Daudar Gora Book 2 page 92


Health College

Daudar Gora Book 2 page 92

 

Daudar Gora Book 2 page 92

DAUDAR GORA 

Book2

92

-.Maganarta ta zama tamkar busa musu kaho da kada musu gangi ne. Dan saukar kibau kawai su ka fara ji shuuuuuu daga sama. Da sauri Sayeed Tasadduq-Husain yace,"Garkuwa sojoji masu karfi da karfafawar ALLAH!!".


   A take suka dunkule waje daya suka zagaye Tajwar Eshaan ya koma tsakkiya tare dama kansu garkuwa kibiyiyin suka dinga sauka akan saman garkuwar karfen hannayen nasu. Da wanna damar yan kabilar su uwa da ke saman bishiyu da duwatsu fara dirgowa kasa suka zagayesu. Sanda suke janye garkuwar bayan gama saukar kibau din sun gama zagayesu. Ko kadan hakan bai razanasu ba, dan kowa a fusace yake da jin tsanar wadan nan kafirai. Sannan sunyi alkawari duk rintsi bazasu bari a taba musu Shahan-shan din su ba. Tuni sukai wata irin rabewar da kaka duk ya tsara musu. Su kuma gain hakan sai sukai tunanin tsorata sukayi ne suka afka kai tsaye da tunanin korar su. Wannan itace damar farko data basu nasara akan wadan nan mutane, cikin kankanin lokaci kura ta tashi waje ya hargitse. Kabilar uwa sunyi shiri ne irin shirin da wuka ko bindiga bazata ratsasu ba. Yayinda Kaka ya bada shawarar fara tunkararsu da wuka sai sunzo hannu ai amfani da maganin daya tanada wajen karyasu su da karfin yakin nasu. Gurin na cakudewa kam wadanda zasuyi feshin maganin ta sama da ga cikin jirgin sojoji suka fara. Tun anan fa ihu-da-ihu ya hargitse, suka fara kaiwa kasa samarin nan a gille kawunansu. Yayinda kabbara ke tashi da amsa kuwwa a cikin jejin. Cikin abinda bai wuce awa uku ba an gama da kaso biyu da rabi bisa uku a cikinsu. Zuwa yanzu fa hankalin uwa da ke kwasar dariya ya fara tashi. A take ta bada umarni ga wadanda ke zagaye da ita fara aiwatar da shirinsu akan Malikat Bushirat. Dan hakanne plan c dinsu, plan b shine wasu kason mutanensu da ke can masarauta dakko karagar mulkin Shahan-shan..




** MASARAUTA **




Kukan da taci ya haifar mata da matsanancin ciwon kai, duk yanda taso kin kwanciya sai da Malikat Haseenat ta takura mata. Kwanciyar tayi, sai dai bata

rufa mintuna ashirin cikakke ba ta tashi a matukar firgice. Hankali tashe Malikat Haseenat da Daneen Ammarah sukai yunkurin riketa amma ta girgiza musu kai. Sun fahimci tabbas akwai matsala, dan haka Daneen Ammarah ta ce, "Mammah barta. Barta kawai akwai matsala ne".


    Hankalin Malikat Haseenat tashi ya karayi, dan tuni itama Daneen Ammarah din ta birkice a cikin kankanin lokaci. Dai-dai nan ko Amintacciyar hadimar Malikat Haseenat ta shigo hankali tashe, cikin hakki take sanar musu babu lafiya, ga was irin mutane nan da ba'asan ta inda suka shigo masarautar ba sun zagaye ko ina. Wasu a cikin jami' ai sun fara harbinsu amma ko gezau da alama ma bindigar bata kamasu. Wasu kaso a cikinsu kuma sun nufi fada ne inga karagar mulki take.


  Kafin ma takai karshe Iffah ta fice, Daneen Ammarah biye da ita. Gaba daya masarautar ta gama harmutsewa. Tuni kowa ya fara gudun ceton rai.Yayinda jami'an masu karfin hali da Ghazi da wasu a cikin hadimai da samari da aka bari sunata kokarin kai musu hari amma mutanen nan babu alamar razani a tare da su, saima wani irin dariya sukeyi cike da karfin iko na ko gezau. Ai babu wanda yasan ta yaya, ta ina

ma, kawai saukar kawunansu aka fara gani bisa kasa. Hankalin Ghazi ya tashi, ganin SARAUNIYA Iffah ce da kanta ba sako ba. Tare da Daneen Ammarah da a yau kowa ya shaida eh lallai ba ita kadai bace itama da nata ifiritan aljanun bisa kai.


   Duk wanda ya tunkari Iffah kai kawai take sauke masa ta matukar fita a hayyacinta da canjawar kamanni. Suko hatsabiban wani irin bulbulo wuta suke ta bakunansu suna kokarin tunkarar fada da tuni aka rufo ruf. Masarautar tayi masifar rikicewa, mata da yara kuka kawai suke. Hakama wasu a cikin mazan tuni sun nema wajen buya. Hatta su Miran Jasim da ke a cikin kurkuku sun tabbatar yau gidan babu lafiya kam......






**

*






Su uwa na tsaka da zagaye Malikat Bushirat da aka gama jikewa da ruwan tsaffi a tsakkiyar gumaka Tajwar Eshaan ya fado musu. Da wani irin jarumta dokinsa yay haniniya mai razanarwa kawai yay kansu.Daga dokin har shi Tajwar Eshaan din gani sukai sun koma musu wata halitta daban. Yau sai ga uwa tsaye akan kafafunta ta mike da ga kujerar tsafinta cikin matsanancin tashin hankalin gain dokin nan fa babban gunkinsu ya nufa. Kafin tai wani yunkuri yay ma butum-butumin gunkin wani irin duka da dukan karfin kwanjinsa shi da dokinsa sai gashi tarwatse a kasa. Ai ko kashin hannunsa yay wata irin karar masifa da ke tabbatar da yaji ciwo a cikin kashi. Hannun yay kokarin rikowa da dayan Hannunsa dake rike da linzamin dokinsa yaji saukar kakkaifar wuka a cikin damtsen hannun.


"Ya Arrahaman!!"


Ya ambata da dukkan karfin murya dana jiki da ya masa saura. Dan wata irin azabar zafi ce ta ratsasa har cikin kwakwalwa, Dai-dai juyowarsa kan wanda ya sokesa da wukar a dartsen hannun ya sauka kasa. Babiy ne da ya biyo bayansa, dan tun barowar Shahan-shan din a cikinsu ya farga yay azabar biyo bayansa. Bummm!!!! Shima Baby uwa ta sauke masa wani mulmulen ice saman kai, kara ya saki shima cikin ambaton ALLAH ya dafe kansa da jini ya balle, luuuu ya tafi kan dokinsa zai zubo cikin karfin hali Tajwar Eshaan yay wani irin juyi ya tallafosa. Gaba dayansa ya dago ya ajiye saman dokinsa. Kafin ya fisgo sarkar da suka shirya rataye Malikat Bushirat a ciki ya watsata, cikin amincin UBANGIJI ya samu nasarar sarko wuyan uwa da ke kokarin zare wata takobin tsafi da ga jikin wani gunki. Razananninayar karar data fargar da wanda ke waje ta saki, dan sarkar ta tsafi ce, amma cikin amincewar UBANGIJI shi Tajwar Eshaan din sai bata masa komai ba. Duk da da yawansu an musu jina-jina haka suka dinga dannowa dakin dan zuwa yanzu suma sun gama da wanda suke wajen, wadan da suka rage kuma an kamesu an daure bisa umarnin kaka.


  Cikin tashin hankali suka nufi Shahan-shan, amma sai ya girgiza musu kai alamar su barsa. Da kansa ya dirgo kasa, su kuma suka kama Baby da babu numfashi tare da shi suka sauke aka fita da dokin Shahan-shan. Shi da kansa ya daure uwa da sarkar nan tare da bama matasan sa umarnin rushe gumakan: a gabanta, rushewar kam suka farayi itako tana kukan bakin ciki da wata irin jijiga a cikin sarkar da ya dauretan.


   Shi kam takawa tay a hankali gaban Malikat Bushirat. Hannu ya kai ya yaye jan mayafin da suka. lulluba mata, dai-dai nan ta bude idanunta sai ko a cikin nasa, kallon juna sukai na kusan sakkani goma. Shi ya fara janye nashi da sukai wani irin jazur cikin lumshesu da budewa. Batare da ya yaye farin mayafin dake a kasan jan ba yasa hannayensa biyu ya dauketa duk da yanda hannunsa a haggu da yaji ciwo ga wuka a ciki jini na zuba ke masa azaba da rawa. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga rige-rigen sakko mata, dan su kadaine ke aiki a jikin ta, amma su Uwa sun sandarar mata da jiki gaba daya babu abinda ke aiki tare da ita sai kanta da idanun.Duk yanda ta kuresa da ido shi yaki yarda ya kalletan.Cikin sauri masu bada taimakon gaggawa da aka taho

dasu cikin sojojin suka nufosa da gadon daukar marasa lafiya. Amma bai daurata ba har sai da yaje ga jirginsu na sojoji da suka sauka. A hankali ya shimfidar da ita, sai da ya tabbatar ya gyara mata mayafin da take ciki dan tsirara take sannan ya dubi matukin jirgin yana lunshe ido. Ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya kame jikinsa tare da salute nashi.


   A gaban su kaka ya tsaya ya wani rumtse danunsa da daura hannunsa saman wukar nan dake kafe a jikinsa zai fincike kaka yay saurin dakatar da shi. "A'a ranka ya dade, hakan da zakai matsalane, dan wukar ba wuka bace takai tsaye kamar saura akwai dafi tare da ita. Kawai ka shiga jirgi dan bai kamata ka koma damu ba a doki".


  Bai cire din ba, sai dai ya bama kaka amsa da cewar"Tare da ku zan koma Jaddi".


   Murmushi kawai kaka yayi shi da Sayeed Tasadduq- Husain, dan yau ne karo na farko da Tajwar Eshaan din ya kira shi da kaka. A dai-dai nan aka fito da Uwar dake daddaure cikin sarka. An tsareta da tambayar ina yaran garin suke amma taki fada, sai ma dariya data sanya musu da cewar, "Bazan fada ba, bazan taba fada muku ba. Dan ku tabbatar karar da mu iyayensu kamar kashe maciji ne baku sare kansa ba hahahahaha!!!!!".


  Babu wanda ace da ita komai saboda isowar jiragen sojoji da shugaban sojoji ya bada umarnin a karo, dan yanda suka jigata din nan babu mai karfin iya komawa ta mota ko doki. Ga wasu shimfide babu alamar rai ma tare da su. Wasu kuma sun jigata matuka da ko yatsansu basa iya dagawa ma. Kin fadar inda yaran suke yasa sukai tunanin ko sun dauke su ma daga jejin ne gaba daya yasa shugaban sojoji bada umarnin ana gama kwashe su a sakama garin wuta kawai. Uwa bataji wannan furuci ba, kasancewar an tisa keyarta ita da sauran mutanensu ashirin da daya daba'a kashe ba cikin motar yaki.Hakama sauran mayakan duk an sakasu a jirage su, marasa lafiya sune farkon wucewa domin zuwa a basu taimakon gaggawa. Kaka da Tajwar Eshaan da Sayeed Tasaddug-Husain da shugaban sojoji sune karshe, za'a warema Tajwar Eshaan jirgi ya dakatar dasu.


    Tuni sauran sojojin da aka bari suka sakama garin wuta gaba dayansa bayan an tabbatar da babu wani kauye a kusa da su da wutar zata iya shafa. Dan su tsabar bakin hali ma basu yarda yin makwaftaka kota kusa da wasu kauyukan ba. Wannan wuta itace ta dinga wasar kogon dutsen da suka boye aransu zafin ya dinga ashes batare da an san anan din suka boyesu ba.







*








Abinda ya far a cikin masarautar ya sasu iske cikin Dahab City a hargitse. Dan jiragen a inda suka dauke su farkon jejin dole anan suka dakata aka dinga kwasarsu a motoci. Nan din ma cike suka samesa da jama'ar gari ga yan jarida. Jinin da Tajwar Eshaan ya rasa sakamakon sukar wukar da aka masa mai dafi a hannu dama ga kananun raunuka yasa idanunsa har sun fara rinjaya, dan sal da taimakon shugaba sojoji da kaka aka fito da shi aka daura a gadon marasa lafiya zuwa mota Hankalin mutane ya tashi matuka dan sun fahimci Shahan-shan dinsu kenan gariin yanda sojoji suka zagaye gadon, hakama da aka saka shi a motar an zagaye motar da uban tsaron da korna miye ya gitta zal iya zama gawa ne….✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post