Daudar Gora book 2 page 87

Daudar Gora book 2 page 87

Daudar Gora book 2 page 87

 DAUDAR GORA 

Book 2 

Page 87

….Bayan dawowar uwa al'amuran mu sun cigaba da tafiya, dukan shardanta a cigaba da cikasu, dan dama ko bayan batanan ban fasa ba, dan ina tsoron abinda ta fada akan Saiful-malik ya tabbata. Dan wannan tsoron da son cimma buri ne suka jagoranceni har zuwa wannan lokaci. Ni naita zungurar Haysam akan yin murabus lokacin da Saiful- malik ke cika shekara talatin da uku a duniya, nayi hakanne kuma bisa umarnin uwa. A duk sanda nai maganar yakan yi murmushi ne kawai, amma baya cewa dani komai, Sai hakan ke cimun rai da tunanin baya son ya sauka ya daura Eshaan din ne. Ni kuma abinda nake hange adadin shekarun da Uwa ta tabbatar min zai rasa ransa a dalilin shayin da nake shayar da shi gabatowa suke, ta kuma tabbatar min infa ya mutu ba'a daura Saiful-malik a karagar mulki ba akwai rikici sosai, domin Haysam nada kanne, shekarunsu kuma sunfi zama shekarun hankali da yan kasa zasuyi jayayya da samun rabuwar kai akan magajinsa Eshaan. Na sake takura masa da tada hankalina akan hakan har takai wata rana ya furta min abinda ya girgizani.

 Ya ce (Bushirat basai kinyi gaggawa akan mutuwata ko rayuwata ba. Idan kaddarar mulkar kasar ruman na rubuce a littafin kaddarar Eshaan sai yayi ko ina raye ko bana raye, abinda na sani kawai ina matukar tausaya masa, ina tausaya masa yaki na cikin gida da waje. Yakin da zai masa matukar wahala musamman kasancewarki ke wa mahaifiya da kika zamto a cikin manyan makiyansa) rai bace nace ban gane ina cikin manyan makiyansa ba? 

Bai sake cemin komi ba, illa murmushi kawai da ya saba mun. Maganar ta zauna min a rai matuka, har ta kaini da fadama uwa. Itama naga alamar ta girgiza, dan haka take anan ta tabbatar min dole muyi motsin da Haysam fa zai bada mulkin nan sannan mu kaudashi, dan alamominsa na nuni da akwai abinda ya sani game da ni, idan kuma har mukai sakaci wahalarmu ta baya zata zama a banza. Babu wani damuwa a raina na bata goyon baya, dan saima tashin hankali da nakeji akan cewar Haysam yasan wani abu game da ni din, ina tsoron ya fadama mahaifinmu, dan wilhy zai iya tsireni ne kawai kasancewarsa mutum mai zafi da bin dokar addini. Haka akai, ta kawo abinda naita saka masa a madara yana sha har tunaninsa ya karkata a yin murabus, babu zato babu tsammani kawai ya dawo da Eshaan gida, ya kuma tabbatar da zai yi murabus ya daurasa a karagar mulkin Shahan-shan. Kalubalen dana so fuskanta shine Eshaan da kansa, dan yaso bijirewa da cewar shifa baya son mulkin nan, bai taba ma birgesa ba, yafi son rayuwar yanci, yayi abinda yake so a lokacin da yake so, a cikin tarin burukan rayuwarsa ma babu maganar mulki a ciki. Na tashi hankalina Uwa tace na kwantar, ta bani wani turare tace na basa kyauta, in har yay amfani da shi na kwana uku sai ya amince. Hakan ce kuwa ta kasance. dan satin bai shigeba sai gashi da cewar ya amince. 

Uwa ta kara shiga raina da jin bani da kamarta duk duniya, zata kuma iya sakani komai nayi amma banda sadaukar mata da Eshaan, dan shine abinda nafiso fiye da komai a duniya. Anyi nadin sabon Shahan- shan tare da shagalin bikin aurensa na mata hudu, ko sau daya bai tanka akan auren ba, baice bai son su ba bai kuma ce yana so ba. 

Ni kuma bam ma damu da tambayarsa ba tunda nasan makomarsu. Kamar yanda uwa ta fada Haysam ya shude, matan Eshaan ma daya bayan daya sun zama labari, an cigaba da auro masa was suma tarihinsu na shudewa, a haka har nazo gab da cikar burina na gama wannan sharadin. Rana tsaka, ina gab da cimma abinda na faro kwatsam yarinyar ta shigo rayuwata. Ba kai tsaye ta shigoba, dan bana jin ma ta sanni ita. Yaki ta shirya, ya ki domin yakar Eshaan saboda rasa yayunta biyu da suka shigo cikin aikina. 

Itama tanada tunani ne irin na sauran mutanen kasar ruman akan Saiful-malik ne ke halaka matansa. Wanna itace mafarin matsala, dan tunkan ta shigo ita nacema uwa ta kauda min ita, dan ina a gabar da zuciyata ta gama dakewa da bushewa zuwa yanzu, hatta hadiman dake mun ayyuka da sunyi kuskure mafita daya nake hangoma kaina shine kawai na kaudasu, idan na kaudasu matsalata ta kare kenan.

 Da nayi din sai inga ta kare kuma, dan haka nake kallon kashe duk wanda ya shiga gabana akan cikar burina kawai na kauda san Uwa ta tabbatar min babu kaddarar mutuwar yarinyar a wannan tsakanin, sai dai mu nemo wata hanyar, a cikin neman mafitar ne muka yanke zamowarta a daya da ga cikin matansa, domin a ganinmu idan ta matso gab da mu sai munfi cin nasara a kanta. Sai dai kuma al'amarin bai kasance yanda mukai hangesa ba, dan tunda ta shigo rayuwar gidan komai ya daina yiwuwa a cin sauki. Labarin farko ya canja zuwa wanda bashi muka tsara ba. 

Dan hatta madarar farko da nake shayar da duk Zawjata-almilk ita kin sha tai, alkyabba da turaren da nake badawa a musu wanka da shi a sako musu tun daga gidansu shima basu akai mata ba, ban hakuraba na bibiyeta da su nan ma taki yarda tai amfani da shi, duk ta inda muka bullo sai ta waske, da ga karshe ma wata rigar da mu bamu san ta ina ta fitoba ce ta sanya, daga haka ta koma sashen Mammah da zama, ita kuma ta kaita sashen Saiful-malik batare da shawarar mu ba bayan mun yanke a yanda zamu mata rakkiya zuwa can. Dan saboda na rabota da sashen Mamma da uwa bata iya zuwa yasa na bada shawarar maidata sashen Saiful-malik ta mana bincike, amma sai Mammah ta canja shirin namu gaba daya. 

Wannan abu ya konamin rai matuka, ya kuma zafi zuciyata na kasance a bakin ciki. Mairakon nasara komai sai sake tabarbarewa yake, da kyar muka samu cikon ayyukan mu akan Zawjata-almilk data tarar, Itako dai ta kasa tabuwa a garemu a duk ta inda muka bullo. Tun ana yakin sunkuru har komai ya fito fili da fitar da ban san mafari ba da ga gareta, yakin ya koma na kasanni na sanka......" ta rushe da kuka mai karfi. Sai da tayi mai isarta babu wanda yace mata ko kanzil sannan ta cigaba da fadin, 

"Babban tashin hankali na a yanzu da jagorantar dukkan karfin halin iya maida martanina ga uwa a wannan gabar da komai na tabbatar da ya lalace shine rasa Saiful-malik, ta sake tabbatar min sai sun amshi jininsa matsayin diyyar kin cika shardansu, bana son na rasashi, shine kadai ya  kuka ya sarketa ta kasa cigaba. Jasrah ma kuka take iya iyawa, sauran yan uwanta kam tagumi duk sukayi kawai. 

Hankalin Iffah gaba daya akan Tajwar Eshaan yake, dan tunda ya dukar da kansa da kamo hanunta ya rumtse a cikin nasa har yanzu bai ko yi wani motsin kirki ba, hannun nata kuma na rumtse a nasan duk da azabar da takeji saboda yanda yake matse a cikin nasan haka ta cigaba da daurewa tana mai ambaton addu'oi da duk sukazo bakinta. Fatanta ALLAH ya saukaka masa zuciyarsa, ya bashi juriyar dauka.


   Gyaran muryar kaka ne ya katse tunanin kowa. Ya nisa a hankali tare da gyara zamansa. 

"Lallai kinyi kuskure, kin kuma shiga rigar yaudara irin ta wadda bokaye kanyima bayin ALLAH saboda son zukatanmu da burin gina DUNIYA mai yankewa. Wannan mushirika tai tasiri da tasirin gurbataccen burinki ne da niyyarki ta shigowa wannan gida. Amma karya take bata da alaka da samuwar cikin Shugabamu da kikayi, dan dama sanda ta baki maganin kina tare da shigar cikinsa…....


 Babu wanda bai zabura ba, hatta da Malikat Bushirat din kanta. Tajwar Eshaan kam sake kankame hanun Iffah yay cikin nasa tsam-tsam fiye da farko.

Kai Kaka ya jinjina musu, "Wanna maganar da nake fada muku haka take, dama akwai cikin. Koda ace babu shi ta bada taimakon magani shi wannan maganin sai dai ya magance matsalar wani ciwo da ya zama sanadin jinkirta samuwar haihuwar bawai ya samar da dan ba. 

To sai a wannan labarin ma akwai samuwar cikin ma kafin ta shigo cikinsa. Rashin samuwar haihuwa jarabawace ga duk wanda baiyiba, jarabawa kuma mai ciwon gaske da radadi a zuciya, bazaka fahimci haka ba sai in ka kasance daya daga ciki. Ya halatta ka nema magani da ga kowace irin cuta a rayuwa. Sai dai fa akwai matakan da ya kamata mumini yabi wajen neman magani kowane irine balle ma akan neman haihuwa. 

A duk lokacin da muka rasa haihuwa idanunmu kan rufe da fadi tashin neman mafita ta kowanne yanayi. Burinmu shine kawai mu haihun. Sam babu tunanin maybe ita haihuwar ba alkairi bace a tare damu, a ganinmu kawai mun rasa shine mu nemota ta kowace irin hanya. Duk da abinda UBANGIJI ya baka ya fika sanin dalilin baka shi, idan kuma ya hanaka ya fika sanin dalilin hanaka da yayi. A rayuwa babu abinda yafi karfin addu'a, sadaka, yarda da kaddara mai kyau ko sabaninta. Idan kuma har ta kama saika nema maganin ka zama sani ba a wata gabar. A neman haihuwa wajen bokaye da malaman tsibbu zakaci karo da abu hudu in har ka samu daya da kaje nema. 

Na farko rasa imaninka da cire yardarka ga UBANGIJI mai badawa da hanawa, dan zaka cigaba da ji a ranka shifa wanna din nan ne ya baka wannan haihuwar (Wa'iyazubillah). Na biyu zata iya yiwuwa dan aljani ma aka samar a cikin naka batare da kasan hakan ba kai tunda kai a kai kanka ai. Na uku wasu matan ko da saninsu, ko bada saninsu ba zata iya yuwuwa bokan yay mata cikin a zahirance ko kuma ta hanyar tsafe-tsafen sa batare da ita tasan hakan ta kasance ba domin shi tsafi gaskiyar mai shine. Idan kuma ALLAH yasa dama ana a kan gabar da ALLAH ya iyakance ne dama haihuwar

tata ta kusanto gareta batare data sani ba sai a samu dai-daito da bada maganin nasa haihuwar ta samu amma zuciyarta na tabbatar mata ta sametane daga wannan bokan ko malamin tsubbun……..✍️

Mu hadu in ALLAH ya kaimu Please🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴 hannuna ya gaji😂

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post