Ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyun PDP, LP da NNPP, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, da Peter Obi sun fara tattaunawa kan yiwuwar hadewa da manufar kafa babbar jam’iyyar da za ta fi kalubalantar jam’iyyar (APC) mai mulki.
THISDAY ta rawaiti labarin wani taron wadannan shugabannin siyasa guda uku, wanda aka gudana tsakanin Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, da Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a (NNPP) a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Zaben Shugaban Kasa: Tinubu, Atiku, Obi Na Dakon Yanke Hukunci
Ganduje Ba Zai Hana Kwankwaso Shiga APC Ba
Tattaunawar wadda aka ce har yanzu tana kan matakin farko, ta ta’allaka ne kan ginshiƙai biyu. Na farko a cewar masu lura da al’amuran siyasa, shugabannin uku sun yanke shawarar jira da kallon sakamakon koke-koken zaben a gaban kotu, wanda zai tabbatar da sakamakon zaben. mataki na biyu na hukuncin, idan hukuncin kotun ya tafi kudu.
Misali, wasu majiyoyi da aka tattauna da su sun yi nuni da cewa shugabannin sun yi fatan cewa kotun zaben shugaban kasa za ta yi adalci don tabbatar da cewa zaben da ya kai Shugaba Bola Tinubu kan karagar mulki ba zabe ne mai inganci ba.
Shugabannin suna fatan cewa kotun za ta yi kira da a sake zaben wanda hakan zai sa su hadu a hadaka domi a zaben su kalubalanci Tinubu da APC a karo na biyu.
Sai dai idan kotun ta yanke hukunci akasin haka, an ce shugabannin na tunanin kafa wata babbar jam’iyya gabanin zaben 2027, inda suka shirya karbar ragamar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
Wata majiya ta ce, “Taron ya fara ne da Kwankwaso da Atiku kuma sun amince a kawo Peter Obi. Ko da yake ba su kai ga tattauna wanda zai jagoranci ‘yan adawar ba, amma sun bar ta har sai bayan shari’ar kotu.
“Bayan shari’ar kotuna, za su shirya su taru domin sake tsayawa takara ko kuma su tsaya a gaba a zaben 2027. Suna tunanin kafa wata babbar jam’iyyar adawa da ta hada da PDP, Labour da NNPP.”