Daudar Gora book 2 page 88

Daudar Gora book 2 page 88

 

Daudar Gora book 2 page 88

DAUDAR GORA 

Book 2

Page 88

."Kamar dai yanda ta kasance a gareki. Ita tana da buri akan wannan masarautar, sai akai sa'a ke ma kinada naki burin da kika kai kanki gareta.

 Ita kuma sai tai amfani da haka kika zame mata yar aiken isar da sakonta ta yanda babu wanda zai fahimci ruhinta ya sake dawowa wanna masarauta balle ma a zargeta akan dukkan abubuwan da suka faru har a maida hankali. Wanna labarin naki yasa na fahimci maganar mahaifina da ya ce, duk saninka kankanuwar samarwace da ga taskar ALLAH da bata yankewa. Sannan haihuwar ita Fhareedah wani mashine da ga UBANGIJI da zai zama sanadin tarwatsa al'amuranku batare da kun fargaba, shiyyasa ya boyeta a cikin sirrinsa har zuwa ranar da

zata dawo gareku cikin karfin ikonsa da zai tabbatar muku babu wani karfi da ke saman nashi. Shirka babbar faduwa ce, ginshikine na gina kaskanci a duniyar bawa dama lahirarsa. A duk lokacin da ka dauki cewar wanin ALLAH a iya baka koda kariyane da ga wani abin tsoratarwa to akwai babbar matsala,dan kuwa shi wanna mushirikin zai bika mataki-mataki ne wajen kaika fie da inda bakai hange ko tsammanin zuwa ba. Kamar dai ke din nan. 

A matakin farko bukatar haihuwa kikaje mata da shi, sai ta ce miki kada kiyi sallar la'asar. Tayi hakane saboda kasancewarki mai bautar ALLAH, sannan kina jingine da wasu muminai da zasu iya saurin fargar dake kuskurenki kuma ki gyara. 

Amma data kafa miki wannan tarkon sai ta busar miki da zuciya ta yanda duk yanda za'a kiraki bazakiji wannan kiran ba, ba kuma zaki saurari mai kiran ba koda ace kin jisa. Hanaki bautama UBANGIJI itace allurar farko mai tsananin dafin data sakaki shagaltuwar da bijire mata zai miki wahala koda ace kina so. Shiyyasa maganin ayima kar a fara, tun farko ma yi kokarin yin addu'a da yakar kanka daga son zuciya ko tunanin nema daga wanin ALLAH. 

Miyasa musulunci ya mana gatan cewa mu tashi mu nemu na kammu? Saboda kare kammu da ga biyayya ga abinda zai iya cutar damu. Dan a mafi yawa ko nace rinjayen dan adam yana son a duk sanda ka nema daga garesa duk sanda wani abu ya taso da zaka iya masa to ya tuna maka wannan taimakon da yay maka wanda zai iya sakaka jin kunyar yimasa abun nan koda ace bai dace ba. Kamar dai cin hanci da rashawa. 

A duk lokacin da mai bada cin hanci ya mika ga mai karba zai iya aikata aiki komai muninsa koda ace zai iya cutarwa ga rayuwar mal karbar shi kansa ne ma. Dan haka maganin data baki a tun farko ma bashi da alaka da abinda kikaje neman. Ta baki shine domin cutar da abinda ke cikin ki data riga ta tabbatar da akwai. Sai dai ALLAH ya riga ya kaddara babu abinda zata iya yi sai ya zo duniya, dan haka ta tafi mataki na biyu wajen rabaki da mahaifarki gaba daya. 

Mataki na uku ta rabaki da mijinki, mataki na hudu tai amfani dake wajen gogama rayuwar danki bakin fentin da zai bakantashi ga al'ummar kasar sa da mulkinsa. Lokacin da ake ihun yay murabus badan Iffah ta shayar da shi wannan madarar mai dafin macizai ba da burinta a tsigesan, hakan yana cikin plans dinta da idan wanna baiyi tasiri ba zata tsallaka na gabansa. Da ace taci nasarar kun hada auren wadda taso ta haifi magajinsa da taci nasarar duka wasan. 

Dan sam wadda take burin ya aura bama mutum bace cikakkiya yar zuri'arsu ce aka raina a anan duk saboda zuwan wannan lokacin. Daga kuma sanda ta samu ciki burinta shine ta kasheki, shima ta kasheshi wanna jinjirin ya amsa suna magaji, da ga haka ta karbe mulkin ta karfin tuwo da ga wanna ahalin. 

UBANGIJI bai gitta rayuwar Iffah a cikin al'amurran ki da rayuwar danki ba sai dan shi tsarkakakkene mai tarin tsoron ALLAH da kiyaye dokokinsa. Ya gadar da shine da ga kyawawan halayyar mahaifinsa sabanin naki dabi' un. Addu'oin da al'umma ke masa na tasiri a tare da shi tare da yin dubi da tsarkakakkiyar zuciyar kakarsa da tai yaki da yakar mushirikai. Mutuwar mahaifinsa da kakansa tazo ne akan gaba bawai bisa karfin ikonta ba. 

Da ace ma tayi hakuri zasu musu, tabbas zasu mutu a dai-dai wanna gabar har su matan nasa. Amma a yanzu hakkin ruhinsu duk ya rataya a gareku ke da ita domin harda amincewarki akai komai ba tilastaki tai ba a aikace.Kaiconmu da irin wannan burin duniya, kaiconmu da irin wannan hangen da babu hango iyakar karewarsa, kaiconmu da zuciyar da ke jin hakkin wani ba komai bane komai Kankantarsa komai rashin muhimmancinsa, Wlhy duk

abinda akace maka ba naka bane sunansa ba nakan ba. Idan kuma harka taba da son zuciya ko izgili sai ka biyashi a ranar da babu kudi irin madadin a duniya. A ranar da cuniya ce zata taru, a ranar da ake biyan hakki da lada ko zunubi. Dan duk hakkin wanda ka taba zaka biyashi da ladanka, idan baka da lada za'a dibo zunubinsa a lafta maka. Shiyyasa mutane da yawa zasuje lahira da tarin lada a taskokinsu, amma yayin kammala musu hisabi sai su koma basu da korai sai tarin zunubai dan an biya duk wanda suka cima hakki da wanna ladan nasu. Haba yan uwa har wane aiki muka tara da har mukejin cin hakkin wani zai isa mu biyasa har mu sami rarar shigar aljanna da sauran. Wani ma har kaji yana izgilin shi hakkin wani ko ALLAH ya isa bata masa komal a jiki, why da tabon da zatai maka a rayuwarka gara ace a jikinka take tsirowa maybe kaji tsoron ALLAH da wuri ka sauke hakkin. Shi kuma wanda ma ya hadiye bai ce dakai komai ba yafi ban tashin hankali fiye da wanda zai furta maka maybe ka razana ka sauke. Wai miyasa bama tunanin cewar wanda muka cima hakkinsu sune masu nasara akan mu ne? Tabbas masu nasara a kammu, dan sun kasance masu ajiyewa a dauka a kuma biyasu a ranada ake farautar ayyukan cika mizani. Kawai akan son farantama was mu mu tauye kammu mu daga nasarar wasu. Wai a hakan dan wawanci murna mukeyi, farin ciki mukeyi mun karya wane, mun kaskantar da wane, mun maida wane baya, waya fada maka dariya ya kamata kayi ko kiyi?Wlhy kuka, kuka ya kamata ki fara tun kafin ganin anar nasarar mai wanna hakkin da taki faduwar,Wadan nan hakkokin da muke rainawa suke hauhawa

su gawurta su zama manyan abubuwan ruguza ayyukanmu. Kamar dai ita, ta fara ne tun a kuruciya, zalinci wancan, tirsasa wancan ana gain yarintace hakan ba komai bane amma sai abin ya cigaba da tasiri a rayuwarta har yay gawurtar da ayanzu ta fado kasan-kasan kafafun wadan da take gain ba komai ba, wanda take ganin murjesu ta taka ko cin hakkokinsu ba komai ba. Gadai shi taji dadin, tayi farin cikin, ta dauki kanta a mai nasarar, amma a karshe itace ta zama mara nasarar, mafi kaskanci.Mafiya masu cin hakki da ruguza rayuwar wasu zamu samu matasane masu tasowa, maybe batai aure ba ko baiyi aure ba, kokuma bata jima da yin auren ba,dan duk wanda, ko wanda ya kai shekaru arba'in a duniya ya zabi take hakkin wani babu babban wawa sama da shi. Amma su wadan nan masu tasowar gani suke abinda sukeyi ba korai bane, yanzu ma aka fara rayuwar. Waya gaya miki koya gaya maka ba komai bane ba. To ko kasa mutum ya gino ya tara kikazo wucewa ko kazo wucewa ka barbaza masa ai hakkine balle abinda ya killace koya nunama duniya abun nan mai muhimmanci ne a garesa koda ace kai baka ganin muhimmancin nasa. Kanada kananan shekaru kana ta daukar hakkin mutane da kake gain bamai muhimmanci ba kana tarawa yana hauhawa a mizanin aikinka yana rusaka, yana rusa rayuwar yayanka masu tasowa, yana rusa cigabanka na duniya dana lahira kai kana shirmen kana nasara akan mai hakkin. Kajifa toshewar basira, shi kana kara masa nasara ne fa, tunda dole-dole ka biyashi a inda babu kudi sai aiki inhar baka biyasa da kudin daya shardanta akan kayan nasa ba. Kamar dai ita a yau, komai yazo mata a gabar da bata da damar neman gafarar wadanda ta zalunta ta cutarma da rayuwa saboda nasararta da neman cikar burinta. Ta rasa a lokacin da su kuma suka samu, wata tayi amfani da ita dornin nasararta ta barta da katon nauyi bisa kai. Kaicon rayuwar da ba'a tuna mutuwa a cikinta. Kaicon rayuwar da ake ginata kamar bazata yanke ba. Kaicon rayuwar da ake daukar hakkin wani kamar ba hakki ba. Kaicon rayuwar da cikar buri ke jagorantar imani da tsoron ALLAH a zuciyar mai shi. Kaicon zuciyar dake bushewa da jin komai tayi dai-daine. Ya ALLAH ka karemu, ka kara tsaremu, ka tsarkake mu, ka kiyaye mu. Ka killace mu, ka karfafa mu, ka jagorance mu bisa tsoronka da tsoron shirka, da tsoron cin hakkin wani komai kankantarsa, ka kyautata neman mu da ga halak, ka karfafa ayyukanmu bisa umarninka da kiyaye saba maka badan halinmu ba. ALLAH ka shiryar da wanda suka kauce, idan ba masu shiryuwa bane UBANGIJINMU mun barka da su kafimu sanin miya dace da su. ALLAH ka rabamu da ruin duniya da kyale-kyalen cikinta. Ya rabbi ka saka DUNIYA a tafukan hannayenmu ka nisantata zama a cikin zukatanmu. Ya rabbi ka wajabta mana tsoronka, ka karfafa imaninmu. Ka yafe mana kura kuranmu, ka bamu ikon kyautatama duk wanda ka hada kaddarar zaman mu a tare ko mu'amularmu, Ya rabbi ka hana mugayen halayenmu cin nasara a kammu, kasa muci nasara akan mugayen halayenrnu da ayyukanmu".


    A tare suka dinga amsawa da Amin kowa na sharar hawaye, yayinda Malikat Bushirat ke kuka mai tsananin gunji. Matuka takejin radadi a zuciyarta da azaba a cikin jikinta, So take ta kara cewa wani abu koda ga tilon danta ne da har yanzu bai dago kai a dubi kowa ba balle ita amma ta kasa hakan. Da ga karshema mikewa yay a hankali cikin tangacfin juwa hannunsa cikin na Iffah har yanzu batare daya kalla kowa ba balle cewa wani abu ya jata suka fice. Ta hanyar sirrin da suka fito ta can suka koma hankalin Iffah a tashe da yanda yake tangadì mai bada tabbacin akwai matsala….✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post