Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 102

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 102

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 102
AIHausa Novels

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

   Kasa ɗagowa yayi daga kan  ƙabarinsa,

  Marshal Omar ne ya ɗaura da cewa"In sha Allah junaid na aljanna,muna yi mashi kyakkyawan fata,Allah yasa ƙarshen wahalarshi kenan,"gaba daya basu ji daɗin irin yadda mutuwar junaid ta kasance ba,kamar wani mara gata,babu mahaifinshi akusa babu ƴan uwanshi,

  Ruƙo hannun Sgr major yayi,tare da janyoshi,jikinshi duk ya saki,daƙyar ya iya mikewa ya tsayar da kanshi akan ƙafafunshi,

  Sojojin dake kewaye da wurin sunyi su 50,Layi sukayi wani na bin wani,kowa yazo wurin ƙabarinsa sai ya tsaya ya tottafa mashi addu'a kafin ya wuce,Na bayan shi yazo shima yayi mashi addu'a a haka har suka kammala,ba tare da mutane sun samu damar tsayawa ganin abunda ke faruwa ba,dama kuma hanyar sam ba mutane sosae.

   Basu bar ƙabarin junaid a fili ba,saboda gudun kada mutane su dinga tattake wurin batare da saninsu ba,ko su zauna abakin bishiyar,waya suka sa suka kewaye bishiyar,


Sun jima a awurin cike da jimamin mutuwar junaid,kafin wani lokaci suka shige motocinsu suka tafi ba don sunso ba,Kuma duk da haka sai da Sgr ya sanya sojoji guda biyu suka tsaya a wurin,batare da uniform ajikinsu ba,


    *RIJF BABY JUNAID*


*Boss Bature*


Wuraren ƙarfe 5:30 na marece,

Slowly motocinsu suka shiga cikin gidan,Bayan sunyi parking ɗinsu Major ya buɗe masu mota,don atare suka zauna shi da Sgr a motar Omar,kowa jiki babu ƙwari haka suka fito daga cikin Motar,kaitsaye suka nufi ƙopar shiga falon,


A lokacin hosana na zaune saman Sofa,duk ta takure kanta,tun da tafarka daga bacci take ta faman yin sintiri acikin gidan tana jiran dawowar Omar don ta faɗa mashi abunda haroon yayi mata,


Jin motsin shigowarsu yasa tayi saurin miƙewa jiki na rawa ta tunkareshi zata rungumeshi,

Da hannu yayi mata alamar karta matso kusa dashi,fuskarshi babu annuri,har cikin ranta bata ji daɗin abunda yayi mata ba,har gaishe dasu tayi amma babu wanda ya kulata,acikinsu,

  Upstairs suka wuce atare,kowa ya nufi part ɗinsa,komawa hosana tayi saman sofa ɗin tana kuka,abun ya ƙona mata rai,Yadda Omar ya dakatar da ita don karta ta6a shi,

  Faɗawa yayi saman gadonshi yayin da idanuwanshi ke fuskantar Ceiling,Fuskar Junaid ya dinga ganin tana yi mashi gizau,ji yake tamkar abunda ya faru mafarkine ba gaskiya ba,saboda wani sashe na zuciyarshi na raya mashi cewa Junaid yana raye bai mutu ba,Yayin da wani sashen na zuciyar tashi ke gasgata mashi mutuwar junaid,runtse idanuwanshi yayi Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi daurewa kawai yake yi,ya jima a haka idonshi na kallon sama,kafin daga bisani ya miƙe tare da faɗawa toilet bayan ya rage kayan jikinshi,


Kwance yayi tsulundum acikin jacuzzi (kwamin wanka)wanda ke kewaye da glass,da niyyar yin wanka ya shiga toilet ɗin,Amma sai kasala ta baibayeshi ko yatsan shi ya gaza ɗagawa,abubuwa sunyi mashi yawa,tunda yake a rayuwarshi bai ta6a fuskantar mummunar rana irin wannan ba,da ace mutuwa hutu ce agareshi da ba abunda zai hana ya roƙi Allah akan ya ɗauki ranshi ya huta,Yaci alwashin saiya ga bayan waɗanda suka kashe junaid,Alƙawari ne ya ɗaukarwa kanshi,Ko bacci bazai ƙara yi ba,in har bai ɗaukarwa junaid FANSA ba,kamar yadda Sgr yaci Alwashin ɗaukar fansa haka shima Omar ya ɗauka,


Kasa jurewa yayi saboda kukan da hosana ke raira mashi ta la6e a ƙopar dakinshi batasan halin da yake ciki ba,

  "Hosana,"ya ambaci sunanta,muryarshi a kasalance,

  Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"

  "Zonan,"

Hannu tasa ta tura ƙopar tare da shigewa ciki,Kwance ta same shi saman gadonshi,Ya baje daga shi sai short,kallo guda zakayiwa fuskarshi ka gane cewa yana acikin matsanancin tashin hankali,

  har Saman gadon hosana ta hau ta zauna tana kallonshi,lokaci guda ta dakata da yin kukan nata,Ganin dry tears asaman fuskarshi,nan fa hankalinta ya tashi sosai,

  "Ya omar,hawaye akan fuskarka?meke damunka ya Omar,Ban ta6a ganin hawayenka ba,Sae yau,"

  A hankali ya bude idanuwanshi da sukayi jawur dasu yana kallonta yace"Hosana,ki taimaka mun kaina kamar zai fashe,Ina cikin matsananciyar damuwa,Zuciyata raɗaɗi take yi mun,pray for me hosana kona samu sauƙi acikin zuciyata,

  Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,hannayenta ta sanya tana kokarin janyo shi hakan yasa ya dan matso daura kanshi tayi saman laps ɗinta,Addu'o'i ta shiga karantowa tana tottafa mashi asaman fuskarshi,shafa sumar kanshi ta shiga yi,tana cewa"Ya Allah ga bawanka nan,kai kaɗai kasan meke damunshi,Ya Allah ka yaye mashi damuwarshi,Ka sanyaya mashi zuciyarshi,Alfarmar Annabi Muhammadu (S.A.W),

  Ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai ya gyara kwanciyarshi sama sama bacci ya fara ƙoƙarin daukarshi,

Yana jiyo muryarta tana tambayarshi Ko zaici abinci ta kawo mashi,

   Daƙyar ya iya amsa mata da cewa"A'a hosana,bana iya cin komai yanzu,"

  "Shikenan ya Omar ɗina,kayi baccinka kawai,zanci gaba da yi maka addu'a,har ka farka,"

   Shafa sumar kanshi taci gaba da yi,tamkar jinjiri haka ta dinga treating ɗinsa har bacci yayi awon gaba dashi,Yau hosana tayi mashi abunda bai ta6a tsammani ba,Ta bashi kyakkyawar kulawa kamar ba wannan mai ta6in hankalin ba,wani iko na Allah ta so sanar dashi damuwarta,amma tunda ta gane cewa baya a hayyacinshi,Sae kawai ta fasa sanar dashi.


*Tashin Hankali!"


Jin dirar motoci acikin gidan yasa shi yin firgit ya farka,tare da yunƙurawa ya miƙe zaune,Hosana ya gani kwance tana bacci,asaman gadon ya ɗauketa,

  Jiki na rawa ya saukko daga saman gadon ya samu jallabiya ya zura ma jikinshi ya bude ƙopar dakinshi da sauri ya nufi downstairs,Tunkan ya ƙarasa ya jiyo Muryar Abbansu yana ƙwalama Junaid kira,ko sallama baiyi ba,Burinshi kawai yayi tozali da junaid,

  "Hasbunallahu wani'e mal wakil"ya furta hakan tamkar zai fashe da kuka,

  Yana cikin wannan yanayin sai ga Sgr shima ya fito daga part ɗinsa,jikinshi sanye da jallabiya shima,kallon juna suka yi kowa fuskarshi ayamutse take,

   "Daga shigowarshi ko sallama baiyi ba sunan junaid kawai ya ambata,yanzu yaya zamuyi dashi'?omar ne yayi maganar tare da kallon Sgr dake tsaye a gefenshi,

   "Yanzu ya dawo yana buƙatar ya huta,yakamata muyi ƙoƙari wurin ganin mun daidaita natsuwarmu,if not za'a samu matsala ne,"


Shigowa cikin falon suka karasa yi,Abbansu ne sai Mommynsu,tare dasu twins,fawan gaba ɗaya matasan gidan sun dawo,hada kanal yousouf su irfan da sauransu,Banda gwaggon katsina suma sun shirya dawowa tare dasu Ammi,zasu zo daga baya,


Agajiye suke kowa ya samu wuri saman Sofa ya zauna,Abba kuwa jiki na rawa ya wuce upstairs,su Sgr najin takun takalminshi hankalinsu ya ƙara tashi,Yana tafiya yana ƙwalawa junaid kira,

  "Junaid!Junaid!where are you?Ur dad is back,Nayi missing ɗinka sosai...."

   

Bai ƙarasa maganar ba,ganinsu Omar atsaye,cirko cirko,ƙaƙaro murmushi suka yi gaba dayansu suka tunkareshi,Sgr ne ya fara yin hugging ɗinshi,Daddy I really missed you,Ya gajiyar tafiya?ya ƙarasa maganar tare da ɗagowa daga jikinshi,Bai amsa mashi gaisuwar tashi ba,yace"Yaushe ka dawo Abuja?ko kun dawo ne'?

   "A'a daddy,Wani uziri ne ya kawo ni,Amma zan koma kano ɗinne,"wani kallo da yaga Abbansu na binshi dashi yasa ya ɗan sha jinin jikinshi,

  "Abba sannu da dawowa,"Omar ne yayi maganar,wurga idanuwanshi yayi akan fuskar Omar,aɗan ruɗe yace"kunyi rashin lafiya ne?meke faruwa ne?naga fuskokinku duk sun kumbura,fuskar Rafayet tayi jawur da ita,kaima haka...."

  Da sauri Omar yace"Am...Abba..I know u are tired,kana buƙatar hutu,yakamata muje bedroom ɗin ka Inyi maka tausa,"

  Harara Abban ya ɗan watsa mashi tare da cewa"a ƙule nake dakai Omar,ina ta nemanka jiya,ka tashi ka kashe mun waya hmmmm..."yana kai ƙarshen maganar ya soma ƙoƙarin wuce wa ciki,Saboda tsabar ruɗu Sgr baisan sa'adda ya tarboshi da hannunshi,Zuba ma hannun nashi ido Abbansu yayi,fuskarshi ɗauke da mamaki yace"Rafayet,lafiyarka kuwa?cikina fa ka tarbe,"

  Zame hannunshi yayi tare da ɗan sosa ƙeyarshi yace"Am sorry Daddy,pls u need a rest,mu sauka down ka huta mana,ka kwaso gajiya,inaso na baka abinci kaci ka huta,Omar zaiyi maka massage ka ɗan ji daɗin jikinka,

  Cike da mamaki Abbansu ke kallonshi,"Rafayet!yau kaine da kanka kake zancen zaka bani abinci a baki na naci?Omar kuma zai yi mun tausa,sae kace wani ƙaramin yaro,"gyaɗa kanshi yayi tare da cewa"Naji toh,Amma saina fara zuwa ɗakin Junaid,idan nadawo sai mu je ɗakin nawa,"yana kai ƙarshen maganar ya wuce tare da nufar ɗakin Junaid yana ƙwala masa kira,

  Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,A hankali Abba ya tura ƙopar ɗakin junaid ya shiga daga ciki,Wayaam yaga babu kowa aciki,Bai kawo komai aransa ba,saboda ƙarar saukar ruwa dayaji a toilet,hakan yasa shi tunanin ko ya shiga wanka ne,ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya fito daga ɗakin,da niyar idan ya huta zai dawo wurinshi,don yau atare yake son su kwana dashi,


Koda suka yi arba da Abbansu yana nufosu sai kowannansu ya shiga ƴan kame kame,fargabarsu kada ace zai tambayesu ina Junaid ya ke,.  

   Tunkan ya ƙaraso wurinsu suka ji yace"Ashe ya shiga wanka ne,idan ya fito daga wankan pls ku sanar dashi cewa nadawo kuma inason ganinshi,a bedroom ɗina,"

  Atare suka haɗa baki wurin cewa"Toh Abba"


Saukowa down sukayi atare da abban yana gaba suna a bayanshi,Sae faman sauke ajiyar zuciya suke yi,


Lokacin da suka sauko down,Su kanal Yousouf na ganinsu kowa ya miƙe fuskar nan ɗauke da farin ciki,Yayin da su kuma kowannansu ya dabarbarce,

Daƙyar suke gaisawa da ƴan uwan nasu,kowa ya lura da yanayinsu shiru kawai su kayi,Su fawan sai tambayar Junaid suke yi,Yana ina?basu ganshi ba,amsa daya suke basu ta yana a cikin toilet yana wanka,Duk wanda yaje ɗakin Junaid yaji sautin saukar ruwa daga cikin toilet,sai yayi tunanin cewa wanka yake yi,Ashe fanfo ne Aka bari a kunne ba'a kashe ba,

   Daƙyar suka samu kowa ya haƙura da ganin junaid,Omar yace su wuce ɗakunansu kowa yaje ya huta,an kwaso gajiya,

  "Nifa ban yarda dasu babban yaya ba,Shi da ya Omar akwai wani abu da suke 6oye mana Allah,"Acewar Jahan,

A yayin da suke shiga bedroom ɗinsu,

  Ayaan yace"nikaina na lura da hakan,musamman faces ɗinsu,kamar sunsha kuka Allah,Gaskiya hankalina bazai kwanta ba,sai naga junaid,ni ban yarda wanka yake yi acikin toilet ba,"

  Jahan yace"mu bari mu huta,Zuwa dare sai muje ɗakin nashi,nasan lokacin idan ma wankan ne ya gama,"

  Ƙarasa shiga cikin ɗakin sukayi,kowa ya shiga rage kayan jikinshi,Jahan ne ya fara shiga waka,Ayaan ya zauna gefen gadon yana jiranshi ya fito shima ya shiga wankan,

   A can falo kuwa,Mommynsu ta tsare Sgr da Omar,Tasa su gaba tayi tana binsu da kallo one by one,dama bakowa Sgr yafi ji ba fa ce Mommynsu,tana da wuyar sha'ani,

  "Mommy,"Sgr ne ya ambaci sunanta,

bata amsa mashi sunan nata daya kira ba,sai cewa tayi"you didn't answer my question,It seems like you are hidding something for us!Rafayet where is junaid!kada kuyi mun ƙarya nasan ba halinku ba ne,just ku faɗamun Gaskiyar abunda ya faru,"

  Murya na rawa Omar yace“Am..mommy,Junaid fa yana a toilet yana wanka zai fito ne...m"daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da take yi mashi,kallon tuhuma,kallon ban yarda dakai ba 

"Wai taya za ku ce mun junaid yana wanka?Nifa ba ƙaramar yarinya bace,balle kuce zakuyi mun wayau,tun daga kan fuskarku na gane cewa akwai wani abu daya faru dashi...."

  Saussauta muryarta tayi,sannan taci gaba da magana"pls idan wani abu ne ya faru da Romeo ɗina ku sanar dani,i will accept it,"yadda tayi maganar yasa su kaji jikinsu ya ƙara mutuwa,

  "Am listening to u guys,ku faɗamun meya faru dashi ya mutu ko"?

  Gabansu ne ya faɗi rass!da sauri Sgr ya ruƙo hannunta muryarshi na kerma yace"Mommy dan Allah kiyi haƙuri,ki rufa mana asiri,I will explain to u mu shiga daga cikin bedroom ɗin..."

  "Rafayet,meyasa zaka sanar da ita"?Omar ne yayi maganar fuskarshi a yamutse,

  "To ya kakeso nayi Omar,Mommy bazata ta6a yarda ba,kwara kawai mu faɗa mata gaskiyar abunda ya faru,Ka wuce wurin Daddy,ni zanji da Mommy,'

  Ya ƙarasa maganar tare da jan hannunta,Suka wuce upstairs bedroom ɗinshi,

  Ajiyar zuciya Omar ya sauke,Ya jima atsaye yana tunanin Yadda zasu ƙare da Abbansu,tsoranshi kada farat ɗaya zuciyarshi ta buga idan yaji cewa Anyi garkuwa da junaid kamar yadda suka tsara,

  "Omar,lafiya kuwa,"firgit ya ɗanyi tare da kai idanuwanshi wurinta,Azmee ta nufo shi,Ganinshi a tsaye kamar akwai damuwa atattare dashi,

  Dakyar ya ƙaƙaro murmushin yaƙe yace"bakomai,"

    "Omar,dama inaso na tambayeka ne,Wai ina junaid ne?tun jiya da suka fita shi da jahad shiru har yau basu dawo ba,nashiga damuwa sosai akan rashin ganinsu,har cewa yayi idan suka je shan ice cream zaiyi min tsaraba," ta ƙarasa maganar tana kallonshi,

  "Aunty Azmee,bazan iya 6oye maki ba,Junaid da jahad anyi kidnapping ɗinsu...."jin wannan maganar yasa Azmee ta dafe ƙirjinta da ƙarfi,idanuwanta suka firfito waje,hankalinta yayi mugun tashi,

  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"kusan sau biyar tana maimata kalmar,

   siraran hawaye ne suka soma saukowa saman cheeks ɗinta,ji tayi tamkar bazata iya ɗaga ƙafafunta ba,saboda nauyin da sukayi mata,

  "Junaid da jahad suna buƙatar addu'armu Azmee,"acewar Omar,

  Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Nashiga uku!Yanzu junaid da jahad aka ɗauke mana...."

Katse ta Omar yayi'pls Aunty azmee,ki daina ɗaga sautin muryarki,na faɗa maki ne don ki taimaka mana,Wurin kwantar da hankalin sauran mutanen gidan nan,Mun shiga damuwa sosai,saboda gudun halin da zasu shiga,musamman mahaifinmu...."

  Cikin shessheƙar kuka tace"Ya Allah ga bayinka nan!ka tsare manasu a duk inda suke,Ya Allah ka ku6utar dasu daga hannun azzaluman da suka yi garkuwa dasu,wannan wata irin masifa ce......"kuka ne yaci ƙarfinta,da gudun gaske ta juya tare da tunkarar kitchen,zama tayi ta dingi kuka kamar ranta zai fita,gani take yi kamar zasu rasa su ne,Ta ƙwallafa rai akan junaid,tana jinshi tamkar ɗan cikinta saboda ta shayar dashi,baiwar Allah,

  Jiki asanyaye Omar ya wuce bedroom ɗin Abbansu,tsaye ya same shi har ya zura kayan bacci ajikinshi,ta cikin mirror ya hango Omar,juyowa yayi fuskar shi ɗauke da murmushi yace"halan junaid ya fito daga wankan ne"?yayi tunanin abunda ya kawo shi ne,

  "Abba,me kake buƙata na kawo maka"ya tambaye shi ne don ya kawar mashi da tunanin Junaid aranshi 

Murmushi Abba yayi tare da cewa"Sannu Azmee,Yau kaine ka kar6i aikinta kenan"?

  Duk da halin daya ke ciki na fargaba sai da ya ɗan murmusa,jin abunda abban yace,

   "No,kawai inaso na baka kyakkyawar kulawa ne saboda nayi kewarka,ka fara faɗamun abunda kakeso sai in kawo maka,"

  Murmushi Abba ya ɗan yi kafin yace"shikenan,junaid nake son gani ka kawo mun shi,idan ma ya fara bacci ka ɗauko mun shi,ina jiranka,"ya ƙarasa maganar tare da samun wuri gefen gadonshi,yana kallon Omar da yayi mashi zuru da ido,

  "Omar,lafiya ka zubamin ido kana kallona'?

  "Babu komai Abba,bari na ɗauko maka junaid ɗin,"yayi maganar tare da juyawa yabar ɗakin,Zaman jiran dawowarshi Abba yayi,sai faman sakin murmushi yake yi,harya ƙosa Omar ya ɗauko mashi Baby Junaid ɗinshi,


A 6angaren Omar yana fita daga bedroom ɗin abban nasu,kaitsaye kitchen ya wuce,Anan ya samu azmee zaune saman kujera tana ta matsar kwalla,

"haba Aunty azmee,meyasa zakiyi mun haka?Addu'a yakamata kiyi masu akan Allah ya bayyanar mana dasu,kukan da kike yi bazai amfane su ba,"

  Zame hannuwanta tayi daga saman fuskarta,idanuwanta sunyi jawur dasu luhu luhu,

  "Omar,ba zaka gane bane,dole inyi kukan rashin su junaid,ko ka manta shakuwar dake tsakanina dashi ne'?

  Shiru omar yayi yana kallonta,Allah yaso bai sanar da ita gaskiyar abunda ya faru ba,da baisan abunda zai biyo baya ba daga gareta itama,

Lallashinta ya shiga yi har ya samu ta saukko,Tsayawa yayi ta shirya mashi dinner asaman tray,ya kar6a ya wuce ɗakin Abbansu,ita kuma ta shiga ɗaukar kayan abincin da ta shirya masu tana kaiwa dining,Lokacin da Omar ya koma bedroom ɗin Abbansu,yana shiga ciki Abbansu yaga tray a hannunshi sai ya ɗaure fuskarshi tare da cewa"Nifa ba yunwa nace maka inaji ba,Junaid nace ka ɗauko mun,"

  Saman table omar ya ajiye tray din tare da samun wuri gefenshi ya zauna,ruƙo hannayenshi yayi tare da sassauta muryarshi

   "Abba pls,kaci abincin ka ƙoshi,idan ka kammala zamuyi magana dakai,"

  Shiru yayi yana kallonshi kamar mai nazarin wani abu yace"Shikenan zuba mun abincin naci,Allah yasa naji alkhairi,"

Serving ɗinshi Omar ya soma yi,sosai yaci abincin bayan ya gama da abincin,Omar ya tsiyaya mashi Lemu me sanyi a cup,yasha,

  "Yanzu ina sauraronka,wata maganace zamuyi,"

  "Abba ko zaka ɗan kwanta ne?ina ga kamar hakan zaifi,muna magana inayi maka tausa,"

  Abun ya daurewa Abbansu kai,gyara kwanciyarshi yayi saman gadon sannan yace"ina sauraronka toh,"

  Hawa saman gadon Omar yayi,A hankali ya fara yi mashi massage ɗin kafarsa,

   A tsanake ya soma magana"Abba dama game da junaid ne,nasan ka yarda dani sosai,kuma zaka fahimce ni ne,

  Tunda ya ambaci sunan Junaid,Abba ya miƙe daga zaune da sauri yana kallonshi

  daurewa Omar yayi tare da cigaba da cewa"mun shiga matsananciyar damuwa Abba,idan ka lura da fuskokinmu duk sun sauya saboda tsabar tashin hankalin da muke ciki...."dakatar dashi Abba yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu,

   "Ka fito fili ka faɗamun ainihin abunda ke faruwa Omar,sai 6oye 6oye kake yi mun,dama ni tuni sai da raina ya bani cewa wani abu ya faru da junaid,dan Allah ka sanar dani!ina ɗana yake"?hankalinshi atashe yayi maganar,

  Cike da fargaba Omar ya ɗaura da cewa"Abba,junaid yana cikin ƙoshin lafiya,sai dai baya atare damu,Jiya bayan fitarsu shan ice cream tare da jahad,kidnappers su kayi garkuwa dasu,bana so ka tashi hankalinka Abba,Ni nayi maka alƙwarin zan dawo maka da ƴa'ƴanka,cikin ƙoshin lafiya batare da sun samu koda ƙwarzane ajikinsu ba....."duk wannan surutan da Omar keyi baisan cewa Abbansu ya jima da sumewa ba,tunda ya ambaci sunan kidnappers sunyi garkuwa dasu,Bai ƙara sanin inda kanshi yake ba,

  "Abba!"ya ambaci sunanshi,yayin da yake kallon fuskarshi,Hannu yasa tare da dafe goshinshi,Dama saida ranshi ya bashi cewar hakan zata iya faruwa,

  Idanuwanshi ne suka cuccuko da kwalla,kamar ya fasa ihu haka yake ji,ta ko'ina babu sauƙi,dirshan ya zauna saman gadon fuskarshi a yamutse,ya zuba ma Abban nasu ido yana kallonshi,


Adai dai Lokacin Sgr ya shigo bedroom ɗin tare da Mommynsu,tasha kuka duk da irin juriyarta,daƙyar ya samu ya shawo kanta,shima ɗin don yayi mata alƙwarin cewa zai dawo mata da ɗanta har gida ba tare da komai ya same shi ba,jin motsin shigowarsu yasa Omar waigawa yana kallonsu,har suka ƙarasa shigowa wurin gadon,Gefen gadon Sgr ya zauna,Mommy ta tsaya daga tsaye tana kallon Abba dake a zaune ido rufe,

  "Omar,ka faɗa mashi ne"!?ɗaga mashi kai Omar yayi alamar eh,Ya kuma cewa"ko ya samu bacci ne"?

  Girgiza kai yayi tare da cewa"a'a,taya zan faɗa mashi wannan tashin hankalin yayi bacci?Kaima ka sani,tun kafin ma na ƙarasa sanar dashi ya sume a zaune,Na rasa abun yi ne shiyasa nayi zugum ina kallonshi,

  Miƙewa Sgr yayi da sauri ya fuce daga ɗakin don ya ɗauko masu ruwan da za'a yayyafa mashi,

  "Mommy,dan Allah ku ƙara haƙuri akan 6atansu junaid,in sha Allah we will try our best don muga mun dawo dasu cikin gidan nan,"

Jinjina kai tayi "Na yarda daku Omar,Nidai burina ku dawo mun dasu cikin gidan nan,Na tambayi Son game da kidnappers ɗin ya sanar dani cewa,Sau ɗaya suka kira waya,Kunyi magana dasu kuma har sun baku Junaid kunyi magana dashi,Naso ace sun bar wata kafa da zatasa ayi tracking layinsu,Amma kashe yace mun Sun kira da hidden number ne,abunda nakeso naji shi ne,basu buƙaci adadin kuɗin da suke so ba?ni koma nawa ne zan bada a kar6ominsu,"

  Jikin Omar ba ƙaramin sanyi yayi ba,gwanin ban tausayi haka yake kallonta,Aransa yana ayyana irin tashin hankalin da zata shiga idan taji cewa,Junaid ya mutu ta hanyar take shi da mota,

  "Omar kayi shiru baka ce komai ba,"ta jifa mashi tambayar,tana kallonshi,

  Girgiza mata kai yayi"A'a Mommy,basu buƙaci komai ba yanzu,Sun sanar damu cewa,Zasu tuntu6emu idan buƙatar hakan ya taso,kuma sunyi warning ɗinmu,kada mu kuskura muyi gigin yin investigation akansu,if not zasu illatasu ne,shiyasa bamu yi wani yunƙuri ba ayanzu,Amma yanzu mu kanmu kiransu muke jira,muji nawa suke buƙata sai a tura masu,"ba don yaso ba haka ya dinga shirga mata ƙarya,kamar yayi kuka wai yau shine ke yin ƙarya,duk da yayi ba'ason ranshi ba,Dole ce tasa su yin hakan,

  Turo ƙopar Sgr yayi hannunshi ruƙe da bottle water,ƙarasawa yayi tare da buɗe murfi ya tarfa ruwan asaman tafin hannunshi,Sannan ya shafa fuskar Abban nasu,Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ware idanuwanshi akansu yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,a hankali ya furta"Ina junaid"?

  Omar na ƙoƙarin buɗe baki yayi mashi jawabi,Alexandra ta katse mashi hanzarinshi da cewa"Ku barni dashi,dare yayi sosai yakamata kuje ku kwanta ku huta,kafin gobe,"ta fadi hakan ne don tasan cewa ba karamin tashin hankali suma suke ciki ba da ganin yanayin su,

    Saukowa daga saman gadon Omar yayi tare da ruƙo hannun Sgr yace"Mu tafi,"sallama su kayi mata tare da fucewa daga ɗakin,

Hawa saman gadon tayi suna fuskantar juna,tallabo fuskarshi tayi da hannayenta biyu,suka zuba ma juna ido,na wani lokaci kafin tace"Hubby,ka natsu ka saurare ni,Nasan zaka fahimce ni,Kuma kai musulmi ne!kayi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau haka ne"?kamar wani ƙaramin yaro haka ta mayar dashi,

Nodding kai yayi mata alamar eh,

  Murmushi ta ɗan sakar mashi tare da cewa"haka nake son ji my hubby,"dakatawa ta ɗan yi da yin jawabin tana kallonshi,saboda ta kasa furta mashi abunda take so ta faɗa,farin ruwa ta gani ya kwanta acikin idanuwanshi,la66ansa na kerma yace"Pls tell me the truth,Meya faru ne?kowa ya sauya mun,Dama ni sai da raina ya bani cewa wani abu ya faru da baby junaid ɗina,"jikinshi har ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama,

   Hawaye ne suka ciko tab a idonta,

"Am sorry to say,Junaid yana cikin ƙoshin lafiya,Amma baya atare damu,Rafayet ya sanar dani cewa,since yesterday night around 8 suna kan hanyar dawowarsu gida,kidnappers suka ɗaukesu gaba ɗayansu,"

  Jin wannan maganar yasa hankalinshi yayi mugun tashi,wata irin zabura yayi yana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon,Da sauri ta ruƙo rigar jikinshi"dan Allah ka natsu ka saurare ne...."

   Girgiza kai ya shiga yi yana faɗin"banga ta zama ba,Anyi garkuwa dasu junaid ɗina,Wlh bazata sa6u ba,duk inda junaid da jahad suke adawo mun dasu cikin daren nan in har anason zaman lafiya,wannan wani irin shashanci ne?har junaid ya kwana a hannun kidnappers tun jiya arasa wanda zai ƙwatosu daga hannunsu,Banga amfanin sojojin dana tara acikin gidan nan ba,Nikaina bani da amfani kenan!Kowa ma bai da amfani mun zama tamkar kwankwan ashana,tunda har bazamu iya ceto rayuwarsu ba,"idonshi ya rufe sai faman zazzaga masifa yakeyi,Ƙarasa saukowa yayi daga saman gadon,buguzun buguzun ya kama hanyar fita daga bedroom ɗin nashi,da sauri Alex tabi bayanshi,tana ambaton sunanshi

  Ko sauraronta baiyi ba,da alama ya zauce ne,

  "Yau ƙafata kafarsu junaid zamu dawo cikin gidan nan duk inda suke saina dawo dasu,abun ban haushi wai anyi garkuwa dasu junaid?sai kace ƴa'ƴan wani me siyar da kifi abakin titi,Ƴa'ƴana ne fa!Ni chief of army staff na Nigeria gaba ɗaya,banga amfanin matsayin da nake dashi ba Allah,tunda har za'a iya yin kidnapping ɗin ya'yana,wlh bazan yafewa kaina ba,in har bandawo da junaid cikin gidan nan ba,"ranshi amatukar 6ace yake yin maganar,jijiyoyin wuyanshi duk sun firfito waje,

  "Pls hubby Calm down ur mind,Ina zaka je ne?acikin daren nan!indai akansu junaid ne,na tabbata zasu dawo ne"

  Guntun tsoki yaja tare da cewa"baki da hankaline,da alama bakisan zafin haihuwa ba,Shiyasa kike faɗin hakan,"

  "Ni fa na haifeshi,taya zaka ce mun bansan zafin haihuwa ba?Ya kake so nayi ne?ka ƙi tsayawa nayi maka bayani,

  Su Marshal na zaune asaman sofa,kowa da abunda yake saƙawa aranshi,kwatsam suka jiyo muryoyinsu,nan fa suka miƙe suna kallonsu,

   Ganin Abbansu ya nufi hanyar fita daga falon ko takalma babu a ƙafarshi,da sauri suka sha gabanshi,

  Rufe ido yayi atsiwace yace"Ku matsa ku bani wuri,wlh Omar ka bani mamaki,ko ince kun bani mamaki,How many hours su junaid na a hannun kidnappers amma baku iya ƙwatomun shi ba,babu wani mataki da kuka ɗauka,to ni zanje in dawo da abuna,"yana magana huci na fitowa daga bakinshi,

   Ruƙo shi Omar yayi tare da fashewa da matsanancin kuka,Girgiza mashi kai ya soma yi batare da ya furta mashi komai,jikin Abbansu ba ƙaramin sanyi yayi ba,Cos ya manta when last yaga hawaye a fuskar Omar,tabbas abun na ci masu rai sosai,Mayar da idanuwanshi yayi kan Sgr,Hawaye ya gani kwance Luf acikin idanuwanshi,wanda tunda yake arayuwarshi bai ta6a ganin ruwan hawaye a idon Sgr ba,tun ma da aka haifeshi har suna expecting ko baida cikakkiyar lafiya ne,

   "Omar!kuka kake yi mun"?yayi maganar yayin da hawaye suka soma wanko fuskarshi,Kallon Sgr yayi tare da cewa"Kaima kukan zaka yi mun"?

  Duƙar da kanshi yayi ƙasa,gaba ɗaya jikin kowannansu yayi sanyi,

  "Abba,ka tausaya mana muna cikin matsananciyar damuwa na rashin Su junaid atare damu,Mun rasa yaya zamuyi,munyi tunanin zaka ƙarfafa mana guiwa wurin ganin mun ceto rayuwarsu,Amma sam kaƙi tsayawa kaji abunda muke son mu sanar dakai balle har musa ran zaka fahimce mu...."ya ƙarasa maganar tare da sanya tafin hannunshi yana share hawayen dake sauka a fuskarshi,

   "Abba,saboda rashin su junaid,ko bacci ba muyi ba,Yadda muka ga dare haka muka ga rana,Ga rafayet nan saboda shi,Ya baro kano ya dawo Abuja tunda sanyin safiya,dukanmu nan babu wanda ya iya kora koda ruwa ne ta maƙoshinsa,duk don saboda 6atansu junaid...."dakatawa ya ɗan yi da yin maganar yana kallon Abban nasu,da alama ya fara saukowa 

  "Kaine ka haifemu,kafi kowa sanin su wanene mu!me zamu iya da kuma wanda baza mu iya ba!Nasan ka yarda damu sosai,Idan har akwai wanda zai bada shaida akanmu kaine Abba!meyasa bazaka yi mana uziri ba?idan har bamu bi komai a hankali ba wurin ganin mun ceto rayuwarsu,Toh zamu rasa su ne gaba ɗayansu!"

  Juyawa Abba yayi ya soma tafiya cikin falon,Saman sofa ya zauna,ganin haka yasa suma suka dawo saman Sofa ɗin suka zauna suna fuskantarshi,Itama Mommy ta samu wuri daga gefen shi ta zauna,


Duk wannan abun dake faruwa akan idon ƙannensu,don tun lokacin da Abbansu ya fito yana sambatun nan,Kowannansu ya fito daga bedroom ɗinshi,Jikin kowannansu yayi mugun sanyi,jin cewa Anyi kidnapping ɗinsu Junaid,Abun ya ta6a masu zuciya sosai,


"Har tsawon wani lokaci,kuke so na baku ku dawo mun dasu junaid"?Acewar Abba,

  Shiru sukayi gabansu na faɗuwa,Omar ne yayi ƙoƙarin cewa"1 week"a hanzarce Sgr yace"Omar that's impossible,ka manta yarda mu kayi dasu ne?Sunyi mana alƙawarin cewa in dae aka yi masu yadda suke so zasu sakosu,Amma ba a tare ba,saboda suna ganin za'a gano su adau mataki, akwai yiyuwar su fara sauko junaid shi kaɗai acikin satin nan ko kuma su fara sakin Jahad,Ni ina ga kamar one month yayi,Kafin lokacin in sha Allah mun dawo dasu duka acikin gidan,

  Girgiza kai Abbansu ya ɗan yi tare da cewa"Har one month!su junaid basa atare damu?idan suka cutar dasu fa?

  "Abba sunyi mana alƙawarin cewa in har zamu biyasu yadda suke so,bazasu cutar mana dasu ba,"

  "Nawa suka buƙata"yayi tambayar yana kallon faces ɗinsu,

   "har yanzu dai su muke jira,sunce zasu kira su sanar damu,sannan sunce mu kwantar da hankalinmu,Bazasu ta6a cutar dasu ba,Zasu basu kyakkyawar kulawa,kuɗi kawai suke buƙata ba wani abu ba,"Omar ne ya kora mashi jawabin

  Cike da takaici Abba yace"just because of money,suka ɗauke mun ƴa'ƴana?Ae da sun sani sun nemi tallafi a wurinmu konawa ne zamu basu basai sun ɗauke mun su ba,"

   Miƙewa yayi sam babu kuzari ajikinshi,tafiya ya soma yi dakyar yake iya ɗaga ƙafarshi,har sai da yabar wurin Sofas ɗin,Sannan ya dakata da yin tafiyar,ya waiwayo tare da kallonsu,gaba ɗaya idanuwansu na akanshi,

  Magana ya soma yi masu babu wasa a fuskarshi"Omar!"

  "Na'am Abba"ya amsa mashi,

"Rafayet"shima ya amsa mashi"Na'am Daddy,"

   "Na yarda daku sosai,abu biyu nake tsammani daga wurinku,Na fako ku dawo mun dasu junaid,Cikin ƙoshin lafiya,Na biyu kuma ku kawo mun waɗannan gur6atattun mutanen da sukayi garkuwa dasu,Wallahi thumma tallahi idan har ku kasa yi mun waɗannan abubuwan dana lissafa maku,inaso ku sani Za ku rasa ni ne,NA HAR ABADA,daga yau zuwa 30 ga watan da zamu shiga,a kowace rana zan fara sa ran dawowarsu acikin gidan nan!kuma daga ranar ku fara ƙirgen ranakun da su kayi mun saura acikin duniyar nan


  *Tashin hankali!*

Mikewa Mommynsu tayi tare da kallonsu gwanin ban tausayi tace"Na yarda daku sosai,ku taimaki rayuwar mahaifinku,Zamu taya ku da Addu'a Har Allah yasa kuyi nasara akan kidnappers ɗin nan,"tana kai ƙarshen maganarta,tabi bayan abbansu,

  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"wannan shi ne abunda ke fitowa daga bakunansu,basu ta6a ganin tashin hankali irin na wannan ranar ba,A tsaye kowannansu ya kwana,har sun fara regretting ɗin ƙaryar da suka shirya ma Abbansu,


Acikin waɗannan kwanakin,Komai ya hargitse masu,safe da marece dare da rana,kullum cikin Zullumi suke,Suna cikin tashin hankali,Duk sunbi sun firgice,kallo guda zaka yi masu ga gane cewar basa a hayyacinsu,Don gaba ɗayansu daga Omar ɗin har Sgr babu wanda baiyi rama ba ajikinsu,gidan ya zama tamkar maƙabarta,Babu wani sauran farin ciki daya rage masu,Saboda rashin junaid babu mai samun isasshen bacci acikinsu,Abinci ma har Azmee ta fara gajiya da girka masu saboda Asarar shi da akeyi,Yadda ta ajiye haka take zuwa ta same shi,duk rana ta Allah sai Abbansu ya tunasar dasu Adadin kwanakin daya rage masu na ƙwato su junaid a wurin kidnappers,yayin da suke cikin wannan tashin hankalin,Abusufyan na can suma ba kwanciyar hankali wanda hakan ya ɗauke hankalinshi gaba daya batare da ya fahimci halin da gidan suke ciki ba,Ciwon abu ya tashi gadan gadan,Kullum da daddare sai ta dinga kuka tana buge buge tana faɗin sunan sayyadi,hakan ba ƙaramin ruɗani ya sanyasu ba,har Sehrish ta fara zargin cewa,kodai yafara yi mata gizau ne?Anya ba wani abu ke faruwa ba?duk yadda taso Oummansu ta sanar da ita abunda take gani,Hakan ya faskara saboda bata da hankalin da zata iya fayyace mata komai,a ƙarshe dole sehrish ta koma ɗakinta da kwana,duk in haukan nata ya motsa da zarar ta fara raira mata karatun Alƙur'ani sai ta samu natsuwa,a haka suke samu tayi bacci,


A 6angaren Su Hayaam kuwa,ba ƙaramin daɗi suka ji ba,lokacin da Abra ta dawo abuja,Batare da tasha wahala ba,bayan An sallami Hayaam daga Asibiti gidan Amani suka koma,Zasu zauna na ɗan wani lokaci kafin su wuce Maiduguri,duk wannan budurin da sukeyi basu son abunda ke faruwa acan gidansu na maiduguri ba,Sun manta da mahaifiyarsu da suka baro kwance ba lafiya rai hannun Allah,


A 6angaren Aunty babba kuwa ba ƙaramin jiki taji ba,tun bayan da mai motar nan ya hankaɗe ta a Enugu,daƙyar aka samu wani bawan Allah ya ɗauketa a motarshi suka kaita asibiti,Taci baƙar wuya kamar bazata rayu ba,tsawon sati tana kwance a gadon asibiti batasan inda kanta yake ba,Komai ya ƙare mata ƙarƙaf,mutumin daya kawota asibitin tun da ya biya kuɗin da za'a yi mata aiki a ƙafarta da ta samu matsala,bai ƙara tako kafarshi yazo ba,Ga ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa,ta ɗuri ruwa,tayi suntum da ita,daga baya ta ru6e sai uban wari dake fitowa daga jikin ƙafar,Likitoci sunyi iya kar bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sunyi mata magani,amma abun ya ci tura,da suka gaji gashi babu wani danginta a kusa,kuma babu kuɗin da zasu cigaba da kula da ita,A ƙarshe Suka sallame ta daga asibitin,Tashin hankali!ko ya  rayuwar Laila zata kasance"?

 


Yau Two Weeks kenan da mutuwar Junaid,Wanda ya kasance Wata biyu cuf da sati ɗaya da yin auren Sehrish Abusufyan da Rafayet salahuddeen,duk da muna sa ran kwanakin auren nasu zai ƙara tsayi saboda Sgr ya ɗaga tafiyarshi ta komawa U.s,Zuwa Next One Month,dalilin ɗaga tafiyar tashi saboda Investigation ɗin da sukeyi na ƙoƙarin gano waɗanda suka kashe Junaid,Ga kuma Abbansu daya zuba masu ido yana jiran su dawo mashi da ƴa'ƴanshi,bawan Allah ko bacci bai samu,duk ya rame ya fige,bai samun bacci da daddare saboda sallar daren da yake yi, haka zai zauna saman darduma yayi ta yi masu addu'a,Allah ya dawo mashi da ƴa'ƴanshi,ita kanta Mommynsu junaid tana cikin mawuyacin hali,cos ta fara zargin cewa ba Kidnapping ɗinsu akayi ba,there's something behind da suka 6oye masu,har sun fara fidda rai da dawowarsu,A ranar Litinin sai ga JAHAD ta dawo gidan da ƙafafunta,Murna a wurinsu kamar su haɗiyeta,duk da sun shiga damuwa ganin yadda ta rame ta fige,duk ta fita hayyacinta,ƙashin wuyanta duk ya firfito kamar zai fasa fatar wuyanta,Taji jiki sosai,Idanuwanta duk sun kumbura,duk yadda suka so jahad ta buɗe baki ta faɗa masu ina junaid yake,taƙi magana bakinta a rufe yake,sai dai kawai ta dinga binsu da ido,bakomai ya hanata yin magana ba,fa ce kukan dake cinta,muddin ta buɗe bakinta to zata fashe masu da kuka ne,kuma ta ɗaukarwa Su ya Omar alƙawarin bazata tona masu asiri ba nace wa junaid ya mutu,har sai lokacin da suka shirya sanar dasu,tunda ta dawo gidan nan,Ta zama salihar ƙarfi da yaji,magana saita zama dole sannan take yinta,ko ɗakinsu batasan fitowa daga ciki,tun hosana na lalla6ata don ta faɗa mata abunda ke damunta,saboda kullum sai ta farka ta sameta tsakar dare tana sallah hawaye na gangarowa akan fuskarta,Har tagaji da tambayarta ta ƙyaleta,


Kullum ne in zata kwanta da daddare sai ta ɗaukko wannan zanen fuskar junaid da tayi a cikin drawing book ɗinta,ta tasa shi gaba tayi ta kallo,Wani lokacin ta fashe da kuka wani lokacin kuma tayi murmushi,bakomai yafi tsaya mata araiba,kamar rana ta farko da ta fara haɗuwa dashi face to face,Yayi tsammanin Sehrish ce,ya ruƙo hannunta ya turata cikin motarshi,ya tasa ta gaba da wannan kyakkyawan murmushin nashi,jahad tayi kuka tamkar ranta zai fita,har ya bi jikinta,in har bata zubda kwallaba ita kanta bata jin daɗin jikinta,wani sa'in idan raɗaɗin yayi mata yawa ƙur'ani take ɗauka ta zauna tayi ta karantawa har ta samu sauƙi acikin zuciyarta,Sau dayawa Omar yakan kirata a garden su zauna yayi ta lallashinta,yana yi mata nasiha,hakan yasa ta fara samun sauƙin raɗaɗin da zuciyarta keyi mata,har ta fara sakewa da kowa acikin gidan,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,Yanzu saura dawowar Junaid suke jira shima Masu garkuwar su sako shi,😥rashin sani yafi dare duhu


*Boss Bature*


Kano State,


Wuraren ƙarfe 8 na dare,Sehrish ta fito daga cikin toilet,chest ɗinta ɗaure da towel,ta canza sosai,duk da babu kwanciyar hankali atare da ita,Ciwon Oummansu ba ƙaramin ɗaga mata hankali yake yi ba,harta fara murnar zasu koma gida,sae kuma abu ya dawo gadan gadan haukan take yi,wardrobe ta nufa tare da buɗewa,ta dauko kayan baccinta riga da wando ta zurasu ajikinta,bayan ta kammala sanya kayan,gaban mirror ta koma ta zauna tana kallon fuskarta acikin madubin,ta ƙara kyau da haske,mayukan da take amfani dasu ba ƙaramin gyara suke yi ma jikinta ba,tunani ta shiga yi yau saura satittika suka rage aurenta ya mutu da Sgr,ta ɗan damu da rashinsa a kusa da ita,kusan kullum ne saita tura mashi text message a wayarshi,Sometimes yana maido mata da reply,harma ya tambayi ya lafiyar Oummansu,hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba,

  Kiran wayane ya shigo,nan take wayarta ta soma ruri,jiki na rawa ta miƙe daga saman kujerar ta nufi inda ta ajiye wayar asaman pillow,hannu tasa ta ɗauki wayar tare da duba sunan mai kiran nata,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ganin sunan Mommy Azeema ya bayyana akan screen ɗin wayar,Cike da zumuɗi ta ɗaga kiran,

   "Assalamu alaikum mommy"

On the other hand mommy Azeema tace"wa'alaikumus salam my Daughter hope kina lafiya,"

  Shiru Sehrish tayi batare da ta bata amsa ba,ƙasa kasa ta soma shessheƙar kuka,

    "Daughter,kuka kikeyi koh"?nan ma shiru bata amsa mata ba,

   "Kinyi missing ɗin mommynki ko?,

  Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Eh mommy,kin manta dani,ina cikin damuwa sosai,ta ko'ina ba sauƙi,dama kece kike kwantar mun da hankalina,gashi yanzu kona kira baki ɗagawa,"

  "Am sorry daughter,Nasan ban kyauta maki ba,Amma yanzu ki kwantar da hankalinki,In sha Allah this week zamu zo nan Abuja,Munyi waya da Abusufyan ya sanar dani cewa,Zaku dawo tare da Oummanku ko!

  sehrish tace"Eh,"

  "Naji daɗi sosai,Ban kira na tayaki murnar ganin Oummanku ba,Wlh na yi farin ciki sosai,har ina cewa gwaurancin Abusufyan ya ƙare tunda sanyin idaniyarshi ta dawo,"

  Murmushi sehrish ta saki,hajiya azeema taci gaba da cewa"Baki bani labarin rayuwarki da Sgr ba?ya ake ciki?ko har yanzu babu wani sauyi"?

   Komawa sehrish tayi gefen gadon ta zauna,A tsanake ta labarta mata irin zaman da sukayi dashi,"

  Hajiya azeema tace"Good,Koba komai ta wani 6angaren hankalinshi ya fara karkata akanki,Wannan ma mataki ne na nasara"

  Dakatawa tayi da yin maganar tana sauke ajiyar zuciya,kasa kunne sehrish tayi tana jiran jin me zatace mata,

  "Yaushe zaku dawo kano?kamata yayi ace kuna tare da juna,banji daɗin komawarshi Abuja ba,"

  "Gobe muka shirya komawa gida,Amma ciwon oumman mu sai ƙara gaba yake yi,bansani ba ko tafiyar na nan,ko an fasa,Daddy nake jira ya dawo na tambayeshi,"

  "Kisan yarda zakiyi Ku koma Abuja,if not duk wani shirin mu zai lalace ne,Ita kuma Oummanku,Allah ya bata  lafiya,zamu tayaku da addu'a,Zan yi magana da daddy ɗin naku gaskiya ƙwara adawo da ita nan Abuja,zata fi samun caring,ga kuma su hosana da jahad,idan tana ganinku ku uku atare sai inga kamar zata iya dawowa hayyacinta in a short time,"

 Sehrish ta Gamsu da bayaninta ita kanta tayi tunanin hakan,

  "Nagode sosae Mommy,Allah yabarmun ke,Har na kosa mu hadu,don nayi missing ɗinki sosai da sosai,"

  dariya hajiya azeema tayi tare da cewa"don't worry ur self in dai nice har sai kin gaji da gani na,Am coming back soon,Dani za'ayi yaƙin karshen nan,da makamaina zanzo,mu bazama a filin daga har sai mun cimma nasara,"cike da Zolaya tayi maganar,hakan ba ƙaramin dariya ya ba sehrish ba,hada dafe cikinta,taji daɗin kiran da Hajiya azeema tayi mata,Ta sanyata farin ciki sosai,Sun jima suna waya kafin daga bisani suka yi sallama,


Wurgi tayi da wayar saman mattress,fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi,tana cikin Nishaɗin nan ta soma jin faɗuwar gaba rass rass!tunani ta shiga yi ko mai yasa take jin faduwar gaba?kodai wani abu na faruwa ne,tana cikin wannan fargabar taji an kashe ƙwan falo,da farko bata damu ba,tun da ba ita kaɗai bace acikin gidan Akwai security guards zai iya yiwuwa ma Daddynsu ne ya dawo,dama ya sanar da ita cewa after isha' prayer zai wuce gidansu Maman sadeeq,


Ƙwala mashi kira ta soma yi don taji idan shi ne ya dawo,

  "Daddy!Daddy!Daddy Abusufyan"!shiru ba'a amsa mata ba,nan fa ta soma zargin kodai wani ne ya shigo masu,Amma ae akwai security a gidan,kasa jurewa tayi hakan yasa ta mike tsaye,ta tunkari ƙopar ɗakin,a hankali tasa hannu ta buɗe ƙopar ɗakin ta fara leƙawa,ko'ina duhu babu haske a falon,motsin takun takalmi ta fara ji,


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post