An sayar da mitsitsiyar jakar da ido ba ya ganin yadda take kimanin Naira 50m

An sayar da mitsitsiyar jakar da ido ba ya ganin yadda take kimanin Naira 50m

An sayar da mitsitsiyar jakar da ido ba ya ganin yadda take kimanin Naira 50m
MSCHF/BBC

An sayi wata 'yar mitsitsiyar jakar hannu "da hankali ba zai ɗauki ƙanƙantar ta ba" a kan $63,750 kimanin naira miliyan hamsin a wani gwanjo da aka buga.

Ana buƙatar na'urar ƙara girman abu don ganin ƙirar jakar, wadda ido ba zai iya fayyacewa ba.

"Ƙanƙantarta ya kai yadda za ta iya wucewa ta ƙofar wata allurar. Jaka ce 'yar mitsitsiya da sai an yi amfani da na'urar ƙara girman abu wato microscope kafin a iya ganin ta," kamar yadda cibiyar adana kayan fasaha da ta saƙa jakar ta ce.

Cibiyar adana kayan fasaha MSCHF mai sansani a Brooklyn, ta yi suna da saƙa kayayyaki masu janyo ka-ce-na-ce.

Cikin kayan da cibiyar ke adanawa, har da takalman da suka ƙunshi jinin mutum da wasu takalman kambas ɗauke da wani nau'in turare a ƙasan shimfiɗarsa, turaren na da ƙamshi kamar na sinadarin feshin WD-40, da kuma wani ƙaton takalmin roba.

A wannan karo, cibiyar ta yanke shawarar ta ƙure duk wani yayi na jakunkunan hannu da aka taɓa saƙawa.

"Akwai manyan jakunkunan hannu, da matsakaita, sannan akwai ƙananan jakunkuna, amma wannan ce ƙarshe idan ana maganar ƙanƙanuwar jakar hannu," Cibiyar MSCHF ta faɗa a wani saƙo da ta wallafa.

Siffofin jakar alfarmar sun haɗar da tambarin kamfanin kayan ƙawa na Louis Vuitton, amma dai jakar ba ta da alaƙa da kamfanin.

An saƙa jakar ne da wani nau'in leda da aka yi ta da ƙaro kuma aka yi amfani da fasahar buga kaya ta tiridi (3D technology) wadda sau tari ake ƙirƙirar kayayyaki 'yan mitsi-mitsi da ita.

Da ake saƙa jakar, wasu samfuran jakar 'yan ƙanana da aka aika wa masu nazari don yin bita, sai da suka ɓata saboda tsananin ƙanƙanta a tsakanin jami'an Cibiyar MSCHF, kamar yadda mujallar Smithsonia ta ba da rahoto.

Sai dai fargabar ɓatan jakar, ba abu ne da ya kamata ya zama abin damuwa ga sabon mai mallakar jakar ba, don kuwa ana haɗa jakar da na'urar ƙara girman abubuwa a cikin tarkacen da aka sayar da ita. Ana iya sayen na'urorin ƙara girman abubuwan dijital daga kantunan intanet kuma farashinsu na farawa ne daga $60 har zuwa $1,000.

Ana iya ganin fasalin ƙirar jakar da zarar an yi amfani da na'urar ƙara girman abubuwa ta microscope.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post