Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 120


Health College

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 120

 

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 120

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العاميت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

_Double page ne,Saboda jiya da bana jin daɗi bansamu nayi ba,that's why na hada maku pages biyu💋_

Lokacin da Abusufyan ya fita a fusace ya shiga motarshi yayi mata key da gudun gaske ya fusgeta,shi kanshi baisan ina zai dosa ba,A ƙarshe gefen bishiya yayi parking ɗin motar Ya kifa kanshi jikin steering,tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,Bai ta6a tunanin Sgr zaiyi mashi haka ba,duk irin yadda yake treating ɗinsu,tun suna yara yake hawa jirgi daga Turkey zuwa U.s don kawai ya gansu,saboda ƙaunar da yake yi masu shi da Omar Amma sai gashi yau Sgr Yayi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba,Tsananin damuwa ne akan fuskarshi,zuciyarshi sai tafarfasa take yi,Zufa tuni ta wanke mashi fuskarshi,cikin shessheƙar kuka Ya furta"Why Rafayet!why!ban ta6a tunanin haka kake ba"lumshe idanuwanshi yayi,Anan Ya yini gefen bishiyar,


Duk ta damu saboda rashin ganin Sehrish ga wayarta dake ajiye saman side drawer tun safe,tun tana zarya acikin bedroom ɗin harta fara tunanin Zuwa nemanta,hijab ta zura ajikinta ta buɗe ƙopar ɗakin ta fito,miƙar hanya tayi tana tafiya,Adai dai ƙopar bedroom ɗinsu ta tsaya,Hannu tasa tayi knocking ɗin ƙopar,


Jahad ce ta buɗe mata ƙopar,jikinta na sanye da pakistan wando Burgujeje pink da Riga fara mai dogon hannu,daga ƙasan rigar anyi mata adon stones,Ta yafa mayafin a ƙafada,Yayin da ta saki sumar kanta,


Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Amrish"ta ƙarasa maganar tare da yin hugging ɗinta,Suka rungume juna,bayan sun kammala gaisawa Amrish ta soma tambayarta

  "dama ina neman Sehrish ne,tun asuba dana farka banganta ba,bansani ba ko tazo wurinku ne,ko ta fita daga gidan," 

  Gaban jahad ne ya ɗan faɗi don ita kanta duk yinin ranar bata sanya Sehrish a idanuwanta ba,

  "Gaskiya bansan inda taje ba,nima duk yau banganta ba,Amma abunda za'ayi bari na bincika cikin gidan may be ko tana wurin Aunty azeema ne,"

  Juyawa Amrish tayi,da sauri jahad ta ce"Ki shiga mana,Ga Hosana can tana kallon drama,". 

  Murmushi ta ɗan saki tare da gyaɗa kai tace"okey,"Matsa mata hanya Jahad tayi ita kuma ta shige ɗakin,A kwance ta samu Hosana ta baje saman gadon,Ga laptop agabanta ta ƙura ido tana kallo,wuri ta samu daga gefe ta zauna,

  "Hosana,ya kike,"

Juyowa hosana tayi fuskar nan a yamutse tace"Lahiya,"ta mayar da idanuwanta kan laptop din,zama sosai Amrish tayi suka cigaba da yin kallon atare,




Tana ƙoƙarin fitowa daga Toilet,tajiyo Muryar Mommy tana sallama,Ƙarasa fitowa Hajiya Azeema tayi jikinta sanye da bubu ta atampa ,fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa mata"Wa'alaikum salam,Aunty ki shigo daga ciki mana,"

  turo ƙopar mommy tayi jikinta na sanye da jallabiya fara,babu mayafi akanta,sam babu kwanciyar hankali atattare da ita,ganin fuskarta a hargitse yasa Hajiya azeema tace"Aunty Lafiya naga kamar akwai damuwa a fuskarki,"

  Mommy tace"Ina fa lafiya,Rafayet yayi aika aika,yabarmu da zullumi,"tayi maganar yayin da take zama daga gefen gadon nata,

  "Me Rafayet yayi"?

"Hmmmm,ɗazu Abban Junaid ke sanar dani,Nasan kinsan da auren sirrin da su kayi mashi ko"?

  jinjina kai hajiya azeema tayi"Eh,nasani,"

  "Oh ashe kema kinsani,Ni aka mayar shashasha,babu wanda ya sanar dani,"

  Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi"Naso in sanar dake Aunty,Kawai ina fargabar yadda zaki ɗauki abunne,"

  Ta6e baki Alex ta ɗan yi,

"Amma meya faru ne"?

Nan Mommy ta kwashe duk abunda Abba ya sanar da ita,tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita,..

Hannu Hajiya Azeema ta ɗaura akai,Hankalinta amatukar tashe take ambaton"Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!Nashiga uku!"duk tabi ta ruɗe,

Cike da takaici Mommy taci gaba dacewa"Wlh tun safe ake ta faman nemanshi ba'a ganshi ba,Ni yanzu babban tashin hankalina shine a wani hali yarinyar take ciki!Ina Rafayet ya kaita!Tana raye kota mutu"?.

Tuni idanuwan hajiya azeema sun cicciko tab da kwalla,bakinta ya mutu,Jikinta yayi sanyi,

  "Amma rafayet bai kyauta mana ba Allah,duk da nasan yayi ne saboda son da yake yi mata,Yaji tsoran su rabashi da ita ne amma....."tunkan takai ƙarshen maganarta,Mommy ta katse mata hanzarinta"aini banso Suka tursasa mashi akan ya saketa ba,Wannan shine kuskuren da suka aikata,Babu wanda baisan halin Rafayet ba acikinsu,tunda ya nuna yana son ya tafi da ita,to tabbas Yana sonta ne,Ni nasan wanene rafayet,Wlh da ace baison yarinyar nan,ko kallo bata ishe shi,balle har ya aureta,Amma tunda yayi accepting aurenta as a contract wlh yana sonta ne,So bana wasa ba,that's the reason why yaƙi sakinta,Shima kuma da laifinshi,komai sai yace zai nuna ƙarfi,Ai akwai abunda ƙarfi ko dukiya basa iya siyawa mutun,duk da ana siyan soyayya da kuɗi,Amma bakowace zuciya bace zaka iya mallakarta cikin sauƙi ba,kuma hada ƙarin shi bai ta6a soyayyaba,balle yasan yarda zai baiyanata,"


Jinjina kai Hajiya Azeema tayi"Allah sarki Sehrish,wlh na tausaya mata baiwar Allah,banji daɗin abunda ya faru ba,Yanzu ya zamuyi?wlh duk na ƙagu da insan a wani hali take,Ga Abusufyan ma,Naji kince Ya fita ba'a san inda yake ba,"ta ƙarasa maganar tana kallon Mommy,Duk sun shiga damuwa,

  "Tun ɗazu suka fita nemansu,Amma har yanzu shiru babu wani labari,yanzu sai dai muyi ta jiran tsammani"acewar Mommy,



Kafin Hajiya azeema ta ƙara cewa wani abu,Jahad ta kwankwaso ƙopar dakin,

  "Wanene"

"Ni ce Aunty azeema,"kallon juna sukayi ita da Mommy kafin tace"Shigo daga ciki,"

Da sallama abakinta ta shiga ɗakin,cikin girmamawa Jahad ta gaishe su,Suka amsa mata,

  "Ina neman sehrish ne,Na bincika ko'ina banganta ba,Nayi tunanin ko tazo wurinki ne," 

  Jin wannan maganar yasa hankalinsu ya tashi,shiru su kayi na wani lokaci batare da sun amsa mata ba, 

  ƙoƙarin juyawa tayi zata bar ɗakin,Da sauri Mommy tace"Zonan,Jahad ce ko Hosana?"

Cikin sanyin murya tace"Jahad ce,". 

  Azeema tace"Baki bambantasu ne,Ae wannan duk tafisu natsuwa,Hosana kuma tafi su jiki,har ƴan kumatu gareta,kuma ita sam bata da natsuwa,ta cika ƙiriniya,"

Murmushi Mommy tayi tare da cewa"masha Allah,Juliet ɗin Junaid ce kenan,ae ko jiya sai da yayi mun maganarta,"

cike da mamaki Jahad ta ɗanyi murmushi,jin tace Junaid yayi mata maganarta,bayan ita ko son kallonta baiyi,

  "Amma Oummanku tasan cewa Sehrish bata nan"?hajiya azeema ce tayi mata tambayar,

  Girgiza kai tayi"a'a bata sani ba,Nima Yanzu nake ji wurin Amrish,tace tun da safe bata ganta ba,"

  Jinjina kai hajiya azeema ta ɗanyi kafin tace"Shikenan,koda ace Oummanku ta tambayeki game da sehrish,ki sanar da ita cewa Sun fita ita da babban yayanku,zasu dawo in sha Allah,"

  "Shikenan,zan sanar da ita hakan,"


Gyaran murya Mommy tayi mata,ɗagowa Jahad tayi cike da jin kunyarta take kallonta,

  "Munyi magana da Junaid,Na bashi shawara akan yazo wurinki kuyi magana,nasan zaki taimaka mashi sosai,"

  Ƙayataccen murmushi Jahad,ta saki daƙyar ta iya cewa"in sha Allah Mommy,"tana kai ƙarshen maganar ta fuce da sauri,murmushi suka saki gaba ɗayansu,daga bisani kuma suka cigaba da tattaunawarsu,


A 6angarensu Omar kuwa,Yinin ranar suna wajen neman Sgr,duk wani wuri da suke tunanin zasu same shi sunje basu gansu ba,lamarin ya fara bashi tsoro,


Har wuraren ƙarfe Goma na dare babu wani Labari me daɗi,duk sun shiga matsananciyar damuwa,ga Abusufyan yaƙi dawowa cikin gidan,Abu kuwa tunda Jahad ta sanar da ita cewa Sehrish sun fita tare da babban yayansu,bata wani sanya damuwa aranta ba,don tasan cewa duk inda take tana cikin ƙoshin lafiya,Tun da ba ita kaɗai bace,duk da ta ɗan damu ganin har goma tayi Basu dawo ba,


Damuwace ta ishi Abba,A ƙarshe ya yanke shawarar sanarma Ammi halin da suke ciki,wata'ƙil ta taimaka wurin shawo masu kan Abusufyan,A lokacin tana kishingiɗe saman gadonta,Abba yayi sallama daga waje,Amsa mashi sallamar tayi,A nutse ya tura ƙopar ɗakin ya shiga,cike da girmamawa ya samu wuri daga ƙasa ya zauna tare da lanƙwashe kafafunshi,cikin sanyin murya ya gaisar da ita,miƙewa daga zaune ammi tayi yayin da idanuwanta ke akan fuskarshi,tayi mamakin ganin jirwayen hawaye,

  Hankali aɗan tashe tace"Hossein!Lafiyarka kuwa?Hawayen menene akan fuskarka"kamar jira yakeyi tayi magana,nan take ya fashe mata da kuka kamar ƙaramin yaro,duk tabi ta ruɗe,

  "Ka faɗamun meya faru ne?Ka tasani gaba kana yi mun kuka,idan wani abu ke damunka bazaka fadamun ba!"

  Cikin shessheƙar kuka ya soma magana"Abubuwa ne sunyi mun yawa ammi,daga wannan sai wannan na rasa yadda zanyi da rayuwata"

  "Ka natsu ka sanar dani meke damunka,"daƙyar ya samu ya tsagaita da yin kukan,a tsanake ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar da ita,


Jinjina kai ammi tayi yayin da idanuwanta ke akanshi sai da yakai ƙarshen maganarshi tukunna tace"Gaskiya banji daɗin wannan abun da kuka aikata ba,nayi masu auren yarjejeniya batare da kun sanar dani ba,sam bakuyi tunani ba wlh,Haba hossein da hankalinka da tunaninka...."ta ɗan dakata da yin maganar tana kallonshi,sosai hawaye ke zuba akan fuskarshi,

  "Dama dole kuga ba daidai ba,kuskure ne tun farko kun riga da kun tabka,Ni yanzu bansan ya zanyi ba,tunda baku yi shawara dani ba lokacin da kuka shirya yi masu auren,bani da abunda zan iyayi maku.... "Tunkan takai ƙarshen maganar,Abba ya zukunna agabanta ya ruƙe hannayenta,"Duk duniya bani da mai sharemun hawayena in bake ba,Dan Allah ki taimaka mun Ammina,ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata"

  Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,tafin hannunta ta sanya tana share mashi hawayenshi,

  "Shikenan,kadaina kukan ya isa haka,idan ba so kake nima in fara kukan ba,"

  Da sauri yace"nadaina ammina,bazan ƙara ba,"

  Jinjina kai ta ɗanyi kafin tace"abun da ciwo,banji daɗin abunda Rafayet ya aikata ba,Yanzu in mahaifiyar yarinyar nan taji ya kuke tunanin zata ɗauki abun?sam bakuyi tunani ba,Shi kuma Abusufyan baikyauta ba abunda yayi maka,Zai dawo ya same ni ne,Sannan inaso ka kwantar da hankalinka,ni nasan cewa duk inda rafayet yake a halin yanzu yana tare da yarinyar,koba komai ita ƴar uwarshice,Jinin dake yawo ajikinta shike yawo ajikinshi,zai bata kyakkyawar kulawa,tunfarko kuskuren da kukayi na tursasa mashi akan ya saketa shine duk yajawo wannan abun,da ace kun bi a hankali da duk baza azo ana danasani ba,"ta ƙarasa maganar tare da nuna mashi gefenta alamar yazo ya zauna,


Miƙewa Abba yayi tare da komawa gefen ammi ya zauna,kwantar da kanshi yayi asaman kafaɗarta,Wani irin ciwon kaine ke damunshi,


"Kayi hakuri da duk abunda ya faru,banason kana sanya damuwa aranka,in sha Allah komai zai tafi daidai,zan tayaku da addu'a akan Allah Ya bayyanar dasu"sosai ammi tashiga tausarshi,tana kwantar mashi da hankali,

  "Ka kwanta ka huta,zanyi kokarin jaraba kiran layinshi,"

  "To ammi,"ya amsa mata,kafin ya gyara kwanciyarshi A saman gadonta,


Miƙewa ammi tayi gaban drawer taje tare da kai hannu ta ɗauki wayarta,Layin Abusufyan ta kira,Cikin sa'a wayar ta soma ringing,yana ɗaga kiran ta kara wayar a kunnanta tunkafin yayi magana tayi saurin cewa"Duk inda kake kadawo gida yanzun nan,ina son ganinka aɗakina,Umarni nake baka,"tana kai ƙarshen maganarta batare da ta jira amsarshi ba,Ta katse kiran,


Safa da marwa ta shiga yi aɗakin tana jiran zuwanshi,kusan minti goma sha biyar da yin wayar,Motar Abusufyan ta kunno kai cikin gidan,bayan yayi parking ɗinta ya fito jiki babu ƙwari ya nufi cikin gidan,Yana shiga babban falon gidan Ya taras da mutanan gidan,bai bi takan kowa ba Ya wuce ɗakin Ammi,da sallama abakinshi Ya shiga ɗakin,


Tunda ya shigo ammi ta kafe shi da ido tana kallonshi,yaji jiki ba ƙadan ba,

  Daƙyar ya iya gaisar da ita"ina yini ammi,"bata amsa mashi ba,Sai nuna mashi wuri tayi saman sofa ɗin dake dakin,Ya zauna yana faman sauke ajiyar zuciya,sai daga baya ya lura da Abba dake kwance ya rufe idanuwanshi,

  "Meya haɗaka da ɗan uwanka'?tayi tambayar tamkar batasan komai ba dangane da abunda ya faru,a ruɗe yace"Wani abu yace nayi mashi"?

  "Kafi kowa sani ae,meyasa Abusufyan kafiye son zuciya ne?Sam baka da kara duk irin halaccin da hossein yayi ma ƴa'ƴanka tunkafin yasan cewa jininka ne su,abunda kayi mashi sam bai dace ba,kuma abunda Rafayet Ya aikata ma ƴar wurinka,Ni banga laifinshi ba,Nafi ganin laifinku ku da kuka shirya auren yarjejeniyar,In har kayi niyyar bashi auran ƴarka don me zaka tursasa mashi akan ya saketa?Gashi yanzu kun jefa rayuwar yarinyar cikin hatsari.....'tunkan takai ƙarshen maganar,Abusufyan yace"Dama nasani,ba sona kikeyi ba,Shiyasa har kike goya mashi ba,yanzu duk girman laifin da rafayet ya aikata baki ga laifinshi ba,Saboda shi jinin Hossein ne,dama can kinfi sonshi ae......'

Bai ƙarasa maganarba,Sakamakon tsawar da Abba ya daka mashi,a lokacin ya miƙe daga zaune ya sauko da kafarshi ƙasan gadon,

  "Dama abunda kake tunani kenan!?Meyasa Abusufyan?Wlh idan ka biyewa zuciyarka Zata kaika ta baroka ne,dani dakai duk abu ɗaya ne awurin ammi,baikamata ka furta mata haka ba,ni a tunani na ƴa'ƴana naka ne,Ƴa'ƴanka nawa ne,Ban ta6a tunanin ina da bambanci dakai ba,wlh nafika jin raɗaɗin abunda Rafayet ya aikatama Sehrish,Yinin yau ko ruwa bansa abakina ba saboda damuwar halin da suke ciki...."hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,

  Maganganun Abusufyan sunyi matuƙar ƙona mashi rai,musamman ammi,tayi mamakin yarda harya iya furta mashi hakan,Son ƴa'ƴa ya rufe mashi ido har yake ganin tamkar ba'ayi mashi adalci,

  "Ammi dan Allah ki ƙyaleshi kada kice komai,kibarshi kawai ya tafi,Abusufyan yanzu baya acikin hayyacinshi,komai ya fito bakinshi zai iya faɗa mana,"

 Ranta a6ace tace "Banji daɗin kalamanka ba Abusufyan,ban ta6a tunanin zaka iya furta mun haka ba,kada ka manta dakai dashi dukanku ni na haifeku,kuma banta6a nuna banbanci atsakaninku ba,Abu ɗaya danasani shine Hossein yafika sauƙin kai,Zan iya cewa duk cikinku babu wanda yakaishi haƙuri,yana yi mun biyayya sosai,aduk lokacin dana shiga wani hali hossein shi nake fara gani,yana faranta mun rai sosai ba kamar kai ba.....'daƙyar takai karshen maganar,idanuwanta sun cika tab da kwalla,hankalin Abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin ammi na shirin zubar da hawayenta kanshi,sai ma lokacin ya farga don baisan ya furta mata maganar  ba,ranshi ne ya 6aci sosai,idanuwanshi sun rufe,


Saukowa yayi daga saman kujerar,Ya zuƙunna saman guiwowinshi agabanta,

Cikin sanyin murya ya soma magana"dan Allah ammi kiyi haƙuri,banaso nayi silar da hawayenki zasu fita,hakan zai ƙara jefa rayuwata cikin matsala,na tuba bazan ƙara ba,Komai kikeso wlh shi zanyi,yaya hossein...."ya ambaci sunanshi tare da mayar da idanuwanshi kanshi"Kayi haƙuri da abunda nace yayana nakaina,nasan kalamaina sun 6ata maka rai,zuciyata ce sam batayi mun daɗi,Nafi kowa sanin yadda kakeson Jini na..."duk yabi ya ruɗe,

    "Ka tashi ka koma ka zauna,inason magana daku,"miƙewa yayi jiki na rawa ya koma saman kujerar ya zauna,gwanin ban tausayi ammi ke kallonsu,

  "Kada ku bari son ya'ya yayi silar da zaku raba kanku,bana fatan hakan ya faru,Ban goyi bayan abunda Rafayet Ya aikata ma ƴar wurinka ba,Kuma ban goyi bayan kowannanku ba,dakai dashi,duk abunda ya faru Laifinku ne,Tunda ku kuka haɗa aurennasu,Sannan kuma kuka soma ƙoƙarin tursasa mashi akan ya sake ta,wanda silar hakan ne yasa shi Rafayet ɗin yayi mata aika aikar da yayi,maimakon daya nuna yana son Ya tafi da ita ku ƙyaleshi yayi rayuwarshi da matarshi,amma sai kuka matsa lamba akan ya saketa bacin kuma kunfi kowa sanin halinshi,Wannan shine kuskuren da kuka aikata......"

  Shiru ta ɗanyi tana kallon kowannansu,gaba ɗaya sun natsu suna sauraronta,cigaba da magana tayi"Abusufyan amadadin Rafayet ina mai baka haƙuri,tabbas ya cutar da ƴar wurinka,Abunda yayi sam bai kyauta ba bai sa hankali ba,Amma inaso ka sani,Duk yayi wannan ne saboda tsananin son da yake yi mata,Yana gudun ku rabashi da ita ne shiyasa ya yanke shawara ya aiwatar da hakan,A tunanin shi in yayi mata hakan ba zaku iya raba shi da ita ba,Sai dai kash ya tabka babban kuskure,Ya kusanceta a lokacin da yake cikin fushi,shi kanshi yanzu nasan yayi danasanin abunda ya aikata mata fiye da tunaninku,kuma duk yacce kuka kaiga jin ɗacin abunda ya aikata mata wlh baku kaishi ba,Yafi ku jin raɗaɗin abunda yayi mata acikin zuciyarshi,da ace da son ranshi yayi mata wlh bazai gudu da ita ba,Anan zai bar maku ita,Ya tafi yabar kasar,Ya zakuyi dashi?tayi tambayar tana kallonsu,duk jikinsu yayi sanyi,

  "Duk inda yake yanzu nasan cewa yana tare da ita,Kuma zai gyara 6arnar da yayi ne,Sannan inaso ku kwantar da hankalinku,in sha Allah zasu bayyana ne,kuma kudaina tunanin cewa ko ta rasa ranta ne,tana araye bi'iznillah,kuma zata ji sauƙi ta dawo kamar yadda take ada"sosai ammi tayi masu nasiha,duk ta kashe masu jikinsu,

  A ƙarshe tace"idan har Allah yasa Rafayet ya dawo da yarinyar nan,zan zaunar dasu agaban kowa zan tambayi ra'ayinsu,idan har duka suka amince zasu rayu da junansu,To bana so wani daga cikin ku ya ƙara tada maganar saki,Idan kuma har ita jikar tawa ta nuna cewa batason shi,Zanyi adalci atsakaninsu in raba auransu,'


Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke,Abusufyan yace"In sha Allah,nima bazan ƙara tursasa mashi akan ya sake ta ba,"

Abba kuma yace"Duk hukuncin da kika yanke masu dai dai ne,mungode sosai da irin nasihar da kikayi mana,kuma in sha Allah,ba zaki ƙara jin kanmu ba,"

  "Allah yayi maku Albarka,Allah ya ƙara hada kan zuri'armu,"

Atare suka amsa mata da Ameen,

"Amma ammi,bansan ya zanyi da zainab ba"acewar Abusufyan 

  "Kada ka damu,idan ta tambayeka akan Yarinyar,ka sanar da ita komai game da auran yarinyar,amma bance ka faɗa mata ainihin abunda ya faru ba game da abunda rafayet ya aikata mata,Idan kace mata Mijinta ya tafi da ita,Bazata damu ba,"

  Jinjina kai yayi"shikenan nagode sosai,Zan sanar da ita hakan,

    "Yanzu yakamata mu mayar da hankali wurin neman inda ya tafi da ita,",'

  "Zamuyi kokarin yin hakan,Yanzu haka Omar tun safe suke gararin nemansu acikin garin nan,Amma har yanzu shiru bamu ji daga gare shi ba,"Abba ne yayi magar,

  "Allah ya taimaka,zasu bayyana ne nasan zai dawo da ita ne"daga haka ta basu iznin tafiya,Miƙewa sukayi atare har sun kusa fita daga ɗakin,Ammi ta kuma kiran Abusufyan Dakatawa yayi tare da juyowa ya dawo wurinta,

  Dafa kafadarshi tayi"game da abunda ka yiwa yayanka,Ya tsaya mashi arai,yaji zafin abun har hawaye saida ya zubar akanka,sam banji daɗi ba daka buge mashi hannunshi don yana ƙoƙarin dakatar dakai,kafi kowa sanin yadda Hossein ke tsananin sonka,yafi kowa son ganin farin cikinka,Bai kamata kayi silar shigarshi cikin damuwa ba,Idan kukayi hakuri komai mai wucewa ne,Wata rana sai dai muji ana ɗaura auren jikokinku,".  

  Murmushi Abusufyan yayi,cike da jin kunya ya sunnar dakanshi ƙasa,

  'Koda yake naji ƙishin ƙishin wurin azeema cewa kanaso ka maida auranku da Zainab,dagaske ne'?

  Hannu yasa tare da shafa ƙeyarshi,

Murmushi ammi tasaki"Allah yasa ina da rabon sake ganin wasu Ƴa'ƴan na Abusufyan,"ƙasa kasa ya amsa mata da Amin,

  Hannu tasa ta ɗan bugi kafaɗarshi"rasa kunya,wayace maka ana amsawa,da ace yayanka ne,Cikin zuciyarshi zai amsa mun,"dariya sosai Abusufyan yayi,

   ɗaure fuska ammi tayi"Nama tuna fushi nake dakai,Ni banji daɗin maganar da kayi ba,nacewa wai nafison Yayanka akanka,kasan irin yadda nake jinka acikin zuciyata"?tayi tambayar tana kallonshi,duk tana yin wannan ne don ta faranta mashi ranshi,ko hankalinshi ya kwanta yadaina sanya damuwa aranshi,

  "Kiyi hakuri mommyna,bazan ƙara ba,nima nace ne kawai,ba don ina nufin haka ba,bana jin daɗin zuciyata ne shiyasa harna furta hakan batare dana tauna maganarba,"

  Shafa sumar kanshi tayi"Allah yayi maka albarka,dan Allah ka sanyaya zuciyarka,Allah ya baka hakuri da juriyar cinye wannan jarabawar,'

  "Ameen ameen Ammina,"rungumeta yayi sosai ajikinshi,Yaji daɗin kalamanta,Daga bisani yayi mata sallama Ya futo daga ɗakin,


Yana kokarin shiga bedroom ɗinshi,Muryar Abu ta katse mashi hanzarinshi,

  "Abban Jahad,"har sai da gabanshi ya fadi,A sukwane ya juyo yana kallonta,

  Jikinta na sanye da hijabi dogo,

Murmushin yaƙe yayi mata tare da cewa"Na'am Oummu Sehrish,"

  Murmushi itama ta sakar mashi,

Matsawa tayi kusa dashi"shiru har yanzu,Yayan sehrish bai dawo da ita ba ko"?tayi tambayar fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa,

  "Waya faɗa maki haka"

"Jahad ce ta sanar dani ɗazu,To naji shiru har yanzu basu dawo ba,duk nashiga damuwa,Gashi tabar wayarta agida,inason nasan a wani hali take ciki,"

  Bai bata amsa ba,sai da ya fara buɗe dakin ya nuna mata hanya"Mu shiga daga ciki,inason magana dake,"

Shiga ciki abu tayi yabi bayanta,Gefen gadonshi ya nuna mata"ki zauna,"

  Girgiza kai tayi"a'a,muyi maganar daga tsaye,inaso in koma ɗakine,

  "Ki kwantar da hankalinki,Ƴarki ko ince ƴarmu tana cikin ƙoshin Lafiya,Tana atare da yayanta kamar yadda Jahad ta sanar dake,

  Aruɗe abu tace"Dare fa yayi sosai,duk inda suka je ya isa ace yanzu sunyi tunanin dawowa gida,"

  "Shiyasa nace ki zauna muyi magana,akwai abunda nakeso in sanar dake,"jin haka yasa abu ta samu wuri ta zauna,tana kallonshi,daga can gefenta ya zauna suna fuskantar juna,

  "Nayi maki laifi bansanar dake ba,"

Cike da mamaki tace"Laifi kuma,na me kenan,"?

Daƙyar ya daure yace"naso na sanar dake amma halin da muka shiga a kwanakin baya yasa ban samu lokaci munyi magana dake ba",

Kasa kunne abu tayi tana sauraronshi,har ta ƙosa ya gaya mata,

  "Ina sauraronka,Ka sanar dani kawai,"

  "Sehrish tana da aure,"

Gabanta ne ya faɗi rass,A ruɗe ta maimaita abunda yace"Sehrish tana da aure?tun yaushe"?

  "Ina tunanin ya wuce wata hutu da yin aurenta,Ita da babban yayansu,Nasan kin gane shi,"

Abun yayi matuƙar bata mamaki,sai lokacin ta tuna da ranar nan da sehrish tayi jinya har ta kwana ɗakinshi,abun ya tsaya mata aranta ashe mijinta ne shi,zurfin tunani ta shiga,Abusufyan kuwa zuba mata ido yayi yana kallonta cike da fargabar amsar da zata bashi,

  Can yaga ta ɗan saki murmushin gefen fuska,

  "Ashe ina da suruki bansani ba,shine ba'a sanar dani bako"?tayi maganar tana harararshi,

  Ba ƙaramin daɗi abusufyan yaji ba,duk da halin da yake ciki,

  "am sorry,nasan nayi laifi amma yanzu na goge laifina tunda na sanar dake komai,"

"Hakane,naji dadi sosai,saboda na yaba da kyawun halinshi,Yana girmamani sosai"

  Kallonta kawai Abusufyan yake yi,acikin ranshi yace"da ace kinsan meya aikata ma ƴarki,da yanzu ba wannan zancen ake yi ba"a fili kuma yace"Ae abun alfahari ne shi,Mutumin kirki,yana da kyakkyawar zuciya,"

  "Yanzu kenan shiya tafi da ita,amma baka faɗamun inda suka je ba,kuma yaushe zasu dawo,"ba don yaso ba,Ya shiga shirga mata ƙarya,

  "Sun tafi kaduna ne,wani aiki ne yakai shi,Shine ya tafi da ita,Amma bai sanar dani lokacin da zasu dawo ba,"

  Jinjina kai Abu tayi"Allah ya dawo dasu lafiya,Har hankalina ya kwanta yanzu,Dama Hosana ta addabeni da tambayar ina Rishi ɗinsu take ne,Kaga yanzu na samu amsar da zan fada mata idan ta ƙara tambayata,"ta ƙarasa maganar tare da mikewa tsaye,

  Tashi yayi shima"mu je na rakaki ɗakin,Inaso na gansu,"

  "Kunya nake jifa,idan wani yaganmu atare fa?Kuma yanzu nasan sunyi bacci ma,"

  "Koda sunyi bacci nidai inason ganinsu,"duk yadda taso ta hanashi bin ta sai da yabita,Lokacin da suka shiga ɗakin A kwance ya samu jahad da hosana suna ta sharar bacci,tamkar ya fashe da kuka haka yaji,Saboda tunawa da halin da ƴar uwarsu take ciki,Yasan tana cikin mawuyacin hali,da ace sunsan halin da take ciki da baza suyi wannan baccin ba,Allah sarki,


Ya jima aɗakin yana kallonsu,Kafin yayi ma abu sallama Ya koma ɗakinshi,


Aranar kowa yayi bacci banda waɗannan mutanan,Abba,Abusufyan,Omar,Da duk wanda Yaji abunda ya faru da Sehrish,Baccinsu ragagge ne,sun shiga damuwa sosai,


*Boss Bature*


Tun da sanyin safiyar,Wayar Mommy dake ajiye saman side drawer ta soma Ringing,can cikin bacci ta dinga jin ringing ɗin wayar,daƙyar ta iya buɗe idanuwanta saboda baccin da ke fusgarta,Mikewa tayi daga zaune,batasamu Abba acikin ɗakin ba tun da suka fita sallar asuba shida Junaid bai kaiga dawowa ba,


Hannu takai tare da ɗaukar wayar,ta duba sunan mai kiran nata,Dr Harriet ce,ɗaya daga cikin aminnanta wanda ke zaune a Nigeria,tayi mamakin ganin kiranta a irin wannan lokacin,don sun jima basu yi waya ba,


Picking call ɗin tayi kafin ta kara wayar a kunnanta,Cikin harshen spanish suka soma magana 

  "Ina fata ban katse maki baccinki ba,"?

  "Kusan haka,ina fata kina cikin ƙoshin lafiya"?

  Lafiya lou,kwana dayawa kin manta dani,Miji daɗi ko?Zaman Nigeria ya kar6eki,shiyasa har kika manta da mutane "acewar Dr harriet tayi maganar muryarta da sautin dariya,

  "Me yafi raina,Ga mijina Ga ƴa'ƴana atare dani,bani da sauran damuwa,"ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da murmushi,

  "Shiyasa kika manta dani kenan,Wai yaushe kika dawo Nigeria ne,baki sanar dani ba,nifa duk tunani na kina America ne ashe kin dawo daga yajin da kikayi,"

  Dariya Mommy ta ɗanyi kafin tace"Najima da dawowa,naso na sanar dake,mun shiga cikin wani hali ne na rayuwa,Amma yanzu Alhamdulillah,In na samu time zanzo,"

  "Oh sai ma kin samu time tukunna zaki zo,gaskiya ban yarda ba kizo kawai yanzu,Inason ganinki,Immediately pls,Wani taimako zakiyi mun,"

  Cike da mamaki tace"To fa!Wani irin taimako kenan"?

  "Kedai kawai kizo pls,I will be waiting for u,rashin zuwanki zai iya haddasa mun matsala,"tana kai ƙarshen maganarta,bata jira amsar da Mommy zata bata ba,Da sauri ta kashe kiran,

  Abun ya ɗaurewa Mommy kai,bata yi niyyar zuwa ba,amma yanayin yadda harriet tayi maganarne yasa ta mike da sauri ta shiga toilet,Shaf shaf Ta fito daga wanka,ta zura doguwar riga ajikinta,Ta ɗauki mayafi ta yafa akanta,


  Handbag ɗinta ta ɗauko,Sai da ta fara tura wayar cikin jakar,tukunna ta fito daga bedroom ɗin,bata samu kowa a babban falon ba,kaitsaye ta nufi hanyar fita daga falon da sauri da sauri,


  Da gudun gaske motarsu ta fuce daga cikin gidan,Wani sergeant ne ke yin driving ɗinta,Kaitsaye suka nufi estate ɗin da harriet take zaune,bayan yayi parking ɗin motar,ya fito tare da zagayawa ya buɗe mata mota ta fito daga ciki,


Da sauri ta nufi ƙopar da zata sadaka da cikin gidan,A bakin ƙopar ta tsaya tare da sanya hannunta taja door bell ɗin ƙopar,Yayi sauti,,


Ko minti ɗaya batayi ba a tsaye,taji an buɗe ƙopar,babbar mace ce fara tass baturiyar asali,a shekaru zata haura arba'in,tana da jiki,Ƙwayar idonta green colour ce,jikinta na sanye da riga da wando sun tsuke jikinta sosai dakyar take motsi acikinsu,Gashin kanta Ja ne sosai,Ta ɗaureshi da ribbom. 

  Lokaci guda suka sakarwa juna murmushi,

  "You're highly welcome,Am really glad to see u,"Ta ƙarasa maganar,Tare da rungume mommy ajikinta,

   "I really missed u,Bamu kyautawa juna ba tsawon lokaci babu wanda ya nemi wani acikinmu sai kace ba abokan juna ba,"Mommy ce tayi maganar bayan sun raba jikinsu,

  Ruƙo hannunta Harriet tayi tajata izuwa cikin gidan"lets get in",

  Katafaren palour ne ya haɗu sosai,yaji komai na buƙata acikinsa,

  Nuna mata wuri harriet tayi"have a seat,".  

  Girgiza kai Mommy tayi"Nifa hankalina ba akwance yake ba,kince kinason gani na,ki fara faɗamun menene kafin in zauna "

  Murmushi harriet tayi"Jiya nayi baƙo,Na ban mamaki kuwa,"

  Zuba mata ido mommy tayi,

"Idan kinason ganin kowanene,mu shiga ciki,"tayi maganar tana yi mata nuni da upstairs,


  Gaba tayi mommy tabi bayanta har suka hau saman stairs ɗin,A ƙopar wani bedroom Harriet ta tsaya"Go in,"

  Sallama mommy tayi tare da sanya hannu ta tura ƙopar ɗakin ta shiga daga ciki,Ya haɗu bedroom ɗin sosai,Aljannar duniya ce,


Slowly mommy ta sauke idanuwanta saman katafaren gadon,Mutun ta gani kwance saman gadon,lullu6e da white bedsheet,ba'a rufe fuskarba,Amma daga inda take bazata iya tantance fuskar wanene ba,kuma daga gani patient ne,Hannun mara lafiyar hada kanula ajiki,da alama Jini aka ƙara mashi,Ga kuma allurorin dake ajiye tare da magunguna gefen side drawer ɗin,


"Ki ƙarasa ciki mana,"harriet ce tayi mata maganar,tana ƙoƙarin ɗaga ƙafarta ta shiga daga ciki,Taji an buɗe kopar toilet ɗin ɗakin,da sauri takai idanuwanta akan mai fitowar,bakowa bane face SGR daga shi sai short ajikinshi,Rass yaji gabanshi ya faɗi lokacin da yayi arba da Mommynsu,Zuba mashi ido Tayi ƙuri tana kallonshi,mamaki ƙarara akan fuskarta,


Duk yasha jinin jikinshi,a ruɗe ya juya zai koma cikin toilet ɗin,Tayi saurin dakatar dashi"Rafayet!"a sukwane ya juyo,duk ya sauya tamkar bashi ba,Jiya zuwa yau har ƴar rama yayi,

  A hankali ya ambaci sunanta"Mommy"juyawa ta kuma yi tana kallon Sehrish dake kwance saman gadon sai da taga Sgr sannan ta gane cewa itace,

    "So u are here?meyasa baka sanar damu ba,gaba ɗaya ka tashi hankalinmu rafayet,Duk mun damu akan son sanin halin da kuke ciki'

  "Mommy,I ave no choice,Nasan babu wanda zai saurareni awannan lokacin shiyasa kawai na yanke shawarar in baro gidan da ita,Omar ma ya juyamun baya,"cikin sanyin murya yayi maganar,kana kallon fuskarshi zaka gane cewa Ba ƙaramin kuka yayi ba,idanuwan duk sun kumbura suntum,hatta la66ansa,Ga Sahun yakushin Sehrish nan a asaman kafaɗarshi da kuma damtsen hannunshi,duk da anyi dressing ɗin ciwukan '

   Shigowa ciki Harriet tayi tana kallon kowannansu,kafin ta soma magana"Jiya da suba Alexander ya kirani a waya ya sanar dani cewa Yana da patient zai kawota private hospital ɗina,Sai na bashi shawarar cewa Ya kawota gidana,tunda dama aikina ne,kuma dayawa masu irin matsalarta a cikin gidana nake dubasu,Gaskiya Yarinyar tasha baƙar wahala sosai,don nayi mamaki data kasance araye bata mutu ba,don ma Allah yasa munyi mata aiki cikin gaggawa batare da 6ata lokaci ba,Amma taji jiki sosai,ta zubda jini,don kusan leda biyu na Jini muka ƙara mata,Alex ne ya bata jininshi aka sanya mata,ni tun da nake duba patient irinta banta6a zubda kwallata ba,Sai akanta Mun sha kuka,daga ni harshi,yarinyar ce ga ƙananun shekaru......."cikin harshen spanish take maganar idanuwanta cike tab da kwalla,Mommy kuwa tuni ta fashe da kuka,dakyar ta iya matsawa gefen gadon da Sehrish take kwance ta sanya hannu ta yaye bedsheet din,Riga ce ajikinta blue colour dai dai guiwarta rigar ta tsaya,duk jikinta ya bushe,kamar matacciya haka take yin bacci,


Yatsun hannunta na kerma ta ɗaurasu asaman fuskar sehrish,tsananin tausayinta ne ya kamata,Juyawa tayi wurin da Sgr yake tsaye ya duƙar da kanshi kasa,duk jikinshi yayi sanyi,Ya karaya sosai,

  "Rafayet yanzu ka kyauta abunda ka aikata mata"?idanuwanta jawur take kallonshi,

  "What i neva expect from u,kai da kanka kake hukunta masu aikata laifi makamancin wannan amma yau kaida kanka kayiwa ƴar uwarka ta jininka,Why rafayet?ko laifi tayi maka ta cancanci wannan hukuncin?balle kuma batayi maka laifin komai ba!saboda kawai sun 6ata maka rai sai ka huce haushinka akanta?Yanzu kalli halin da ka jefata!Ka ƙiyasta irin raɗaɗin azabar da take ji a lokacin da kake kusantarta da kuma wannan lokacin da take halin jinya......'


Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla,Sam ya kasa ɗagowa su haɗa ido da ita,

  "Pls Alex,bai kamata muna tuna abunda ya wuce ba,Wannan abu ya riga daya faru,Sai dai kawai mubi ta da addu'a,Allah ya kawo mata sauki,very soon zata wartsake,"

   Cike da takaici Mommy tace"don bakisan Halin da iyayen yarinyar nan suke ciki bane,sun damu sosai akan rashin ƴarsu,ni banma san me zance masu ba idan suka ganta,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana share hawayen dake zarya akan fuskarta,

  "Baikamata asanar dasu ba,Don ta yanzu,Gaskiya in suka ganta a halin da take ciki yanzu zasu shiga matsananciyar damuwa,saboda har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba,da zarar ta farka sai ta dinga sambatu akan abunda Alex yayi mata,"

  Ajiyar zuciya mommy ta ɗan sauke before tace"What's the solution now?zata kai tsawon wani lokaci kafin ta dawo hayyacinta,"

  "Koda wani lokaci zata iya dawowa cikin hayyacinta,Yanzu ma baccin nan da kikaga tanayi munyi mata allurar bacci ne,abunda za'ae yanzu shine kada ki sanar da kowa inda suke,Har sai ta dawo cikin hayyacinta,zan sanar dake,Sai asan yadda za'ae a mayar da ita can gidan taci gaba da jinya,ina ga kamar hakan zaifi,"

Mommy tace"Hakan yayi,thank u so much Harriet,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin gode maki ba,kin taimakemu sosai,Yanzu zan koma gida kada su nemi ni,"ta ƙarasa maganar tare da mikewa tsaye,

  Rungume juna suka kumayi ita da harriet kafin Ta mayar da idanuwanta kan Sgr,

  Tausayinshi ne ya kamata,a hankali ta furta sunanshi"Rafayet"

  ɗagowa yayi da idanuwanshi ya kalleta,

  "Don't u need me"?

Yana jin haka jiki asanyaye ya nufeta,sosai ta rungumeshi ajikinta,

"Mommy i need ur prayer,am in serious dilemma,bani da wani sauran kwanciyar hankali daya rage mun,Mommy i ave regretted wlh,Nasan Uncle da Daddy fushi suke dani"

   Cikin sigar lallashi ta sanya hannunta abayanshi tana ɗan bubbugashi tace"Allah ya bata lafiya,nasan zaka bata kyakkyawar kulawa,dan Allah rafayet ka rage wannan zafin zuciyar naka,baida amfani,ni nasan cewa kana son yarinyar nan,ka mika wuya kawai ka nuna masu cewa kana sonta,Zaka tafi da ita a matsayin matarka,Shine fa 

kawai abunda suke buƙata a wurinka,simple and short amma ka kasa yi masu,har sai da ka illata masu yarinya,


Sun jima suna magana dashi,Kafin tayi masu sallama ta fuce daga gidan,


*Boss Bature*


Tun bayan da Mommy ta koma gidan bata sanarwa kowa game da inda rafayet yake ba,kamar yadda suka tsara,duk da tashiga damuwa sosai akan halin da Abusufyan yake ciki,Shi da Omar da kuma Abba,ko abincin kirki basu ci,Bacci kuwa tuni ya ƙauracewa idanuwansu saboda damuwa,Yanzu kowa na cikin gidan Ya gane cewa Mutun biyu basa nan,Sgr da Sehrish,Amma mommy bata bari sun gano wani abu ba,Da zarar sun soma tambayarsu sai ta sanar dasu cewa Sunyi tafiya ita da Sgr,wannan dalilin ne yasa basu tashi hankalinsu sosai ba,,yau a ƙalla kusan 2 weeks kenan babu su babu alamarsu,


Wuraren ƙarfe 1:30 na dare,Sgr na rungume da ita ajikinshi,dayake shi yake kula da ita,koda yaushe yana manne da ita,tamkar jinjira haka yake riritata,jikinta yayi sauƙi sosai sai dai abunda ba'a rasa ba,Saboda har yanzu bata ida dawowa hayyacinta ba,can cikin bacci ya dinga jin sambatunta"Ya rafayet bazan iya jurewa ba,mutuwa zanyi,Wayyo Allah na,Daddy kazo ka taimaki rayuwata,Ya rafayet baisona,Kashe ni yake so yayi,ƙoƙarin ƙwace jikinta take yi daga nashi,Da sauri ya zura hannunshi ya ta6o bedside lamp ya kunnata,Haske ya ɗan kawo,


Slowly ya mayar da idanuwanshi kan fuskarta,har sai da gabanshi ya faɗi ganin yadda ta zazzare idanuwanta,suna haɗa ido dashi,A gigice ta soma ƙoƙarin zame kanta daga ruƙon da yayi mata,

  

  Yunƙurawa yayi tare da miƙewa zaune Ya taimaka mata ta zauna,Ya sanya mata pillow daga bayanta,

  "Are u feeling hungry?"yayi tambayar yana kallonta,shiru bata bashi amsa ba,Sai dai kallon da take binshi dashi,Saukowa yayi daga saman gadon Ya nufi fridge ɗin ɗakin Ya ɗauko mata fresh milk mai sanyi,tare da ruwa,


Hawa saman gadon yayi dab da ita suna fuskantar juna,buɗe murfin robar yayi tare da kafa mata ita saitin bakinta,Buɗe baki tayi sosai tasha madarar,kusan duka ta shanye,Magungunanta ya soma bata tana sha,har ta kammala,


  Sai faman lumshe idanuwanta takeyi da alama baccin bai isheta ba,

  Nuna mata fuskarshi yayi"Look at my face,Kin gane  ni kuwa,"

  A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskarshi,ta jima tana kallonshi batare data tanka mashi ba,hannu yasa tare da janyota jikinshi,ya zaunar da ita saman laps ɗinshi,ya kasance kanta yana asaman ƙirjinshi,a hankali ya ɗaura hannunshi asaman sumar kanta,shafa sumar kan nata yaci gaba dayi,kafin ya duƙo da fuskarshi zuwa gefen tata,tsinin hancinshi yana gogar fatar wuyanta,

  Calmly ya soma magana"I made a mistake,but I still have time to correct it,idan nace kiyi haƙuri nasan nacuce ki.......'ya ɗan dakata da yin maganar,baisan ko tana fahimtarshi ba,

  "Amma ashirye nake dana kar6i koma wani irin hukuncine daga gareki,"cikin sanyin murya ya ƙarasa maganar,shi kaɗai yasan yadda yake ji acikin zuciyarshi,still bata nuna mashi wata alama da zata nuna cewa tana acikin hayyacinta,tunda ta kwantar da kanta saman wide chest ɗinshi,bata ƙara motsawa ba,ta lumshe idanuwanta, 

  "Reesh,"ya kuma ambaton sunanta,bata amsa mashi ba,sai dai motsin hannunta dayaji abayanshi,dayake ta zagayo dasu,

  "Can't u talk to me?i know you're hearing me,"

  Tabbas kuwa tana jinshi,duk abunda yake cewa kaf acikin kunnanta,domin kuwa ta dawo hayyacinta,a ƙule take dashi,don taci alwashin sai yabata takardar sakinta,bazata ta6a cigaba da rayuwa dashi ba,ta tsorata da irin rashin imanin daya gwada mata,Yanzu ta daina kallonshi a matsayin mutun Dodo ya koma mata,a zaunan da suke bacci ya ɗauketa,shima ya fara gyangyaɗi,A hankali ya kwantar da ita,kafin ya kwanta tare da janyota ya ƙanƙameta jikinshi,


A washe garin ranar wuraren ƙarfe 7 na safe,Dr harriet ta kira Mommy awaya take sanar da ita game da cigaban da akasamu na Lafiyar Sehrish,ba ƙaramin daɗi taji ba,suna cikin yin wayar nan,tajiyo knocking daga waje,Da sauri tayi rejecting kiran,Ta juya bakin ƙopar ɗakin ta buɗe,

  Omar ta gani atsaye,duk ya rame kamarshi ya aikata laifin,

  "Ina kwana Mommy,".

  "Lafiya lou,"ta amsa mashi fuskarta asake,

   "Mommy still Rafayet bai tuntu6eki ba"?

  Shiru tayi tana tunanin kodai ta faɗa mashi inda suke,ganin yadda ya shiga damuwa over,

  "Omar,i won't hide it for u,Nasan inda rafayet yake,bansanar ma kowa bane saboda gudun halin da ƴan uwanta zasu shiga idan suka ganta a halin da take ciki na jinya,"

  Tunda ta fara magana Omar,Ya zuba mata ido yana kallonta Ya rasa me zaiyi farin ciki ko baƙin ciki,Duk irin halin da suke ciki na neman Sgr ashe ta sani?

  Daƙyar ya iya buɗe baki yace"A ina suke mommy,"

  "Banaso kowa ya sani Omar,nafiso saita samu sauƙi sosai,Yadda hankalin Abusufyan zai kwanta,"

  Jinjina kai yayi"bazan fada masu ba,"

  "Yana gidan Dr harriet,Nasan kasanta,"

  Tunkafin takai ƙarshen Maganar,Omar yayi hanzarin juyawa a gaggauce Ya fuce daga cikin gidan,Mota ya shiga,Major yajasu da gudun gaske zuwa gidan,dan bazai manta kwatancen gidan ba,tunda sun ta6a zuwa a lokacin baya,


Yana yin parking ɗin motar,tunkafin Major ya zagayo ya buɗe mashi ƙopa,Yasa hannu ya ture murfin motar,kaitsaye ya nufi cikin gidan,A buɗe ya samu ƙopar da zata sadaka da palourn gidan,ko sallama baiyi ba ya faɗa cikin gidan,A saman dining ya taras da Harriet tare da twins ɗinta matasan ƴan mata su biyu suna yin breakfast,Tana ganin shi ta soma sakin murmushi,

  "Omar yau kaine a gidana,"bai amsa mata tambayarta ba,Sai cewa yayi"Ina Rafayet yake,"?jim ta ɗanyi tana kallonshi Sam babu natsuwa atattare dashi,dama tayi mamakin ganinshi,

  Nuna mashi upstairs tayi"Suna acan sama,"ko kwatancen ɗakin bai tsaya tayi mashi ba,Da gudun gaske ya haye stairs ɗin,cikin sa'a ya gano ɗakin,Yana turo ƙopar Ya samu Sehrish zaune ta jingina kanta jikin headboard na gadon,Duk atakure take,


"Sister,"ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya,

  Firgigit sehrish ta ware idanuwanta akanshi,tana ganinshi wani irin farin ciki ya lullu6eta,"Ya Omar",Da sauri ya ƙarasa gefen gadon ya zauna,Zuba mata ido yayi yana kallon Canzawar da tayi,Ta rame sosai takuma yi haske,


"Ya jikin naki"?bata amsa mashi ba,saboda kukan daya ciyota,Sosai ta fashe mashi da kuka,ruƙo hannayenshi tayi"Ya Omar dan Allah ka tafi dani gida,Wlh banjin daɗin zama anan,nafison na ganni cikin ƴan uwana"

  Tsananin tausayinta ne ya kamashi,tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,

   "Ya Omar wlh ka tafi dani gida tunkafin Ya rafayet Ya fito,don bazai ta6a bari ka tafi dani ba,Ni kuma natsani zama a gidan nan,duk a ƙuntace nake babu daɗi,"

   "Yana ina rafayet ɗin"?

  "Ya shiga wanka"

  Jinjina kanshi ya ɗanyi,kafin yace"Zaki iya tafiya,"

  Girgiza kai tayi"a'a bazan iyaba",don tasan in dae da kafafunta zata taka to kuwa har sgr ya fito ya gansu,

  Batare da 6ata Lokaci ba Omar ya ɗauketa saman kafadarshi ya sauko downstairs da ita,Dr harriet na ganinshi da ita,Hankalinta ya tashi aruɗe ta tare shi tana faɗin"Omar where are u going with her?Rafayet ne ya baka izni?Ko alex ce tace kazo ka ɗauketa,

  Tunkafin Omar yayi magana Sehrish tace"Ya Omar kada ka saurareta,wlh in ka barni acikin gidan nan Poison zansha in mutu,"yana jin haka ya ƙara harzuka,

  Ko kallon Harriet baiyi ba Ya fuce daga falon,Major ya bude mashi mota ya shigar da sehrish yana cewa"nasan idan ya fito yaji cewa Mun tafi da ita,dole ya dawo gida,"


Da gudun gaske Motar major ta fuce daga cikin gidan,Sehrish sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,baiwar Allah daga ita sai wannan rigar mai kama da uniform,Ƴan ƙafafuwan ko takalma babu,Kanta ko mayafi babu sai dai gashin kanta dake a cukurkuɗe,duk ta ƙosa taga Mahaifiyarta da mahaifinta,da kuma ƴan uwanta,Rafayet ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,ya ƙumsa mata baƙin cikin da bazata ta6a mantawa ba,Ya sanya mata ƙiyayyarsa acikin zuciyarta,


A hankali Major Ya shigar da motar ta cikin babban gate ɗin gidan,Bayan yayi parking ɗinta,Ya fito da sauri Ya buɗe mashi Mota,Saukowa marshal yayi tare da zura hannayenshi Ya kinkimo Sehrish asaman kafaɗarshi,

  "Thank u Major"Yana ambaton hakan ya wuce da ita cikin gidan,A lokacin  babu kowa a palour sai dai mutanan dake kitchen suna shirya breakfast,Yana yin sallama hankalinsu Ya dawo kan Omar dayake suna hangenshi daga inda yake,Koda abu tayi arba da matashiyar dake kwance asaman kafaɗarshi,nan take taji aranta cewa Sehrish ce,Da gudun gaske ta fito daga kitchen ɗin,Hajiya azeema tare da Mommy suka biyo bayanta,Ai koda Mommy taganshi ɗauke da sehrish sai da gabanta Ya faɗi,Har warning tayi mashi akan kar ya sanarwa kowa inda ta suke,Sai gashi ɗungurugum Ya ɗauko ta,

 

Aruɗe abu take kallonta"Sehrish ce?Meya faru da ita"?tayi tambayar tana ƙare mata kallo,har lokacin bai sauketa daga kan faɗarshi ba,

  Hajiya azeema kuwa Alhamdulillah ta soma faɗi,fuskarta ɗauke da murmushi,duk da ta damuwa sosai ganin yadda ta rame,

  "Dan Allah ku faɗamun meya faru da ita,Meyasa nake ganinta haka?kamar bata da lafiya,"

  Omar na ƙoƙarin Yin Magana,Sehrish Tace"Oumma,Lafiyata qalou,Yaya Omar ka kaini ɗaki inaso inga ƴan uwana,"

   Wucewa bedroom ɗinsu yayi,da sauri suka bi bayanshi,jikin abu duk yayi sanyi,koba a fada mata ba tasan cewa babu lafiya atattare da ita,tunda har bazata iya tafiya da ƙafafuwanta ba,Suna ƙarasowa kopar ɗakin,Oumma ta buɗe mashi Ya shiga da ita,A lokacin Jahad na zaune gefen gadon Tana karatun al'qur'ani,Hosana kuma ta kabbara sallah,Don bata samu yin sallar a lokacinta ba,


A firgice Jahad ta miƙe tana kallon Ya Omar dake ɗauke da Sehrish,da ƙarfi ta ambaci sunanta Sehrish!Ae Hosana najin an kira sunan Sehrish Ta katse sallar da take yi dama tunda suka shigo take ƴan waige waige,A hankali Omar ya zaunar da ita samam gadon,Ya sanya mata pillow a bayanta,ɗaya bayan ɗaya take bin fuskokinsu da kallo kamar yadda suma suke binta da kallon ƙurulla,Hosana sai tsalle take yi tana ambaton sunanta saboda murna,


Fashewa Sehrish tayi da matsanancin kuka,Da sauri ta sanya tafin hannunta asaman fuskarta,tsananin tausayinta ne ya kamasu,da sauri Oumma ta zauna gefen gadon"Sehrish meya faru dake ne?na damu sosai akan rashin ganinki,Har Abusufyan na tambaya yake sanar dani cewa kunyi tafiya keda babban yayanku,"kasa buɗe baki sehrish tayi,saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare mata makoshinta,A duk lokacin data tuna abunda Sgr yayi mata,

  Zuƙunnowa Hajiya azeema tayi saitin fuskarta"Pls stop crying,Wlh nashiga damuwa sosai akan rashinki,banji daɗin abunda ya faru ba,Amma kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara maki,Yanzu dai ki sassauta kukan nan naki,kodan saboda mahaifiyarki zata shiga damuwa sosai"tayi maganar ne ta yadda abu bazata iya jiyota ba,

  "Koda sun tambayeki meyake damunki,Kice baki da lafiya zazza6ine ya kamaki,"cikin shessheƙar kuka Sehrish ta ɗaga mata kai alamar zatayi yadda tace,Miƙewa Hajiya azeema ta yi,Jahad ta zauna saman side drawer na gadon tana tambayarta Lafiya,

  Cikin shessheƙar kuka tace"Bani da lafiya ne,Amma jikin da sauƙi,kawai nayi kewarku ne sosai,"

 Kallonta kawai Jahad take yi ba don ta yadda da abunda tace ba,

  "Tana buƙatar hutu,Bai kamata mu takura mata da tambayoyi ba,idan ta huta sai muyi magana da ita,"acewar Hajiya Azeema,daga haka babu wanda ya ƙara tambayarta,

  Matsawa abu tayi kusa da ita,ta sanya hannunta ta rungumota jikinta,wani irin zafi dama kullum cikin zazza6in take,

  "Allah ya baki lafiya Sehrish,"

 "Ameen Oumma,"_


Mommy kuwa bayan fitar Omar da sauri tabi bayanshi,

  "Why omar meyasa zaka ɗaukota?haka mukayi dakai"?

  Juyawo yayi fuskarshi sam babu annuri acikinta,.  

  "Haba mommy,don me zan barta acan?An ƙuntata rayuwar yarinyar nan sosai,Na farko an cutar da ita,na biyu kuma an kaita wani wuri inda batasan kowa ba,Hakanan ya rabata da kowa nata,lokacin dana je kuka ta dinga yi mun tana ruƙe hannuwana akan in tafi da ita gida kota kashe kanta,Shiyasa na yanke shawarar ɗaukota,Tunda jikin nata da sauƙi,"

  "Shikenan Omar,Nima nayi tunanin a dawo da ita gidan,Kawai ina fargabar halin da Zasu shiga ne idan suka ganta,"

  "Kada ki damu Mommy,rashin ganinta a kusa dasu shiya fi haɗari,Amma in tana atare dasu,To da sauƙi,ita kanta tafi son cikin ƴan uwanta,"

   Jinjina kai Mommy tayi"Wannan haka yake,nagode sosai Omar,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa Ta nufi kitchen,shi kuma Ya wuce ɗakin Abusufyan,Hannu yasa yana kwankwasa kopar,A lokacin Abusufyan yana ta faman zarya cikin ɗakin,Damuwa duk ta isheshi,jin knocking ɗin ƙopar yasa shi yin hanzarin juyawa yaje ya buɗe mashi,

  Tunda yaga fuskar Omar awashe ranshi ya bashi cewa Akwai labari me daɗi,. 

  Muryarshi na kerma yace"Omar,An gano inda suke,".  

  Fuskar Omar ɗauke da murmushi yace"yanzu haka Sehrish tana aɗakinsu,"tunkan yakai ƙarshen maganar Abusufyan Ya fuce da sauri har yana tuntu6e,


Suna zaune saman gadon sun zagayeta,Sai gashi Ya banko ƙopar dakin Yana ambaton sunanta"Sehrish!"yadda kasan makoshinshi zai 6allo,

  "Daddy,"ta amsa mashi fuskarta ɗauke da murmushi,Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi,Da sauri ya ƙarasa suka matsa mashi,Ya hau saman gadon Ya rungumota jikinshi,Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya Ya sauke,Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,

  "Daughter,Am sorry for everything,i ave regretted already,duk nine silar halin da kika tsinci kanki,"sosai yayi tighting ɗinta ajikinshi,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,

  tamkar raɗa haka yake yi mata maganar don kar suji abunda yake cewa,tunda bakowa yasan ainihin abunda ya faru da ita ba,

  Cikin shessheƙar tace"Daddy kamar Bazan rayu ba,Nasha wahala,Lokacin mutuwa nane kawai baiyi ba,'

  "Nasani,wlh naji ajikina Daughter,danasan hakan zata faru da ban tursasa mashi akan ya sakeki ba,da duk hakan bata faru ba,"Sai lokacin Sehrish ta gane dalilin dayasa Sgr yayi mata hakan,

  Janyeta yayi daga jikinshi,tare da sanya hannunshi asaman fuskarta yana share mata hawayenta yace"Ina babban yayan naku?nayi tunanin atare dashi zaku dawo,'

  Girgiza kai ta ɗan yi"A'a,Sai zuwa anjima zai dawo,Ya Omar ne ya kawo ni,Na matsa mashi ne akan inaso na dawo gida," sunyi pretending ne don kada Oummansu ta gano gaskiyar abunda Ya faru da ita,

  "Allah ya baki Lafiya Daughter,"

 "Ameen daddy,"

  Turo kopar ɗakin akayi,Mommy ce ta shigo hannunta ruke da plate mai ɗauke da farfesun nama,da zafi zafinshi sai ƙamshi yake yi,


  Ƙarasowa ciki tayi fuskarta a ɗan sake tace"Ya jikin naki,"

  Batare da sehrish ta kalleta ba ta amsata"da sauki Mommy,"

  Miƙa ma Abu plate ɗin tayi"Ga wannan nasan zata buƙace shi,Akwai tea dana haɗa mata,bari naje na ɗauko mata shi,"

  Hannu bibbiyu Oumma tasa ta kar6i plate ɗin"Mun gode sosai,"

  "Kada ki damu,duk yiwa kaine"takai ƙarshen maganar,tare da juyawa a hanzarce tabar bedroom ɗin,Abusufyan ya lura da sehrish,tunda Mommy ta shigo bata kalli fuskarta ba,tayi hakanne saboda ta tsani ganin fuskar Sgr,Ita kuma Mommy dashi take kama shiyasa taƙi kallonta,

   Shafa fuskarta yayi"Daughter,"murmushi ta ɗan saki batare data ɗago da idanuwanta ba,Sun cika tab da kwalla,

  Juyawa yayi tare da kallon Abu dake tsaye hannunta ruƙe da plate,. 

  Kar6ar plate ɗin yayi daga hannunta,

  Ruƙo hannun Oumma Mommy azeema tayi"mu koma kitchen munbar Aiki acan,In sha Allah zata samu sauƙi,"atare suka fuce daga ɗakin,

  Ya rage daga Abusufyan Sai Hosana da Jahad dake kewaye da ita,

   jim kaɗan Mommy ta dawo hannunta ɗauke da Cup wanda ta haɗa mata Kakkauran tea acikinsa,

  Asaman side drawer ta ajiye mata Cup ɗin,

    Kafin ta juya tabar dakin,

 "Rishi wai ina kika shiga ne?Kin tafi kin barmu da tunani,"Hosana ce tayi maganar fuskarta a yamutse,

  Jahad tace"Dan Allah kibarta ta huta,Ba kiga bata da lafiya ba,Sannu Sehrish Allah ya baki Lafiya,muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mata da Ameen,

  Abusufyan da kanshi Ya zauna yana bata farfesun abakinta,Cike da kulawa,ba ƙaramin daɗinshi taji ba,sosai tasha,kusan duka ta shanye duk da hosana ta tsoma masu hannu,Ta dinga ɗaukar naman tana turawa abakinta wai ae itama bata ci ba,


Bayan ta kammala Ya ajiye plate ɗin Ya dauki cup of tea ɗin da mommy ta ajiye mata,A baki ya kafa mata shi,Sosai ta shiga kur6arshi abakinta,

  "Amma nima ka bani tea ɗin abaki"?

Hosana ce tayi maganar,tana tura mashi bakinta,Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya basu ba,murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallonta,

   "Daddy ka bata tasha,"

Cike da zolaya Abusufyan yace"Na mara lafiya ne,Hosana kiyi hakuri wannan na sehrish ne,bata baki tausayi ba Kalli fa ki gani duk ta rame,"

  A shagwa6e Hosana ta langwa6ar da kanta,tasa hannu tana nuna mashi ƙashin wuyanta,

  "Daddy ae nima banda Lafiya,Kalli ka gani,"

  Kallon wuyanta yayi acike yake babu wani ƙashin daya leƙo,

  Harara Jahad ta ɗan watsa mata"Saboda kofin tea zaki jama kanki ciwo,Tirr da wannan halin naki,Shegen Ci kamar gara"

  Guntun tsoki Hosana taja"eh ɗin ina ruwanki,Ƴar shigar shugula,ba'a kasa dake ba,kin tsomo mana baki,".

  Dariya sosai Abusufyan yayi yana kallonsu,ita kanta Sehrish murmushi ne kwance akan fuskarta,Hankalinta Ya kwanta sosai,gata ga iyayenta ga kuma ƴan uwanta,


Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Abusufyan yace"Wanene"?

 "Nice Amrish,"

 "Okey shigo daga ciki,"turo ƙopar ɗakin tayi,jikinta sanye da hijabi dai dai guiwa,Waro ido waje tayi ganin Sehrish 

  Da ƙarfi ta ambaci sunanta"SEHRISH"

  Wani irin farin ciki ne ya lullu6ete,har ta manta da abusufyan dake zaune,Da gudu ta ƙarasa gefen gadon,Ta haura sama ta rungumota ajikinta,

  "Sehrish ina kika shiga ne?ina ta nemanki?Oumma tace mun kunyi tafiya keda Babban yayanku,"

  Fuskar Sehrish ɗauke da murmushi tace"Am sorry Amrish,Nayi laifi ban sanar dake ba,Tafiyarce ban shirya mata ba,ni kaina bansan da ita ba,"

  ɗagowa amrish tayi daga jikinta ta sanya tafin hannayenta ta tallabo fuskar Sehrish"Duk kin rame,Baki lafiya ne "

  "Zazza6i nake yi,"

  Gyaran murya Abusufyan yayi mata,Da sauri Amrish ta sauko daga saman gadon ta zuƙunna tana gaishe shi"Ina kwana daddy,An tashi lafiya,Ya mai jiki,"

 Murmushi Abusufyan ya sakar mata tare da cewa"Lafiya Lou,yaushe rabon dana sanyaki acikin idanuwana,bakyason zuwa kina gaishe ni ko"?

  Sunnar dakai ƙasa tayi cike da jin kunyarshi tace"A'a,inason zuwa,"

  "Baki ɗaukeni a matsayin mahaifinki bane"?

  Da sauri tace"Na ɗauke ka,"

  "To meyasa bakya sakin jiki dani ne"?

  Shiru tayi batace Komai ba,

  "Daga yanzu inaso ki saki jikinki dani,Dake dasu Sehrish duk ɗaya kuke a wurina,duk wani abu da kike buƙata na rayuwa,ki sanar dani ni kuma zanyi maki shi,"

  "Nagode sosai Daddy,"ta ambaci hakan tare da miƙewa,

  "Sehrish wayarki na ɗaki,bari na ɗauko maki ita,"

  Da sauri ta juya ta fuce daga ɗakin,Kallonta Abusufyan yayi,

  "U need a rest,ki kwanta ki huta,Zuwa anjima zan sake zuwa dubaki,Yanzu hankalina ya kwanta,ashe da rabon yau inyi bacci hada minshari don tunda kuka tafi wlh ban runtsawa sai dae bacci 6arawo ya dan dauke ni Daughter,"

  Murmushi ta ɗan saki,mikewa yayi tare da kallonsu Jahad yace"Ku kulamun da ita pls,"

  Atare suka amsa mashi da toh,kafin ya bude kopar ɗakin ya fuce,


Baijima da fita ba,Amrish ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da wayar Sehrish,zama gefen gadon tayi tare da miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar,

   "Ya jikin naki"?

 "Am feeling better now,nayi missing dinku sosai,"

  Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Nima nayi missing ɗinki sosai,Kullum saina tambayi Oumma yaushe zaki dawo,"

  "Allah sarki,nagode sosai da nuna damuwarku akaina,"


Bayan fitar Abusufyan kaitsaye ya nufi ɗakin Ammi,A lokacin khadija da nafeesat suna acikin ɗakinta,Suna tattaunawa game da bikin da za'ayi,


Da sallama ya shiga ɗakin,atare suka amsa mashi,da sauri suka soma gaisar dashi,fuskarshi asake ya amsa masu,Suna zaune ƙasa sun lankwashe kafafunsu,Ammi kuma na zaune gefen gadonta,

  Agabanta ya zuƙunna"Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya,"

  "Lafiya lou,Autana,Ina fata kaima haka,"

 "Alhamdulillah"ya amsa mata,

  "Da alama yau akwai labari me daɗi akan fuskarka,murmushi ya saki tare dacewa"Ammi Sehrish ta dawo,Yanzu haka daga ɗakinsu nake,"

  "Masha Allah,Kai amma naji daɗi sosai wlh,Amma waye ya kawota?

  "Omar ne ya ɗaukota,"

  "Amma ya lafiyar jikin nata"

  "Da sauki ammi,"

Miƙewa tayi hannunta ruƙe da sandarta,kallonsu Nafisat tayi"yanzu zan dawo,Zanje na duba jikin jikata ne,"

  Mikewa sukayi atare"Muma zamu je ammi,"

  Murmushi tasaki"shikenan bismilla,"Abusufyan Ya shiga gaba suka bi bayanshi,har zuwa ɗakin Su Sehrish,

Ba ƙaramin farin ciki ammi tayi ba,Ganin yadda sehrish take ta faman sakin murmushi,tashi Amrish tayi daga gefen gadon,Ammi ta sauna suna fuskantar juna ita da sehrish,

 Atare suka haɗa baki suna gaishe da ita,Bayan ta amsa masu tace"Ya jikin naki"?

  "Naji sauki,"

Jinjina kai ammi tayi"Alhamdulillah mun godewa Allah,Haka mukeso,"Takai ƙarshen maganar tare da kallonsu Khadija dake atsaye,Ga ƴar uwarku nan,ɗaya daga cikin ƴan ukun Abusufyan ne,Bata da lafiya ne,"


Har suna hada baki wurin yi mata Ya jiki,fuskarta asake ta amsa masu,kafin ta soma gabatar masu dasu,

 "Jikokin modibbo ne,Ƴa'ƴan ƙanwar Mahaifiyarsu Omar,sannan kuma nan bada jimawa ba,Zasu zama surukan Abba,ta 6angaren Adam Da Osman"


Farin ciki ne ya lullu6esu,Ammi taci gaba da cewa"su kuma waɗannan zasu bi sahunku suma,Wato zasu Zama surukan Abba,Ga Sehrish nan Amaryar Babban Yayansu,ɗan wurin Fatima," tunda ammi ta ambaci hakan ran Sehrish ya 6aci sosai,tuni ta ɗaure fuskarta,Sam babu wanda ya lura da ita,

  "Bayan ita kuma Sai Jahad,Amaryar shalelen Abba wato Junaid,"da sauri jahad Ta kife kanta saman katifar saboda kunya,

  "Ita kuma wannan,Mai hankalin cikinsu,Amaryar Omar ce in sha Allah,"

  Fashewa Hosana tayi da dariya,kowa najin kunya banda ita,

  "Inason nayi magana da ita, ku ɗan bamu wuri,"


Amsa mata suka yi da toh,Gaba ɗaya suka fuce daga dakin,A waje suka tsaya suna fira atsakaninsu,Amrish dai tayi shiru saboda ita batasan matsayarta ba,Amma taso ace hada ita za'a ɗaurama aure,Itama ta zama ɗaya daga cikin amaren gidan,


 Bayan fitarsu Ammi ta zauna tayi mata nasiha sosai,ta kuma nuna mata 6acin ranta akan abunda Sgr yayi mata,A ƙarshe ta ruƙe hannayenta"Bazanso abunda zai cutar dake ba,Dama jiran dawowarki nake yi,Saboda inaso inji ra'ayinki game dashi,Kina son Cigaba da rayuwa dashi,Ko kuwa A'a,"

  kamar jira takeyi da sauri tace"Banaso ammi,dan Allah ku rabani dashi,wlh bazan iya rayuwa dashi ba,Ni dai kawai asanyashi Ya sake ni,"hada hawayenta,

  Shiru ammi ta ɗan yi tana kallonta,Kafin tace" Amma fa yana sonki sosai,Wanda silar hakan ne yajawo har ya aikata maki hakan,Saboda anyi ƙoƙarin rabashi dake,"

  Cikin shessheƙar tace"Nidai bana sonshi ammi,wlh yafita araina,"

  Ajiyar zuciya ammi ta sauke,

  "Shikenan,In sha Allah zan shiga tsakaninki dashi"


WANNAN KENAN!


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post