Raina kama 1-3 Complete Document

Raina kama 1-3 Complete Document

 

Raina kama 1-3 Complete Document

_Typing📲_*

  *_HASKE WRITERS ASSO...💡_*

       ♦RAINA KAMA......!!♦

               {Kaga gayya}

         *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._*

👉🏻1⃣

     *Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba.

   Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in “kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?”.

     gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, “ashema mu akanmu fitinar take yau?”. yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.

      “wlhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan dan kutu.....

    Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.

   Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.

    Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji.

    Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin duka....

     Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen.

Domin cigaba sauke raina kama ta hanyar danna download da ke kasa.

Download
Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post