Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 4 complete

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 4 complete

 

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 4 complete

https://chat.whatsapp.com/EcCtf5VAlpo8kdQCkDY4z

*The Destined Prison*

*💋by Boss Bature💋✍️*

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ

 وَسَلَّمَ الدُّنْيَا سِجْنُ الْمُؤْمِنِ وَجَنَّةُ الْكَافِر

2956 صحيح مسلم كتاب الزهد والرقائق

*Episode 4*

Sun sha wahala a hannun ƴan sandan,Yinin ranar har dare yayi ana Bincike akansu,Daƙyar suka samu Akayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu,Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh,Ya bata address din Ps din da zata same su,


Ba'aɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station din,hankalinta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police,Bayan Tayi parking ɗin motar,Ta fito sanye Cikin doguwar riga Ta yafa mayafi akanta,A hanzarce ta nufi cikin station ɗin,Lokacin da ta shiga Ciki,ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su,batasan lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj,duk ya fita hayyacinshi kamar wanda yayi hatsarin mota,Saboda jigatar da yayi,


Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin"Why why!why pls?Laifin me suka aikata da zaku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin,"

  Copral ne Ya bata amsa da cewa"Ana zarginsu da sace Ƴa'ƴan mutane suna Amfani dasu"

  Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallonsu,

  "Amma baka da hankali Officer,Ka iya bakinka,Shin kuna da hujja akan abunda kuke zarginsu ne?waye ke baisan Taj da uzair ba....."bata kai ƙarshen maganarta ba,Muryar dpo ta katse ta"Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu,"

  Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin,,Cikin sanyin murya ta furta"where's the evidence"?


Kafin dpo ya bata amsa,Sae ga Angel tana fitowa daga Office ɗinshi,


Aruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,


Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel,itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita,Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka akan Wannan bawan Allahn daya sace ta,Ya raba ta da iyayenta don baƙin zalunci,"yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen,


Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami"You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce,"muryarta adisashe takai ƙarshen maganar,


"Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi,"acewar dpo,


Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh,Girgiza kai tashiga Yi tana kallon angel,

  "Wlh officer Ƴarshi ce,Sharri take yi mashi,Yarinyar bata da cikakken hankali ne,"

  Da buɗe bakin angel sai cewa"Ni ƙarya take yi mun officer,itama hada ita suke yi ae"


Curo handcuff Inspector yayi tare dacewa"You are under arrest"ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa

Ganin dagaske Kamata zasuyi ne yasa tayi saurin cewa"Ku dakata,kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer,akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta,zaku Iya bincika wayarshi ku gani,

  Girgiza kai Dpo yayi"Wannan ba hujja bace,duk shirinku ne"

  Jinjina kai tayi to shikenan,Me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test,this is the Only solution"

 Jinjina kai dpo "Good idea,Copral"Dpo ne ya kira sunanshi

  "Yes sir"ya amsa mashi,

  "Ku tafi da Mutumin da yarinyar,Ayi masu gwajin DNA,ku tabbatar anyi komai agabanku,"

  "Consider it done sir"Ya ambaci hakan tare da sara mashi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin,Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi,sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafunshi,wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayinshi ba,ko son kallonshi ma batayi,


A cikin mota suka sanyasu,Aneelerh kuma Ta shiga motarta,tare da angel,


Bayan zuwansu asibiti,Akan idon Police men ɗin akayi komai,Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,


Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba,Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu,Sun sha mamaki,Lamarin Yayi matuƙar girgizasu,Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu,dpo yafi kowa girgiza,har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zarginsu da suka yi,Anan aka kwantar da Tajuddeen,Sam ya fita hayyacinshi,hada drip suka sanya mashi,


Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da sukayi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin Tsakaninshi da yarinyar ba,A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗata da manyan malamai su cire shaidanun dake ajikinta,ko kuma akaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,


Binshi da kallo kawai aneelerh  tayi don ita tasan Wacece Angel,Lafiyarta ƙalou,itace aljanar kanta da kanta,yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi,Lafiyarta qalou "


Kwananshi uku a gadon asibiti,saboda jikinshi da yaƙi sauƙi,cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya dashi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba,da yake suna waya dashi kusan kullumne sai sun kirasu kosu su kirasu,A ƙarshe suka koma gida da jinya,Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu,jin Abunda ya faru dashi,Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba,kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane,Bawan Allah Taj,kullum yana kwance saman gado,Wanka da sallah ne kaɗai suke tada shi,Wani sa'in yana ɗangyashi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet,Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba,sai in tana jin yunwa ne zata addabeshi wai ya tashi yayi masu girki,in ba haka ba zata je ta daura da kanta,


In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar  dashi,dama Cikin ƴan kwanakin nan mai aikinsu Uzair hada Su taj take girka ma abinci,duk in zatayi,bisa umarnin Uzair ɗin,Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko'ina Yana gida,Wuraren ƙarfe biyar na marece,ya fitowa daga wanka jikinshi sanye da short baƙi,saman Gado ya haye bacci mai daɗi ya ɗauke shi,Yayi nisa acikin Baccinshi,Yadinga Jin  Hayaniya acikin gidan,jiki amace Ya miƙe daga saman gadon,ya nufi ƙopar ɗakin,Leƙawa yayi don yaga  su wanene 


Waro ido waje yayi ganin mutane maƙil Cike da falon,Kasa kunne yayi yana sauraran me suke cewa

  "Allah ya jiƙanshi,Taj mutumin kirki,halinshi na gari Ya bishi,"

 Can kuma yaji wani yace"A ina ne za'ayi jana'izar tashi"?

 Wani ya bashi amsa da cewa"Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji,"

  Shiru yayi la6e bakin ƙopar Ya kasa fitowa,Jikinshi duk yayi sanyi,tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu?dama akwai wani taj ne bayanshi"?sam bai damu da rashin ganin angel ba,Yasan bata wuce Gidansu Uzair,Komawa Cikin ɗakin yayi Jikinshi duk ya mutu,Wayarshi Ya ɗauka dake ajiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs,Nan yaga miss Calls sunyi ɗari uku na mutune,abun ya ɗaure mashi kai,


Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira,Tana fara ringing uzair Ya ɗaga,

  "Assalamu alaikum"batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa"Uzair kana ina ne"?

  On the other hand Uzair yace"Gida mana"

  Cike da damuwa yace"Uzair na shiga Uku,Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana,Na kuma taras da miss calls awayata Yayi ɗari uku na mutane,Wai meke faruwa ne"?Muryar uzair da ɗan ruɗi yace"Kodai angel tayi wani abu ne?bata jima da shigowa Gidanmu ba,Take sanar dani cewa Ta ɗauki wayarka kana bacci,Ta sanya yatsanka ta buɗeta"tunkafin Uzair yakai ƙarshen maganar shu,Taj Yayi rejecting call ɗin,Ya shiga laluban wayarshi,Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appear,Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi,A hanzarce Ya shiga facebook dinshi,Anan Yaga hotonshi da angel ta ɗauka yana bacci tayi share ɗinshi a facebook,a ƙasa ta rubuta RIJF,Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawansu sunyi tunanin ko matarshice Tayi amfani da wayarshi donta sanar masu mutuwarshi,Shine suka kwaso ƙafafuwansu zuwa Gidan don ayi jana'ixa dasu


jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasarshi,lalla6awa yayi ya samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha,Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta,da kuma abunda zaiyi silar barina duniya ashe ƴar Cikina ce,Laifin me nayi mata ne data tsaneni?sai kace ba mahaifinta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta,Wayyo Allah na,Sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF,a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta'aziyarshi,daga ƙasan hotonshi aka Sanya RIJF,Rest In jannatul firdaus,shine take tambayarshi wai me yake nufi,da yake ta iya tambaya,kamar yar jarida,Baiyi tunanin komai ba ya sanar da ita ma'anar hakan,Shine tayi mashi aika aika,


Kiran Uzair Ne ya shigo wayarshi,A sukwane Ya ɗaga Kiran anan yake sanar dashi abunda ta aikata mashi,Uzair yasha ruwan mamaki,A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba,Yana raye mistake aka samu wurin Yin posting din,ƙin tafiya sukayi Har saida suka ga Taj da ƙafafunshi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah kyauta,A falo suka zauna gaba ɗayansu,Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku,Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine,

  "Yanzu menene mafita"?taj ne yayi maganar yana kallonsu,

  "Lamarin Angel Yafi ƙarfin mutun sai dai Allah,ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruƙiya ta sace takalmanshi,tun daga nan Jikina Yayi sanyi,"acewar Uxair,

  "Benazir ta tafi tabarmun bala'e"tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,.  

  "Me zai hana ka jaraba Bugunta"?a ɗan firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar,

 Cigaba da magana tayi"Idan har bazaka iya bugunta ba,shawarar da zan bada shine,Kasan mafi akasarin kananun yara akwai abunda suke tsoro,Ni ina ganin ajaraba samo Mage ko kare ko kuma ƙadangare,Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu,Sai adinga Yi mata Barazana dashi,Koya kuka Gani"?tayi tambayar tana kallon Taj,wanda yayi zugudum yana kallonta,yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare,Taya zata Ji tsoron waɗannan halittun,Acikin zuciyarshi ne yayi maganar,

 Jinjina kai Uxair yayi"Good idea,idan na fita Yanzu xansa Almajirai su samo mun Duka ukun asanya agidan,Nasan dole asamu wanda take matuƙar tsoro acikinsu,"

  "Allah yasa danafi kowa Farin Ciki"acewar Taj,Sun jima suna tattaunawa kafin Sukayi mashi Sallama,Atare suka bar gidan,


Kishingiɗawa Yayi saman Sofa din,Ya miƙe kafafunshi yana Jiran Almajirin da zai kawo mashi dabbobin,Bada Jimawa ba Sai ga baba mai gadi Yay mashi sallama,Daƙyar Ya mike ya taka zuwa bakin ƙopar Falon,A tsaye Ya samu baba mai gadi,Gaisawa suka Fara yi,Yayi mashi Ya jiki,

   Daga bisani Yace"Yaro ne Yazo Da kare da mage,Yace wai uzair ne Ya aikoshi akawo maka,naga hada kaɗangare ma"jinjina kai taj yayi"eh ni nasa akawo mun,kace masu su shigo dasu,"

  Juyawa Baba mai gadi yayi da sauri Yaje ya isar masu da saƙonshi,


Shigowa Cikin gidan Alamjiran sukayi su ukune,Kayan jikinsu duk sun yayyage,Hannun kowannasu na ruƙe da Abunda Yasa a kawo mashi,Jibgegen kare ne Sai haushi yake yi,Yana jijjiga jikinshi,irin karnukan turawan nan masu gashi ajikinsu,magen ma jibgegiyace baƙa wuliƙ,ƙadangaren Kuma Jankwataki ne,Babu kyan gani Jikinshi,


  Kuɗi yabasu Sannan Yayi masu godiya suka tafi,Acikin falon Gidan ya sanyasu,Karen da magen sai Yawo sukeyi suna tsalle tsalle saman Sofa,Magana yayi ma maigadi,Yaje ya dauko mashi angel a gidansu, Aneelerh,bada jimawa ba sai ga baba maigadi Ya dawo ruƙe da hannunta,Taj har wani murmushin mugunta Yake yi,Yau xaiyi maganinta Virus,kamar abun Arziƙi Taj ya ruƙo hannunta Ya turata acikin falon,Tukunna Yaja ƙopa Ya rufeta aciki,Ya koma wurin baba mai gadi Yana Jiran Yaji ihunta,don yasan da zarar Tayi Arba da kadangaren nan har suma Zata Iyayi "Asaman Benci suka zauna shida baba mai gadi,Suna ɗan tattaunawa game da Halin angel,


Suna Cikin magana,suka soma Jin Ihun angel Ya cika gidan,hada kururuwa irin na tashin hankali,a ruɗe taj ya miƙe cike da fargabar karsu kashe mashi ƴa,Bin bayanshi baba mai gadi yayi suka nufi Cikin gidan,Tunkafin Ya buɗe ƙopar falon jikinshi yayi sanyi Jin tsit babu ihun Angel alamar wani abu Ya faru da ita,tuni idanuwanshi suka Ciko tab da kwalla,


Hannunshi na kerma Ya tura ƙopar ɗakin ya shiga ciki,baba mai gadi Yabi bayanshi,Lokacin da suka shiga tsakiyar Falon Jini suka gani,a ruɗe suka kalli Juna,la66an Taj na kerma Ya furta"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un"

  Baba mai gadi yace"Munyi kuskure yalla6ai,Allah dai yasa ba wani mummunan abunne ya faru ba,


  Kamar ance baba mai gadi Ya zagaya Ta bayan Kujerun,Karaf idanuwanshi suka sauka akan Karen dake kwance yana ta fitar da numfashi sama sama Sai faman Zullo da harshe waje yakeyi,kai kana ganinsa zaka shaida halin da yake Ciki,gefen karen ƙadangaren da aka kawo ne,An kwankwatsa kanshi,Yayi jaga jaga da jini,

  "Yalla6ai zo ka Gani"mai gadi ne ya kirashi,Jiki na rawa Ya zagayo ta bayan kujerun,turus ya tsaya yana kallon Ikon Allah,suna Cikin shan mamakim nan,Sai ga Angel Tana saukowa daga saman Stairs,hannunta shaƙe da wuyan magen da aka kawo,gashin jikinta duk ya jiƙe sharkaf da Ruwa,Sai kuka take Yi miyau miyau,


A sukwane Taj da baba mai gadi suka kalli Juna,Abun yayi mugun ɗaure masu kai,

Karasa saukowa tayi daga saman benen Tana nufo su,

  "Daddy,Kalli ka gani wanka nayi mata"


Wato ita atunaninta Ya siya mata su ne don tayi wasa dasu,Shi ne ta kashe wanda bata so,Ta dauki magen,shi kuma karen tayi mashi bugun tsiya shiyasa ya jigata,


 Ƙarasowa Tayi gabanshi,Ta miƙa mashi magen"Kaga Tayi kyau ko"?


Girgiza kai taj ya ɗanyi tare da kallon baba mai gadi yace"Ni dama nasan za'a rina,Dan Allah baba ataimaka a mayarwa Uzair da karen nan tunkafin ta kashe shi shi kuma ƙadangaren a kawar dashi"amsa mashi yayi toh kafin Ya zuƙunna Ya ɗauke karen da ƙadangaren Ya fuce dasu,Zama Angel tayi saman Sofa,ganin Ya tsareta da ido yana kallonta yasa tace"daddy what"?

 "Bakomai,"ya bata amsa a yayin da yake ƙarasawa gabanta,Yayi zaman Cin tuwo Yana fuskantarta,

   Sam ya kasa magana Sai kallonta yake Yi,

  Cikin sanyin murya ya soma magana"Laifin me nayi maki,da baki sona Angel"

  Murmushin gefen fuska ta ɗan saki har dimple ɗinta Suka Lotsa,

  "Daddy,Na ta6a cewa bana sonka"?  

  "Ga alama nan angel,kullum sai kinsa na zubar da hawayena akanki,why angel?Nifa mahainfinki ne,"

 Shiru ta ɗanyi tana kallon Cikin ƙwayar idonshi,kamar mai nazarin wani abu,

   Sauke magen hannunta Tayi a ƙasa,ta mayar da idanuwanta akanshi,

  "Yanzu me kakeso nace"?

  "Oh baki ma san me zaki ce mun ba"

  ɗaga mashi kai tayi"eh,

 Jinjina kai yayi tare da miƙewa gudun kada ta ɗaura mashi wani hawan Jinin,

  Bedroom ɗinshi Ya koma ya kwanta saman gadonshi,ƙwalla ta ciko tab acikin idanuwanshi,A hankali ya furta"In sha Allah Angel,Baƙin Cikin ki bazai kashe ni ba,"Lumshe idanuwanshi ya ɗanyi,kafin wani lokacin bacci yayi awon gaba dashi,Acan palour kuwa magen dake a hannun angel ta kubce mata,Saukowa tayi daga saman sofa  ɗin takai hannu zata dauki magenta data sanyawa Suna Chu chu,Aikuwa magen Ta watsa aguje tana kuka,tabi bayanta da gudu,Suka shiga zagaye palourn,Sune har cikin kitchen,Magen ta haye saman Dish racks,inda Jerin Plates na tangaran suke,Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din,Suka tarwatse kasa duk suka faffashe,Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran,Ruƙo ƙafar magen Angel tayi,Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse,Kubce mata magen tayi da gudu  ta sauko ta nufi Store da kopar shigarshi ke anan cikin kitchen ɗin,Aguje angel tabi bayanta,Suka shiga yin yar tseral,Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su,A ƙalla sunyi crates goma sha biyu,Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe,hayewa sama magen tayi cikin Cabinet inda aka jera Sunƙi sunƙin bready,Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja,Ta haye samanta,Ta cakumo wuyan magen,jarkar da ta hau saman kantace ta Karkace da ita da magen Da jarkar man,Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa,Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa,bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi,tamkar Bola,duk Ta hargitsa komai ba,


Da taga Tayi 6arna sosai,Saita Saki Cucu,Ta ruga da gudu ta nufi gate,A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib,Ya hangota ta nufo shi,


Tunkafin ta ƙaraso Take nuna mashi gate ya buɗe mata,Sanin Tsiwarta yasa Ya buɗe mata ƙopar jikin gate ɗin ta fuce,Sai gidansu Aneerlerh,lokacin data shiga Gidan,A bedroom ta samu aneerlerh ta kabbara Sallah,Saman Gadonsu ta haye Taja bargo ta kudundune,Bayan aneelerh ta kammala Yin sallar,tana daga zaune saman darduma ta kalleta"Angel Lafiyarki kuwa"


Kasa ƙasa da murya tace"Zazza6i nake yi"


"kin sha magani"


"Eh nasha,daddy ne yace inzo wurinki kiyi mun wanka,in ya dawo daga masallaci zaizo ya dauke ni"


Mikewa aneerlah tayi,bayan ta cire hijabin ta tura a wardrobe,


"Tashi muje nayi maki wankan"


Yaye bargon tayi ta sauko daga saman Gadon,rigar jikinta duk ta cukuikuye,hada manjan daya gogu agaban rigar,

  "A haka kika hau mun gadona?Ina kika samu manja ajikinki"

  Ashagwa6e tace"nace maki bana lafiya,Ni bana iya magana sosai"

  Sam aneelerh bata yarda da ita ba,ta kyaleta ne kawai,


Within minutes tayi mata wanka,suka fito daga cikin toilet,ta shafe mata jikinta da mai,Canza mata kaya tayi,dama Saboda Ita ta siyi kayan Yara dai dai Size dinta,saboda sun ɗauketa tamkar ɗiyarsu,pink gown ta sanya mata,ta kuma ɗaure mata sumar kanta da ribbom,ba ƙaramin kyau tayi ba,hada light make up aneelerh tayi mata,


"Aunty aneelerh,Zan koma saman gadon in kwanta,dan Allah ki hadamun fura,A sanya kwakwa da yogurt aciki,da ƙanƙara"


Jinjina kai aneerlah tayi fuskarta dauke da murmushi tace"Okey My daughter in law,je ki kwanta,"da gudu taje ta haye saman gadon,Bayan Aneerlerh ta hado mata furar acikin Cup,ta kawo mata,Nan tazauna tasha ta ƙoshi,kafin ta koma ta kwanta,tuni bacci yayi awon gaba da ita,A 6angaren Taj kuwa,Lokacin daya tashi,toilet ya shiga,ya dauro alwala,Ya dawo Cikin ɗakin Ya dauko Jallabiya Cikin Closet dinshi Ya zura ajikinshi,Fitowa yayi daga ɗakin yana ta faman sauri Ya fuce zuwa masallaci,


Bai tashi sanin aika aikar da Angel tayi mashi ba,Sai daya Dawo daga masallaci,wata irin yunwa ta farmasa,ba arxiƙi Ya nufi kitchen,Shigarshi keda Wuya Tun abakin ƙopar yaci karo da Fasassun kwanukan da angel ta 6aro,A razane ya dago yana kallon cikin kitchen ɗin,har wani hayaki yake ganin cikin idonshi saboda tsabar 6acin rai,ashe baiga komai ba,sai daya Shiga Cikin store,Hannu ya ɗaura akai yana ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!Nashiga Uku!Na bani!Ya Allah laifin me nayi aka jarrabceni da Angel?wani zunubi na aikata,dafe baki yayi da sauri jin sabon da yayi yana mai fadin astagfurullah....."yana cikin sambatun nan yaji kukan Mage,Aikuwa a harzuƙe ya juya ya kalli magen dake abakin kopar store ɗin,Shaƙo wuyanta yayi tare da jijjigata Yace"Ke da ubanwa kukayi wannan"?

    Ƙura mashi ido magen tayi tana Cigaba da yin kukan Yunwar da take yi,wurgi yayi da ita,Ya naɗe hannun rigarshi Ya fuce daga gidan,kaitsaye Ya shiga Gidan Uxair,tun abakin gate mai gadin Gidan Ya soma tambayarshi"Yalla6ai Lafiya"


Baiko tanka mashi ba,Idonshi Ya rufe,Angel kawai Yake nema,Ko sallama bai tsaya Yi ba,Ya faɗa Cikin Falon Gidan,Ganin bakowa Yasa shi fara kwala mata Kira"Angel!Angel!Angel!!' tamkar makoshinshi zai 6allo,


Da gudun gaske Aneelerh ta fito daga bedroom ɗinta Jin muryar Taj Cikin tashin hankali,


"Me ya faru ne"?tayi tambayar tana kallonshi,

  "Where is Angel"?

 "Ɗazu ta shigo bata Jin dadin jikinta,yanzu haka bacci take yi adakin"bata kai ƙarshen maganarta ba,Ya wuce ta a fusace Ya faɗa dakin,Can ya hangota saman gado a kudundune tana ta sharar bacci,"


Hannu biyu yasa ya Cakumeta,da sauri aneerlerh ta biyo bayanshi Tana tambayarshi Meya faru ne,


Da budar bakinshi sai cewa yayi"kashe ta zanyi,"


Yana faɗin  hakan  ya nufi hanyar fita da ita,gida Ya koma da ita,a dakin Ya jefar da ita saman gado,sai lokacin ta farka tana kalleshi da manyan idanuwanta,

  "Daddy what"?


"Zaki Ci ubanki ne"ya faɗi hakan tare da Janyo pillow Ya hau saman gadon Ya turmushi fuskarta dashi,Mutsu mutsu ta shiga Yi,tana kokawar fitar da numfashinta,sae faman harba ƙafafunta take Yi,tana neman Ceto,Amma Taj sam Babu alamar zai sarara Mata,Saboda Baya acikin Hayyacinshi,Dagasken kasheta Zaiyi,Faɗowa ɗakin aneelerh tayi ko takalma babu a ƙafafuwanta,Anan ta same shi Saman Gadon Ya danne angel Da pillow,A gigice ta fasa ƙara,Tare da yin kukan kura Ta haye saman Gadon,Da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta cakumi wuyan jallabiyar jikinshi Taj tare da Yin Wurgi dashi gefe guda Ya faɗa  saman mattress din,


Cikin shessheƙar kuka take fadin"Taj bansanka da haka ba,meyasa zaka yanke hukunci Cikin fushi ne?Meye ribarka idan ka kashe Angel?yarinyar da bata wuci 7years ba,idan kayi hakuri Wata rana zata daina ne,


"Wlh bazan ƙyaleta ba,Kafin ta kashe ni,Ni zan fara kashe ta,"ya ambaci hakan tare da yunkurawa Ya miƙe Yana ƙoƙarin Cakumar Wuyan angel data sume,da sauri Aneelerh Ta sanya hannu ta ɗauketa,tana ƙokarin saukowa da ita daga saman gadon,A ƙokarin Ya damƙo angel Ya janyo wuyan rigar Aneelerh gaba ɗaya aneelerh tayi baya ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi,Angel kuma tayi gefe ɗaya saman gadon,Karo na farko da jikinta ya fara ta6a namijin da ba muharraminta ba,shi kanshi baiyi tsammani hakan zata faru ba,saboda ba ita yayi niyar Janyoba,Angel dake a hannunta Yaso Ya damƙo,hatta mayafin da aneelerh ta rufe kanta dashi ya warware sumar kanta mai tarin yawa ta sauka har saman kafadarta,wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarci kowannansu,ƙoƙarin mikewa aneelerh tayi sai dai ina wani magnet ne Ya ruketa,Runtse idanuwanta tayi da karfi ta soma ambaton a'uzubillahi minasshaiɗanirrajim,tun da ta ambaci hakan sai gashi ta samu ƙwarin guiwar Raba jikinta daga Na taj,aikuwa A gaggauce ta hanzarta sauka daga saman gadon,ko mayafinta bata tsaya ɗauka ba,ta watsa da gudu tabar ɗakin,A hankali taj ya lumshe idanuwanshi,yayin da hancinshi ke shaƙar mashi ƙamshin turaren Jikin aneelerh daya gauraye Jikinshi,bakomai Ya tuna ba face Matarshi data gudu tabarshi,maca ce mai matuƙar son ƙamshi,shima kuma  ma'abocinsa ne,baisan Ya akai ba Ya tsinci kanshi da tariyo yarda Aneelerh ta faɗo saman ƙirjinshi,da kuma yadda yalwataccen gashin kanta Ya zubo har a jikinshi,da kuma daddaɗan kamshin turarenta,


Ganin Zuciyarshi na ƙokarin Zayyana irin kyawun surarta ne yasa shi saurin Ambaton A uzu billahi minasshaiɗanirraji'um,Astagfurullah Ya Allah,


Mikewa Yayi zaune Duk kasala Ta rufe shi,saukowa yayi daga saman gadon ya fito palour,babu kowa Hakan ya tabbatar mashi da cewa Neelerh ta gudu,frigde ya buɗe ya dauko Swan Mai sanyi,Ya dawo bedroom dinshi,daga gefen gadon Ya zauna,buɗe murfin yayi ya tarfa ruwan a hannunshi Ya watsa ma angel asaman fuskarta,nan take Taja dogon numshi,Slowly ta buɗe idanuwanta akan fuskarshi,Suna hada ido ta fashe da matsanancin kuka,


Natsuwa yayi yana kallonta ko kusa baiji tausayin kukanta ba,tun da ya lura Ba sonshi take Yi ba,


Cikin shessheƙar kuka tace"You want to kill me because you don't love me,yanzu da na mutu Allah zai kamani,so kake in shiga wuta ko?tayi tambayar tana kallonshi,har lokacin idanuwanshi na akanta baice uffan ba,

  "Kana Jina ka share ni ko"


Gyaran murya ya ɗanyi can kasan makoshin shi ya furta"Dama kina tsoran Mutuwa"!

 A tsiwace tace"Eh mana,malaminmu ya karanta mana wani hadithi wanda ke magana akan mai munana ma iyayensa ba zai shiga aljanna ba,A wuta za'a babbakashi......"


Ƙiris Ya rage taj ya ɗan murmusa"So you know that but u keep hurting me ko"?


Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan,Ganin tasha Jinin jikinta sosai yasa shi kwantowa Yayi mata rumfa da faffadan kirjinshi,cikin sanyin murya ya soma magana Yayin da idanuwasu ke kallon Cikin na Juna,


"Angel,zan sanar dake wani abu da baki sani ba,Baki da wanda yafi ni aduniyar nan,baki ta6a tambayata mahaifiyarki ba,Bansani ba ko kina tunanin Namiji yana iya haihuwa ne,Shiyasa kike ganin kamar ni na haife ki,Baki da abun wulaƙantawa Irin mahaifinki,"shiru ya ɗanyi yana nazarin wani abu,ita kuwa ta kasa kunne tana sauraronshi,


Cigaba da magana yayi"Angel,mahaifiyarki a wulakance ta haife ki,Cikin bathtub tabarmin ke,Cikin Jini kinata kuka,Ni ina bacci,kukan ki ne Ya tashe ni,haka naje na sameki,Na ɗauke ki na rungumeki ajikina,duk da jinin dake ajikinki,Ni ban gudu nabarki ba,kuma ban bari kin wulakanta ba,Sai da na tsaya akanki angel da taimakon Allah har kika kai wannan lokacin,Tun da kike ƙuntatamun dai dai da na rana ɗaya ban ta6a Tunanin na tafi nabarki ba,kuma ban ta6a tunanin in sanya hannuna wurin ta6a lafiyar jikin ba,amma angel......"kasa ƙarasa maganar Yayi jin yadda ta rushe da kuka kamar ranta zai fita,ɗagowa Yayi zaune yana kallonta,


Hannu ta ɗaura akai tana faɗin"Wayyo Allah na nashiga Uku,Na bani Na lalace!"hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin yadda babynshi take Kuka,


Lallashinta ya soma ƙokarin"Am really sorry daughter,I don't mean to hurt u darling,Na faɗa maki ne don ki ɗauke ni da muhimmanci,don ki san cewa Ina sonki,kuma ina buƙatar tausayawa daga gare ki,"bata tsaya sauraronshi ba,Ta sauko daga saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe,


A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta,tura ƙopar yayi yaji tayi Locking dinta,


Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta"My angel am sorry,kada hakan Ya ta6a zuciyarki,kinsan ina sonki,banason zubar hawayenki"


Daga Cikin toilet ɗin yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faɗin"I hate my self daddy,cikin toilet aka haife ni,kuma ta gudu tabarni saboda bata sona......"

  Runtsewa idanuwanshi Yayi tare da ɗan Cizon lips ɗnshi Calmly ya kira sunanta"Angel,pls forget about it,Tunda kina da ni don me zaki damu kanki?Ni ne mom dinki kuma daddynki,

  Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar,yana ji aranshi cewa tana zaune agaban ƙopar,tsit yaji tadaina kukan

  "Pls say something to me,ko naji sanyi acikin zuciyata"

   Shiru bata tanka mashi ba,

  "Ki buɗa mun ƙopar"

 Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa"daddy inaso na mutu,kodan saboda nadaina 6ata maka rai"

  Cikin matsananciyar damuwa Yace"idan kika mutu angel,shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima,saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa,"


Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin,don Yaji daɗin Jin muryarta


 "I made a mistake daddy, I won't hurt you anymore,"Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya ɗan  dago da kanshi,Yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne,


"I love u daddy"ya kuma Jin ta furta mashi,aruɗe yace"Repeat it  pls"

  "I love u daddy"

"sake maimaita mun naji"fuskarshi ɗauke da murmushi Yayi maganar,

 Sake maimaitawa tayi kamar yarda Ya nuna yana son tayi mashi,


"I love U daddy,Bani da tamkarka aduniyar nan"

Wani irin ihu ya saki,Irin wanda Ƴan kwallo keyi idan sunci nasara akan wasansu,


A ƙagare Yace"Come out pls,inaso naji duminki a jikina"


Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar,kamar jira yake yi,tana ƙarasa budewa,Ya janyota Jikinshi yayi hugging ɗin very tight,hannunshi na acikin sumarta,Wani irin farin Cikine Ya lullu6eshi kamar wanda akayima Albishir da gidan Aljanna,'dole Taj yayi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana sonshi amtsayina mahaifinta,Yaji tausayinta sosai,bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau,data ji cewa mahaifiyarta ta gudu ta barta,Jikinta yayi sanyi,da yasan da haka da tuni ya faɗa mata,da duk wannan abun bai faru ba,daukarta Yayi asaman bayanshi,yakaita Cikin motarshi,atare da ita suka je masallaci,Ya barta acikin mota,Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant,komai takeso shiyasa aka kawo masu,sai da suka ci suka ƙoshi,sannan Suka dawo gida,A palour suka zauna saman Sofa,tana rungume ajikinshi,Suna kallon tashar Mbs 3,dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon,tafi sha'awar kallon Cartoon da kuma zombie,


Tuni bacci ya dauketa ajikinshi,asaman kafaɗarshi ya dauketa Ya nufi bedroom dinsu,don ya kwantar da ita,a hankali Ya tura kopar dakin Ya shige,A saman gado Ya kwantar da ita,Sai daya fara daukar wayarshi dake ajiye agaban mirror,Tukunna Ya haye saman gadon ya janyota ajikinshi,Yana shafa sumar kanta,cikin magagin bacci yaji tana fadin"I luv u daddy"murmushi ya dansaki,Tare da manna mata kiss agefen fuskarta

 "Luv u too My own daughter"


Number Uzair Ya kira,tana fara ringing Uzair ya dauka,

 "Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikinka"

  "Na hutasshe ka basai kazo ba,Jiki yayi sauƙi Alhamdulillah"

  "Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe ƴarka,Ae ni har na shirya zuwa ɗaukar rahoto"

  Fashewa Taj yayi da dariya"Ta 

6atamin raine,ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba,"

  "Yanzu Ina virus ɗin taka take"?acewar uzair,don tun ranar da ta Sa ƴan sanda sukayi masu shegen duka tun daga ranar Yake kiranta Virus,

Murmushi Taj yayi,tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel,Virus tayi bacci,Mutumina ka tayani farin Ciki,"

 Uzair yace"Meya faru"?

  Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakaninshi da angel ya sanar mashi,"

 Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi,

  "Ja'irar taji ƙamshin mutuwa,Allah yasa Karshen wahalarmu ce tazo,Amma fa nayi farin Ciki,


"Ameen mutumina"

Shiru suka ɗanyi,yana so ya tambayeshi aneelerh amma ya kasa,

 "Muyi video call mana"acewar uzair,

Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call,A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu,ya dan tada kanshi saman pillow,Jikinshi na sanye da kayan Bacci,

 "Show me her face"murmushi taj yayi tare da haska mashi fuskar angel,ta saki baki da hanci tana ta sharar bacci,

  Dariya uzair yayi"wayaga  mashasha,wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a,a haka zata zama surukarmu,"

 Fuskar Uzair ɗauke da murmushi yace"cin mutuncin ya isa haka aminina,kai kasani Wlh angel koda kuɗin mutun saida rabonshi,koda rabonshi sai in Allah ya nufa"

 Jinjina kai Uzair Yayi tare da dan yatsina fuska yace"Virus ɗin"?Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani,adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet,Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya,Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota,yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakinshi baya,wanda hakan yasa har Taj ya hango fitowarta,


Baisan ya akaiba Ya tsinci kanshi da satar kallonta,Yabar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daɗi,gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel,


"Me kake tunani ne"?a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair,muryarshi na inda inda yace"Bakomai,zan kwanta mutumina,Sae Allah yakaimu,"da sauri yayi rejecting kiran tunkafin ma uzair yayi mashi sallama,


Lumshe idanuwanshi yayi zuciyarshi a cunkushe,duk yadda yaso Ya hana kanshi tunanin abunda ya faru tsakaninshi da aneelerh abun ya faskara,daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba dashi,


Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba,koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakaninsu,mutu ka raba takalmin kaza,tabbas Angel taba kowa mamaki,irin yadda take son mahaifinta,tarairayarshi take yi,biyayya take yi mashi sau da ƙafa,Xaman Lafiya ya samu tsakanunsu,

Mu haɗu a Next Page,....................

_Paid Book ne,500 Amma Ba'a fara payment ba,Sai an kammala free tukunna👌_

_Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i wannan numbobin_

08103884440

08169856268.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post