Daudar Gora Book 2 page 68


Health College

Daudar Gora Book 2 page 68

 

Daudar Gora Book 2 page 68

DAUDAR GORA 

Book 2

68

.Lokacin da azhar ta gabato Tajwar Eshaan ya tashi yay wanka ya kimtsa babu alamar Iffah zata motsa, kwance take sharkaf tana kwasar barci kamar wadda ta mutu. Zama yay a bakin gadon ya zuba mata ido, tare da kai yatsunsa saman goshinta da wuyantan amma babu alamar wani zafi da ke nuna tana a cikin ciwo. Da kyar ya tadata tana faman tura baki gaba, ya kafeta da kaifafan idanunsan nan, sake tunzura bakin tai ta kauda kai. Sai shima ya dan girgiza kan a fusge ya furta, "Ki daina turamin wannan bakin na dinga kai azumina lafiya batare da ya raunana ba. A haka za'ai ibadan Nigar?".

    Kwalkwal tai da idanunta kamar zata saki kuka tace, "Nima zuwa fa barcin kawai yake, konace bazanyi ba sai na kasa". Shi dai kallonta kawai yake zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa. Amma sai bai furtaba ya ce, "Okay tashi ki shirya muje massalaci ga su Sultan na jiranmu". Babu yanda ta ia dole ta tashi ya taimaka mata ta shirya din, dan a hakan ma sai faman lumshe masa idanun take da sakin hamma. Shi dai lallabata yay suka wuce dan ya fahimci abin bana lafiya bane. Kilama Aljanun nata ne ke sakata barcin dan kar tai ibadar....

(A gurguje Please munada sauran aiki, gashi nagaji walle. Gara muyi mu gama kowa ya huta 🏃‍♀️).

Rayuwa a Saudiyya wani rubutaccen al'amari ne da Iffah bazata taba mantawa da shi ba a rayuwarta, dan rubutaccen labarine tsakaninta da Maleek dinta mai zaman kasan ga ma'abocin bibiyar labarinta, amma ta tattara ta killacema zuciyarta kawai kuma sai ku kiyasta da hasashenku. Duk da dai ta samu nakasun raunana a dalilin barcin da bata san kansa ba balle karshensa. Amma duk da haka tana matukar yaki da shi da ganin tayi cikakkiyar ibada. Dan abu mafi birgeta shine yanda Tajwar Eshaan ke tsaye akan kafafunsa koda yaushe babu wasa tattare da shi ko nuna gajiyawa a dare da rana. Gaba daya ya maida hankalinsa a bautar Sarkin sarakunan nan mahaliccin duniya da kayan cikinta, mai rahama da mukullin aljanna. Sarkin da babu kamarsa kai koda kwatankwacinsa ma babu. Gaba daya ya mika lamuransa garesa cikin kaskantar da kai da zubda gwiwunsa bisa kasa. A duk sanda yake addu'a zaka samesa da hawaye share-share da inba gaban UBANGIJINSA ba bazaka taba gani ba. Kullum cikin gayama ALLAH yake kan samun warwarar al'amuran da suka shige masa duhu musamman akan mutuwar yaran da basujiba basu gani ba a daliln aurensa. Duk da wannan jajircewar tasa kuma yana bata kulawa a dan kankanin lokacin da suka daukarma kansu na hutawa. Dan ko bayan kammala Umrah din su bai lamunce su zama a karkashin inuwar lalaci ba.

 A gefe kuwa wata Irin shakuwace ta shiga. tsakaninta da uwargidan Sultan. Mace hamshakiya ma'abociyar kyawawan halaye da nuna tsattattacen iko saman na kasa da ita. Nutsuwa sosai Iffah tai tana koyan abubuwa, yayinda itama bata tsaya boye-boye ba ta fito tana gyarama Iffah'r duk abinda zai bata martaba da kima a wajen mijinta da al'ummar da mijin nata ke shugabanta. Dan tayi dubi ne da karancin shekarun Iffah'r da ma labarin data bata na cewar ita iyayenta basu da alakan mulki. Ba halayyar Iffah da dabi'u ba hatta jikinta wani irin gyara yake samu na musamman ga uwargidan Sultan din.


    Hadimanta kam tunda sukazo bata gamsu sun ganta sau cikakken biyar ba. Hakama duk dokinta da tsammanin zal hadata da su Babiy tunkan su taho babu alamar zai yi hakan. Har magana ta masa cikin hikima amma sai baice mata komai akan hakan ba. Dole ta hadiye komai ta nuts bisa shawarar uwargidan Sultan din.

  Shanyewar tai kuwa, dan yanzu Iffah an koyi halin dattako da shanye abu a ral, sai dal fa à gaban Tajwar Eshaan bakin baya mutuwa, idan kin jita shiru barci take, a lokacine kawal zai huta da tsiwarta.

Alhamdulillah yau an kai azumi na ashirin da shida, a yau ne kuma su Iffah sukayi ziyarar bankwana cikin dakin ka'aba ita da Tajwar Eshaan da Sultan na saudiya, da uwargidansa, sai wasu manyan masarautar tasu. Iffah tasha kuka lokacin da taganta cikin tsakkiyar dakin ka'aba, Abune da bata taba zaion kasancewarga ba koda a cikin matarkinta. Kal ita ketare kasar ruman ma bata taba zaton tana da rabon yi ba a rayuwarta. Amma yau sai gata da kwanaki ashirin da biyar cikin kasar Saudiyya, tare da mijin aurenta shugaban kasarta. Hannunta kawai ya rife cikin nasa alamar lallashi har suka fito, suna shige mota kuwa ta fada jikinsa ta kankamesa. Murmushi yay mai sanyi da dagota yana mata yan harara tare da lakace mata hanci. "So kike ki karyamun azumi ne?"

    Baki ta dan tura tana wan kikkitata Idanun dake cike da hawaye, a shagwabe tana war idanun da yanayin mamaki ta ce, "Dama maza azuminsu a karyewa ne?". Murmushi kawal yay ya dauke kansa, sai kuma ya sake juyowa a yanayin wanda ya tuna wani abu, kallonta yay da ga sama har kasa kafin ya jeho mata tambayar data daure kanta da bata yar kunya-kunya. "Mrs Eshaan kin sha wani magani ne dan kar kisha azumi?". Da kunya-kunya mamaki-mamaki ta dubesa, sai kuma ta girgiza kanta alamar a'a. Itama kuma sai kirjinta ya shiga harbawa da sauri-sauri. To al bama watan azumi kawal ba, idan bata manta ba rabonta da ganin proud din ta fa kamar tun wanda ta gama da kwanaki kadan ya ziyarceta bafa ta sake ba. Kai kodai ta sake ta manta, to idan ma ta sake din ai a watan nan ne na Ramadan ya kamata ta gani farkonsa, juya mata kanta ya fara yi saboda neman takurama kanta da tai na sai ta tunano. "Kinga relax karki takurama kanki"., Ya fada a hankali yana kwantar da ita a kujerar.Gaba daya jiyay yama kagara su koma cikin masarauta, suna isa kuwa masaukinsu aka zarce da su. Duk da an bude mata kamar yanda aka bude masa kofa shima sal ya fito da ita ta inda ya fita, basu fi zaman mintuna goma ba doctor din da ya bukaci gani ya iso tare da uwargidan Sultan da hankalinta ya tashi da tunanin ko kukan da Iffah tayi ne ya zame mata matsala,

    ita Iffah sai ma abin nasu ya bata mamaki da dariya,ta kal dubanta ga Tajwar Eshaan da yay zaman kasaitar nan tasa. Cikin langabe kai ta masa magana da ido alamar wai mike faruwa? Dauke kansa yay gefe a ransa shi kadal yasan miyake ji na farin ciki, ya kagara doctor din tace wani abu. Amma a zahiri baka isa fassara abinda ke ko"a kan fuskarsa ba balle zuciyarsa. Doctor da tai yan gwaje-gwajenta a gabansu abinka da gidan manya ta dago tana murmushi, cikin girmamawa ta fuskarci uwargidan Sultan ta mika takardar da tai yan rubuce-rubuce.

"Ya ALLAH"

   Uwargidan Sultan ta fada fuskarta da kayataccen

murmushi. Ta kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke jin kamar ya fisgo takardan hanuntan amma ya dake a zahiri. "Ina mai farin cikin kasancewa ta biyu bayan doctor akan sanar muku samun karuwa da mukai, ALLAH ya sauki Zawjata-almilk lafiya". Wani irin lumshe idanunsa yay da sauke sassanyar ajiyar zuciya kamar wanda aka zarema numfashi. Yayinda Iffah tai fakare tana kallonsu cikin rashin fahimta sam. Dan ita kanta ma sat ya toshe kawai a wanna gabar. Har suka gara bidironsu Uwargidan Sultan ta wuce bata iya tofa komai ba..

Wani irin dagata yay bayan ficewar kowa a falon ya shiga juyi da ita. Kawal ita sal abin ma ya bata dariya ta shiga kyalkyalawa. Bai hakura ya direta ba sai da yaga ta fara date kal alamar jujuyatan da yake akwai matsala. A tare suka dinga sauke numfashi, ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifi ga kayataccen murmushi mai matukar tada da yakan dace baka gani a fuskarsa ba, Sal dal kuma a zahirance bakin ya gagara cewa komai. Sal da ya mula dan kansa a hankali ya furta "Mrs Eshaan kin mallakeni da komal na. Da gaske fa ni din bawanki ne". Da sauri tasa hannu ta rufe bakinsa tana zaro idanu da girgiza kanta. Cikin rawar murya kamar mai shirin sake masa kuka ta ce, "Please Sultan ka daina fadar haka karma yan kasar ruman suji sumin yankan rago. Kai fa shugabana ne, sannan ashekaru ka fini, gaka mijina,uban yayana", Hawayen suka silalo mata a hankali. Hannunsa ta kamo ta daura akan cikinta. "Nagodema ALLAH da ka kasance mahaifinsu badan ya baka daukakar mulki data dukiya ba. Domin su a duniya aka samar mana da su a cikinta kuma zamu tati mu bari wataran. Ina alfahari da kai ne matsayin uban yayana saboda nagartarka da adalcinka. Tsoron ALLAHn ka da kyakylyawar zuciyarka. Maleek kai na dabanne a cikin daban. Ba yan kasar ruman bane kawal suka dace a dalm shugaba ba. Daular musulunci ma kai abin alfaharinta ne. Sannan kuma nice kololuwar dacewa da ka kasance miji gareni, Nauyin mulki bai sa ka gaza bani farin ciki da sauke duk wasu hakkokina ba. Kana samar da nishadi a tsakaninmu ka manta da kai sarki ne mai jagorantar talakawan kasa bawai jaha ko wani dan yanki ba,

Kwanciyar hankalin da nake samu da ga gareka bana jin wasu matan da mazansu basu da nauyin kowa na sarun makamancin sa. Maleek kai ne gwarzo na, kai ne Barde na, kuma kaine gagara badau dina".

    Idanunsa kawai ya lumshe a zahiri, maimakon ita da ke kuka a bayyane shi a zuciya yake yin nasan. Tabbas yaga ribar hakuri, kai shi baima san mizaice da UBANGIJI ba akan kyautar wanna yarinya da ya bashi. Ita din ta dabance. Tabbas itace komansa. Tsam-tsam ya rungumeta a jikinsa na tsawon lokaci, sal da ya ji tana sauke numfashi a hankali alamar barci ya dauketa sannan ya dagota. Kwantar da ita yay a hankali ya cigaba da kalionta hannunsa saman shafaffen cikinta da kamar babu komai a cikinsa abubuwa da yawa na masa kaikawo tun daga randa ya fara ganinta soyayyar farat daya ta shigesa har zuwa yau da ajiyar gudan jininsa ke à cikin jininta…..✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post