Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 5 complete

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 5 complete

 

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 5 complete

https://chat.whatsapp.com/EcCtf5VAlpo8kdQCkDY4zh

*💋𝑇𝑎𝑘𝑢𝑛 𝐹𝑎𝑟𝑘𝑜💋*

قصة حب رومانسية سحرية💋💘💔

*𝐵𝑜𝑠𝑠 𝐵𝑎𝑡𝑢𝑟𝑒✍️*

                          _Dedicated to Aunty kubrah Allah yabar zumunci atsakaninmu_

*𝐸𝑝𝑖𝑠𝑜𝑑𝑒 5*

A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki,jikinshi sanye da jallabiya ash colour,da sauri ya nufi bedroom ɗinshi,Da sallama abakinshi ya shiga,tunkafin ya ƙarasa shiga ya sameta akwance tsakiyar gado tana ta sharar baccinta hada minshari,Agogo ya kalla shida ta kusa,ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin yayi a gefen gadon ya zauna,tare da ɗan juyawa yana kallonta,tayi ɗaiɗai asaman gadon,Kayan baccin daya sanya mata jiya sune ajikinta riga da wando blue sky,curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe,

a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancinta,yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba,

  "Wake up My lovely daughter"Cikin kunne yayi mata raɗa,

  Buɗe gray eyes ɗinta ta ɗanyi slowly tana kallon fuskarshi biji biji,

  "Nauyin bacci ko?Oya wake up,kada muyi late,ki tashi inyi maki wanka,in girka maki abinci,muci mu ƙoshi,kafin nasauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina


Jin tayi shiru batace komai ba,yasa shi fara Yi mata cakulkulo,lokaci guda ta 6a66ake da dariya,white teeth ɗinta kamar gonar auduga,saboda tsabar kyau,kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda haskensu,



Sosai ya sanyata nishaɗi,a ƙarshe Ya ɗauketa saman kafadarshi Ya nufi toilet da ita,almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayanshi,Ya ɗaura mata towel ajikinta,


A saman  mirror chair  ya zaunar da ita,Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin,Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu,runtse ido tayi tana dariya,Murmushi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura,zura hannunshi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da ita,Bayan Ya kammala ya kashe dryer din,ya mayar da ita inda ya ɗaukota,ya kuma ɗauke Comb,Ya shiga sharce mata gashin,Sai faman sakin murmushi take yi,A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi take ji ba,har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci?



ta cikin mirror taj ke kallonta,ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu take tunani,Man gashinta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata,Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta dake ajiye gaban mirror din,Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta,Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse,Yawan gashine da ita ga tsayi,don ayanzu gashinta yakai mid back ɗinta,sai da taj yayi dagaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi,


   "Daddy ni da kai wayafi kyau"tayi tambayar tana murmushi,

  Dungurin kanta yayi"Kinfi kowa sani ae"yayi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu,Hannu yasa ya buɗe murfin,Jerin kayan sawanshine da kayanta,Uniform ɗinta Ya ɗauko mata,riga fara sai mini skirt red colour,Abaya fara ƴar short,Yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta,ga wayau da Allah yayi mata uwa dila agari,


bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare,Ya zaunar da ita gefen gado"Am coming now"ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin,jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta,madara ce me sanyi Acikin roba,tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips,

    Ajiye mata yayi a gefen gadon,Shaf shaf Ya shige toilet Yayi wanka,Ya fito sanye da short,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,.  

  Harara ya ɗan jefa mata"Zansa kaya"

 ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi,tamkar bata ji me yace ba,

  Gyaran murya yayi mata"Can't u hear me?Ki koma Falo inaso zan shirya".

 Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace"Amma ae ni har wanka kake yi mun,kuma kana ganina ba kaya,Amma ni kullum saika kore ni in zaka sanya kaya'


Tashin Sense,zaro ido waje yayi yana kallonta Cike da mamaki,Ya ma rasa gane wai me take nufi,sai lokacin ya gane kuskuransa na rashin ɗaukar mai aikin da zata dinga kular mashi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin,


"Angel don't waste my time,Oya hold ur basket,ki jira ni a falo,"

Ganin ya ɗaure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket ɗinta ta fuce falo,Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa,Bayan ya kammala shiryawa cikin suits, Ya fito daga ɗakin Ya nufe ta,Hannunta ya kama suka fito daga falon,


Baba maigadi ya samu,A harabar ajiye motocinshi,Yana goge mashi motar da zai fita da ita,


Tunkafin su ƙarasa baba maigadi keta faman washe ma angel baki,ita kuwa ta tsuke fuska,Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san tayi kyau,Daƙyar take ma mutane magana,


Suna ƙarasowa bakin motar,Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa,kafin Ya kalli angel"Ƴan mata makaranta za'a tafi"?

Ɗaga mashi kai tayi alamar eh"

  "Allah ya bada sa'a Angelata"maƙe mashi kafaɗa tayi"Ni ta daddy ce"dariya sukayi gaba ɗayansu,


Taj yace"Bari mu wuce kada mu makara"baba maigadi yace"Allah ya tsare adawo lpy'ya amsa mashi kafin ya buɗe mata motar ta shiga ciki,ya zagaya ta left hand,ya buɗe ya zauna a driver seat,



A tsanake Yayi ma motar key,tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin,da sauri baba mai gadi Ya rigashi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin,Ya fuce daga gidan,


A hankali yake driving,Ta wutsiyar idonshi ya kalleta,Ta natsu ta kame kanta,

  "Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa"

  "Ba bacci nake ba,Ina tunani ne"

"Daddy wlh ni banaso mu rabu,dama kadinga tafiya dani wurin aikinku"

  Murmushi ya ɗan saki"Karatun naki fa"?yayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana,

   Shiru bata amsa mashi ba,

"Ni inaso kiyi karatu angel,sai da ilmi ita kanta rayuwa take yin kyau,ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane zasu yi alfahari dake"?


"Inaso"ta amshi amsa a takaice,

"To faɗamun me kikeso ki zama"?

Da buɗar bakinta sai cewa tayi"house wife"ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske tayi maganar,

  "Daddy why are u laughing?did i say something wrong"?

 Girgiza kai yayi"a'a,May be u did'nt understand my question,Ina nufin wani aiki kikeson Yi idan kika girma,a aikin gomnati?yayi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar,Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin,A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar,


  Fitowa yayi tare da zagayawa Ya buɗe mata motar"baki amsa mun tambayata ba"!?

   Ɗagowa tayi suka haɗa ido dashi 

 "Daddy my answer is the same,I wanna be a house wife"Sakin baki yayi galala yana kallonta,Ya rasa tayaya akai tafara tunanin zama house wife,dududu fa primary school take,

  Gudun kada ya makarar da ita,Yasa shi yin shiru bai ƙara tanka mata ba,Ɗauko mata food basket ɗinta yayi  kafin ya ruƙe hannunta suka nufi Cikin makarantar,kamar kullum har Cikin class ɗinsu Yakaita,English teacher ɗinsu ya samu Mrs favour,Cikin harshen turanci suka gaisa dashi,ya damƙa mata angel kafin Ya fito daga class ɗinsu Ya nufi motarshi,Zuciyarshi a cunkushe duk ya rasa sukuni,tunani ya shiga yi taya za'ae ya canza mata ra'ayinta na zama matar aure?don wannan ba ƙaramar matsala bace agareshi,ƴar ƙaramar yarinya tana tunanin zama matar aure,


Karasa shigewa Cikin motar yayi a tsanake Yayi mata key,Ya nufi gate ɗin makarantar maigadi ya buɗe mashi,Ya fuce,


Harya haura saman titi,Hankalinshi na akan Kalaman angel,shi da yake da burin ta zama babbar ma'aikaciyar gomnati,ashe ita sam Ba wannan bane agabanta,A karshe dai ya yanke shawarar idan ya tashi daga aiki ya ɗaukota suka koma gida,Zai zaunar da ita yayi mata karatun ta natsu,Ko ya samu ya canza mata ra'ayinta,



Wuraren ƙarfe biyu na rana,Ya tashi daga aiki,Sai daya fara zuwa masallaci Yayi sallah cikin jam'i,tukunna Ya nufi school ɗinsu,Lokacin daya karasa makarantar,tunkafin ya fito daga cikin motar,maigadi ya sanar dashi cewa Dr tazo ta dauketa,


Baƙaramin daɗi yaji ba,kaitsaye 6atare da 6ata lokaci ba,yaci gaba da da driving,har ya ƙarasa Gida,Tun abakin gate ya tambayi baba maigadi ko aneelerh ta kawo angel,Yace mashi a'a,,hakan na nufin tana agidansu,



Bayan ya ajiye motar Ya nufi Cikin gidan,Bedroom ɗin ya shiga,Shaf shaf Ya rage kayan Jikinshi Ya fada toilet don yayi wanka,ko yaji daɗin jikinshi,



Adai dai wannan Lokacin Aneelerh ta shigo Cikin gidan,ɗauke da angel,da alama tayi bacci,lokacin data shigo falo tana ta kwala sallama ba'a amsa mata ba,kawai sai ranta ya bata cewar kobai kaiga dawowa gidan bane,don bata lura da motarshi ba,hakan yasa ta nufi bedroom ɗinshi kaitsaye,tura ƙopar tayi kafin tasakai Cikin ɗakin,Asaman gadonshi ta kwantar da angel,short gown ce ajikinta,daga gani hada wanka aneelerh tayi mata ta kuma canza mata kayanta,ranƙwafawa ta danyi daga tsaye tana shafa sumar kanta,



Jin motsin ƙopa yasa Aneelerh tayi saurin ɗagowa tare da juyawa bayanta don taga wanene,ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Taj dake fitowa daga Cikin toilet,daga shi sai short 


Burki yaci lokacin da yayi arba da ita,duk tabi ta ruɗe,a gigice ta watsa da gudu zata fuce daga ɗakin,Unfortunately ta take rigarta dake jan ƙasa,gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa,Da hanzari Taj Yayi ƙwaƙƙwaran Taku Ya ruƙota,ta dawo jikinshi,tana faman sauke ajiyar zuciya,taji tsoran faɗuwa ƙasa don ba ƙaramin buguwa zatayi ba,


Sam ta manta Jikin wa take,ta ƙaƙameshi sosai,har sai da ya ɗanyi gyaran murya tukunna ta dawo hayyacinta,tayi saurin raba jikinta daga nashi,duk kunya ta rufe kowannansu,


Daƙyar ya iya buɗe baki yayi mata magana

  "Sai kace kin ga dodo,kawai daga gani na kin zabura zaki gudu,yanzu da kinji ciwo fa?so kike uzair Yasa a ɗaure ni ko"?

  Murmushi ta ɗan saki batare data ce uffan ba,idanuwanta na akan yatsun hannunta,

  "Thank u so much aneelerh,kina ɗawainiya da angel ɗina,tamkar mahaifiyarta,naso ace benazir tana da kyakkyawan hali irin naki sai dai kash ni ban yi sa'ar mata ba,"

  Juyawa ta ɗanyi jiki asanyaye ta soma tafiya tana tunkarar ƙopar ɗakin sai da takusa fita tukunna ta ɗan dakata da yin tafiyar,A tsanake ta soma magana,

  "Zan tayaka addu'a Allah ya baka mace ta gari wadda ta fini"tana kai ƙarshen maganarta,da sauri ta fuce daga ɗakin,


Murmushi taj ya ɗan saki,tare dakai hannu ya shafa sumar kanshi,juyawa yayi ya koma gaban mirror,lokaci guda kasala ta baibayeshi,kamshin turaren aneelerh ne,Ya cika mashi hancinshi,ita koda yaushe Cikin ƙamshi take,Zama yayi asaman chair din gaban mirror,Ya kura ido yana kallon fuskarshi ta cikin mirror,



A 6angaren aneelerh kuwa,Da sauri ta fuce daga Cikin gidan,Tana shiga falon gidanta,A saman sofa ta zauna tana faman mayar da nunfashi kamar wadda tasha gudu,tarasa dalilin dayasa a ƴan kwanakin nan take jin faduwar gaba aduk lokacin data ci karo da taj,


A tsanake Ya kammala Shirya kanshi Cikin farar t shirt,tare da jeans,ya feshe jikinsa da turare mai kamshi,


Yasan aneelerh bazata bar angel da yunwa ba,Shiyasa ma baiyi tunanin shiga kitchen ba,


Wayarshi ce ta soma ringing,da sauri yakai hannu ya dauke ta daga saman drawer,


  Kallon screen ɗin wayar yayi sunan Aminina ne ya bayyana akai,murmushi ya ɗansaki tare da picking call ɗin ya manna wayar a kunnanshi"Assalamu alaikum,ɗan uwana rabin raina"

  On the other hand Uzair yace"Ka koma gida lafiya"?

 "Lafiyalou,Yanzu na fito daga wanka ma"

 "Ka ci abinci"?

 Dariya taj yayi sosai,jin irin tambayoyin da yake yi mashi sai kace wani ƙaramin yaro,

  "Meyasa kake mun dariya?yau nafara tambayarka hakan"?

 Tamkar yana agabanshi Ya girgiza kanshi"Nop,just naji abun wani irine,kana tunamun rayuwarmu agidan Uncle"

    Muryarshi yajiyo da sautin murmushi"Unforgettable momeries,Allah Yabar ƙauna aminina,Zan shiga stadio Sai mun haɗe anjima"


  Taj yace"Okey,take care of ur self for me pls"

  Uzair yace"U too," fuskarshi ɗauke da murmushi yayi rejecting call ɗin,


Yana ajiya wayar saman drawer,Yajiyo muryar baba maigadi daga Can cikin falo,Yana kwala sallama,


A hanzarce Ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin,Yayin da yake amsa mashi sallamar"Wa'alaikum Salam"


Cikin falon Ya nufa,A bakin entry ɗin ya same shi a tsaye,Karasawa Yayi yana kallonshi,

  "Barka yalla6ai"ya amsa mashi da "yawwa barka"

 "Dama baƙone kayi"

Da ɗan mamaki akan fuskar taj yace"baƙo kuma"?yayi tambayar ne don shi a iya saninshi,basuyi da kowa  zaizo gidansa ba,


 "yalla6ai,Wannan malamin ne daya ta6a zuwa yima angel ruƙiya?'cike da son fahimtar dashi baba maigadi yayi maganar,

  "Kana nufin maisalati"?

Da sauri baba mai gadi yace"kwarai kuwa shine"?

  "Okey,Kace mashi ya shigo"

 "To yalla6ai,"Yakai karshen maganar tare da juyawa yabar falon,


Tajo na atsaye Yana jiran ƙarasowar malamin Yaji sallamarshi,Fuskar nan dauke da murmushi,Jikinshi na sanye da jallabiya wadda tsayinta bai kai ƙabrin kafarshi ba,Hannunshi na ruke da cazbaha,Kanshi yasha uban rawani,Wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,


Sakar mashi fuska taj yayi tare da miƙa mashi hannu cikin girmamawa suka soma gaisawa

  "Allah ya gafarta malam,barka da rana,Ya iyali,ya jama'a ya kokari,Allah yataimaka,Allah Ya kara ɗaukaka"

 "Ameen ameen tajo,Fatan na sameka lafiya,Ya aiki,ya kuma ɗiyarmu"


Taj yace"Alhamdulillah,Duk muna lafiya Mu shiga daga Ciki,"ya ruƙo hannunshi,suka nufi sofa ɗin falon,maisalati ya zauna asaman 2 seater,Sae faman sakin murmushi yake yi,Dama shi haka yake kullum fuskar nan awashe,Da wuya kaga bakinshi a ƙulle,


"Bari na kawo maka ruwa"da sauri Malam maisalati ya dakatar dashi"samu wuri  ka zauna tajo,Magana ce mai mahimmanci ce ta kawo ni,"


Tunda Taj yaji hakan,Sai ya zauna saman 1 seater ya tattara kwandon hankalinshi kan maisalati yana sauraronshi'


"Game da ƴarka injila"da sauri taj yace"Angel sunan yake"

  "Oh toh,eh ita ɗin dai"shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara yi mashi jawabi,

  Taj kuwa ya tsare shi da ido,Jikinshi har tsuma yake yi,don a ƙagare yake yaji me angel ɗin tayi,


Gyaran murya malam maisalati Yayi kafin ya soma magana atsanake,

  "ranar da aka kirani Inyi mata ruƙiya,nayi wani laifi,laifin kuwa shine,Bansanar dakai wani abu da nake hasashe akan yarinyarka ba,bama hasashe bane inada tabbaci kanshi,"

  Tunda taj yaji hakan,Gabanshi ya faɗi rass aruɗe yace"malam wani abu kenan"?

  Numfashi ya danja kafin yaci gaba da kora mashi jawabi tiryan tiryan

  "Akwai abunda nagani atattare da yar wurinka,A lokacin da nake yi mata ruƙiya,Sai dai tsoro da firgici ya hana in fada maka,abun gaskia yana da matuƙar daure kai saboda ba ƙaramar sarqaqiya bace a cikin lamarin kuma ni kaina nakasa tantance sihiri ne ajikinta ko kuwa saboda gaskiya abunda nagani ajikinta babbar al'amari,

  Tuni jikin taj ya soma kakarwa,muryarshi na kerma yace"Malam dan Allah kayi mun bayani,hankalina atashe Yake wlh"


Cigaba da magana malamin yayi"Kaitsaye bazan Iya ce maka ga abunda nagani atattare da ita ba,Amma ina da tabbacin akwai wani abu dake faruwa da ita a jikinta .......",


  Muryarshi na ɗan rawa yace"am..amma malam ni inaga kamar lafiyarta kalau,yanzu haka da nake maka magana mun samu sasanci atsakanina da ita,Tana sona ina sonta ba kamar lokacin baya ba"


Murmushi maisalati yayi dama yasan zaiyi wuya taj ya fahimce shi,jinjina kai yayi tare da cewa"Shin ka ta6a tunanin ka zauna da ita ka tambayeta game da abubuwan da take yi maka a baya gamon kanta ne ko kuwa?kuma bata ƴan gane gane haka"?


Shiru taj ya ɗanyi,Shi kadai yasan halin da zuciyarshi take aciki,duk da yana kokwanto akan kalaman malamin amma kuma yana tsoron Zancenshi ya zama gaskiya,"girgiza kai yayi alamar aah"gyara zama yayi to gaskia abinda ya kamata kayi kenan dan musan Mike faru ta hakane xamu samo bakin zaren"

  "Shikenan malam in sha Allah zan tambayeta,"

 

Maisalati yace"Yawwa ko kaifa,Sannan kuma shawarar da nakeso na baka,Ka tabbatar kana Yi mata addu'o'i akai akai,idan bata iyaba ka koya mata,hada azhkar na safe dana marece,ka kuma koya mata addu'ar shiga toilet,idan zata kwanta da dare kayi mata addu'oi'in neman tsari,kuma akodayaushe ta kasance kanta akwai ɗankwali,ka lullu6e mata gashin kanta,Hatta kaya idan zaka sanya mata kayi mata addu'o'a,Daso samune ma duk in zaka kwanta bacci ka kunna maku karatun al'qur'ani mai girma ku kwana dashi,"sosai malam maisalati ya bashi shawarwari a ƙarshe yace"Idan Allah yasa ƙarshen wahalarta kenan sai kaga Allah ya yaye mata,Amma dai ina ƙara gargaɗinka kada kayi sakaci wurin Yi mata addu'a akoda yaushe,na manta ma ban tambayeka ba,Tana zuwa islamiyya"?


Dakyar ya iya buɗe baki yace"Eh amma tajima bataje ba,


Girgiza kai maisalati yayi"Banso haka ba tajo,kanaso kayi mana buƙulin samun Hafizar al'qur'ani,wadda zata yiwa addini hidima nan gaba,kamar yadda nake fata,Allah ya baka yarinya mai wayo tubarkalla,ga hali kamar na manyan mutane,baikamata kayi wasa da wannan damarba,Gaskiya ina baka shawara ka hanzarta mayar da ita makaranta,idan da hali harma tahfeez ka sanyata,"


Ajiyar zuciya taj ya dan sauke"in sha Allah zanyi hakan,Nagode sosai malam,Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba,wurin gode maka,Allah ne kaɗai zai iya biyanka,Allah dai yasaka maku da alkhairi,"sosai taj yayi mashi godiya,Koda ya mike zai tafi saida taj ya ƙara tambayarshi ya kawo mashi ruwan sha,

  Yace a'a,Shidai burinshi yayi kokari wurin ceto rayuwar ƴarshi,Shi ma kuma zai taimaka mata da addu'o'i shida ɗalibansa,daga haka sukayi sallama dashi,Yabar gidan,


Tofa,Bayan tafiyar tafiyar maisalati,kasa zama taj yayi saboda rudanin da zuciyarshi ta shiga,Zarya ya shiga yi a falon,Zuciyarshi acunkushe take,wani irin faduwar gaba yake ji,tabbas yayi kuskure sosai akan angle wurin rashin maida hankali yayi bincike sosai lokacin da take cikin wannan halin"


A hanzarce Ya juya ya nufi bedroom ɗinshi,tunkafin Ya ƙarasa shiga Ya hango angel zaune saman gadon Ta jingina bayanta jikin headboard(kan gadon)

  

Ƙura mata ido yayi yana kallonta,ganin ta lumshe idanuwanta,tamkar mai tunanin wani abu,


Shiga cikin ɗakin yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna yana fuskantarta,


 "My daugher"da budar bakinta sai cewa tayi"Daddy,Malam mai dogon gemu yazo ya cika ka da surutu kamar radiyo mai jini"idanuwanta arufe tayi maganar,


Da mamaki akan fuskarshi yace"Taya akai kikasan yazo keda kike acikin ɗaki"?


Bude idanuwanta tayi a hankali,


"Tun dazu nafarka daddy,har leƙa ku nayi,"


"Kinji me muka tattauna dashi"girgiza kai tayi"ae ka hanani yi maka la6e,shiyasa ban tsaya ba,nadawo na zauna"


Ajiyar zuciya ya ɗan sauke,Kafin ya kuma cewa wani abu ta riga shi cewa"aunty aneelerh ce ta kawoni gida"?ɗaga mata kai yayi alamar eh,

 "ta kawomin uniform ɗina da kuma bag dina"?ta kuma jefa mashi tambaya,

  "A'a,zanje na kar6o maki su anjima"


Jinjina mashi kai kawai tayi,


Shiru sukayi na dan wani lokaci,kafin ya ruƙo hannunta cikin nashi,

"My daughter"!

Ware mashi manyan idanuwanta tayi"na'am daddy"


Murmushi ya ɗansaki,ya rasa ta ina zai taro zancen,kamar maijin tsoronta,


Can dai ya daure Ya soma yi mata magana atsanake"Nasan kina sona sosai,kuma kina kyautatamun,koba haka ba?


Da sauri tace"Hakane daddy"


Jinjina kai yayi"um..Yanzu kina sona,ba kamar lokacin baya ba da kika ɗauramun karan tsana tamkar ni ba daddynki bane,Pls inaso na tambayeki,a wannan lokacin ke kike ƙuntata mun da kanki ko kuwa akwai wani ɗan mutun mutumi dake sanyaki kina yi mun"?


Cikin rashin fahimta tace"daddy i don't understand me kake nufi"?


"Ina nufin,A time din da kike 6ata mun rai,Wake sanya ki kina yi mun,i know there must be a reason,babu yadda za'ae ki tsani mahaifinki lokaci ɗaya,"


Wurga eye balls ɗinta sama tayi tana kallon ceilling,ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana kallon ceilling ɗin yasa shima ya ɗaga kai yana kallon shi,wai ko zaiga abunda take gani,


Ganin bata da niyar daina kallon ceilling ɗin yasa shi dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Pls explain to me kinji babyna"


Mayar da idanuwanta kanshi tayi tadan turo baki irin na shagwa6a66u,


"Nidai bansani ba,Amma bani nake yi ba,kamar ana ce mun inyi kaza ni kuma sai inyi"takai ƙarshen maganar tana ƙyafƙyafta mashi ido,


"Magana akeyi maki acikin kanki ko kuwa"?ya kuma tambayarta,


"Daddy nifa bana ganewa,


"Angel kina mafarki"?ya kuma tambayarta,bubbuga hannuwanta tayi saman Mattress ɗin"Wlh daddy ni kayi disturbing dina,kana rikita ni"


Lallashinta ya shiga yi"Am sorry,wannan ce tambaya ta karshe,idan kika bani amsa,Zan baki wayata,kiyi game,"yasanta mayyar wayace,aikuwa da sauri ta soma kora mashi jawabi

  "Daddy,ko yanzu dana kwanta,nayi mafarki,kuma kullum ina yin mafarki,"


  "Fadamun meke faruwa acikin mafarkin"?a ƙagare yayi maganar,


Angel tace"Ina ganina a cikin wani ƙurmin daji mai duhun gaske mai ban tsoro,kuma idan nayi mafarkin ina ganina Acikin wasu mutane masu sanye da baƙaken kaya,Bana iya ganin fuskarsu,hannunsu zako zako da akaifa,Ni kuma Ina sanye Cikin jajayen kaya,riga da wando,kuma bani kadai bace hada wasu ƴan yara,Kuma suma red uniform ne ajikinsu,Daddy akwai tsorofa mafarkin,Kuma babu alkairi acikinsa"


Tunda ta soma magana zuciyar taj tashiga harbawa da ƙarfi da karfi,tamkar zata faso daga kirjinshi,


"Amma kinsan kina irin wannan bad dream ɗin shi ne baki  ta6a sanarmun ba"?


"Banaso na tayar maka da hankaline,Aunty aneelerh tace indinga faranta maka rai,kada na 6ata maka rai,Zaka Iya mutuwa ni kuma banso na rasa ka,sometimes ma in nayi yinqurin fada maka sai wani abu ya daukemin hankali na manta"fashewa tayi da matsanancin kuka,


Da sauri Ya janyota jikinshi sosai ya rungumeta,baisan lokacin da hawaye suka soma sauka akan fuskarshi ba,yana jin kukanta har cikin zuciyarsa


"In sha Allah zanyi iyakar bakin ƙokarina wurin ganin na ceci rayuwarki,Bi'iznillahi duk wani mai nufinki da sharri zai koma masa ne,Tabbas akwai wani maison shiga tsakanina dake,akwai wanda yake Yi mun maƙarƙashiya,Bansan wanene ba!!Amma Allah ya sani,Kuma zai bayyanarmun dashine,duk mun daren daɗewa,"!!!!!!!!!!!!!!!!!!


Yayi maganar ne don yasan Yana da maƙiya awurin aikinshi,masu yi mashi hassada saboda ɗaukakar daya samu,kuma har akan idonshi suna nuna mashi ƙiyayya,shiyasa yayi zargin kodai wanine keson ya 6ullo mashi ta bayan fage,shine akayi amfani da ita wurin cutar dashi,


Sun jima a wannan yanayin manne da juna shi da ita,sai da aka fara kire kirayen sallar la'asar,tukunna Ya ɗago da ita daga Jikinshi,Ganin ta fara bacci Ya dan jijjigata,firgit ta farka"time din sallah yayi daga yanzu bana so kina wasa da sallah,kinji ko'?


Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ya kuma cewa"Addu'ar shiga toilet kin iya"?ɗaga mashi kai tayi"Eh"yace to karantamun,nan ta shiga karanto mashi,ya kuma tambayarta addu'ar kafin a kwanta bacci da kuma in antashi daga bacci duk ta karanto mashi,Yace"masha Allah,haka nakeso My daughter,Sannan kuma zankoya maki azhkar da zaki dinga yi nasafe dana marece,pls ki bani haɗin kai,ki dage kinji indai bakyaso arabani dake"da sauri tace"zanyi daddy,"yace"that's good,yanzu tashi ki shiga toilet kiyi alwala ina jiranki"


Amsa mashi tayi"toh"da sauri ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin,harta kusa shiga ya dakatar da ita"wait"ta tsaya tare da waiwayowa tana kallonshi,saukowa daga saman gadon yayi ya nufi can cikin ɗakin wurin closet ɗinsu,buɗewa yayi tare da kai hannu ya ɗauko hijabi da mayafi"asaman gadon ya ajiye mata hijabin,shi kuma mayafin ya taka zuwa inda take ya ɗaura mata shi akanta,sosai ya lullu6e mata gashinta"yawwa daga yanzu haka nakeso gashin kanki ya kasance a lullu6e,sannan kuma idan kin kammala sallah,ki dinga karanta surorin da nake koya maki"amsa mashi tayi"toh"kafin ta bude toilet ɗin ta shige ciki,"


Tsayawa yayi har saida ta fito tukunna ya sanya mata hijabin,kafin ya wuce cikin toilet,lokacin daya fito salla ya sameta tana yi,baisan lokacin daya saki murmushi ba,yaji daɗi har acikin ranshi,



Dasauri ya fuce zuwa masallaci,a bakin gate suka ci karo da Uzair yana ƙoƙorin shigowa ciki,dama biyo mashi yayi donsu tafi masallaci atare,


Bayan tafiyarshi,Angel ta kammala sallah,ta zauna tana karanta surorin daya koya mata irinsu falaki da nasi,su tayi ta biyawa,duk don saboda yace tadinga yi indai bataso  arabasu,Tana cikin yin ƙira'ar,Wayarshi daya manta saman gadonsu ta soma ringing,


Zumbur ta miƙe takai hannu ta ɗauketa,Sunan Uncle ne Ya bayyana,Kafin ta ɗaga kiran ya katse,ganin wayar babu finger print din daya ke sanya mata,dama tun lokacin da suka shirya da ita ya cire security din wayarshi,Zama saman gadon tayi ta dinga buga game na spider man,


Sai da tayi mai isarta tukunna ta shiga contact dinshi,Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira,wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya,Har ya katse kiran,ta kuma haɗa wasu numbobin ba'a ɗaga ba,kusan number waya biyar ta kira mashi wasu ba'a ɗaga ba,Sai na ƙarshene aka ɗaga kiran,


Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana,shiru taji ba'ace mata uffan ba,kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karade kunnuwanta"who is on the line"?


Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace"Angel ce,"


Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta"kinsan dawa kike magana"?


Girgiza kai tayi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace"a'a,"


"Ur age"?ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinyace ƙarama,


"7yrs"voice ɗinshi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs?ina mai wayar yake'?


"Daddyna ne,ya tafi masallaci,ni kadaice agidan,shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"


"Can i call u video"?


Da sauri tace eh,


Nan take ya mayar da kiran Video call,ɗago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan tayi picking,Bata ga komai ba,a screen ɗin sai duhu sosai,Amma shi wanda  take wayar dashi da alama yana kallonta,


"I can't see u"tayi maganar tana faman gwale ido,


Shiru taji baya magana,saukowa tayi daga saman gadon,a tunaninta rashin network ne,yasa bata ganinshi a video din,Tana Cikin zagayen palour Tajiyo Sallamar daddynta,


A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers ɗin data kira,tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci,



Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna,


"Ban fada maka bane kawai,Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana dana da aljanu,zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta samesu tunda anan Benazir ta haifeta,kuma kaga shi toilet madaddalarsu ce,"acewar uzair, .


*Ni kuma nace mu haɗu a next page donjin Yadda zata kaya*

*Free pages ne,Game son Cigaban Story ɗin  zai biya 500 ne asanyashi A paid group,after an kammala na free,kada ku bari abaku Labari,Wani sabon salonne,Mai zaman kanshi,wanda baku ta6a ganin makamancinshi ba*

*Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i wannan number 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post