ƙyanƙyamin nan,Amma a haka yace zai kwana acikin gidan,Koya zasu ƙare,?

  "Daddy,kada ka damu,tunda yaji ya gani,zai kwana anan ɗin ka ƙyaleshi kawai,"

  Gyaɗa kai Abusufyan yayi tare da cewa"Shikenan kawai,Yanzu dai bari na shiga da kayan abincin nan kitchen,"

  Yayi maganar tare da sa hannu ya dauki buhu ɗaya,hannu tasa itama ta kama ɗayan buhun,taja shi izuwa cikin kitchen,bayan sun kammala kwashe kayan sunkai kitchen,

  Ta dube shi tare da cewa"Zan iya dafa mana ko taliya ce?

  Abusufyan yace"Kina jin yunwa ne"?

  "A'a,bana ji,saboda kai dama zan dafa,naga bamu ci Dinner ba,

  "Ki barshi kawai,akwai kayan tea dana siyo da bread,idan kina jin yunwa ki haɗa ki sha,Yanzu dae bacci nake ji,"

  Yayi maganar yana hamma,

"A ina zamu kwana"tayi tambayar tana kallonshi,

"Ki wuce inda mijinki yake mana,Ni zan kwana a palour ne,Ki dauko mun bargon da zan ɗan shimfiɗa in akwai"

  "Toh" ta amsa mashi tare da

  Kama hanya ta fuce daga cikin kitchen ɗin,Shima fitowa falon yayi ya tsaya a tsaye yana jiranta,


Lokacin da ta shiga bedroom ɗin,A kwance ta samu Sgr yana bacci ya ƙure fankar ɗakin har ƙarshe,iska ta ko'ina,hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wurin wardrobe ta wuce ta sanya hannu ta buɗeta,daga gida na kasa blanket din suke tare da bedsheet,hada mosquito net,

   Bargo ta dauko mashi,Sannan ta koma falon,har lokacin Abusufyan na atsaye,yana jiranta,

   Ƙoƙarin shimfiɗa mashi tayi,da sauri yasa hannu ya kar6i bargon tare da cewa"Yawwa My Own Daughter,nagode sosai,"

"Sae Allah yakaimu Daddy,"fuskarta asake tayi maganar,

  "Allah ya kaimu lafiya,take care of my son,don't allow even one mosquito to bite his skin,If not ranki zai 6aci,"cike da zolaya yayi maganar,

  Fashewa tayi da dariya,tare da juyawa tana faɗin"don't worry daddy,In sha Allah i will look after him,very well,"

  Gyara kwanciyarshi yayi saman sofa ɗin,cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dashi,

  Komawa cikin bedroom ɗin tayi,bedsheet ta dauko acikin wadrobe ta shimfiɗa a kasa,sannan ta matsa wurin gadon,ta ɗauko pillow guda ɗaya ta ajiye shi saman zanin gadon,

   Wurin switch taje,ta kashe light ɗin ɗakin,Nan take duhu ya gauraye ɗakin amma ba sosai ba,akwai hasken ƙwan dake a falo guda daya da aka bari akunne,ya ɗan haska ɗakin nasu,

    Moving tayi izuwa wurin gadon inda Sgr ke kwance yana bacci,addu'o'i ta shiga karantowa tana ɗan tattofa mashi,bayan ta kammala ta koma saman shimfiɗar da tayi,ta gyara kwanciyarta,sai da itama ta karanta addu'o'in tabi ta shafe jikinta kafin ta rufe idanuwanta,bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,


Around 1:30 na dare,Ƴan nepa suka yi tsiyar tasu da suka saba,Tashin hankali,Ƴan sakanni da ɗauke wutar fanka ta tsaya cak,Wani irin zafi ya fara ziyarta ɗakin,Sai ga mutanen da gudun gaske sun fara kwararowa cikin ɗakin,Buuuuuuuuuu da wani irin kuka mai sautin gaske,tun yana juyi saman gadon yana kai hannu yana buge sauron dake ƙokarin attacking ɗinshi,har ya fara ƙokarin farkawa,Wata irin zuface ta soma tsastsafo mashi ajikinshi,Sharkaf ya jiƙe,tuni numfashinshi ya soma kokawar fitowa daga hancinshi,kamar an toshe shi,A firgice Sgr ya farka yana faman zazzare blue eyes ɗinshi,Hankalinshi yayi mugun tashi,arayuwarshi ya tsani sauro ko miskala zarratin baisan halittar nan,bai taso a inda ke akwai taba,Amma yasanta sarai a matsayinshi na Dr yasan irin cututtukan da take haifarwa,Gashi ya tsani duk wani abu da zai naƙasa lafiyar jikinshi,tuni jikinshi ya soma kerma,hannu yasa ya ɗebe rigarshi gaba daya,ya shiga kokawar korarsu daga kusa dashi bayan ya kunna fitilar wayarshi dakin yayi haske,ji kake fass fass!kaff kaff!!haka ya dinga bubbugesu,duk yabi ya ruɗe,


Cikin bacci Sehrish ta dinga jin muryarshi yana faɗa da sauraye yana fadin"Don't come close to me!Am gonna shoot you"tashin hankali Sgr fa ya zauce da alama,duk sun rikitashi sun mayar dashi ƙaramin mahaukaci,Idan ya sanya riga bala'e biyu,ga zafi ga sauro,idan ya cire rigar kuma Sauraye zasu sha jini,bai da choice,

  A firgice ta farka,hankalinta a matukar tashe ta mike daga kwancen da take saman bedsheet ɗin,Wurin shi ta ƙarasa,yanayin da ta ganshi gaba ɗaya ya rikice ba ƙaramin tausayi ya bata ba,gaba daya yabi ya susuce ya hargitsa sumar kanshi,

   "Ya Rafayet,"ta ambaci sunan shi da wata irin kasalalliyar murya ta mai bacci,ƙoƙarin hawa saman gadon tayi don ta taimaka mashi ta kore mashi su,kafin su san abunyi,ae tana hawa saman gadon,ya ƙanƙameta ya rungumeta sosai,A faɗace yake ce mata ta kori saurayen su fita su bar ɗakin,ko ya harbesu da bindiga,tuni taji hawaye sun cicciko mata acikin idanuwanta,tsananin tausayinshi ne ya kamata,dama sai da Uncle yace bazai iya kwana a cikin gidan ba,Amma yace zai iya,wani iko na Allah,babu halittar da Sgr ke jin shakkarta irin sauro,Gashi Yau Allah ya haɗasu,ƙananun ƙwari sun firgita babban kwaro,Shaggu sun ga Farar fata,burinsu kawai su tsotsi jininshi,Dama abu tubarkalla masha Allah,

  gaba daya hannayenta na asaman bayanshi,ya cusa kanshi a kirjinta,numfashin shi da wani irin huci yake fita,

   Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Ya rafayet,dan Allah ka natsu,zanje wurin daddy na kar6o mana maganin sauron,"tayi maganar tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi,ƙin barinta yayi,yaƙi yarda ta motsa daga jikinshi,gani yake kamar in tabar wurin Saurayen zasu shanye mashi jinin jikinshi ne,

  Ganin yaƙi sakinta yasa takai hannu ta ɗauki rigarshi da yayi wurgi da ita gefe saman bedmattress ɗin,Ruƙo rigar tayi a hannunta,ta shiga kore mashi saurayen dake akewaye dasu,


Duk wannan budurin da akeyi,Abusufyan na kwance saman doguwar kujerar,Shi kanshi zafi ya ishe shi ga saurayen a kewaye dashi,Amma hakan baisa ya farka ba,sae faman juyi yake yi,

   (Allah sarki,haka talaka ke fama,da zarar an ɗauke da wutar nepa lokacin zafi,Ya rasa inda zaisa kanshi,ga sauro ga zafi,yayin da masu kuɗi ke can suna shan sanyin A.c,a lokacin zafi,idan kuma na sanyi ne su kunna room heater,Talaka kuma Ya hura garwashin wuta😥)


Jikinshi sae kerma yake yi,Duk da ya ɗan ji sauƙin Zafin saboda fiffitar da take yi mashi tana kore mashi saurayen,ko gajiya bata yi baiwar Allah,Haka ta hana idonta bacci,ta zauna tana kula dashi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi,har lokacin yana manne da ita,

   A hankali bacci yayi awon gaba dashi,kamar wani jinjiri,gyangyaɗi ta fara yi,tana fiffitar bacci na fisgarta,idanuwan nan sunyi jawur dasu,taƙi bari bacci ya ɗauketa,saboda gudun halin da Sgr zai shiga,idan ta daina yi mashi fifitar,

   Tafin hannunta ta sanya asaman fine face dinsa,ta shafa gefen fuskarshi har izuwa saman pink lips ɗinshi,kafin ta mayar da hannun saman dogon wuyanshi,fatar wurin tayi haske sosai mai matukar jan hankali,la66anta takai asaman cheek ɗinsa ta manna mashi kiss,ɗagowa tayi tare da aza tsinin hancinta cikin sumar kanshi,daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga wurin ta dinga shaƙa,tana faman lumshe idanuwanta,da hannu ɗaya take yi mashi fiffitar,


  Tana cikin wannan yanayin,ta galabaita sosai saboda baccin da take ji,Ƴan nepa suka dawo da wutar,a hankali fankar ta soma jujjuyawa,nan take iska ta karaɗe ko'ina na bedroom ɗin,wani irin farin ciki ne ya ratsa zuciyarta,

   "Allah na gode maka,da suka dawo da wutar nan,nayi farin ciki sosai,"

   Lokaci guda Mosquitoes ɗin nan kowa ya kama gabanshi,saboda wutar mai ƙarfi ce,iska duk ta kaɗa shaggun,

  A hankali ta lalla6a ta janye Sgr daga jikinta,ya koma saman mattress ɗin,ta dauki wayanshi ta kashe fitilar ta daura ta saman bedside drawer,gefenshi ta kwanta,tare da jan bargo ta lullu6e jikinta,banda nashi saboda ta lura dashi baisan Zafi ko misƙala zarratin,


*Boss Bature*


Wuraren Sallar asuba,Abusufyan ya farka,Saukkowa yayi daga saman Sofa ɗin,yana faman murza wuyanshi,Wurin yayi mashi zafi saboda kujerar tayi mashi karanta,ya takure kansa sosai,Ƙopar ɗakinsu yaje tare da sanya hannu yana ɗan kwankwasa ƙopar,

   Sehrish ce ta farka,saukowa tayi daga saman gadon,sai da ta fara kunna hasken ɗakin,sannan taje ta buɗe ɗakin,

  "Daddy,"ta ambaci sunanshi,

"Na'am,Daughter,"

"Wlh jiya munji jiki daddy,dama haka Yaya Rafayet ke da jin Zafi? Ga sauraye suka takura masa,jiya daga ni harshi bamu samu isasshen bacci ba,"muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,

"Ae dama saida nace mashi,Yaje hotel amma yaƙiya,banji daɗi ba gaskiya,duk ban shirya ma zama gidan ba,dana sani tun kafin muzo,nasa an gyara shi,An sanya generator da A.C an kuma yi mashi feshin maganin sauro,Amma ban yi tunanin hakan ba,Wllh koni jiya naji jiki,"

  Ya ƙarasa maganar tare da cewa"Yanzu ya yake?Yana lafiya kuwa,"?yayi tambayar yana jiran amsarta,

  "Ya samu bacci,da suka dawo da wutar,bansani ba ko yana lafiya ko kuwa,Still dai bacci yake yi bai farka ba,"

  Jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"je ki taso munshi,Yazo mu tafi masallaci,Lokacin salla yayi,"

  "Toh daddy"tayi maganar tare da juyawa ta shige cikin ɗakin,


Yadda tabarshi haka ta same shi,kwance yana bacci,

  Zama tayi daga gefen gadon,sannan ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet"!shiru bai motsa ba,sake kiran nashi tayi"Babban yaya ka tashi,time ɗin sallah yayi,"_

  Ganin yaƙi motsawa yasa takai hannunta saman damtsen hannunshi,ta ɗan bubbugashi,dogon numfashi yaja a hankali ya soma ƙoƙarin buɗe idanuwanshi,

  Biji biji ya fara ganinta,kafin idanuwan nashi suka washe,

  "Ankira sallah,Daddy yana jiranka a palour,"

  daƙyar ya iya furta mata Okey,miƙewa yayi daga zaune,yakai hannu ya ɗauki shirt ɗinshi,Ya zurata ajikinshi,Hada ido su kayi da ita,da sauri ta kawar da idonta gefe guda,miƙewa tayi daga tsaye,ta bashi wuri don ya wuce,

  Saukowa yayi daga saman gadon,Ya kama hanyar fita daga ɗakin,

  "Adawo lafiya," 

"Okey,"yasa kai ya fuce,


Bayan fitarshi,toilet ta shiga,ta ɗauro alwala,bayan ta fito ta ɗauko darduma ta shimfiɗa,a natse ta kabbara Sallah,tana gama yin sallar ta ɗebe hijabin ta ninke dardumar ta turasu cikin wadrobe,

  Wani irin bacci take ji acikin idanuwanta,saboda jiya bata samu isasshen bacci ba,Cire doguwar rigar jikinta tayi tare da sagala ta saman Murfin wardrobe ɗin,

  Toilet ta wuce,Saboda jikinta duk babu daɗi,After some minutes ta fito jikinta sanye da Brazier,tare da Short,farare,ba ƙaramin kyau su kayi mata ba,dama dasu ta shiga wankan,

   Tunda ta fito kuma,baccin ya ya ci gaba da addabarta don ba karamin dadin jikinta taji ba,bata samu ta sanya kaya ajikinta ba,Saman gadon ta haye taja bargo cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita,bata ƙara sanin inda hayyacinta yake ba,


*Marshal Omar*


Yayi nisa a cikin baccin shi,yajiyo muryar Hosana tana raira mashi waƙa,

    _Wataran wata rana_

   _za'a kaika gidana_

    _matsayin mijina_

    _kaine madara na_

_na matsu!na matsu na matsu inga wannan rana_

Cike da jan faɗa take yin wakar hada matsawa saitin kunnanshi,Rai a matuƙar 6ace ya farka,tare da wurga mata uwar harara,tana zaune saman gadon tayi zaman cin tuwo,

  A faɗace yace"Hosana!bana hanaki shigomin bedroom ɗina ba?Meyasa baki jin maganata ne"

  Hura mashi hanci tayi tare da murguɗa baki tace"Haramun ne idan nashigo ɗakin ɗan uwana,?to idan ma haramun ne,Sai ka aure ni kowa ma ya huta,"

Hannu yasa tare da dafe kanshi,yana faɗin"Allahumma ajirni fi masibati,wa'aklif ni khairan minha,"

  A ƙule tace"Ya Omar,Ni ce masifar"?

  Banza yayi da ita bai tanka mata ba,

  Jin yayi shiru yana kallonta,yasa tace"haushina kake ji ko?to ka kashe ni mana kowa ya huta,"

  Yunƙurawa yayi tare da miƙewa daga zaune,yace"Meyasa kike mun haka ne?kin takurawa rayuwata Hosana,A haka kikeso na"?

  Turo baki tayi tana ɗan satar kallonshi,

  "Baki son farin cikina,kullum burinki ki addabi rayuwata kib hanani sakat,Zunubin me na akaita maki ne,"

   Ashagwa6e tace"Bakomai,"

  "Kinfi so ki ga hawaye na ko,"

Girgiza mashi kai tayi alamar,A'a,

Hannu yasa ya rufe fuskarshi yana raira mata kukan ƙarya,

  Nan fa hankalinta ya tashi,tabi ta ruɗe,

  "Ya Omar bazan ƙara zuwa ba,dan Allah kadaina kukan,yanzu zan tafi na barka,"jiki na rawa ta sauka daga saman gadon tana ja da baya baya tana faɗin"ka gani ko?tafiya zanyi,bazan ƙara dawowa ba,dan Allah ka daina kukan toh,"

  Ƙasa ƙasa ya dinga dariya batare da taji shi ba,har sai da ta fuce daga ɗakin sannan ya zame hannunshi aranshi yace"fitinanna,Allah yasa Daddy ya dawo cikin week ɗinnan zansa a ɗaura mana aure,At first night,zan koya maki hankali,duk wani hauka da kike ji asaman kanki saina sauke maki shi,"

  Yana maganar yana dariya,a yayin da yake saukowa daga saman gadon,jallabiya ce ajikinshi,toilet ya wuce,


Wuraren karfe 8,Sehrish ta farka da wata irin matsananciyar Yunwa,a gaggauce ta miƙe,ta ɗauko jallabiya ta zura a jikinta,kitchen ta wuce,batare da 6ata lokaci ba,ta ɗaura girki,bazata iya jure dafa abu mai wuyar dafuwa ba,Shiyasa ta ɗaura Indomie shaf shaf ta kammala dafuwarta,A cikin plate ta kwasota ta fito daga cikin kitchen ɗin,ta zauna a palour tana ci,sai lokacin ta shiga tunanin ko'ina su Uncle suka tafi?daga fita sallar Asuba har yanzu basu dawo gidan ba,yanke shawarar kiransu tayi idan ta kammala cin taliyar,asaman table tabar plate din da sauran taliyar,ta koma kitchen ta haɗo kakkauran Tea wanda yaji madara da bournvita,dawowa tayi falon ta zauna tana kur6arshi a hankali,


Tana cikin shan tea ɗin nan,taji dirar motarsu acikin gidan,Uncle Abusufyan ne ya fara shigowa cikin gidan,Miƙewa tayi da sauri tana fadin"Daddy,sannu da dawowa,"

  A gaggauce ya amsa mata"Yawwa Daughter,ɗaukko mayafinki mu tafi,dattijon nan ya kira ni a waya,badajimawa ba,"

  Jin haka yasa ta ajiye cup din hannunta asaman table ɗin gabanta,Jiki na rawa ta wuce ɗakin,jimm kaɗan ta dawo sanye da mayafi tayi rolling ɗinshi,hannunta ruƙe da wayarta,

  Shigowa cikin palourn tayi batare da 6ata lokaci ba,Abusufyan ya ruƙo hannunta suka fito waje wurin motarshi,Security ta gani suna tsaron gidan,tana ganinsu ta gane cewa mutanen babban yaya ne,

   buɗe motar tayi ta shiga,Abusufyan ya shiga ya zauna a mazaunin driver,tashin motar yayi tare da yin reverse ya karya kwana,da gudun gaske ya fuce daga cikin gidan,Kai tsaye suka haura saman titi,hannunshi har kerma yake yi saboda saurin da yake yi,burinshi kawai su ƙarasa cikin unguwar,

   "Daddy,ina yaya Rafayet ɗin?naga banganshi ba,"

  "Nabarshi a hotel,tun bayan da muka kammala sallar Asuba,Ni kuma na wuce gidan wani Old friend ɗina dake anan,Na jima acan,ina kan hanyar dawowa Dattijon ya kira wayata,Yake sanar dani cewa Malam Nura ya dawo"ya ƙarasa maganar adai dai lokacin da yake ƙoƙarin juya sitiyarin motar,Cikin unguwar suka shiga,a bakin bishiyar bedi yayi parking ɗin Motar cikin layin,tun kafin su fito daga cikin Motar suka hango ƙopar gidan a buɗe,bayan sun fito daga cikin Motar,Abusufyan ya daga hannunshi sama tare da cewa"Ya Allah kasa muji alkhairi!"

  Sehrish ta amsa mashi"Ameeen Daddy,"

  A ƙopar gidan suka tsaya,Abusufyan ya kwaɗa sallama,cikin sa'a suka ji an amsa masu sallamar tasu,Jimm kaɗan sai ga wani matashin saurayi dogo siriri ya fito daga cikin gidan,jikinshi na sanye da yadi,

  Miƙa ma Abusufyan hannu yayi suka gaisa,kafin yace"baƙi mukayi ne,"Abusufyan yace"Eh,baƙine,muna neman Malam nura ne,Allah yasa yana nan,"

  Tunda saurayin ya fito idonshi na akan sehrish,kallon sani yake yi ma fuskarta,ita kanta kallon nashi takeyi,kamar taso ta gane shi,da alama tasan shi tun yana da ƙuruciyarshi,Ranta ne ya bata cewar kodai Sadeeq ne ɗansu ya girma haka"!?

  "Da ace kun ƙara minti Biyar baku zo ba,da kun rasa shi,don kuwa yanzu yake shirin komawa Islamiyya,"

  Wani irin farin cikine ya lullu6e Abusufyan"taimaka kayi mana sallama dashi,". 

  "Toh,"ya amsa tare da juyawa ya shige cikin gidan,after some minutes ya dawo hannunshi ɗauke da tabarma,A cikin zauren gidan ya shimfiɗa masu ita,

   "Ku shigo daga ciki ku zauna,yanzun nan zai fito,"

  "Yawwa mun gode ƙwarai,"Abusufyan ne yayi maganar tare da ruƙo hannun Sehrish suka shiga zauren,A saman tabarmar suka zauna,Suna jiran tsammanin ganinshi,

  Wayar Abusufyan dake acikin aljihunshi ce ta soma ringing,da sauri ya zaro wayar,yana duba mai kiran nashi Sunan My first in~law ne,Amsa kiran yayi tare da kara wayar a kunanshi,

  "Uncle,A ina zan same ku"?Rafayet ne yayi maganar,

   Abusufyan yace"muna a hotoro,Amma kaɗan jira kaɗan zan tura maka da address ɗin gidan,Sai kazo,"

  Sgr yace"okey,I will be waiting,"

Rejecting call ɗin yayi,yana ƙoƙarin mayar da wayar cikin aljihunshi,Wani babban mutun ya shigo cikin zauren,bakinshi dauke da sallama"Assalamu Alaikum,"atare suka amsa mashi sallamar,yayin da suka bi shi da kallo,

  Daga ganin mutumin ya kwana biyu a duniya,ya manyanta sosai ya fara tsufa,Jikinshi na sanye da shiga ta musulunci,ta waɗanda suka amsa sunansu malamai,hannunshi na ruƙe da cazbaha,kanshi kuwa rawanine,A mutuncen shi yazo,

  Kamar yadda suke kallonshi shima haka yake kallonsu,yanayin kallon dayake yi masu kamar kallon sani ne,wuri ya samu agefen tabarmar ya zauna suna fuskantar juna,Shi dasu,

  Da sauri Abusufyan ya shiga gaisar dashi"ina kwana baba,mun same ku lafiya,"

  Fuskarshi asake ya amsashi lafiya lou,Alhamdulillah"

  Gaba daya hankalinshi na akan fuskar Sehrish,kallon ƙurulla ya shiga yi mata,nasan gano a ina yasan fuskar yarinyar,Sunnar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta,

   ɗauke idanuwanshi yayi daga kan sehrish ya mayar dasu kan Abusufyan yace"Ince dai lafiya ko?naji kunyi shiru baku gabatarmun da kanku ba,Gashi ni bansan ku ba,"

  Murmushi Abusufyan ya ɗan yi tare da gyara zamanshi,Atsanake ya soma kora mashi jawabi,

  "Ni sunana Abusufyan,Wannan kuma ƴa tace,Sunanta Sehrish,'

  Gabanshi ne ya faɗi rass,aɗan tuɗe ya maimaita sunan"Sehrish"kamar irin ya ta6a jin sunan,

  Cigaba da magana Abusufyan yayi"nasan baka gane ta ba,saboda sanin da kayi mata tun na ƙuruciya ne,Amma nasan ba zaka iya mantawa ba,Da ZAINABU ABU BUZUWA MATAR MAKWABCINKA YA SAYYADI,"

  Saboda tsabar kiɗima Malam Nura ya zabura tare da miƙewa tsaye yana kallonsu hankalinshi aɗan tashe yace"dan Allah kuyi mun bayanin su wanene ku?menene alaƙarku da zainabu abu da kuma sayyadi"?

  Miƙewa Abusufyan yayi yana ƙoƙarin kwantar mashi da hankali yace"pls baba,dan Allah ka koma ka zauna muyi magana atsanake,"

  Rai a6ace malam Nura yace"Idan maganar wannan fasiƙin mutumince ta kawoku to ku tattara kubarmin gidana!Banason ganinku,banason ganin duk wani abu daya shafe shi,ku fuce kawai tun kafin ranku ya 6aci a wurin nan "yana magana jikinshi na kerma saboda tsabar 6acin rai,

  Ganin yana ƙokarin korarsu yasa sehrish miƙewa tsaye cikin sanyin murya tace"Baban sadeeq,Ka manta da ƴan ukun zainabu abu da ta haifa"?

  Mayar da hankalinshi yayi sosai akanta yana kallonta,

  "Ni ɗaya ce daga cikinsu,nasan baka manta damu ba,Nice Sehrish ƴar uwarsu Jahad da Hosana"

   Cike da mamaki Malam nura ke kallonta,hannunshi na kerma ya nunata da ɗan yatsanshi daƙyar ya iya furta cewa"kek..ke..ƴar wurin zainabu abuce?

  Jinjina mashi kai tayi alamar eh,tace"Ni ce SEHRISH Baban sadeeq,su jahad ma suna nan araye,"

  Wasu irin zafafan hawaye ne suka soma sauka akan fuskar malam nura,ruƙo hannunta yayi yana kallonta,la66ansa sae kerma sukeyi,yayi matuƙar mamaki ganin yarinyar,bai ta6a tsammanin cewa yaran zasu rayu ba,abun yayi matukar daure mashi kai,

  Cikin shessheƙar kuka yace"Allahu akhbar!Wai dagaske ƴa'ƴan abu suna araye a doron duniyar nan?Dagaske ne abunda idona suke gane mun kuma suke jiyomun!Ya Allah kasa ba mafarki nake yi ba,"kuka sosai ya fashe dashi,duk yabi ya ruɗe bawan Allah,

  Kama hanyar shiga cikin gidan yayi,yana kwaɗama maman sadeeq kira"Murja!!murjanatu!kina inane kizo dan Allah,Ki ganemun wannan abun al'ajabin,Yau gani ga jinin zainabu abu har cikin gidana,Abun da muka daɗe muna jira,yau Allah ya amsa addu'armu"

  Jin wannan maganar ta Baban sadeeq yasa Maman sadeeq ta miƙe zumbur daga zaunen da take saman sallaya,buguzun buguzun ta faɗo cikin zauren,turus ta tsaya abakin zauren tana ƙarewa Abusufyan da Sehrish Kallo,

  Malam nura yace"kin gani ko?Yaran nan sun rayu,Wahala batasa sun mutu ba,dama nasha faɗa maki cewa Allah yana tare dasu a duk inda suke,Allah shi zai kula da abunshi,Yau dai maganata ta tabbata,kalli ki gani wannan yarinyar ƴar wurin zainabu abu ce fa,Sehrish ce"yayi maganar yana nuna mata sehrish,

  Hannu murja tasa ta daki ƙirjinta tare da Ambaton sunan Sehrish da ƙarfin gaske,

  Da gudu sehrish ta ƙarasa wurinta suka rungume juna,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,kamar ransu zai fita,

  Tuni idanuwan Abusufyan sun cicciko da kwalla,shi kanshi baisan lokacin da hawaye suka wanke mashi fuskarshi ba,

  Gaba dayansu sun shiga cikin wani irin yanayi na ban tausayi,kowa da abunda yake tunawa acikin ranshi,

  Cikin shessheƙar kuka Maman Sadeeq ta dafa kafaɗun Sehrish tana faɗin"Ashe rai kanga rai!Rishi kece kika girma haka?lallai Allah Al musawwir ne,Kalli yadda rayuwa ta sauyaki,Ban manta lokacin da kuke rayuwa a wulakance ko takalma babu a kafafuwanki,Ya Allah na gode maka daka nuna mun wannan ranar,Yau gani ga ƴa'ƴan aminiyata zainabu abu,Wayyo Allah farin ciki,"zubewa ƙasa tayi ta fuskanci gabas tayi sujjada tana kuka tana godewa Allah,hakan ba ƙaramin ta6a masu zuciya yayi ba,

  Sun ɗauki tsawon lokaci suna wannan koke koken,kafin daga bisani komai ya lafa,Saman tabarmar suka koma suka zauna,cike da jimami,kowa yayi shiru na ɗan wani lokaci,

Kafin Abusufyan ya soma magana"Baba waɗannan ƴaran ƴa'ƴana ne,bana sayyadi ba,Ya yaudaremu ne gaba ɗayanmu ya auri abu da cikina,batare da saninmu ba,Wannan shine silar duk wani abu daya faru a rayuwarsu...."

  Tunkan ya ƙarasa maganar Baban sadeeq yace"Dama najima ina zargin cewa,ƴan ukun nan bana shi bane ashe dagaske ne,Ya Allah kayi mana maganin Fasiƙin mutumin nan,Ka kawo mana ƙarshen shi,Mugu azzalumi ya jima yana cutar rayuwar yaran nan,In sha Allah ƙarshen shi bazaiyi kyau ba,"ranshi a 6ace yake yin maganar,

  "Sehrish ina Hosana take baiwar Allah"Maman sadeeq ce tayi maganar har lokacin hawaye ne ke shararowa akan fuskarta,

  "Duk suna nan lafiyarsu ƙalou muna atare dasu cikin danginmu,"

Murmushi Maman sadeeq ta saki tare da cewa"Allah sarki,rayuwa kenan,"

  "Baba ko kuna da labarin Abu"?Abusufyan ya jefo masu tambayar,

Gabansu ne ya faɗi atare suka kalli juna jin tambayar da Abusufyan yayi masu,

  Hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,tun daga kan irin kallon da yaga sunyi ma juna yasa shi shan jinin jikinshi,.  

  Hankalin Sehrish a matuƙar tashe tace"Dan allah,ku faɗamana a ina Oummanmu take?nasan kuna da masaniya akai,"

  Shiru sukayi batare da sun basu amsa ba,nan take Sehrish ta fashe da kuka tana cewa"dama nasani,zai yi wuya mu sameta araye,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"

  Ƙiriss ya rage zuciyar Abusufyan ta buga,zumbur ya miƙe yana ƙoƙarin barin wurin,hannunshi dafe da saitin zuciyarshi,

    Muryar Baban sadeeq ce ta katse mashi hanzarinshi,

   "ABU TANA RAYE,"

jin wannan maganar yasa,Abusufyan komawa dirshan ya zauna,muryarshi har shaƙewa take yi wurin cewa"dagaske abuna tana araye?dan Allah ku faɗamin gaskiya,abu tana raye?tana ina?a ina zan ganta?"

  A natse baban sadeeq ya soma kora masu jawabi,

  "Tun bayan lokacin da Hosana tayi jinya a asibiti sakamakon Buguwar da kanta yayi harta samu ta6in hankali,nasan kunji labarin nan a wurinsu Sehrish,"ya ɗan dakata dayin maganar yana kallon fuskokinsu,

  "Hakane,munji komai a wurinsu,"a ƙagare Abusufyan yayi maganar,jikinshi sae tsuma yake yi,ita kanta sehrish ta ƙosa taji abunda zaice,

   "Tun bayan da aka kwantar da Hosana gadon asibiti,lokacin ana ƙoƙarin tattara kuɗin da za'ayi mata aiki,kwatsamm aka nemi mahaifiyarsu aka rasa ƙasa ko sama,tun bayan da ta sanar masu cewa zata je gida ta sanar da sayyadi halin da yarinyar take ciki don tunda aka kwantar da ita bai leko asibitin ba da tunanin ko asamu wani abu daga wurinshi,Don acika ayima yarinyar aiki,tunda ta haura ƙafa tabar asibitin bamu ƙara jin ɗuriyarta ba,"

  Shiru ya ɗan yi yana sauke ajiyar zuciya kafin ya daura da cewa"A lokacin Hankalin mu ba ƙaramin tashi yayi ba,ga yarinya ba lafiya kwance gadon asibiti rai hannun Allah,Ga sauran ƴan uwanta dake a cikin ƙuncin rayuwa na rashin ganin mahaifiyarsu da basu yi ba har tsawon kwanaki,wannan yasa muka bazama neman abu acikin unguwar nan,Saƙo da lungu ba'a sameta ba,Gashi gidansu a garkame da kwaɗo,har muka fara tunanin cewa kodai Abu ta gudu ne tabar yaranta,wata'ƙil damuwace tayi mata yawa,shiyasa ta ta tafi tabarsu,Jinyar hosana ta koma hannun Maman sadeeq itace taci gaba da kula dasu a asibiti,"

  Dakatawa ya ɗan yi da jawabin,na wani lokaci kafin yaci gaba da cewa"Ana haka,wata rana na dawo daga masallaci,ina ƙoƙarin shiga gidana,sae ga wani yaro nan,Umari ɗan wurin makwabcinmu ne shima,Yana tsaron shagon mahaifinshi abakin hanya,shi ya tare ni yayi mun sallama,Na juya na amsa mashi sallamar,yace mun malam inason magana dakai,game da Matar mutumin nan makwabcinka,Ya sayyadi,koda naji ya ambaci hakan sai na mayar da hankali sosai akanshi nace mashi"ina sauraronka,Anan ne yake sanar dani cewa,Ya gamu da abu akan hanya tana hauka babu takalma a kafafunta babu mayafi a jikinta,tana kuka tana sambatu tana fadin cewa Ya kashe mun babana,Ya rabani da mijina!kuma zai kashe mun ƴa'ƴana,'lokacin da Umari ya sanar dani wannan maganar hankalina ba ƙaramun tashi yayi ba,tun kafin ma ya ƙarasa maganar,jiki na rawa na hau babur ɗina na koma asibiti,a gaggauce na tattara yaran nan,nasa aka kaisu katsina wurin kishiyar babata,bakomai yasa nayi hakan ba,sai don gudun kada kalaman Zainabu abu su tabbata da gaske,Saboda a nazarin da nayi,wannan sambatun da akace tana yi yana da alaƙa da haukanta,Tabbas ya sayyadi shine yayi silar mutuwar mahaifinta,shiyasa har abun ya tsaya mata aranta,kuma ya ta6a mata zuciya har ta samu ta6in hankali,wannan dalilin yasa na ɗauke yaran gaba ɗaya na mayar dasu can,saboda inajin tsoran Ya sayyadi ya halakar dasu,"


Ganin ya dakata da yin maganar yasa Abusufyan saurin cewa"Yanzu a wani hali abu take ciki?kun samu nasarar gano inda take,"

  Miƙewa Maman sadeeq tayi tare da shigewa cikin gidan,Jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da tray,ruwa ta ɗebo masu acikin Jug,sae ƴan kofuna guda uku,Ajiyewa tayi agabansu,tare da tsiyaya ruwan ta miƙa ma Baban Sadeeq,hannu yasa ya kar6a tare da kai kofin bakinshi yana sha,

  Ƙara zuba ruwan tayi a sauran kofunan ta dauka ta miƙa ma Abusufyan,girgiza mata kai yayi tare da cewa"Bazan iya shan komai ba,in har banji a wani hali abu take ciki ba,"sam babu kwanciyar hankali atattare dashi,

  Miƙa ma Sehrish ruwan tayi,"kar6i kisha ƴata,"hannun sehrish na kerma ta kar6i kofin takai ruwan abakinta tana sha,


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post