Daudar Gora book 2 page 91

Daudar Gora book 2 page 91

 

Daudar Gora book 2 page 91

DAUDAR GORA 

Book2 

91



....Sun hadu ne a mahadar shiga jejin su da sojojin kasar da suka rigasu isowa kasancewar su a dokuna ne. Shine ya fara dirgowa da ga dokin nasa. A tare sojojin suka mika gaisuwar girmamawa ga Shahan. shan din nasu. Ya amsa musu da kulawa, tare da basu umarnin mikewa. Duk mikewar sukai, sannan shugaban sojojin ya iso garesa tab…. a hannunsa ya mikama Sayeed Tasadduq-Husain dake a gefensa. Amsa Sayeed Tasadduq-Husain yayi tare da matsawa kusa da Tajwar Eshaan, shi din masanine na gaske akan ilimin sanin taswura da bibiyar waje, dan haka cike da kwarewa ya fara sarrafa tablet din cikin bibiya ya saita abinda suke bukata. Tab.. din a maidama Sayeed Tasaddug-Husain yana mai dubansu gaba daya. Kowa sake nutsuwa yayi akan kafafunsa har shugaban sojojin.


   Taku daya biyu yay sai kuma ya tsaya cak hannayensa goye a bayansa. "Bazai yuwu ace mun fito wannan yakin batare da an rasa ran wani ba a cikinmu, ina fatan koza'a rasa din to ya kasance ni ne!?.……." babu wanda maganarsa bata razanar ba a cikinsu. Dan sai da duk suka zabura suka kallesa.Basarwa yay tamkar bai fahimta ba ya cigaba da fadin, "Kowanne shugaba yakanyi yaki ne domin kare al'ummarsa da kasarsa. Haka ma kowace al'umma kanyi yaki ne domin kare shugabansu da kasarsu. To a wannan gabar ina son kuyi yakine domin kare kasarmu da kayinku. Karku damu da bada kariyarku gareni zan kasance a karkashin kariyar UBANGIJINA.Mutanen da zamu tunkara duk nan mun san mutane ne masu hadari, wanda kuma bai sani ba ya sani anan sunada hadari, sannan an raini zukatansu ne da daukar fansa tamkar yanda uwa ke rainon yaronta da abincin jikinta. A mu duka da muke nan akwai masu mata da iyaye da yaya, akwai masu yaya da mata kawai, akwai masu yaya kawai, akwai masu iyayen ma kawai. Mu duka mun barsu ne suna kuka, kuka, mai ciwon shiga kila wa kala a saran dawowarmu ko mun rabu kenan. Ya zama dole musa a ranmu mun barsu da wannan tabon, musa a ramu koda bazamu dawo ba to mu kasance su mun karesu da ga sharrin wadan nan mutanen ta hanyar shafe babinsu a doron kasa na har abadan abada. Dukanmu bamu taba yaki ba a zahirance, amma sanin kowane dan kasar ruman iyayensa kan horesa da iya wasan takobi tun yana kankaninsa musamman mu maza. Wanna yasa bana jin ko dar da ga gareku jarumaina. Zamu tunkaresu da karfin ikon ALLAH, da karfin zukatanmu, da karfin kwanjinmu, da karfin horaswarmu, da karfin kare

kasarmu, da karfin kare al'ummar mu da addininmu.

Ka tuna a ranka mafifici a halitta ya yaki kafirai ne da duk wadan nan karfin ikon domin mu kasance a yau din mu cikin bautar UBANGIJI babu wani mai kuntatamu. Sai dai idan har mune muka wofantar da darajar daya sama mana tun a wancan lokacin sai mu rayu a karkashin mulkin mallakar kaskastattun kafirai. Bana fatan mu kasance hakan da karfin ikon ALLAH "


    A tare sukace insha ALLAHU. Murmushi yay a karo na farko tare da duban kaka da shugaban sojoji. "Mu ukun nan mune kwamandojin wannan yakin, kar'a taba kananan yara, dan zamu iya zama jagororin canja musu alkibla bayan sun dawo hanunmu. Daga basu ba kowa abin harinmu ne. A lokacin da kuke shagalta da yakarsu, ni zan tunkari shugabar tasu ne..


   Duk sun amsa da girmamawa. Daga haka aka fara nufar abin hawa. Wasu a cikin sojoji sun shiga jirage, inda aka bukaci Tajwar Eshaan shiga daya da aka kawo domin shi amma ya ce shi akan doki zaije. A dai duk cikin matasan idan da mai sha'awar haka ko rashin jimirin tafiya a doki ya kasance a cikin sojojin.Wasu sunyi hakan, wasu ko suna tare da shi a dokunansu. Bayan anyi doguwar addu'a masu bibiyar hanya ta na'urori suka fara aikinsu. Masu dokuna ne a gaba, motocin yaki na sojoji a biye da su, ta sama jiragen yaki da suka rarrabu a jejin domin sanar musu motsin komai da zai iya tunkarosu a tafiyarsu su da suke kasa musamman ma nakan dokuna. Kamar yanda Tajwar Eshaan ya bada shawara kowannensu bakinsa dauke da addu'oi..


   Anan ma cikin kasa da kewaye tuni an dukufa addu'oin musamman ma cikin masarautar ruman.Yara da manya kowa ya nutsu gayama UBANGIJI da fatan kariya ga wadan nan bayin ALLAH da suke tunkaran hadarin rayuwa ko mutuwa. manyan malamai da al'ummomin yankunan su an dukufa gayama ALLAH.Yayinda mutane suka dinga cincirindon taruwa a kofar jejin ta kowacce kusurwa zaman jiran tsammani..

**

Sun nausa matuka cikin jejin da bakajin motsin halitta irin ta mutane sai tsuntsaye nau'i-nau'i,yayinda a farko-farko suka dinga wuce kauyuka. Duk kauyen da suka gifta aka sanar da Shahan-shan ne da kasan sai kaga matasan kauyen sun daura dammarar bin bayansu suma. Dan sunfi kowa sanin dazukan wajen da abinda ya kunsa. Ga sojoji ta sama suna isar da sakon duk inda suke tunkara. Tafiyar awanni biyu cur ta iso da su gab da bataliyar sansanin da su uwa suka kafa gari. Anan suka taka birki bisa umarnin Shahan-shan aka gabatar da sallar la' asar, yayinda jiragen sojoji keta kai kawo da sake bincike jejin ta yanda su Uwa bai zama lallai su fahimta ba a tunaninsu.


    Sai dai kuma abinda basu sani ba su Uwa nada yan leken asiri a wasu kauyuka, hakama sunada na hatsabibanci tsaface-tsafacensu da suka kafa domin shirin kota kwana a irin wanna yanayin. A yanzu haka ma yan leken asirinsu sun isar musu da sakon shigowar su Shahan-shan din. Jin harda Tajwar Eshaan wata irin kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya uwa ta shiga babbakawa da dukanin budaddiyar muryarta, sautin yay wani irin karade dajin. Sai da tayi mai isarta sannan ta bada umarnin kowa ya kasance

cikin shirinsa. Dandanan suka fara shiryawa mazansu da matansu, masu hayewa kan bishiyu nayi, masu hawa kan dunitsina nayi, yaran aka tattaresu cikin wani kogon dutse gaba dayansu dake nan jikin kauyen.


   Dai-dai nan jiragen sojoji suka mamaye garin ta sama. Dabbobin da su uwa ke kiwo kawai suka iya gani, dan haka suka sanarma da Tajwar Eshaan akwai matsala fa. Dan kauyen babu kowa cikinsa sai dabbobi. Da mamaki yace,


"Kamar ya babu kowa?".


   Shugaban sojoji ya ce, "Wlhy babu kowa sai dabbobi”.


  Yanke wayar Tajwar Eshaan yayi, kaka dake kusa da shi duk yaji komai, murmushi kawai yayi, kansa a kasa batare da ya kallesa ba ya furta,"Babu inda sukaje ranka ya dade, hakan na nufin sun san da zuwanmu zuwa yanzu. A sanar musu kar jirgi ko daya ya sauka kasa har sai mun fara shiga".


     Sayeed Tasadduq-Husain Tajwar Eshaan ya mikama wayar, dan haka shi yay kiransu ya sanar musu.Shugaban sojoji zaiyi gardama Tajwar Eshaan ya sake amsar wayar, babu alamar wasa tattare da shi ya furta, "Kuyi yanda akace". Cikin girmamawa yay saurin amsawa. Daga haka suma suka hau dokunansu, kaka ya juya yana kallonsu, "Kowa ya kasance bakinsa da addu'a, duk abin tsoron kuma da za'a iya bude maka do da shi karka razana. Kar kuma mu yarda addu'a tabar bakinmu dan itace babban makamin da zai iya rusa wadan nan mutanen bakwai makaman hannunmu ba".


   Duk sun amsa da girmamawa garesa, da ga haka Tajwar Eshaan ya yunkura. Shi da Kaka sune a gaban,sai tawagar masu dokunan biye da su, sai motoci sojoji da duk wanda bazal iya tafiyar kan doki ba. Har suka iso tsakkiyar garin suma basuga komai ba sai farin dabbobi. Shiru sukai tsaiwar shirin kota kwana suma da baza idon son gain ta inda wani zai fara bullowa. Mintuna uku shiru sunata ambaton ALLAH sudai, sai jirage da ke ta kai kawo ta sama.


  "Kodai zamu sauka mu bincika ne?".


   Daya da ga cikin samarin ya fada. Alamar yay shiru kaka yay masa. Kai ya jinjina masa. Cikar minti daya da hakan bai karasa ba dajin ya dauki wani irin sautin kuka mara dadin ji. Hatta wanda ke cikin jiragen sal da zukatansu suka shiga bugawa da sauri-sauri. Sai dai kowa yayi tsam bakinsa da addu'a. Kukan sake cika musu kunnuwa yake da tunkarosu, hakan yasa kowa sake shiri. Wasu inn halittune masu ban tsoro da rashin dadin kallo suka zagayesu. Cikin dakiyar zuciya Kaka ya furta. "Kar wanda ya firgita". A zahiri dai kowa ya amsa masa da to, amma a zukatansu wasu dai kam sun razana. Amma sai ambaton ALLAH da sukeyi ya saka musu wata jarumta da jin karfi, kafin ma halittun sun yunkura su sun yunkura a dokunan batare da jin zasu gagaresu ba duk da yawansu. Na cikin motoci ma duk sun fito, haka ma wanda ke cikin jirage, jirgin na daga sama suka dinga silalowa ta sama sai ya zamto sunma halittun kawanya. Su Tajwar Eshaan a tsakkiya, sai halittun,sojoji a karshe. Cike da jin karfin zuciya Tajwar Eshaan ya fara ketawa cikin halittun sai ga kawunansu yana saukewa da takobin hanunsa shi da kaka. Gain hakan yasa a cikin samarin ma wasu suka afka sura. Tuni halittun suma sun fara tsalle a kawunansu, sai kusan uku su taru a kan mutum daya, cikin dai amincewar UBANGIJI suka gama kaudasu a abinda bai wuce mintuna ashirin ba. Da yawansu sun jijii musu ciwuka da farautansu. Ganin haka su Uwa suka sake turo wasu. A yanzu kam kaka ne yay wani irin dirowa daga saman dokinsa. A kausashe ya dubi halittun da suka sake zagayesu da fadin, "Ku kananun hatsabibai, idan har baku kasance matsoratan kafurai ba ku bayyana kayinku mana mushirikai. Ko kun tsorata ne? Nace ko kun tsoratane Uwar gijiyar taku  ta reneku da tsafine kawai amma babu karfin zukata

da jarumta!!!".


Tabbas wadan nan kausasan maganganu na kaka sun matukar musu dacin, dan kuwa jikin uwa da ke a dakin gumakansu ga Malikat Bushirat shimfide sun zagayeta cikin wata kaya da kayan tsafi rawa ya kamayi, cikin wani irin kara ji da mummunan sauti ta ce, "Ku fito ina bukatar kan shugaban nasu a gabana. Kuma ina bukatar karagar mulkin ruman a gabana a yanzun itama tare da kan tsohon nam dana matar shugaban nasu da ya bari gadin gida"….✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post