Daudar Gora book 2 page 63

Daudar Gora book 2 page 63

 

Daudar Gora book 2 page 63

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲        ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (63)
........A ɓangaren Iffah kam itama dai wanka tai ta gyara jikinta, yunwa ta hanata cigaba da zaman ɗakin ta fito neman abinci. A irin wannan lokacin. Babu kowa a falon sai daddaɗan ƙamshi da sanyin ac mai ratsa ɓargon jiki, mamaki ya kamata, duk da ɗan sanyi-sanyin garin na hadarin dake tasowa dan fitina sai an kunna na'urar sanyaya waje, baki ta taɓe abinta ta nufi dining room ɗin da glass ne kawai ya gitta tsakaninsa da falon dan komai a tsare yake. 

       Shayi tai ƙoƙarin fara sha dan shi take buƙata, wani irin masifar sarawa kanta yay lokacin da hanunta ke sauka kan abinda aka zuba shayin. Janye hannun tayi da sauri ta ƙurama flaks ɗin shayin ido, sake kai hannu tai a karo na biyu, nan ma kanta ya ƙara sarawa al'amarin kamar wata almara. Sake janyewar dai tayi tana kaiwa zaune jagwab idonta akan flaks ɗin dai. Ta kwashe mintuna uku tana kallon sa sannan ta sake ɗaurawa a karo na uku, yanzu kam duk da abinda takeji a jikinta na azaba bata cireba tsahon wasu mintuna. Idanunta sunyi jazur cikin ƙanƙanin lokaci, gaba ɗaya kamanninta sun canja kamar ba Iffah'r ba. A wani irin fusace ta miƙe ɗauke da tray ɗin da flaks ɗin ke kai zuwa kitchen.

         Taku take cikin nutsuwarta da ƙasaita kamar wata tarwaɗa ko budurwar hawainiya. Kwarjininta da cikar kamalarta kan shafe ƙarancin shekarunta musamman idan tana a cikin irin wannan yanayin. Kasancewarta a kitchen ba ƙaramin ruɗani bane ga ma'aikatan cikinsa. Hannu kawai take ɗaga musu da ga gaisuwar da suke miƙowa gwiyawunsu kan ƙasa. Kwalayen gayen shayi uku da ɗaya daga cikinsu ke ƙoƙarin fitarwa ta zubama idanunta da sukai jazur. 

     “Wannan fa?”.

Cikin sauri suka bata amsa da “Ganyen shayin shugaba ne”.

        “Daga ina ya fito?”.

    “Wanda ke kawowa a koda yaushe”.

   “Ina buƙatar ganinsa daga nan zuwa awa biyu”. Daga haka tai gaba tana ƙoƙarin haɗa sabon shayi da kanta. Sunyi ƙoƙarin ganin sun amsheta amma ta hana hakan, cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala ta fice batare data sake bi takan kowa ba. Dai-dai kuma da fitowar Tajwar Eshaan cikin shiga mai sauƙi ta zaman gida alamar bazai fita ko'ina ba. Har yanzu fuskar ciɗin-ciɗin take babu alamar yasan minene murmushi. A sanyaye Iffah ta ƙarasa cikin dining room ɗin kamar yanda shima can ɗin ya nufa kamar bai ganta ba. Kama kanta tai itama suka kai zaune a tare tana ɗan satar kallonsa ta ƙasan ido ganin ya kai hanunsa kan jug mai ɗauke da madara. Ta zubama madarar ido itama, wani irin kallo takema jug ɗin na ƙurilla, sai kuma cikin ɗauke kai da cije lips muryarta a sanyaye da girmamawa ta ce, “Shi wannan madaran illane ga duk wanda ya sha shi, barinsa a inda aka gansa shi yafi alkairi”.

        Shiru kamar bai jita ba, sai kuma ya waiwayo a hankali ya dubeta, fuska ta shagwaɓe tare da marairaiceta ta jinjina masa kai. “Dan ALLAH karka sha akwai matsala tare da madaran”.

       (Ya arrahaman wai yarinyar nan mutum ce kuwa?) ya faɗa a zuciyarsa kaifafan idanunsa a kanta. A hankali ta ɗaura hanunta kan nasa ta zare jug ɗin madarar ta ajiye gefe. Shayin ta haɗa masa, tare da ajiyewa gabansa tana faɗin “Zakaji daɗin wannan shayin fiyema da madaran”.

       Nan ma shiru babu alamar zaice wani abu, ya kumaƙi ɗaukar shayin. Sai ma gani tai ya yunƙura zai miƙe cike da izzar nan tasa ya taka zuwa ƙofar barin dining room ɗin, Iffah ta bisa da kallo ta gefen ido zuciyarta na wata irin tafasa itama. Sai dai girmansa da kimarsa bazai barta ta nuna ba koda a fuska. Kanta kawai ta duƙar, da ƙarfi ta matse idanunta da cije lips ɗinta shima da karfi. Kaɗan ya dawo da jikinsa baya alamar dama bai ficee da ga dining room ɗin ba ya kafeta da kallo. A karon farko ya saki ƙasaitaccen murmushin da ganinsa a fuskarsa ba ƙaramin yaƙi bane. Dawo wa yay a hankali ya zauna ya ɗauka shayin ya fara sha. Sosai kam ya masa daɗi, amma babu alamar hakan a fiskarsa. Itako ta ɗauke kanta gefe tama daina kallonsa. Cak taji anyi sama da ita batare da tasan sanda ya gama shan shayin ba ma. Wutsil-wutsil ta farayi da ƙafafu tana tura baki, bai kulata ba har sai da ya kaita bedroom ya dire a gado...


      😏Yau dai bazan ɗauki rahoton ba.


    ★★.....


      Cikin ƙanƙanin lokaci zartar da umarnin Tajwar Eshaan na rufe su Arshaan da Ameera Haifah ya zagaye masarautar. Nan fa aka fara ƴan ƙananun maganganu kamar yanda al'adar take. Yayinda kowa ke tambayar kansa mi yakai Haifah sashen Miran Arshaan ɗin sanin babu wata alaƙa tsakaninsu ta zahiri face matar yayansa. Anya kuwa babu wani abu a ƙasa da shi Tajwar Eshaan ɗin ya shinshino dan kasancewar tasu tare kam dole akwai wani al'amari mai girma na ɓoye. Wasu ma dai tuni suka fara fassara al'amarin da cewar akwai dai abinda suke aikatawa. In ba hakaba minene ya kaisu haɗuwa a irin tsohon daren nan ba mata ba, ba ƙanwa ba, ba uwa ba ko wata shaƙiƙiya, kuma har takaisa da neman kasheta irin haka. Labarin ya fara zama gaskiya lokacin da Jasrah ta farfaɗo. Cikin kuka take sanarma Mammah da take dubata tare da Malikat Bushirat cewar dama ta taɓa zargin Haifah a wani lokaci da tai kiransa tsakar dare, ranar ta samu damar ganin kiranne dalilin manta wayarsa da yay ya fita wani kiran ujila da batasan wayayi masa ba. Tana ɗagawa Haifah ta yanke kiran, sai dai ta riga taji muryata, koda ta dauki number ta kira da wayarta ba'a ɗaga ba, washe gari ta bada a mata bincike kan number ɗin aka tabbatar mata bata akan waya. Taci gaba da saka masa ido akan hakan amma ba'a sake kuskuren kiran ba, sai dai a wasu lokuta takanji ƙamshin wani irin turare na mace wanda shine taji a daren jiya Haifah nayi. Ta rushe da kuka mai cin rai da zuciya. Babu abinda Malikat Bushirat keyi sai cika da batsewa, tana matuƙar son Jasrah a rayuwarta, sannan ga Haifah da ke matsayin kishiya da ma akwai ɓurɓushin wani abu a ƙasan rai na kishin zama da miji ɗaya da sukai, duk da ita shaida ce mijinsu bai taɓa son Haifah ba, dan haka bata taɓa zama mai wata power a cikin masarautar ba shi yasa tuni bata a cikin jerin wanda suke a gabanta itama, duk da tayi aiki a kanta kamar su Malikat Ashwaq, dan acewar uwa ba'a sakaci da maƙiyi komai ƙankantarsa.

     Ta tabbata Jasim da Haifah neman juna suke a bakin kowa bisa zancen Jasrah, sai abinda Tajwar Eshaan ɗin yayi yay matuƙar burge ahalin masarautar har wasu na saka masa albarka da rage jin zafinsa a zukatansu. Oho shi baima san duk anai ba, dan yana can tare da ƴar shilarsa suna hutawarsu. Shirunsa kuma na nufin bazai fitoba yau gaba ɗaya kenan....


★★.... ★.....


       Kamar yanda Iffah ta bada umarnin ganin mai kawo kayan shayin Shahan-shan an isar da saƙonta. Bayan sallar la'asar tana tsaka da nazarin littafi aka sanar mata zuwansa ta hanyar wayar landline. Bataso katsewar karatun nata ba, sai dai kuma haɗuwa da mutumin nada matuƙar amfani dan haka ta tashi ta kimtsa. Tun ɗazun ta riga ta gama tsara shirinta yanda ya dace, dan sun tattauna da Daneen Ammarah ta kuma bata shawara duk da a farkon bayanin Iffah ɗin jimm tayi na rashin fahimtar manufar hakan. Sai da Iffah tai mata bayani dalla-dalla dai-dai da yanda ta tsara sannan ta gamsu ta kuma bata goyon baya ɗari bisa ɗari.

        Hurumin duk wani baƙo a sashen Shahan-shan iyakarsa falon farko ne, wanda har ya tsallake zuwa na biyu ya kai babban baƙo kam na musamman, balle na uku kuma da a tarihi ma bayan masu hidima Malikat Haseenat da Malikat Bushirat ne kawai suka taɓa iya tsallake wannan hurumin sai ko Daneen Ammarah da tai dalilin Iffah, dan Tajwar Eshaan fa bai zauna a sashen da mahaifinsa ya rayu ba. Shi da kansa mahaifin nasa yasa akai masa wannan ginin tunkan ya dawo ƙasar ruman. Hakan yasa har yanzu babu wani mahaluki daya san sirrikan tsarin wannan sashe sai mai shi ɗin.

       A kowane falo Iffah na samun gaisuwar girmamawa, dan ta stairs ta biyo ko'a jikinta duk da wahalar hakan, yayinda amintattun Hadiman Tajwar Eshaan da'a ƙa'ida basa sakkowa ko falo na biyu sai da dalili ke biye da ita. Dattijon mutum da alamu suka nuna shima ɗin dai wani babbane dan babu wata ƙazamar shiga tattare da shi yay saurin miƙewa domin girmamawa ga Zawjata-almilk ɗin. Iffah takai zaune tana ɗan satar kallonsa ta gefen ido batare da kowa zai iya lura da hakan ba. Rissinawa yay domin gaisheta ta ɗaga masa hannu kawai da masa nuni da wajen zama.

     “Godiya nake ranki ya daɗe”.

Ya faɗa cikin ƙanƙan da kai yana kaiwa zaunen”.

       Sai da taja kamar minti biyu falon shiru kafin ta nisa. “Na buƙaci ganinka nan ne bisa wani dalili da bai gaza biyu ba. Na farko daga yau na dakatar da kawo duk wani ganyen shayi da sunan Maleek a gidan nan. Na biyu akwai aikin da zakamin”.

    Hankali tashe ya ɗan dubeta sai kuma ya rissinar da kansa. “Ranki ya daɗe ki gafarceni, wani abu ya faru ne?”.

         “Komai bai faru ba. An samu sauyin sabon tsarine kawai. Shin kozan iya sanin sunayen abubuwa da ake haɗa kayan shayin Maleek?”.

     “Sosai kuwa ranki ya daɗe, mi kike buƙatar sani?”.

  “Komai”

Ta bashi amsa a taƙaice. Da sauri ya buɗe jakkar gefensa ya zaro wani littafi. Da sauri ɗaya daga cikin hadiman ta amso ta kawo mata bayan ta kai har ƙasa. A dake Iffah ta amsa babu alamar wani ɗar tattare da ita ta fara duba littafin daya kasance ɗan babba.

      Duk da yasan babu wani abu na cutarwa a ciki tunda a sirrance kuma aka bashi ganyen shayin da ya aiko jiya da dare a tsorace yake, dan harga ALLAH gizagon wannan baiwa da kwarjininta ya cika masa ido matuƙa har yana jinsa a takure cikin falon ma. Da ɗin daɗawa kuma wannan shine karo na farko da akai masa irin wannan kiran ma saɓanin da da sai ya haɗa wani samfur na sabon ganyen shayi yakan zo ya gabatar kozai birge Shahan-shan. 

          Kusan mintuna biyar Iffah nabin littafin daki-daki har kusan tsakkiyar, ɗan gajerun bayanai ne akan yanda ake haɗa ganyayyakin da sunayensu. Rufewa tai tare da ɗan ɗagowa ta dubesa. “Uhm komai dake anan kam bashi da wani aibu, sai dai saɓaninsa daga yanzu muna bukatar fresh ganyayyakin ne. Kuma za'a dinga noma su ne a cikin masarautar nan”.

    “Yanda kike so haka za'ayi ranki ya daɗe”. Ya faɗa cikin tashin hankali a bayyane. Iffah da tai kamar bata fahimcesa ba ta miƙe, “Ka haɗa duk abinda ya dace a turamin, idan na kammala da nawa shirin zan nemeka”.

          “Godiya nake ya Zawjata-almilk. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai amfani”.

     Hannu kawai ta ɗaga mai tai wucewarta, hadiman da al'ajabi ya sandarar a tsaye suka take mata baya da sauri.......✍️


      

 _(Wato wannan yarinyar ko? Humm🥱😂)._


   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post