Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 6

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 6

 

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 6

_*BAKON MUNAFIKI!!!*_

_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_

                _👺🏡👩‍👩‍👦‍👦

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

  _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

       __AREWABOOKS:MSSXOXO_

     _WATTPAD:MISSXOXO00_

            _PAID PAGE:06_

*KANDEM ESTATE*

   Babban gidah ne da ke dauke da jimillar yan uwa wanda suka hadu waje daya suka zama tsintsiya madaurin ki daya. 

Dukkanin wanda ke a birnin Nukaa ya san da ahalin zuri'ar kandem. Fulani ne na usul. Tarihi ya bayyana cewa tsatson ahalin zuri'ar kandem sune suka kafa garin Nukaa..

Domin a shekaru masu tarin shudewa ance ahalin nasu ne suka taho suka yanki jeji suka baza dabbobin su. Suke kuma sassake bishiyu suna yin itache dasu suna hada wuta suna zama abakin ta. Shanuwa suke tatsa suna sha shine abincin su....


Ance kakan kakan kakan su wato Ardo kandemi..... Bayan zuwan hausawa da basu iya fayyace sunan ba saboda harshen fulatanci ne a hausan ce sai suke cewa da shi 'Ado Kandem...' a haka kuma sunan ya zamo ya tumbatsa har ya zama cibiyar kasuwanci. Allah ya sanyawa yankin albarka ake ce da gurbin kasuwar kandem...


Bayan sun hayayyafa sun tara iyalai masu tarin yawa. Sai ya zamto sun mamaye ilahirin yankin da gaurayen sa. Sai ake kiran wajen yankin kandem...


Daga nan bayan samuwar yanci da zaman lafiya ya yawaita sai aka basu masarautar garin baki daya tunda su suka samar da yankin ake cewa da wajen garin kandem..

Daga nan bayan mulkin damokaradiyya sai ya zamto an yarje musu. Kasa ma ta san da birnin sosai. Ya zamto shine cibiyar kasuwanci ta kasar baki daya. 

Ardo kandemi wato kakan kakan kakannin usulin dangin ya zamto yana da matan sa na aure biyu. Akwai yafendo asalin sunan ta 'Nusaibatu.' Sai Yagwalgwal ita kuma usul din sunan ta 'Kausar'...

Alokacin da kasar ta samu yancin kanta ... A baya lokacin  mulkin sojoji kenan, Sai wanda yake a matsayin shine shugaban sojojin da ke mulkar kasar sai ya zamto ya sanyawa yankin kandem suna. Da farkon sunayen matan Ardo, wato Nusaibatu da Kausar... Ya yi masa laqabi da birnin 'NUKAA' 

Masarautar kuma sai ake cewa da ita masautar kandem... Wanda zuriyar Ardo kandemi ke karagar mulki suna mulkar garin...

   To a hakane cikin ikon Allah da buwayar sa da hikimar sa zuri'ar marigayi Ardo kandemi ta tumbatsa tayi reshe tayi ya'ya da jikoki da tattaba kunne da uhumhum masu tarin yawa da albarka ..

Har ya zuwa lokacin da Nigeria ta karbi yancin kai ta nada Lagos a matsayin babbar birnin ta ya zuwa sanda akalar komai ta koma birnin Abuja...

Zuri'ar Ardo kandem ta wuce duk inda ake tunani. Sun zama reshe da ko'ina yayi ya'ya. Duk wani bangaren alkalanci na kotu, likitanci, injiniiyoyi, frofesosi, masu aikin gidan jarida da na tv, gidajen rediyo, Yan siyasa, hakimai da sarakai da dakatai, Yan kasuwa , jakadun Nigeria dake sauran kasashe... Kai da duk ma wani babban mukami na gidah dana waje idan aka duba kashi chassa'in cikin dari zuri'ar Ardo kandem ne. Allah ya sanya musu tarin albarka da dimbin nasibi mai tarin alkhairai...

Wasun su na zama ne a kasashen waje, wasun su na wasu garuruwan, wasu na wadansu anguwoyin acikin garin Nukaa din wadanda aure ya sauya musu wajajen zama. Ma'ana mafi yawan matan dangin dake auro wasu mazan da ga wasu dangin... Duk kuwa da kashi tamanin na cikin dari auren zumunci suke yi. An taba samun sabani ne sau biyu akan wasu auren da aka hada na zumunta. Har abun ya fara kawo tangarda da son rabuwar zumuntar. Dakyar aka iya sasantawa aka kuma kawo karshen hadin auren zumuntar. Ya zama dik me son auren babu takura yaje waje ya auro... 

     ×××××

   Hancin motocin su Amb. Junaid ne da iyalan sa suka shiga dandatsetsen katafaren babban gidan na kandem estate. 

Babban gidah ne daya ci sunan a kira shi da 'aljannar duniya' komai yaji. Domin tsayawa ma a baku labarin yadda gidan ya kawaatu da komai na rayuwa tabbas bata lokaci ne. Sannan zuciya zata iya tantama akan hakan. 

Masu gadin suka tashi da sauri suka yo kan motocin da number jikin plates din motar ke rubuce da manyan bakin kandem 01 zuwa kandem 05...

Tsayawa motocin sukayi. Amb junaid ya bude kofar mazaunin da yake. Masu gadin da maaikatan gidan maza sukayi dafifi akan sa. Sanin shi mutum ne mai karamci da adalci, dattako ya kamata, da Kuma kyautatawa da jikin sa, gumin sa da kuma aljihun sa. 

Haka ya rika basu hannu suna musaba. Bakin sa abude yanata musu murmushi suma suna rissina masa cike da girmamawa. 

Sai da ya tabbatar ya gaysa da kowa acikin su sannan ya daga musu hannu . Suka rufe masa murfin motar direbobin suka ja motar zuwa ciki.

Kai tsaye motocin sukayi bangaren mahaifiyar sa... Wanda shima nasa gidajen a sashen suke. Gate ne kawai ya raba su. Nata yayi dama nasa ya kalli hagu. Amma da yar tazara a tsakani. 

Motocin suka danna kai cikin gate din. Suna karasa parking suka furfuto daga cikin motar . Shine agaba suna biye da shi a baya...

Ya doka sallama ya shiga cikin babban  parlorn. Dattijuwar hajiyar na zaune akan wata kujera samfurin Italy. Babban Qurani ne a hannun ta. Fuskar ta saqale da gilashin kara ganin ta.

"Hajjaju na.... Hajiya ta" ya fada da sauri cike da madaukakiyar murna marar misaltuwa

Ta dago ta kalle su tana amsa sallamae. Murmushi tayi faffada. Ta mayar da kanta kan quranin da take karantawa. Ka'dane sai ta kai aya take ajiyewa. Allah ya temaka tana karshen shafin tana karashewa kuwa ta daga hannun ta tana addua kamar ko da yaushe . Suma suka daddaga hannuwan.

Amb Junaid nata kada kai yana cewa,

"Aamin, Allah ya amsa... Allah ya amsa Hajiya... Amin Amin."

Karbar Qur'anin yayi ya ajiye a inda take ajiyewa. 

Tayi murmushi tana kallon su daya bayan daya,

"Allah yasa Qur'ani ya cecemu. Amin"

"Amin Hajiya"

"Aamin Amin"

"Allahumma Aamin hajia."

Suka shiga amsa adduar da tayi. Domin Hajiya Maryam akwai Ibada da yawon karanta alqurani. Tunda kananuna shekarun ta har girman ta. Shi yasa Allah ya amince duk tsufan ta ganinta bai tafi ba. Tana iya karanta komai idan rubutu yayi karanchi ne take karawa da temakwan gilashin karatu na kara girman ganin rubutu.

"Hajjaju barka da Rana... Mun same ku lafiya? Ya jiki hikin na ki? Fatan komai da komai kalau Hajiya? Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa yasa kifi ha ka, Amin...."

"Amin junaidu, Allah ya maka albarka, Allah ya maka albarka, Allah ya maka albarka junaidu."

"Amin Hajiya Amin."

Ya matsa daf da ita. Hawayen dadi daya nabin daya a fuskar sa. Duk girman sa idan yana gaban hajiyar su ganin sa yake dan karami. 

"Allah ya albarkaci zuriyar ka junaidu. Allah ya albarkaci dukiyar ka junaidu, Allah ya albarkaci komai na ka junaidu. Allah Amin."

"Aamin Hajiya... Aamin."

Nan da nan daya bayan daya suka rika tasowa suna gaishe da Hajiya tanata amsa musu. Amb Junaid yaki matsawa daga gaban ta sai ma sake gyara zama da yayi sosai yana jin sa cikin wani irin nishadi marar misaltuwa 

Amaal ce karshen tasowa ta nufi wajen hajiyan tana murmushi. Hajiya Maryam ta bude baki tana murmushi.

"Ahh takwara ta ce? Zo nan yar albarka..." Ta janyota jikin ta tana shafa kanta,

"Hajiya ya kafar ta ki?" Ta tanbayeta tana mammatsa mata su 

"Da sauki maryama. Nagode kinji? Je ki huta Allah yayi albarka Amin."

"Bangaji ba Hajiya."

"To ai shikenan idan sarkin agaji yazo ka kyale."

Suka saki dariya baki daya idan aka tsame hadiza da iyalan ta da kuma ruwaida da nata yaran da ke ta kumbura zasu fashe...

Wayar sache tayi kara. Ya janyota da sauri ya shiga wajen sakonni. Dubada ko da yaushe sai an ajiye masa saqo kala kala ta kafafai da dama na social media da ma text message ta ainihin number sa. 

Amma duk da tarin lokutan da aka diba bai taba ko sai daya ba zuwa dan a bincika masa mai bibiyar tasa ba, Ya dai barwa kansa sanin koma wanene, BAKON MUNAFIKI!! ne wanda (BANA MUTUM DAYA BANE) 

Dubada yan uwa da dama sun juya masa baya ciki harda wadanda suka fito ciki daya wato uwa daya uba daya ..Ya Kuma tabbatar wa kansa BAKON MUNAFIKIn ne ke qissima komai. Amman koma wanene ko ma wacece da sannu gaskiya zata bayyana.. Domin komai nisan dare gari zai waye. Allah zai bayyana mai gaskia .

Sakon ma dariya ya bashi alokacin daya kai karshen karantawar. Ya sake karantawa daga farko yana girgiza kai kawai cike da rashin bacin rai,

"Ban hane ka da kada ka waiwayo zuriyar kandem ba? Ba ka ji ba sai da ka dawo gidah ko? To ka sani cewa ka debo ruwan dafa kan ka.... Ka jira ka ga abubuwan da zasu biyo baya....."

Kashe wayar yayi baki daya ya zurata a aljihu. Ya saka hannun sa duka biyun ya janyo kafar mahaifiyar sa daya ya dora akan cinyar sa. Ya yinda amaal ke matsa mata daya kafar.

Heat Balm din da ke hannun sa ya bude ya lakuta ya shafe kafar hajiyan da ita ya shiga matsa mata ahankali. Yana ta mata hira..

  Tuni maaikatan suka shiga kawo musu abinci da sauran abubuwan sha dana motsa baki. Suka cikata gaban su da shi....

Kowanne ya shjga diba yana ci yana korawa da lemo da ruwa mai sanyi... Yayin da maaikatan ke ta kai kawo akan su sunata hidima akan su......

  _Afuwan abisa rashin ganin cigaban paid pages na littafai biyu daga cikin ZAFAFA BIYAR. Hakan ya faru ne sanadiyar rashin lafiya da ta riske mu. Muna baku hakuri dan Allah. In shaa Allahu da mun karasa samun sauki zaku ji mu duka da yardar Allah.... Mungode da zabin litattafan zafafa biyar. Allah ya kara budi_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post