Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 129 end

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 129 end


Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

*Boss Bature*

Bayan Wani Lokaci,

Alhamdulillah junaid Ya samu damar kammala Karatunshi,Ya zama ƙwararran Likita,batare Da 6ata Lokaci ba,Sgr Ya sama mashi Aiki a katafaren Asibitinshi na L.a,A 6angaren Su sehrish Kuwa Suma sun taƙarƙare karatun Secondry ɗinsu,Sgr Ya sama masu gurbin karatu a College of Nursing and Allied Health dake anan Los angeles,Rayuwa fa Tayi kyau,Ta ko'ina Sai sambarka,Hankali kwance suke yin karatunsu,Mazajansu suna ƙarfafa masu guiwa,Ƴa'ƴansu kuma Akwai Nannies ɗin dake kula dasu,hosana tana ɗauke da ƙaramin ciki,saboda takurar da take yiwa omar akan tana son baby tunda ita ɗaya gareta,a dole aka dakatar da planning din da take yi,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 9 na dare,Kwance suke a katafaren gadonsu,Komai na bedroom ɗinsu Pink colour ne,An ƙawata shi da duk wani abu na more rayuwa wanda yaro zai buƙata,triple bed ne,Guda uku A jere,da alama sunyi nisa acikin baccinsu,Kowannasu na sanye cikin Night dress ɗinsa,Mazan suna sanye ciki riga da wando White colour,Ƴar macen tana sanye cikin riga da wando Pink colour,ba ƙaramin kyau suka yi mata ba,Sumar kanta dark brown very smooth,kamar yarda Zainab take da dogon gashi haka mazan ma,domin kuwa sun ɗauka irin sumar kan Sgr,Gashin kansu ya sauko har saman kafaɗansu,A ƙalla yanzu sunkai shekara Biyar a duniya da ƴan watanni a duniya,da farko a gado ɗaya suke kwana,Amma saboda rashin jituwarsu yasa Aka kawo wasu bed ɗin biyu,abunda ke faru aduk lokacin da Iyayensu suka kwantar dasu,da zarar sunbar ɗakin,Ƴar macen zata Soma tsokanar mazan faɗa,Gasu miskilaine,Don hossein Halinshi sak irin na Sgr,ko kallo wannan Mutun bai isheshi ba,mugun jan ajine dashi,bai ɗaukar raini ko kaɗan,Mugun miskiline,Suna kiranshi da Gentle Ƙwara Little Omar,Shiya ɗauko Halin Sehrish,Hatta tsoran nan na Sehrish haka yake shima,Ko tsawa akayi sai ya gigice,Yaci ka sanyi,Bai bar komai na daga halinta ba,Zainab kuwa Tafi ƙarfi 6angaren Sgr,Sai dai ita ba miskila bace,mafaɗaciyace,Kamar ƴar dambe haka take,dama tun suna jarirai,In ta fara tsala ihu,Sai ta firgita kowa,Pretty suke kiranta,Allah yayi mata ƙarfi,tun tana ƙanƙanuwarta inaga inta girma,

A hankali ta turo ƙopar ɗakin sai kayi tsammanin babban mutunne zai shigo sai ka kalli ƙasa tukunna Zaga iya hangenta,azeema ce ƴar wurin Jahad Wadda suke kira da Beauty Saurin Shiga rai gareta ta,saboda sanyin Halinta,matsalarta ɗaya muguwar sangartacciyace,Ga shagwa6a Komai nata irin na junaid ne,hannunta na ruƙe dana ƙaninta Littafin abusufyan,shi halinshi Sak na jahad ne,Kowannansu na sanye Cikin kayan baccinshi yadda suke tagwaye haka kayan jikinsu ma Suka kasance Launi ɗaya,Riga da wando brown colour,wannan ɗabi'arsu ce duk mun dare bayan iyayensu sun kwantar dasu,In har suka farka to sai sun nemi ƴan uwansu,Abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yake yi ba,kamar masu iskokai,Sunfi son kwana ɗaki ɗaya kamar yadda suka saba yin wasa atare,

Suna shiga ɗakin suka saki Hannun Junansu,Da gudu Little Ya haye Gadon Omar ya kwanta gefenshi,don sunfi shiri dashi,Beauty kuma ta nufi gadon Hossein zata kwanta,Tana ɗaura hannunata Ya ware Manyan blue eyes ɗinshi akanta,Gaba ɗaya ta furgice,Ashe idonshi biyu tun lokacin da suka shigo,Wani irin kallo yake binta dashi,Ko Uffan baice mata ba,Ya juya mata baya,Don karma su fuskanci juna,Bai hanata kwanciya ba,lalla6awa tayi saman gadon ta kwanta,

Basu jima da shigowa Ba,Sai ga Little Rafayet,Hannunshi ruƙe da ƙaton teddy ɗinsa har yaso yafi ƙarfinshi,Farin cikine Ya lullu6eshi ganin ƴan uwanshi duk sun haɗu guri guda,da gudu Ya ƙarasa Saman Gadon Zainab Ya haye ya kwanta,Tare da ɗaura mata teddy ɗinshi asaman Jikinta,Cikin bacci tajishi,aikuwa a harzuƙe ta farka,Tayi wurgi da teddy ɗin tare da ɗunƙule hannunta zata kai mashi naushi,koda tayi arba da fuskar Little Rafayet,Sai ta janye hannunta,Tana faman Cizon le6enta Allah yaso shine dayasha Naushi,juyawa tayi ta ɗauko mashi teddy ɗinshi ta miƙa mashi"take it,"a tsanake tayi maganar,

 Cikin harshen turanci don dashi suka taso amma suna jin hausa,Iyayensu nayi masu,saboda Suna yini a school,yasa suka fi ƙarfi ta 6angaren turancin da french,

   girgiza mata kai yayi"Naki ne,Na kawo maki,"murmushi tasaki har dimple ɗinta Ya lotsa,a tsakiyarsu ta ajiye teddy ɗin,a haka suka rungume juna,da ƙaton teddy a tsakiyarsu,cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dasu,

*Reeshraf*

A hankali take saukowa daga saman stairs ɗin da zai sadaka Da Swimming Pool area ɗinsu,A yayin da Sgr Yake tsulundun acikin ruwan yana jiran ƙarasowarta,Ƙayataccen swimming pool ne mai faɗi,Ruwan cikinshi yayi blue sky,wata irin ni'emace ke sauka a wurin,Jin motsinta,Yasa  shi yin saurin kai idanuwanshi akanta,tun ɗaga ƙasa ya fara kallonta,Swim suit ne Ajikinta(Kayan wanka),Ƴar rigace me haɗe da pant,red colour,tabi shape ɗin jikinta,gaba ɗaya ta tafi da imaninshi,Santala santalan Cinyoyinta ba ƙaramin fusgarshi suke Yi ba,Iska sai kaɗa sumar kanta takeyi,Yalwataccen gashin kanta sai kaɗawa yake yi saman iska,yana ƙoƙarin rufe mata fuskarta,A hankali take kai hannu tana Janye gashin,Yadda kasan bata ta6a ɗaukar Cikin ƴan uku ba,Jikinta yayi kyau sosai,ba ƙaramin gyara take yi ma Jikinta ba,tana kiyaye duk wani abu da zai 6ata Shape ɗin Jikinta, kuma Tana yawan motsa jikinta,Ga mayukan gyaran jiki da take Using dasu kullum,duk cikinsu ita kaɗaice bata yi jiki ba,Duk da suma Su Jahad basu 6uttuke ba,

Lumshe idanuwanshi yayi a yayin da yake kallonta,A ƙagare Yake data ƙaraso Ya rungumeta Ajikinshi,da wata irin kasalalliyar murya yake ambaton Sunanta"Reesh....pls come quickly"sai ja mashi rai take yi,Koda ta ƙaraso Gaban pool ɗin,Zagayeshi ta shiga yi,duk in tayi taku ɗaya sai jikinta Ya girgiza,

  "Pls reeesh why kike yi mun haka?bazaki shigo ciki ba"?maƙe mashi kafaɗa tayi alamar bazata zo ba,sai faman haɗiyar yawu yake yi,

  "Kada ki bari na hasala,Zan damƙo kine,"

  Kashe mashi ido ɗaya tayi"Nafison haka,Kafin ka fito daga cikin ruwan ni kuma zan watsa a guje"

  ɗaure fuskarshi yayi"haka kike ce"?

  ɗaga mashi gira tayi,Kamar ta ƙara tunzurashi,batayi tsammanin zai fito ba,sai dai kawai taganshi akan ƙafafunshi,daga shi sai short ajikinshi,Faffaɗan ƙirjin nan nashi a buɗe kamar zaiyi dambe,A firgice Ta juya da gudu zata Koma Saman benen,Sai dai ina kafin takaiga stairs ɗin tuni sgr Ya cimmata,ƙwaƙƙwarar damƙa yakaima Qugunta,ya ɗago da ita sama ya nufi Pool ɗin da ita,Kamar tasan abunda zaiyi tadinga bubbuga bayanshi tana faɗin"Am Sorry Ya rafayet zanyi biyayya,"

  Wurgi yayi da ita cikin ruwan Ruwan  tsulundum ta faɗa ciki,Kafin shima Ya daka suka ya faɗa ciki,Tare da janyota jikinshi,suka fiddo da kawunansu daga cikin ruwan,Sae faman haki take yi,natsuwa yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta,fuskokinsu sharkaf da ruwa,hakan ba ƙaramin kyau yayi masu ba,Hasken Electric bulbs ɗin dake a wurin sun haskakasu sosai,Babu kowa,dama babu mai zuwa wurin,Wannan swimming pool ɗin nasu ne musamman saboda jin daɗinsu,bashi kaɗai bane acikin gidan,Akwai wasu kusan guda biyu duk acikin gidan,

   "Reesh..."daƙyar ta iya buɗe idanuwanta akan fuskarshi,ruwan ya tsaya mashi adai dai stomach ɗinshi,ita kuma yakusa taddo chest ɗinta 

  Zuba ma juna ido sukayi Tamkar zasu haɗiyi junansu,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,fuskarta akwai light makeup,hada janbaki tashafa red colour,duk da ruwa Ya jiƙa fuskar hakan baisa kwalliyar ta goge ba,slowly ya zagayo da hannunshi asaman ass ɗinta Ya ɗaura tafin hannunshi,tare da janyota,Ya haɗe gabansu sosai tun suna kallon juna,har yakai ga Haɗe bakinsu wuri guda,sosai suke kissing ɗin juna,moving ya shiga yi da hannunshi acikin rigar jikinta,Martani  ta shiga mayar mashi tafara sarrafashi da hannuwanta,lokaci guda yabi ya ruɗe ya susuce mata,Zame hannun rigar jikinta yayi,Ya sabule ta,Zuwa waist ɗinta Yadda zaiji daɗin ganin komai muraran,Bakinshi yakai ya kama nipple ɗinta,Sosai ya shiga sucking ɗinsu,duk ta fita hayyacinta,a lokacin ta dawo da hannunta cikin sumar kanshi,ƙara ƙanƙameshi tayi sosai,cos she is enjoying it,a ruɗe take Ambaton sunanshi"ya rafayet"ƙasa yayi da kanshi can can,Yana bin ko'ina na jikinta,Yana licking ɗinsa,rurruƙeshi tayi sosai saboda yanayin daya jefata kamar tayi hauka,batasan lokacin data fashe da kuka ba,wuta sosai yake bata,lokacin daya ɗago komawa jikinta yayi,Ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta,yana mayar da numfashi,bata bari Ya gama mayar da numfashin nashi ba,Taso ma nata Salon,Zame mashi short ɗin jikinshi tayi,Tashiga sarrafashi,Ta gigitashi ya soma yi mata wannan sambatun nashi Aruɗe yake faɗin"keep!keeep!keeep doing it Reesh,You're giving me fire........."

Saida saukayi mai isarsu,Kafin suka dakata kowa Yana mayar da numfashi,sam idanuwansu sun gaza tsayuwa,Sae faman lumshewa sukeyi,a hankali Ya zura hannu cikin ruwan Ya janyo short ɗinshi Ya mayar,Ya ruƙo rigar jikinta,A hankali Ya janyo ziririn hannun rigar Ya mayar mata da ita,rungume juna sukayi sosai,A hankali Ya shirga furta"Reesh Allah yayi maki Albarka,daga ke ba ƙari,banga mace a duniyar nan ba,in bake ba,"kalamansa ba ƙaramin daɗi sukeyi mata ba,musamman idan ya sanya mata Allabarka,daɗi take ji sosai,

  "Allah ya faranta maki,Kamar yadda kike faranta mun,"

  "Ameen Yayana mijina,"

bacci sosai suke Ji su dukansu,So yake ya ɗauketa gashi Jikin nashi duk kasala ta baibayeshi,Daƙyar Ya tattara dukkan ƙarfinshi Ya sa6eta asaman kafaɗashi ya nufi stairs ɗin da zai kaisu kaitsaye Upstairs,part ɗinsu,Lokacin daya shigo da ita ɗakinsu ya sauketa,Shaf shaf suka Shirya kansu cikin Night dress ɗinsu Ash colour,Hannunsu ruƙe cikin na juna suka nufi ɗakin triplet ɗinsu,time din da suka shiga ɗakin,Basuyi mamakin ganinsu Little rafayet ba,Kallonshi tayi suka haɗa ido,Murmushi suka saki at same time 

  "Ina mamaki wannan al'amarin nasu,sunfiso su kwana cikin ƴan uwansu,ko tsoro basa ji,Su kwaso ƙwafa Don ma akwai haske ko'ina acikin gidan Shiyasa basa fargabar komai,"sehrish ce tayi maganar,

  "Ƙuruciyace da kuma Shaƙuwar dake tsakaninsu,nan da wani lokaci zasu daina ne,"yakai ƙarshen maganar tare shigewa cikin ɗakin itama tabi bayanshi,Agaban gadonsu suka tsaya suna ƙare masu kallo,

  "Yanzu wannan duk namu ne"?tayi tambayar tare da kallonshi"Are doubting"?girgiza kai tayi"a'a,Kawai tsabar farin cikine shiyasa na furta hakan,

   Ƙayataccen murmushi ya saki,kafin ya kuma cewa wani abu, sai ga Hosana ta faɗo ɗakin jikinta sanye da night gown doguwa,ta yafa mayafi akanta,juyowa su kayi atare suna kallonta jin shigowarta,

   Bayan tayi masu sallama suka amsata,sai ta tsaya shiru tana hangen little rafayet dake akwance saman gadon pretty,

   Murmushi sehrish tasaki"kinbiyoshi ne halan"?ɗaga mata kai tayi alamar eh,

  "Kawai na farka naga babu shi,daga ni har ya Omar bamusan lokacin daya fita ba,a tsakiyarmu muka kwantar dashi,Shi sarkin wayau hada sanya mana teddy a tsakiyarmu don kada muyi saurin gane ya fita,"

  Dariya sukayi gaba ɗayansu,Sgr Yace"its okey,kibarshi kawai tunda yafi so Ya kwana tare da ƴan uwansa,nan da wani lokaci zasu daina dakansu,"

  Jinjina kai tayi"shikenan,Sai Allah yakaimu,"

  "Mu kwana lafiya"juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin,murmushi sehrish tasaki,6ata ta6a tunanin irin wannan ranar zata zo ba,Yanzu hosana ta natsu,hankalinta ya dawo kan saiti,

  Ruƙo hannunta sgr Yayi"Bacci nake ji fa,"

  "Me too"

Kamar yadda suka Saba,Atare suka soma yi masu addu'a suna tofa masu ajikinsu,Bayan sun Ja masu lallausan blanket dinsu,ta Kashe masu hasken ɗakinsu,Hannunsu ruƙe dana juna suka koma bedroom ɗinsu,Saman katafaren gadonsu suka kwanta,yayi hugging ɗinta tighly,then Ya Janyo lallausar blanket ɗinsu Ya lullu6esu,

   Bayan komawar Hosana ɗakinsu,a zaune ta samu marshal daga shi sai short,

  "Ae dama saida na faɗa maki,"

Murmushi tasaki"ashe yana acan,Yaron nan yaci ka wayau,"

  Dariya yayi yana girgiza kai,Saman Gadon ta hau,Suka gyara kwanciyarsu rungume da juna,

  "Ya Omar"Ya amsa mata"Na'am My baby"

   "Kayi mun kalaman Soyayya mana kafin muyi bacci".  

  Gyara muryarshi yayi cike da zolaya yace"Yake akuyar dake cin ciyawar zuciyata"gaba ɗaya suka tuntsire da dariya,

*JunHad*

Tayi mamakin ganinshi zaune saman gadon,Ya jingina bayanshi jikin headboard ɗin gadon hannunshi ruƙe da hoton abbansu,ya ƙura mashi ido yana kallonshi ko ƙyaftawa baiyi,

  "My romeo,"ta ambaci sunanshi,batare daya juyo ba,Ya amsa mata"My juliet,"

  "Meyasa ka barni ni kaɗai"?

Murmushi ya ɗansaki"Am sorry,Yanzu nake shirin kwanciya,ina kallon Sanyin idaniyata ne"

  Miƙewa tayi ta zauna gefenshi,hannu takai tare da shafa fuskar Abba mai ɗauke da murmushi"Allah sarki Abba,we really missed you Ni da babyna,tayi maganar tana shafa sumar kan Junaid,

  "My Juliet"ya ambaci sunanta

 " na'am My romeo,"

"Idan su babban Yaya suka ajiye aiki zamu koma nigeria da zama,Ni nafison can,"

  "Nima nafison mu koma Nigeria,ba don bana jin daɗin nan ba,sai dan saboda ƴan uwanmu"acewar Jahad,

ɗaura hoton yayi a ma'ajiyarshi saman drawer,

  "Yaushe zamu ƙara samun baby"?

"Duk lokacin daka shirya,My doctor"

"Ae ni kinsan koda yaushe a shirye nake,ko yanzu ma,ko kina ganin wasa"?

  A'a,Na yarda da maganarka,Ae kai ɗin bana wasa bane tayi maganar tare dakai hannu ta ɗan bugi ƙirjinshi,murmushi yasaki"duk da haka bazan ƙyaleki ba,'tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,Yayi saurin haɗe bakinsu wuri guda,Ba halin Yin magana,Sosai ya ruƙota ajikinshi,Romancing ɗin juna sukayi kafin daga bisani ,Suka gyara kwanciyarsu rungume da junad,A ƙanƙame,

Wuraren sallar asuba,yana cikin bacci Yaji shessheƙar kuka acikin kunnanshi,Gabanshi ne ya faɗi,A hanzarce yakai hannu yana shafa gefenshi saman mattress,Jin  wayam babu ita Yasa ya ware idanuwanshi,Yayi mamaki Ganin babu Sehrish asaman gadon,Ga kuma shessheƙar kukan da yake ji acikin kunnanshi,saukowa yayi daga saman gadon,kaitsaye ƙwayar idonshi ta sauka akan ɗigon jinin dake a ƙasan tiles ɗin ɗakin,A jere jinin yake har zuwa toilet ɗinsu,Lokaci guda Hankalinshi Ya ƙara ɗunguma,A gigice Ya miƙe ya nufi toilet ɗin Yana faman ƙwala mata kira"Reesh!reesh!where are u"?Hannu yasa ya tura ƙopar toilet ɗin,Sai dai kash adatse take,ƙwaƙƙwaran naushi yakai ma ƙopar,ta buɗe Ya afka ciki a haukace,tuni idanuwanshi sun ciko tab da ƙwalla,Kwance ya hangota acikin bathtub ruwan dake acikin kwamin wankan ya gauraya da jinin dake ajikinta,Alamu sun nuna cewa ta jima Da mutuwa,hawayene suka wanke mashi fuskarshi,Sam Ya kasa ƙarasawa cikin toilet ɗin,Zubewa Yayi asaman guiwowinshi,sosai ya fashe da kuka,fuskarshi tayi jaga jaga da hawaye,sam bazai iya jure rashinta ba,Zuciyarshi barazanar harbawa take yi,Jiya jiyan nan suka sha soyayya da daddare gashi yau Ya wayi gari batare da ita ba,ashe dama na bankwanane sukayi"?

Runtse idanuwanshi Yayi sosai,Kafin Ya buɗesu a hankali,zurfin tunani ya shiga,Ƙura ido yayi yana kallon ɗagon jikin dake a gabanshi,Yatsanshi yakai tare da dangwalo jinin Yana kallonshi,Kokwanto ya shiga Yi Kamar ba Jini ba,Sam babu ƙarnin jini Ajikinshi,Azafafe Ya miƙe ya ƙarasa shiga Toilet ɗin,Ya tsaya gaban Bathtub ɗin yana kallonta,cike da saran abunda yake zargi,

  Muryarshi na kerma Ya ambaci sunanta"Reesh...."shiru bata motsa ba,Almost 3 times Yana Calling Name ɗinta bata amsa mashi ba,jikinshi yayi sanyi sosai,dagasken dai ta mutu,Ya rasa reesh ɗinsa 

  Girgiza kanshi ya shiga yi la66ansa na kerma Ya shiga faɗin"Reesh why kika barni,Meyasa mutuwa zatayi mun yankan ƙaunane,wlh bazan Iya rayuwa batare dake ba,Zan kashe kainane,"A hanzarce Ya juya Ya fito daga toilet ɗin,jikinshi Na kerma Ya nufi bedside drawer ya ɗauko bindiga,cikin kunnanshi Ya saita bingidar Tare da rufe idanuwanshi,yana karanto kalmatusshahada,Sam batayi tunanin Sgr zai Iya aikata abunda Ya faɗa ba,da gudun gaske Ta fito daga cikin ƙwamin wankan daga ita sai undy data ja har zuwa saman ƙirjinta,tana ƙoƙarin buɗe ƙopar toilet ɗin Tajiyo ƙarar fitar bullet,Wata irin gigitacciya ƙara Sehrish tasaki,tana fitowa Ta same shi baje a ƙasa,jini duk ya wanke fuskarshi,Fashewa tayi da matsanancin kuka,A sukwane ta zube saman guiwowinta

  "Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya rafayet!ka tashi!Nifa wasa nake maka Wlh ban mutu ba Wayyo Allah nashiga uku,Na bani Na lalace,gaba ɗaya tabi ta rikice Ta ruɗe,hannunta duk ya 6aci da jininsa,jijjiga shi tadingayi tana kuka kamar ranta zai fita,a ƙarshe ta rungumeshi tana kuka,ta tsorata sosai,daga wasa tayi silar mutuwar masoyinta,sai da ta jigata sosai,duk ta fita cikin hayyacinta,Sautin dariyarshi data dinga jine yasa ta yin saurin ɗagowa Tana kallon fuskarshi,Zazzare idanuwanta tayi akan fuskarshi,Ganin Yana ta faman tiƙar dariya,ya buɗe idanuwanshi sosai,

  Daƙyar ya samu ya tsagaita da yin. Dariyar yace"Reesh ke kika iya tsara drama irin wannan balle ni da nake soja?I can do better than u,'

  Fashewa ta kumayi da matsanancin kuka Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Meyasa kayi mun haka Ya rafayet!Nifa wasa nake maka,"

  Jifa mata harara yayi"haka ake wasa a gidanku?waya gaya maki ana wasan mutuwa?ko shima duk cikin Soyayyarne?da ace tunfarko ban gane so6o bane kika sanya me kike tunanin zai biyo baya,Zuciyata har kusan bugawa tayi lokacin da naganki kwance cikin jini,

Kowannansu Yaji jiki,

Sosai take kuka"Wlh bazan Yarda ba,Ya rafayet Ka tsoratar dani"tayi maganar muryarta na kerma,

  "So6on da kikayi amfani dashi kika ajiye bottle ɗin Saman fridge dashi nayi using na kwararama Kaina," Still  hawaye basu daina zuba akan fuskarta ba,har wani zazza6i take ji ajikinta,

Kafeta da ido yayi yana kallonta,Kamar wata ƙaramar yarinya,kowa ya bata shawarar tayi mashi irin wannan wasan,

  "Naji tsoran na rasaka,"tayi maganar ashagwa6e,

  "In har zaki cigaba dayi mun irin wannan wasan to kuwa tabbas wata rana zaki rasa nine,"

   Fashewa ta kuma yi da wani kukan  Sosai ta sanya mashi rigima,tana faɗin Wlh bazan  yarda ba,Ae ni ba haka nayi maka ba,ka tayarmun da hankalina......"

  Cikin sanyin murya Ya bata hakuri"Am really sorry,"

  Girgiza kai tayi"a'a Bazanyi haƙurin ba,"miƙewa Yayi daga zaune"Yanzu me kikeso nayi maki?wanda zaisa ki yafe mun,"

   "Frog jump"ashagwa6e ta bashi Amsa,

   Zaro Eyes ɗinshi Yayi "Frong Jump"?Ya maimaita abunda tace,

  Ɗaga mashi kai tayi"Eh shi nakeso kayi mun,"

   "Zanyi kneeling agabanki,In baki haƙuri"

   Bubbuga ƙafafunta Tayi"idan ba zakayi Tsallen kwaɗi ba,ni bazan haƙura ba......."

   Ganin Ya tsareta da ido Yasa ta Fashe da wani sabon kuka Hawaye duk suka wanke fuskarta,A ruɗe Sgr ya Zuƙunna tare da kama kunnuwanshi,

"Can zaka tafi,idan kakai saika dawo nan,"da hannu take nuna mashi inda zaije,Bakinta ƙumshe da dariya,Sam bai kawo komai aranshi ba,Ya soma Yin tsallen kwaɗi ya nufi inda ta nuna mashi Ya juyo Ya nufo inda take,

  Tuntsirewa Sehrish tayi da dariya Tare da buga tsalle Tana faɗin"Na rama !Na rama!"

   Abun ya ɗaure mashi kai,Sakin kunnuwanshi Yayi tare da miƙewa tsaye yana kallonta,Tsantsar farin ciki Ya gani akan fuskarta,Kamar wadda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,A ruɗe yace"Reesh are u ok"?

   "bakaine kake sanyani Yin tsallen kwaɗi ba,lokacin  da muna a gida?Yau nima Na rama,Na sanya Surgeon General Rafayet Tsallan kwaɗi,",tana  kai ƙarshen Maganar,Ta watsa da gudu Ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi Tana dariya,

 "Ke ko"?ya faɗi hakan fuskarshi ɗauke da ƙayataccen Murmushi,Abun ma dariya ya bashi,Wai ta rama,Ashe abun ya tsaya mata aranta,kamar zautacciya Haka taci gaba da dariya tana faɗin "I luv u Ya rafayet!Mijina nakaina"

   "I luv u too,matata takaina,"ya amsa mata cikin so da ƙauna..............." 

    💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃*HAPPY ENDING*

*💋Boss Bature💋


1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post