Dubban magindanta, mata, maza da matasa ne suka amfana da tallafin kudi daga wata baiwar Allah mai kishin al’umma anan jihar kaduna.
Biyo bayan janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarraya tayi wanda hakan ya jefa al’ummar Nijeriya cikin wani mawuyacin halin kakanni kaye na yau da kullum, Wata baiwar Allah Hajiya Bilkisu Gidado wanda akafi sanin ta (Bilsoq) ta taimakawa al’umma da tallafi kudi domin rage masu radadin wanan yanayin.
A ranar talatan nan ne dai ta bada wanan taimakon akan titin Alkali road, da yankin anguwan Malali dake ne nan Kaduna domin ganin ta sanya farin ciki a zukatan alumma.
Haka zalika, ta dangana izuwa anguwan Kyauta dake yankin Millennium City, anan kuwa ta taimaka ma mazauna Wanan yankin da tallafin Shinkafa ga magidanta domin iyalai su amfana da Kuma Sanya su Farin ciki.
Ganin yada Wanan baiwar Allah ta Sanya al'umma daga anguwani dabam dabam an Wanan Rana, yasa bamuyi kasa a guiwa ba.
Koda muka zanta da Bilkisu Gidado, ta bayana cewa tayi wanan abun ne a matsayin ta na ‘Yar siyasa da take da kishin ta taimakawa al’umma a duk yanayin da ake aciki, inda tace wanan lokaci ne da al’umma ke cikin wani mawuyacin yanayi da zaka ga magidanci da kyar yake iya ciyar da gidan sa.
Bilsoq, ta kara da cewa mafi akasarin jama’a da zaka gani acikin wanan yanayin suna tafiya akan hanya ne wani ma ba tare da sanin inda zaije ba saboda irin wanan matsanancin yanayin da ake ciki.
Tayi kira ga ‘Yan Siyasa da masu hannu da shuni da su taimakawa al’umma a irin wanan lokacin da ake ciki domin yin walwala.
Malam Aminu Idris da Malama Zainab Othman, dukanin su sun nuna jin dadin su da wanan tallafin da wanan baiwar Allah ta basu a daidai lokacin da suke da bukatar hakan a rayuwar su.